Showing 387001 words to 390000 words out of 429394 words

Chapter 130 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

961

kadan kuma zeyi mata ta hau fushi da koke koke ya rasa inda ze tsoma ransa ta kasa yi masa uzuri akan abinda shi kansa yana damunsa, a yanzu data rigada tasan dadin jikinta a kullum cikin zuwar masa da buqata takeyi wadda yake gaza biya mata, ya lura ta raina qoqarinsa dukda cewar Abubuwa sun qara daidaitar masa dan a yanzu yana iya takarta amma bayayin dogon zango, abinda ya lura dashi ita kuma halittarta me zurfi ce tana daukan lokaci kafin ta samu gamsuwa duk kuma yanda ya sabayi mata yanzun baya wadatarta tafi so yayi mu'amala ta gaske da ita duk kuma da qoqarin da yakeyi dan lokaci da yawa bayan sun gama hala zeyi ta murqususun ciwon Mara a maimakon ta yaba masa sedai tayi ta bata rai yinin ranar kuwa zir haka zasuyi cikin qunci daga shi har ita dan baya taba iya walwala idan batayi ba.

Sau da yawa yakan zaunar da ita yayi qoqarin fahimtar da ita amma setaqi qarshe ko tasa masa kuka ko tayi shiru har ya gaji da magana yayi shiru, be san me take tunani ba gani takeyi shine baya so yayi mata yanda take ko yaya sam shi be fahimta ba yanzu da safen ma rigimar da suka tashi da ita kenan, har yayi wanka yana shiryawa ta shige masa jiki, yasan me take so a lokacin kuma bashi da sha'awar hakan a tattare dashi amma gudun shiga haqqi dole yayi mata yanda take so, haka kawai yama jikinta ta tureshi, cikin fushi take ce masa
"Daman an fada idan Namiji baya son mace ko burgeshi batayi, inda wacce kake so ce ba rashin lafiya ba koma menene zakayi mata yanda take so ai" ta shige bandaki ta barshi cikin tsananin mamakinta. Ransa ya ringa baci zuciya tana harzuqo masa, ba yau din ta fara fada masa haka ba duk ranar da Yara suka ambaci Mamansu taga wani sauyin yanayi a tattare dashi ta ringa yada masa da magana kenan akan saboda an tuna masa da wadda yake so zeyita daure fuska yana fushi a gidanamma be taba daga kai ya kalleta ba shine yau zata kafa hujja akan abinda ba haka yake ba shi yaushe rabonsa da ko a tunani ya tuna da wata Umaimah?

Idan ba Bibi ta tada rigimar zata gurinta ba wlh shi mantawa yakeyi da ita amma ota Humairan ya fahimci ta tsaya mata a zuciya tana yawan son kawo zancenta ya kuma zaunar da ita ya nuna mata baya so amma ya lura duk in tana so ta bata masa rai ne take ambato Umaiman. Haka yayi wanka suka fito, yana yai mata uzuri ne da cikin jikinta shi kansa yana iya qara mata fitina da neman rigimar da takeyi yana kuma fatan idan Allah ya sauketa lafiya ta canza karta ce zasu ci gaba da rayuwa hakan dan zaman baze musu dadi ba idan har zata cigaba da quntata zuciyarta tana quntata shi. Tun farkon daya gamu da ibtila'in irin abubuwan daya ringa hangowa kenan har yayi tunanin sawwaqe mata amma tace taji ta gani zata zauna dashi se yanzu kuma data gama mamaye zuciyarsa sannan zata tsiro da wasu baqin halaye na daban gaskiya baze dauka ba.

Seda ya jirata ta gama abinda zatayi a Asibitin saboda ya Driver yara ya tafi kai Hajiya Gaya gaisuwar rasuwa, sun fito daga office din Dr Al'amin suka wuce pharmacy zasu karbi magungunan Awo, yana gaban me bada maganin tana daga can bayansa ya juya da niyyar ya tambayeta idan tana da sauran Paracetamol ko a hada musu dashi idonsa yayi kyakykyawan ganinta da wani Dogon saurayi fari suna dariya. Kallon saurayin ya ringayi yana qoqarin tuna inda ya sanshi take ya gano wanene wani kalar tashin hankali ya rufto masa daga inda yake yana jin muryarta tana fadin
"Nuru kaine ka zama haka?" Ta sake fada cikin madaukakin farin ciki tamkar yanda Noor din dake tsaye gabanta da rigar Lab coat shima fuskar sa ta nuna farin cikin ganinta.
"Nine, Ashanty, oh my God look at you kin zama wata big Mama dake, but wait ya naganki heavenly pregnant While naji ance Mijinki ya zama mace? Ina ta neman contact dinki nayi miki jaje duk wanda na tambaya seya hanani bayan kuma dai ai ko babu SO yanzu tsakaninmu akwai zumunchi dukda ni har abada bazab dena sonki ba" Noor ya sake fada yana qarashewa da wata kalar dariyar shaqiyanci take murmushin kan fuskarta ya dauke ta kalli bangaren da Khalil yake tsaye suka hada ido ya saki ledar magungunan hannunsa saboda yanda qirjinsa ya shiga bugawa da qarfi cikin dabarbarcewa ta kalli Noor din tace

"Uhm Nuru se anjima Habibi muje idan ka gama"
"Oh ashe tare kuke?" Noor din ya sake fada fuskarsa dauke da murmushi ya miqawa Khalil dake tsaye tamkar an dasashi hannu da niyyar Musabaha seya kalleshi ya kalli hannun kafin ya dauke kai, be ko bi takan magungunan dake qasa ba ya bar gurin cikin takunsa na nutsuwa. Dakyar ta iya daga qafa tabi bayansa tana jin Noor din ya biyota da wayarsa yana cewa ta saka masa numberta amma taqi koda kallonsa, zuciyarta ta tsinke da tsoro bazata manta kashedin sa ba tun a zamanin baya akan Noor din ballantana a yanzu da take matsayin mallakinsa lah shakka kuma tasan yaji maganar su ita bata ma san yanda zata wanke kanta ba dukda ai ba wani tayi ba da be kamata ba.

Kamar munafuka haka ta bude murfin motar ta shiga, ta saci kallonsa ya riqe haba da hannu daya dayan kuma ya dafe sitiyarin motar sedata maida murfin ta kulle kafin ya tayar da motar ba tareda tace masa komai ba.
"Wlh Habibi kawai ganinsa nayi a gurin" ta fada cikin rarrabewar murya, shiru ya mata kusan minti biyar suna ta tafiya kuma ba hanyar gida suka nufa ba ta cire ran baze kulata ba kamar daga sama taji yace
"Wanene shi?" Da sauri tace masa
"Nuru ne"
"Nuru?" Ya maimaita da sigar tambaya seta dafe bakinta yanda kasan zata rusa kuka tace
"Noor ne, wannan dan makwaftan nan namu Abokin Yah Habib"
"Dan maqwaftanku ko tsohon saurayinki? Shine har kike jaddadamun sunan soyayyar da kike kiransa dashi wato NURU ko a gaban mutane kina washe masa baki kina dariya saboda kinga abinda zuciyarki take so ai shikenan" Khalil yayi maganar a fusace.

Kuka ne ya kwace mata ta fara rantse rantse ya dakatar da ita da cewa
"Karki qara harzuqani, idan dai dai kikayi kanki Allah dai yana kallo kuma har yamadidi wato kukeyi dani na zama mace bana amfana miki komai tsohon saurayinki yaci zarafina kina tsaye kina murmushi nagode, tunda naga yanzu ya nutsu ya samu abinyi idan kinada buqata sena sawwaqe miki kije ki aureshi shida yake Namiji yake da abinda ze baki ni kuma naci gaba da rayuwata a yanda Allah yaso ya ganni" Khalil din ya sake fada daidai sanda ya faka mota a qofar gidan Mama Hauwa. Ta daga kai ta kalli gidan a firgice ta sake kece masa da kuka tana cewa
"Wlh Yah Khalil ba haka bane ni ban san a ina yaji maganar nan ba rabona dana ganshi tun ranar daka koreshi daga gidan sama da shekara hudu ban sanke ganinsa ba. Kaga gidansu can ma Tunda Hajiyarsu Tayi aure an raba musu gado babu kowa a ciki sunma siyar da gidan a ina zan ganshi me zanyi dashi kuma sannan daka kawo ni gida yanzu me zanyi?"

"Ki fitar mun a mota" ya sake fada a fusace, wani irin mugun kishi ne yake cinsa, saqe saqe kawai zuciyarsa takeyi masa idan bata matsa daga kusa dashi ba ze iya rufeta da duka a yanda yake ji"
"Ba zaki fita ba" ya sake daka mata tsawa ganin taqi fita sema kai data hade da guiwa tana rizgar kuka seya ja wani dogon tsaki saboda yanda kukan nata kuma yasa yaji ba dadi, tada motar yayi suka bar layin shi bema sanme yasa ya kawo ta gidan ba tsabar yanda ransa ya baci ne yasa ya rasa ina ya kamata ya kaita ma kai tsaye Kamfani ya wuce da, a office dinsa ya barta ya shiga meeting tasha kuka ta gode Allah haka siddan tana lallaba rayuwarta Nuru ze jangwalo mata tashin hankali. Ita wlh ta manta dashi, koda a yanzu ba zaman dadi takeyi da Khalil ba amma rashin wani abu be taba sa ta tunano wano Namiji ba balle Noor da tun data auri Khalil ya zama tarihi a zuciyarta tamkar an goge mata tunaninsa haka taji se yanzu kwatsa ze dawo ya haddasa mata fitina da Mijinta shida Allah.

A nan tayi sallar Azahar Sakatariyarsa ta kawo mata lafiyayyen abinci da nama fal dan wannan cikin ya mayar da ita kamar Kura. Ranta ya danyi sanyi tunda har ya tuna da akawo mata abinci irin wanda take so tasan ya huce ko ba duka ba. Tana zaune a qasan carpet din Office din bayan ta gama cin abinci tana maida numfashi ya shigo ya mata kallo daya ya dauke kai dukda fuskarsa babu fushi irin na dazu. Kalar tausayi tayi tana masa sannu da zuwa ya amsa a ciki kafin ya shiga hada kan takaddu yana cewa
"Ki tashi akai ki gida"
"Ni zan zauna idan ka tashi se mu tafi tare" ta fada cikin muryar shagwaba, seya waiwaya ya kalleta kafin yaci gaba da abinda yakeyi kawai yaji ta fasa masa kuka. A fusace ya sake juyawa yana cewa
"Saboda kinga na kulaki bayan haushinki nakeji shine zaki zo kina mun kukan banza to ki tashi ki tafi idan ba haka ba kuma ki kwana a nan dan ni fita zanyi kuma daga inda zani zan wuce gida".

Cikin kukan ta shiga cewa
"To ai gara na kwanan da dai na koma gida kana wannan fushin dani bayan kuma Allah na gani ni ba laifina bane hanya ce ya hadamu kuma indai ba zargina kake da wani alkaba'i ba menene zesa ka dauki fushi daga kawai na gaisa da Noor, kai da kake zuwa gidansu tsohuwar matarka har mafarkinta kakeyi me na taba ce maka akai seni daga gaisuwa se cibi ya zama qari".

Jikinsa ne yayi sanyi ya zuba mata ido kawai yana kallonta dan kalamanta sun taba shi amma ai shi da ita ba daya ba. Shi namiji ne Allah ya yardar masa ya kula Mace sama daya amma ita ai Macece kuma matar aure bata da wata hujja da zata kula wani Namiji kuma ma tsohon saurayi babu ta inda alaqa ta kamatu a tsakaninsu tunda dai har So ya taba giftawa kodan gudun shigar shaidan be kamata ace an ci gaba da wata mu'amala data zarce ta dolen dole ba idan ta kama. Dukda haka seya gyara tsayuwa yace
"To ai ni namji ne kuma tsohuwar matata kikace kinga idan naga dama zan iya maido da ita kona auro wasunta na ajiye cikin gidana ke kuwa sedai ki zaba ko ni ko shi"

"To na zabe ka ni babu abinda zanyi dashi ko a da dinma yarinta ce tasa na kulashi amma yanzu dan Allah so kakeyi na wulaqanta shi daga ya gaishe ni ai kaima ba zakaji dadi ba kaifa kake gaya mun babu kyau wulaqanta dan Adam abinda ya fada nima beyi mun dadi ba, kuna badan ina gudun karna kulashi ka sake fusata ba ai da zan mayar masa da martani da yace maka Mace Aryaan da wannan kuma a ruwa na sha su kenan" tayi maganar tana nuna cikin jikinta, seya dan sassauta fushin yana cewa

"Kodan gaba bana so, karna sake ganinko dashi balle magana ta hadaku"
"In sha Allahu, yau dinma ai hanya ce ta hadamu" ta sake fada seya daga mata hannu yana cewa
"Kawai ki amsa mun da Toh, ko a dakin Mama kuka hadu banyarda ki amsa gaisuwarsa ba haka ko kallonsa baya ga na rashin sani banyarda ki qarayi ba. Asibitin ma canzawa zamuyi indai na tabbatar a gurin yake aiki"

"An gama ranka ya dade hasken zuciyata" ta fada tana isa gareshi ya riqe hannunta yana cewa
"Bana so ki kirani da komai banda Haske dan sunansa ne haka kuma kike kiransa. Baki san yanda zuciyata tayi baqi ba sanda naji kin ambace shi da NURU wlh ba qaramindauriya nayi ba na iya danne zuciyata da dake dashi zan hada na muku dukan tsiya a Asibitin yanda gaba baze qara gigin kula matar wani ba kema ba zaki sake kallon Wani da bani ba" dariya tayi tace

"Kayi haquri, kuskure nayi kuma bazan sake ba in sha Allah yanzu ka dena fushin zaka bari na jiraka idan ka tashi se mu tafi gida?"
"Na haqura yanzu ma zamu tafi ai amma kafin nan muje kiji wani abu" ya jata kan Kujerar dake gefe gane nufinsa ya sa tayi saurin janye jikinta cikin dabara tana cewa
"Naqi wayon ni dai mu tafi gidan kawai na gaji ma bacci nake so nayi".

"A sanyaya ya zauna ya janyo ta itama dole ta zauna yana kallon fuskarta yace
"Humaira, kar kiji nauyin komai ki fada mun damuwarki bana so Allah ya kamani da haqqinki ko kuma na zama silar da zaki cutu". Kanta na kallon gefe ta qi yarda su hada ido, kwana uku da suka wuce seda sukayi Magana da Anty Sumayya dataje mata ita ta fara takalarta da maganar wai taga bata da walwala menene matsalarta da yake tafi Anty Unaizatu iya bugun ciki da jan mutum a jiki se gashi ta bude baki ta fada mata abinda yake damunta dan gane da rashin samun gamsashishiyar nutsuwa a gurin Khalil. Ta gaya mata qunci da damuwa basu zasu bata mafita ba ta bude baki ta gaya masa sannan dole se tayi haquri akan wani abun tunda tasan ga abinda ya sameshi ko baya ga haka masu lafiyar ma da yawa haquri akeyi dasu dan haka suyi magana ta fahimta dashi to ita me zata ce masa bayan duk irin dabarun da Anty Sumayyan tace anayi yana mata fiye dasu amma a yanzu bata jin suna mata ita dai kawai wancan abun da da bata so shi take qulafuci har mafarkinsa takeyi.

"Humaira" ya fada yana girgizata ganin tayi nisa a tunani, ta kalleshi idonta ya kawo kwalla seta sunkuyar dakai yajata jikinsa ya rungumeta yana cewa
"Karki bari shaidan ya lalata zamanmu, karki yarda magauta su mana dariya ki daure ki gayamun menene damuwarki me kike so"
"Kaji rainib wayo bayan yasan menene damuwar tawa kuma zezo yana wani tambayata" ta fada a zuciyarta a fili kuma taja Majina kafin tace
"Ni babu komai".
Rungumeta yayi a ransa yana jin babu dadi, iyakar qoqari yanayi gurin nemawa kansa lafiya a kullum kuma cikin addu'ar Allah ya tsare masa iyalinaa yakeyi shi yasa hankalinsa ya tashi sosai da ganin da yayi mata da wancan yaron, baya zarginta ba kuma ya tunanin zata iya aikata wani abu makamancin wanda shaidan yake yawan kawo masa amma kuma hakan baze sa ya nade hannu ba tareda ya miqe da Addu'a ba da kuma kulawa da lamuranta. Sau da yawa irin wadannan matsalolin da maza sukeyin shakukatun bangaro dasu akan matansu su suke jefasu a halakar da daga baya kowa zezo yana tofin A????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? !la tsine dasu bayan kuma Mijin shi ya bada qofar da barakar ta shigo gidansa.

Sun dade a zaune yana rungume da ita kafin ya saketa saboda bugun qofar da akeyi ya bada izinin shigowa Anwar ya shigo da takaddu. Cikin mutuntaka suka gaisa yana tambayarta yara
"Yan China nan ne suka zo fa yanzu nan kawai Jacob yake gaya mun suna conference room ya musu iso" Anqar din ya fada yana miqa masa takaddu ya karba ya duba yana cewa
"Amma gobe sukace"
"Yau ko gobe dai, sun dai fi qarfafa zuwan goben so kuma tafiya ta kama shugaban kamfanin nasu yau da dare ze tafi shiyasa ya turo su yau dan a gama abinda za'ayi kafin ya tafi dan ze jima" Anwar ya sake fada seya ja kujerar gaban system dinsa ya zauna yana cewa

"Allah yasa na gama hada takaddun bari na tura maka ta Mail dan ban fito da system dina ba tana gida seka projecting mana". Seda ya gama tura takaddun ya kalleta yace
"Na bar miki ita a kunne akwai Korean movies a ciki wannan ne ya saka" ya nuna Anwar,Anwar din yayi dariya yace
"Saboda irin haka kinga bakya zauna boring ba zaki samu abin kallo tunda nasan ku mata daman daga India se Korea kuke kallo".

Khalil ya tashi suka fita yana ce mata
"If you need anything ki kira Secretary se ki gaya mata ba zamu jima ba in sha Allah da mun gama se mu wuce ko?"
"Allah ya bada sa'a yasa a qulla Alkhairi" ta fada suka amsa mata da Amin gaba daya dan Anwar kansa yaji dadin Addu'ar, abinda ya rasa kenan matarsa ta ko ina bata da makusa seta bangaren yi masa addu'a idan ze fita ko godiya idan ya mata abu, qarqarinta tace "Nagode, A dawo lafiya" shikenan.

Kan kujerar daya tashi ta koma ta shiga Media, a maimakon ta bude movies din seta wuce gurin hotuna wata folder guda taga an rubuta
'LIFE' ta bude. Hotuna sun wuce ta irgasu kala kala shida Maman Bibi, wani irin abu ya ringa taso mata zuciya ta ringa tunzurata har ta kasa haquri kai tsaye ta dannawa folder gaba daya delete saboda bacin rai ma ta kashe system din gaba daya ta sauka qara ta dirar ma ragowar naman da bata cinye ba tana huce fushinta a kansa.

Bayan sun koma gida da daddare ma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login