Showing 228001 words to 231000 words out of 429394 words

Chapter 77 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

934

idonsa yake gani, "kan bala'i" ya fada a fili kafin ya watsar da takaddun ya juya da sauri ya shiga hada matakala biyu biyu saboda sauri.

Kamar iska haka ya nufi dakin da take, Ruqayya data ga yanda ya sakko ta miqe kanta a qasa tana cewa
"Yallabai Uwar dakina tace zatayi bacci kar a tashe ta"
"Get lost my friend" ya fada cikin tsawa jijiyoyin kansa har tashi sukayi saboda bacin rai nan ya shiga dukan qofar dakin da take cikin saboda ya murda yajita a kulle, Umaimah dake kwance akan gado lamo dan ba bacci takeyi ba tunanin yanda zasu kwasheta da Khalil take. Ba tayi nadamar kiran Dr Sabitu ba illah na goge masa Laptop shi ya dameta. Data sani bata taba ba danta tabbatar ita zagin datayiwa Baban Zahra ya isa ya hana shi auranya kuma kwace kwangilar.

Yanda yake dukan qofar kamar ze ballata ya bata tsoro, wayar Hajiya ta shiga kira tana dagawa ta saka mata kuka tana cewa
"Hajiya kizo Khalil ne" bata jira amsarta ba ta kashe wayar ta wullata kan gado ta shiga yarfe hannu cike da tsoro.

Khalil kuwa wayarsa da ake kira ya sakashi dakatawa da bugun qofar,bema san waye ya kira ba ya daga muryar Dr Sabitu ta daki kunnensa cikin tsananin bacin rai yace
"Ka tabbata kafin qarfe sha biyun rana ka kawomun da duk wasu takaddu da suka shafi kwangilar nan idan ba haka seka fuskanci wulaqancin Khalil, badai ni ka bawa Matarka waya ta zageni ba zaka san cewar ba'a wasa da Dr Sabitu Bashir" yana gama fadar haka ya kashe kiran.

"Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un" ya fada yana dafe kansa, Umaimah ta saka shi a Bala'i ta janyo masa masofa yana zaman zaman wai shi wace irin mata ya aura se kace dangin shaidan. Saman ya koma da sauri ya zazzage jakar ko Allah zero saka ya samu takaddar Da Dr yake da buqata amma babu komai ciki se flash drive daya fado, gefen gadon ya samu ya zauna yana dafe da kansa, yanzu ya zeyi da rayuwarsa? Takaddun kwangilar ta yaga ta jiqasu me ze koma ya gayawa Dr Sabitu bayan bashida masaniyar irin dibar Albarkar da tayi masa a waya?

Laptop din ya janyo gabansa ya fadi ganinta a bude bayan yasan ya rufe daze tafi karbo mata danwaken, kai tsaye folder ya nufi budewa ganin babu ita babu alamarta yasa ya shiga Recycle Bin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin yanda zuciya take yunquro masa kamar zeyi amanta. Wallahi yau me raba shi da Umaimah se Allah daya hadasu, duk iskancin da take yi masa yake shanyewa yau ta kaishi bango tunda ta taba masa bangaren aiki seta gane bata da wayo.
Kamar wani mahaukacin zaki haka ya sakko daga Saman, Anty Laure ta rafko sallama ta shigo palour suka hada ido da Khalil take tayi baya tana dafe qirji dan harga Allah yanda idonsa ya canza kala badan kamannin fuskarsa ba cewa zatayi Gamo tayi.

Qarar faduwar qofa dataji ce ta dawo da ita daga hayyacinta ta dora hannu biyu aka tana kiran
"Na shiga uku ni Laure me yake faruwa a gidan nan a cikin Daki kuwa Hajiya da shigowarta kenan Umaimah ta bude mata bayan ta tabbatar Khalil baya qasan yana balla qofar a tare suka fasa ihu saboda razana da ganin yanayinsa.



*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 54

Gadan gadan ya nufi Umaimah dake take jin tamkar numfashi ta ze dauke saboda Azabar tsoron yanayin data ga Khalil din a ciki, Hajiya da ita kanta jikinta rawa yake ta shiga tsakiyarsu, cikin muryar da bata taba jinsa da ita ba yace
"Hajiya ki matsa, ki matsa karkisa nayi Abinda Allah zeyi fushi dani"

"Khalil saurara tsaya Khalil ka tsaya nace maka" Hajiya ta fada a rude tana tokare qirjinsa da hannayenta ganin yana neman zagayeta ya isa ga Umaimah data durqushe a jikin bango tana jiran jin sauakar Aradu
"Wallahi Hajiya sena illata yarinyar nan yau sena illata Umaimah" ya fada cikin qaraji kafin Hajiya ta ce wani abu ya isa gaban Umaimah cikin qasa da second biyu ya dagota tsaye da hannu daya kafin ya sharara mata mari da daya hannun ya shaqe mata wuya duk a lokaci daya.

Kuka Hajiya ta fashe dashi ta shiga qoqarin kwatarta amma ina Ran Maza ya baci jikinsa rawa yake kamar Mazari ya zurawa Umaiman idanunsa da suka koma Ja yana kallon yanda nata idon suka firfito tana kokawa da Numfashi.
"Laure ze kashe ta kira su Sammani" Hajiya ta fada cikin kuka sanda Anty laure ta shigo dakin ta kuwa kwasa da gudu tayi waje tana kururuwar azo a taimakawa Umaiman.

Khalil kuwa seda yaji jijiyar wuyan Umaimah daya matse ta dena bugawa kafin ya saketa kamar kayan wanki a qasa ya juya a zuciye ya bar dakin. A palour ya tsaya daidai sanda yan agajin da Anty Laure ta kwaso suka shigo ya watsa musu wani kallo daya sa babu shiri suka juya kamar muna fukai suka bar gurin se ya juya yabi bayansu dan be gamsu da abinda yayi mata ba idan yaci gaba da zama a gidan tabbas ze koma ya qarasata.

Tsakanin Hajiya da Anty Laure rasa me rarrashin wani akayi sanda suka kai Umaimah data Suma Asibiti. Hankalinsu be dan kwanta ba seda Likita ya tabbatar musu da tana lafiya sunyi mata Allura dan ta danyi bacci ta samu sauqin firgicin da ta shiga. Se a sannan Anty Laure ta iya kiran Mama tana kuka tace
"Malika ashe mahaukaci kuka aurawa Umaimah? To ki taho idan kinada rabo ku gana da yarki dan ya dandana mata qamshin mutuwa gamu a Asibiti babu tabbacin ta mutu ko tana raye".

MAMA
Salati ta saka tana kallon Abba dake shan shayi jin salatinta ya sakashi kallonta shima.
"Laure ce, ban fahimci abinda take fada ba tadai ce muzo Asibiti Umaimah bata da lafiya" Maman tayi qarfin halin gaya masa se Abban ya miqe yana cewa
"Subhanallahi jikin ne ya tashi? Muje to daman na gama se mu ganota".

Seda suka shiga mota sannan ta lura da dan mayafin Abaya ne ta yafa akanta daman doguwar riga ta saka budaddiya, bata da nutsuwar da zata koma sako Hijabi haka suka tafi Abban na cewa
"Ikon Allah wannan cikin dai ya zowa Umaimah da sammatsi Allah ya rabasu lafiya"
Mama dai bata iya cewa komai ba dan tunaninta gaba daya yana can, Allah Allah takeyi su isa taga Umaiman da Laure tace tazo idan suna da rabon ganawa wane mugun abu Khalil yayi mata har haka?

Sun isa Asibitin a Reception suka tarar da Hajiya da Anty Laure kowa da inda take kallo dan bala'in haushin Hajiyar Laure takeji shiyasa tunda ta gama wayarta ta juya mata qeya tana sharar hawayen tausayin Umaiman. Tana ganin su Mama ta miqe da sauri tana sake rushewa da kuka gaban Mama ya fadi data kalli fuskokinsu, shi kansa Abban hankalin sa tashi yayi nan take suka qarasa cikin kuka Anty Laure take cewa
"Shaqeta yayi, haka muka kawota bata numfashi. Daman tunda muka koma nake lura dashi sam basa jituwa da alama wancan ciwon ma dukanta yayi shine yanzu kuma yake neman daukar ranta"

"Subhanallahi wace irin magana ce haka kikeyi Laure? Yanzu dai ina likitan naji abinda ake ciki Hajiya kiyi haquri ki dena kuka haka" Abba ya fada yana kallon Hajiya dake sharbar Hawaye har sannan jikin baiwar Allah be dena bari ba saboda yanda ta tsorata da yanayin Khalil. Gurin likitan Abba ya wuce, kamar yanda ya gayawa su Hajiya haka ya sake maimaita masa cewar babu wata matsala bacci kawai takeyi data farka komai ze daidaita. A Asibitin ya bar Mama ya wuce kasuwa haka suka zauna su ukun babu me cewa wani qala se Anty Laure ce take ta maimaita Khalil mahaukaci ne kuma idan wani abu ya samu Umaimah se sunyi qararsa.

Guraren La'asar Umaimah ta farka a firgice, Nurse ta shiga cire mata ruwan daya qare ta farka yanda taga tana zare ido ya sakata kama hannunta tana cewa
"Is ok you are in a safe hand". Umaimah ta qarewa inda take kallo ta sake maida kallonta kan Nurse din kafin a hankali cikin muryarta data dashe saboda Azabat shaqa tace
"Khalil, is he here?"
Nurse din ta girgiza mata kai alamar Aa kafin tace
"But your Mum and Aunties are outside, let me call them for you" ta dafa kafadarta cikin son kwantar mata da hankali kafin ta juya ta fita. A tare su ukun suka shiga, Umaimah na ganin Mama ta fashe da kuka Maman kanta zaro ido tayi ganin yanda gefen fuskarta ya kumbure idon ya shige ciki ga wuyanta nan inda ya shaqeta shima yayi baqi.

"Na shiga uku Hajiya me Khalil yayiwa yarinyar nan?" maman ta fada tana qarasawa kusada Umaiman, tana zuwa kuwa ta riqeta tareda qarawa kukanta qarfi tace
"Mama ki tafi dani wallahi kasheni Khalil zeyi idan na koma" ta sake fashewa da wani kuka tana tuna qanshin mutuwar dataji. Shaqar daya mata tasa sam bata ji zafin marin ba har yanzu maqogaronta a cushe yake wani mugun tsoronsa ya darsu a ranta dan ko a mafarki bata taba zaton Khalil ze aikata mata haka ba.

Rarrashinta Mama ta shigayi Hajiya da gaba daya jikinta yayi sanyi tace zataje gida ta dawo. Tana fita Anty Laure ta kalli mama tace
"Kingani ko Malika, duk lokacin da aka debo rigima se a dorawa yarinyar nan laifi gashi yanzu a gaban ido na na gani ashe cutar ta yakeyi yanzu wannan shaqar da yayi mata yau da da qarar kwana ai mu ze bari da Jimami shi bashi da asara ga mata nan birjik yana kulawa kullum da wacce zakiji shi suna waya yana qyalqyala dariya se ya shigo gurinmu ya ringa daure fuska ai wallahi ya bani mamaki".

Daga Maman Har Umaimah ido suka zuba mata, qirjij Umaimah ya shiga lugude wato ba Zahra kadai yake kulawa ba she sunada yawa? Ta tambayi kanta Mama kuwa duk ta rasa inda zata ajiye maganganu su. Ita dai tasan sedai idan Khalil shaye shaye ya fara shine kawai zeyiwa Umaimah irin wannan abun in kuwa ba haka ba toh wani mugun abun tayi masa da har ta kaishi bango wanda kadan ne daga aikinta, ita ta haifi abarta ta kusan me zatayi. Numfashi taja ta kalli Umaiman tace
"Ke me kikayi masa da har ya shaqe ki?"
"Me kuwa zatayi masa? Bafa ya nan ya tafi Zamfara yau kwana uku, ni na fita da safen naj dubo Inna ai na gaya miki shigowar da zanyi na ganshi ya sakko daga sama kamar wanda Aljanu suka koro. Ze jin kururuwar uwar sa nayi tana a kawo musu dauki da alama daman ya zaba ita take zuwa ceto ko shiyasa yau din tun kafin ya fara ta shigo" Anty Laure ta ceci Umaimah dake zare ido dan bata san me zata cewa Maman ba Kallonta Maman tayi take ta karanto zallar rashin gaskiya ko daga yanda take sunkuyar dakai kasan da wata a qasa dan haka bata qara magana ba taja bakinta tayi shiru.

Sallamar Anty ce ta katse mata shirun suka shigo tareda Salman daya ruqo kwandon Abinci, cikin jimami ta qarasa gadon tana kallon Umaiamah. Suka gaisa da Anty Laure shigowarta baby dadewa sega Nurse tace su fito likita ze dubata suka fita gaba daya Anty Laure na mayar mata da yanda akayi.

Bayan Dr ya gama dubata ya rubuta magunguna tareda Sallama ya basu. Salman ne yaje Pharmacy ya karbo ya tambayesu kudin sukace yaje kawai an saka a bill ya karbo ya dawo suka tattara suka wuce gidansu suna Hanya Hajiya ta kira Mama akan ta dawo Asibiti ance an basu sallama tace mata eh sun wuce gida. Jiki a sanyaye Hajiya tayi mata fatan samun sauqi suka kashe wayar, Anty Laure ta mere baki tace
"Da so take a mayar musu da ita su qarasa kashe mana ita ko to baze yuwu ba auren babu dole se a haqura, daman an fada ai yawancin matan da suke a qaton gidan nan in ka tona zaman da suke se kasha Mamaki amma dai yaron nan ya shammaceni yanda nake masa kallon mutumin arziqi ban zaymta haka yake ba".

Babu Wanda ya tankata har suka isa. A dakin Mama Umaimah ta kwanta bayan tayi wanka tasha kunu dan ta kasa hadiyar Abinci, maganin ma dakyar ta iya sha daga nan bacci yayi awon gaba da ita.

KHALIL
Rasa inda ze nufa yayi bayan daya bar gidan ga Dr Sabitu dake ta faman antayo masa kira a waya shi har mamakin yanda yake abu kamar wani qaramin yaro yakeyi. Daman yayi blocking number Zahra, yana ga Mahaifinta ya sanar mata da halin da ake ciki ne data fara kiransa babu qaqqautawa take ya jefa lambar a blacklist.

Shi tun farko ma meya aike shi ya yarda da wannan abunne gashi nan yanzu babu biyan buqata se damuwa da ya jefa kansa duk Anwar ne yaja masa da baqin nacinsa babu yanda beyi akan su haqura ba ya kafe yace su gwada ai gashi nan yanzu basu samu ba kuma sun janyo matsalar da zata iya shafar company su gaba daya.
"Umaimah, Umaimah, ya fada a fili zuciyarsa na tafasa.
Ya yarda Umaimah bata da hankali, tsantsar raina shi da tayi ne kuma tana taking nasa for granted shi yasa har tayi masa hakan tunda ta saba sha idan tayi masa abu ya qyaleta to an gama, baze sake daukar iskancinta ko misqala zarratin ba tunda bata san Annabi ya faku ba toh dole ya saita mata tunani.
Kiran Hajiyarsa ne ya sakashi komawa gida saboda yanda ta bashi umarni duk inda yake yazo tana neman sa.

Dafe kuncinsa yayi yana kallon Hajiya data sharara masa mari abinda ko zamanin yarinta da wayonsa baze tuna sanda ta mare shin ba se yau a shekarunsa kusan Arba'in Hajiyar ta mareshi a tsakar gida gaban ma'aikatan gidansa duk saboda Umaimah. Hadiye wani qululu daya taso masa yayi dakyar Hajiya dake huci kamar ta hadiyi wuta ta ce
"Kana kallona ko nima zaka shaqe nin ne kamar yanda ka kusa hallaka yar mutane iye? Anya Khalil kanka daya kuwa baka fara kora abinda yake gusar maka da hankali ba?" Ta sake fada cikin tsananin fushi.

Kallon su Sammani da sukayi cirko cirko suna nadar gulma yayi kafin kace me sun fashe daga gurin ya juya dakyar ya iya bude baki yace
"Hajiya mu shiga ciki kiga abinda tayi mun"
"Me tayi maka? Har akwai abinda yafi ranta da lafiyarta ne a gurinka" Hajiyan ta fada se ya miqe daga tsugunnan da yayi a gabanta ya shige bangarensu dan a compound ya tarar da ita ta sharara masa Welcome Marin. Bin bayansa Hajiya tayi tana cewa
"Tabbas wuyanka yayi Kauri Khalil wato harni zan maka magana ka tafi ka barni a tsaye saboda ka isa ko?

Shidai be tanka ba kai tsaye ya haye sam, roba ya samu ya zubo takaddun a ciki dan daya taba suke narkewa ya dawo palour inda Hajiya take bambami kamar ta ari baki ya ajiye mata yana kallonta yace
"Takaddun kwangilar da kullum nake ce miki kiyi mana Addu'a ta jiqa, ta kuma goge na cikin laptop dita sannan ta kira wanda ya bamu aikin tayi masa zagi na rashin mutunchi" ya fada dakyar saboda zafin da zuciyarsa take masa.

Tsam Hajiya tayi tana kallon takaddun, kwangilar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login