Showing 396001 words to 399000 words out of 429394 words

Chapter 133 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

976

tare ya tsare har seda ta gama komai ya maida ita gida kafin ya wuce office, seda suka jera sati biyu yana kaita kullum sukaje kuma se yaga Noor din amma baya taba bari su hadu da Humairan.

Haka kawai ta tashi da rigima a cewarsa kenan wai bata jin dadi ita Asibiti zataje, takaici ya qumeshi, daman kwana sukayi suna rikicinta da bashida qarshe yanzu da cikin ya tsufa lamarin ta qara tabarbarewa yakeyi kullum cikin nemansa da magana take tana sane tun dare ya gaya mata zeje Katsina duba wani aiki amma safiya nayi ta shiga riqe qafa wai ciwo take mata bata iya tafiya dole yace ta shirya su tafi Asibitin. Har sun fito ze kaita Jamila ta kirashi Danta ya fado daga Bene kansa ya fashe gashi babu kowa a gidan Babansu baya nan ita kuma bata iya mota ba daman ta roqeshi akan ya tura mata Khalifa idan yana gida ta kira bata same shi ba.. Khalifan baya gari yana Dutse inda yake aiki a CBN dinsu dole ya bar Humairan ta tafi da Driver shi kuma ya wuce gidan Jamilan ya daukesu ita da yaron da yake ta kuka saboda yanda yaji jiki, seda sukaje Asibiti aka fada musu bayan fashewar kan ya samu karaya a Hannunsa na hagu da Targade a yatsun qafa.

Suna Asibitin amma hankalinsa yana kan Humaira, ya kira wayarta ta ringa qara bata dauka ba ya sake kira nan ma haka seya maida akalar kiran ga Manniru inda ya sanar dashi har sannan suna Asibitin basu fito ba. Ganin da yayi anyi stabilizing Amir, duk sun liqe masa ciwu kan har an bashi gado yasa shi cewa Jamilan zeje ya dawo
"Ai bama seka dawo ba kawai ka tafi aikinka tunda komai ya daidaita munyi waya da Babansu yana hanya ze zo shima nagod kwarai Allah ya qara zumunchi" Jamilan ta fada seya fita bayan ya sake yiwa Amir din fatan samun sauqi. Zuciyarsa cike da wasiwasin abinda ze hanata daukar wayarsa, ya saqa wancan ya kwance shaidan na son kawo masa wasi wasi yana kaucewa shi a haka ya qarasa Asibitin. Kai tsaye office din likitan da take gani ya wuce ta sanar masa da ta turata Lab ayi mata test ita dinma zaman jiran ta kawo mata result takeyi dan ta gama sallamar kowa ita kadai ta rage seya wuce Lab din zuciyarsa na bugawa da qarfi, daga inda yake tsaye yana kallonsu ta cikin Glass Noor din riqe da hannun Humaira ya daure sangalalen da farar roba yana shafa inda jijiyoyinta suke fuskarsa dauke da wani murmushi da Khalil ya fassara daban ita kuma ta shagwabe fuska harda kwalla a idonta irinta me tsoron Allura.

Daga wajen ya tsaya saboda yanda qafarsa tayi masa nauyi amma zuciya ta harziqo masa har wani rawa jikinsa ya dauka cikin zafin nama ya tura qofar Lab din ba tareda ya bi dokar hana mutane shiga dake rubuce a jikin qofar ba yana shiga beyi wata wata ba ya make hannun Noor dake shirin sokawa jijiyar daya nemo Allura dan ya debi jini da qarfin da Allah ya bashi, Allurar ta fadi qasa shi kuma ya miqe a razane dan jiyayi kamar ya kwada masa rodi a hannun saboda zafi ya ware ido yana kallon Khalil kamar yanda shima yake kallonsa tsoron yanayinsa ya shigeshi da kuma gargadin da Dr Al'amin mamallakin Asibitin ya kirashi takanas yayi masa akan Matar mutumin daya kira Khalil.

Ya kalli Humairan ya kalli Noor gaba daya sunyi tsilli tsilli kamar ace musu ket su fece da gudu, shi fargabar rasa aikinsa ceta cikashi wanda dashi yake riqeda mahaifiyarsa da qanwarsa dan tun bayan da aka raba musu gado Yayyensu da suke uba daya suka dena yi musu komai Mijin data aura kuwa daman dashi gara babu dole yayi nutsuwar dole ya koma makaranta ya saki Aikin Sojan daya kwallafa rai akai da rayuwar shaye shayen daya fara dalilin rasa Humairan ganin Rayuwar Mahaifiyarsa na nema shiga garari na rashin mataimaki, yana kuma gama karatun ya samu aiki a wannan Asibitin da taimakon wani Malaminsu da suke shiri sosai kuma abokin Dr Al'amin ne, ko sanda ya kirashi yayi masa kashedin kula Humaira seda ya kira Malamin ya zamar musu shaida yanzu idan labari ya komawa Director yasan korarsa kawai zeyi wannan tunanin ya sakashi kai guiwoyinsa qasa ya dage hannaye yana cewa

"Dan girman Allah kayi haquri kayi mun rai gasu nan ka tambaye su muna zaune ta shigo Lab din nan kuma duk sunyi sun kasa samun jijiyarta shiyasa ma karba wlh bada wata manufa nayi ba karka ce zaka hadani da Dr ni bani na gayyato ta ba da kanta tazo". Wani matsiyacin kallo Khalil din ya jefa masa ya sake kallonta ta sunkuyar da kai qasa ta kasa koda motsi a gurin seya ja tsaki ya juya kamar iska ya fice. Badan karya zubda mutunchinsa ba kuma duk inda akaje doka zata bashi rashin gaskiya dase ya nadawa yaron dukan tsiya a gurin. Da sauri kamar zata fadi tabi bayansa ganin ya nufi hanyar fita, ita kam yau ta shiga dari ma ba uku ba tsautsayine ya sakata zuwa Asibitin data sani ta daure ciwonta tayi zamanta kota bari seda daddare kamar yanda yace mata tun farko yanzu ta tabbata fassara daban zeyiwa Al'amarin saboda yanda yake tafiyar cikin fushi kafin ta fito harabar Asibitin fuce da motarsa babu bata lokaci ta shige itama Manniru yajata. Text ya shigo wayarsa ta bude hannunta na rawa tana ganin abinda yake ciki ta fashe da kuka kawia tana cewa Manniru Sharada ze kaita.

Hankalin Mama Hauwa ya tashi da ganin Humairan dan a safiyar ma sunyi waya kuma bata ce mata zatazo ba sannan gata ta shigo tana kuka ta ringa tambayarta meya faru ta kasa bata amsa se Kuka dan bata san me zata ce ba, tana gudun suyi mata gurguwar fahimta kamar yanda Khalil din yayi ganin taqi shiru kuma taqi magana Mama ta dauki waya tana cewa
"Bari na kira Hajiyar naji ko wani abun ne ya faru a gidan tunda kin kasa magan" se tayi saurin riqeta tana cikin kuka tace

"Aa Mama karki kirata zece nakai qararsa, sabani muka samu da Yah Khalil yace na taho gida Hajiyan ma bata sani ba". Salati Mama ta dauka bayandata ajiye wayar tana kallonta tace
"Yace ki taho gida? Me kika masa Humaira? Daman Sumayya ta gayamun kin saka jaraba a ranki gana daya kin kwarzabi rayuwarki kikayi haquri a sanda ma babu se yanzu rashin qoshi ze saka ki tayar da hankali to auran kike so ki kaso ki dawo gida kome?"

"Ni wlh Mama ba wannan bane, laifi na masa daban yayi fushi amma nasan yana hucewa ze zo ya daukeni" ta fada tana kauda fuska tareda tura baki gaba. Daman ita Anty Sumayya matsalarta kenan Hansfiri ba'a maganar sirri da ita Anty Unaizatu kuwa kunya tasa ta kasa buda mata sirrin tasan lafiya lau da babu Wanda zeji amma yanzu ace har kunnen Mama ba zatayi mamaki ha idan Yah Habib ya sani ma.
"Kyaci ubanki sakarya da bata da wayo, idan kikayi sagegeduwar da auran ya mutu ke kika sani kin ga kinyi tutar babu, kuma abinda kike rainawa wata idan ta samu godiya zatayi banda mafitina kina fama da kanki kina jaye jayen magana yanzu daya koroki ai shikenan" Maman ta sake fada kafin ta shige daki tana mita. Tunda Sumayya ta mata zancen har tace zata kira Humairan ta hanata a ganinta sunyi maganar sirri idan ta saka baki gana ba zata sake gaya masa cikinta ba.

Humaira kuwa dakinta nada ta shige itama ta kwanta kukan da tayi yasa kanta yake mata ciwo ta kira layinsa duka biyu a kashe ta tabbata kuma kashewa yayi alamar fushin nasa me yawane amma ai ya kamata ya bata dama ta kare kanta ba wai kawai ya yanke hukunci daga abinda ya gani ba.
Har Magriba tana gidan cike da zullumi dan har sannan wayar Khalil a kashe take sannan nabu wanda ya biyo sahunta. Ruqayya ta kirata tun da yamma akan Aryaan da Imaan sun dawo makaranta sunata rigimar nemanta tace ta rarrashe su tana gidan Mama idan Dadynsu ya tashi ze biyo ya dauketa se ce mata tayi ai ga Dadyn a gida tun gurin sha biyu ya dawo gabamta ya fadi kenan daga Asibitin gidan ya wuce lallai abun Azimun ne ita take daukarsa wasa. A sanyaye tayiwa Ruqayyan Sallama akan zata kirashi yanzu. Mama dake tsaye a bakin qofa da Hijabin data idar da sallah ta qarasa ciki tana kallonta tace

"Laifin me kika masa idan na sasanci ne ayi tun wuri ki tattara ki komadan bazaki kwanar mun a gida ba idanba haka ba kuma sedai ki tafi gidan Unaiza tunda tun Asali daman ita take zugaki ko kashe auranki, se kace ba gara nako Mijin ma da nata ba".

Ta sunkuyar da kai qasa wai ita Mama ba zata bar wannan maganar ba se tonata takeyi sannan ita ba zata iya fada mata abinda ya hadasu ba, ai ta tababta seta gwammace fushin Khalil akan Mama taji wannan labari.
"Shikenan bari na kira Hajiya Aishar na gaya mata, ai baya koroki gida da tsohon ciki ba kuma tana gidan koma menene ai da gabanta ya kamata ku fara zuwa" Maman ta sake fada tana miqewa se Humaira ta marairaice mata danba zata manta ba yana yawan jaddada mata duk abinda ze hadasu komenene ta tunkareshi kai tsaye ta gaya masa, baya so takai qararsa gurin kowa musamman Hajiyarsa idanbata fada mata Alkhairinsa ba toh karta kuskura tayi masa lamba a gurinta dan shima baya kai qarar Mace gidansu danta masa abu, a ranta take ayyana qila Maman Mu'ayyad haka ta ringa masa shiyasa yake ja mata kashedi.

"Ayya Mama dan Allah kiyi haquri karki kira Hajiya, na gaya miki zezo daya huce wlh koba yau ha gobe da safe zaki ganshi inma kiran kike so to shi ki kirashi ai shiya koroni ba Hajiya ba" Ta fada tana riqe hannun Maman, seta maka mata harara tace
"Naqi na kirashin ita zan kira tu da ba zaki gaya mun abinda kika masa ba ai kinga seki fada a gabanta"
"Dan Allah Mama karki kiraya wlh fushi ze qarayi ya gaya mun baya so ina kao qarar sa gurin kowa shima baze kai tawa ba"
"Idan bekai qararki ba ai gashi ya koroki gida qarewar qara kenan ni raina ya baci ni kadai ko to sedai mu raba da uwarsa daga nan a tantance koma wacece me laifi a bashi yawwa" Mama ta fada tana ficewa daga dakin.

Tsaf ta tsarawa Hajiya zuwan Humairan da kuma yanda sukayi da ita, Hajiya ta ringa salallami tana cewa
"Shiyasa yau najita shiru kuma yanaji inata jajenta amma yayi muqus ya shigo tun Azahar yace mun baya jin dadi ko aiki be fita ba a bakin yara ma naji bata nan itana da suka dawo daga makaranta, dan Allah Hajita kiyi haquri yanzu kuma zan taso shi yazo ya maidota ai na gaya masa nice uwarta duk abinda tayi amsa kafin ya kaiwa kowa kukanta ya gaya mun shine ze turata gida saboda ya nuna mun ban isa ba zamu gamu duk baqin ran da yake ji dashi kwana biyu ina sane dashi zan kumayi maganinsa"

"Aa Hajiya ba'ayi haka ba be kamata ayi masa dole ba tunda bamu san me ta masa ba har ya turota gidan danita ma da kike ganinta ja'ira ce ta gaske kawai dai na sanar dake ne dan kisan abinda ake ciki tsakaninau kuma mu zuba ido harsu daidaita dan kansu ba shikenan ba" Mama Hauwa ta fada, Hajita ta dage se yazo Mama Hauwa ta dage akan kar a taso Khalil ta barshi dakansa idan yayi niyya zeje sannan ta qara da cewa
"Kuma dan Allah karkice zaki masa fada Hajiya tunda taqi fadar abinda ya hadasu na tabbata ita ce bata da gaskiya" daga haka sukayi sallama.

Jalilah dake maqale a gefen Hajiya tana jin abinda suke cewa ta tafa hannaye tana cewa
"Ahaf, ai wlh nasan se an rina. Wannan shige da ficen da yara suke tsakanin gidannan da nasu ni nasan swta qullo abinda ta saba ta aiko su dashi to kuwa tayi kadan dataga bayan Khalil da matarsa duk mugun abun da tayi ya koma mata wlh". Hajiya tayi sakato tana kallonta tace
"Ke kuma dawa?"
"Tsohuwar matarsa mana, ko kaffara bazanyi ba idan na rantse cewar ita ta saka musu hannu. Daman bana gaya miki ba ashe turo yarta takeyi ta sashi gabada tambayar wai yaushe ze maidata daman an tura masa yar azuciya kina kallo duk abinda ta fada ya zauna haka zeyi mata to wlh bata isa ba yanda ta bar gidan nan ta bar shi har abada alfarmar Annabi da Alqur'aniduk kuma wani qulumbotonta sedai ya koma mata" Jalilan ta fada tana hura hanci Hajiya ta saka ido tana kallonta kafin tace

"Kardai ki daukarwa kanki nauyin da ba zaki iya saukewa ba haka kawai zakiyi mata Qaharu kina da shaidar da zaki bayar akan ita tayi musu wani abu? Ko a baya da kike babatun zancenki idan ance ki bada shaida baki da ita zatone kawai kuma babu kyau dan haka bana so karna kuma sake jin kinyi magana makamanciyar haka, abinda ya rigada ya faru Allah ya tsara faruwarsa tilas seya kasance hakanan rabuwar Babana da Umaimah daga Allah ce yanda tazo ba a dadin rai ba kawai shine abinda ba'aji dadi ba".

Hangame baki Jalilan tayi itama tana kallon Hajiya kafin ta sauke ajiyar zuciya tace
"Yanzu Hajiya duk bayan abinda tayi miki tayi masa shima har zaki iya kare ta idan an fadi aibunta? Umaimah ce fa Hajiya kin manta tarin haqqoqin mutane da ita ta diba har kike cewa karna dauki haqqinta?"

"Ita dinfa Umaimah ina sane, bari kiji Jalilah har gaban Ubangiji na yafewa mata duk abinda tayi mun kuma ina mata fatan abinda ya faru ya zama darasi a rayuwarta ta gaba, meya ragu a jikina bayan abinda ya faru? Sannan shi dan uwan naki ya fasa rayuwa ne ko kuwa wata nakasa ta sameshi? Duk abinda ya faru babu laifin kowa qaddararmu ce a haka kuma mun karbeta bamu da ja akan hakan" Hajiyan ta sake fada se Jalilah ta miqe tana cewa
"Babu shakka Asirin data miki har yau he sake ki ba ko kuna an sake ninninkashi, to wlh ko da buzun baqin Jaki take tsafi tayi kasan a wannan karon kuma mu bamu yafe Tozarta mana Mahaifiya da lahantana mana Dan uwa da tayi ba Allah ya isan mu kuna se Munyi shari'a da ita a gaban Allah sannan wlh muddin wani abu ya sami auransa seta gane kurenta" tana gama fada ta fice daga falon a fusace Hajiya ta bita da kallo tana cewa

"Allah ya shiryaki Jalilah, Allah ya sanyaya miki zuciyarki ya azurtaki da yafiya ya yaye miki qullaci".

Jalilah kuwa na fita bangaren Khalil ta wuce suka ci karo a hanya yana fitowa ran nan a hade saboda tunda ya dawo da rana abinda ya gani yake damunsa. Gaba daya zuciyarsa ayyana masa takeyi da gangan ta fita saboda tana so su hadu dashi dukda be kawo wata Alfasha a tsakaninsu ba amma zuwan da tayi yayi bala'in yi masa ciwo akan me? Me take nufi da take so lallai seta ringa haduwa dashi? Tunda tasan baya so kuma tayi masa alqawari akan me zata bari harya kama hannunta yana shafawa har wani murmushin jin dadi yakeyi Allah kadai yasan abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.

Jalilah ta girgizashi ganin ya zuba mata idonsa da suka kada sukayi jaa saboda tunanin daya tafi tana cewa
"Nema take ta zautar dakai ma kenan to wlh tayi kadan, idan tana taqama da Boka mu da Allah muka dogara kuma se munga qarshenta". Rintse idonsa yayi saboda yabda take maganar a sama kansa kuma yana sara masa, da muryarsa dake nuna bacin ran da yake ciki yace
"Ke kuma hayagagar me kikeyi haka keda nakya rabo da abin magana?"
"Zakace haka mana tunda ina shiga Al'amuranka muna murna mun rabu da kaska ashe tana can tana jiqo mana aiki, sake kayi da addu'a shiyasa har ta taradda kai kenan ka bari abin yayi tasiri a ranka ka kori matarka to wlh tayi kadan duk kuma shirinta nata dawo baze tabbata ba in zaka miqe da addy'a ka miqe dan wadda muke maka ba isa zatayi ba naga alamar hatsabibancin ta gaba ya sakeyi ba baya ba tunda har ka fara tafiya kana tunani ba tareda kana ganin hanya ba".

Tsaf ya fahimci inda maganarta ta dosa sharrin da kullum takewa Umaimah ne na cewar Asiri take masa shi kuma yace mata idan Umaimah batayi asiri ba ita ta tafi lahira da tulin laifin Qazafin da take mata ai. Yanzun ma Tsaki yaja me qarfi ya rabeta yana cewa
"Ki bar mutum yaji da abinda ya dameshi dan Allah ba wata Umaimah ba, ke take a gabanki shiyasa har kika kasa mantawa dacita shekara hudu kullum se kinyi zancenta" tayi sakare tana kallonsa harya shige part din Hajiya kafin ta juya tana cewa

"Maganina kenan danake shiga sabgar wanda besan mutunchin kansa ba, su Maza daman macen da zata tijara su taci musu mutunchi ita sukewa naci, me biyayya da kwantar da kai itace shararsu ai shikenan idan ta dawo ta qarasa abinda ta fara randa ka farka ka ganka a kabari ka kiyayi Umaimah" ta ringa sababi harta fita saga gidan Sammani na mata Allah ya tsare bata ma jishi ba.

Khalil kuwa yana shiga falon Hajiya ta rufeshi da fada,
"Saboda ban isa ba Khalil ina cikin gidan nan ka tura matarka gida se uwarta ce ta kira take gaya mun ko? To ka kyauta kuma yanzu zaka tashi kaje yanda ka turata ka dawo da ita dan ni ba butulu bace bana manta Alkhairi. Yanda Yarinyar nan da iyayenta sukayi mana Halacci bana tsammanin ko Dukanka takeyi zaka ce ta tafi gida ballantana akan abinda na tabbata bekai ya kawo ba".

Ransa yayi bala'in baci, wato Qararsa ta kawo gurin Hajiya bayan yasha jaddada mata baya so. Irin halin Umaimah zata dauka kenan, su guma masa sannan su hadashi da mahaifiyarsa tayi masa fada toh kuwa zata gane kurenta,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login