Showing 210001 words to 213000 words out of 429394 words

Chapter 71 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

929

tafe Ajalinsa na binsa a baya be sani ba haka a daren nan aka kawo gawar Yaya Aminu daya fita daga gida cike da burika kala kala ba tareda yasan yayi fitar da baze dawo bane. Fadar irin tashin hankalin da Iyalan gidan suka shiga bata bakine, Daga dare zuwa safiya Suman Mama biyu, Mamy matarsa ko tunda ta zube ba'a sake jij bakinta ba har seda safe da aka zo fita da gawarsa sannan ta sake fasa wani ihu ta zube sumammiya a gurin dole aka hada ita da Mama da Jininta ya haye akayi Asibiti dasu Abba kansa daga maqabarta Asibitin aka wuce dashi saboda yanda Numfashinsa keta hawa da sauka har ana ganin dagawar qirjinsa gashi ya kasa magana toh ya za'ayi? Allahn daya fisu son Aminu ya karbi abinsa ba tareda yayi shawara da kowa ba sedai a bishi da fatan samun dacewa kamar yansa ya samu kykykyawar shaida daga bakin jama'ar unguwa da Abokan aikinsa. Sun bada shaidar mutum ne me Amana ba kuma ya karbar cin hanci haka mai laigi duk daurin gindinsa idan aka sakashi akan case seya tsaya iya yinsa yayi ansha kaiwa rayuwar sa Hari Ubangiji na tseratar dashi se yanzu da tafiyar tazo babu wanda kuma ya isa ya dakatar da ita.

Rasuwar Yaya Aminu ta sake maida kowa na gidan cikin hayyacinsa musamman Umaimah da wasiyyar da yayi mata ta qarshe ta samu guri radam ta zauna a kwakwalwarta, damanya fada wata rana baya nan bare akai masa qararta gashi kuwa ashe abinbada nisa bane yanzu sedai su tunashi su sakashi a Addu'a Allah sarki Anty Mamy ta shiga sahun su Anty Hafsa Allah ya daga musu. Wannan rasuwa ta sakata watsar da makaman yaqi sabon gidanma gaba daya ji tayi ya fita a ranta qila ma duk haqilon da takeyi ta mutu kafin a tare ko idan an shiga ba zata dade ba zata mutu. Ranar da tayi tunanin idan ta mutu Khalil wata ze auro kwana tayi tana kuka har abin ya bashi tsoro ya rinfa tofa mata Addu'a da farko duk a zatonsa Yaya Aminu ta tuno amma se yaga ta kalle shi seta rushe da kuka se kuma ya fara tunanin ko shima mutuwar zeyi ne ta fara Alhini?
Alwala ya dauro ya fara jera salloli, idan ma mutuwar zeyi ya mutu yana sallah haka suka kwana ita kuka shi sallah.

Bayan wasu watanni

Yaya Khalil, bari naje na kaiwa Hajiya abin nan" Umaimah dake tsaye akansa ta sako wani uban zumbulelen Hijabi ta fada. Khalil ya zare Glass din dake idonsa kafin ya ture takarddun gabansa ya nuna mata kan cinyarsa yana cewa
"Bazaki dena cemun Yaya Khalil bako? Gashi nan kin koyawa su Bibi sun deba Dady se wani Yaya zan saba miki fa" ya qarasa yana jan hancinta daya fara budewa. Yar qara ta saki kafin tace
"Toh za'a dena, suma zan hanasu fada"

"Yawwa ko kefa, me zaki kaiwa Hajiyar?" Ya fada yana qoqarin bude kwanan hannunta ta qanqame tana cewa
"Bazaka gani ba"

"Wai dagaske kike matar nan rowa zaki mun ko kadan bazaki sammun ba?" Ya fada sanda yayi nasarar bude kwanon ya debi dambun naman dake ciki ya zuba a baki yana taunawa yana lumshe ido. Bubbuga qafa ta shigayi da kuka qarya wai seya biyata, kwanon ya karbe ya sake dibar wani ya watsa kafin ya ajiye gefe yana cewa
"Zo na biyaki toh, ai abun bana rigima bane".

Bakinsu ya hade ya shiga kissing nata passionately, seda suka kwashi kusan minti goma kafin Umaimah tayi saurin janye jikinta jin Alamun ana hawowa saman da gudu. Tana zama kusadashi kuwa Mu'ayyad ya fado da gudu yana sallama Bibi a bayansa tana kuka da yar tsanarta a hannu babu kai"

Jikin Umaimah ya fada ita kuma ta wuce gurin Khalil ya riqeta yana cewa
"Meye haka, me kayiwa Mamana take kuka?" se ta sake fashewa da kuka cikin magarta da bata gama nuna ba ta nunawa Khalil din kan yar babynta tana cewa
"Yaya ya kace ta, ya ciye mata kai".

"Lalala baka kyauta ba Yaya, ya zaka kashe mata Babynta ka cire mata kai? Kyaleshi kinji Mamana an jima zamuje mu siyo wata babba maza share hawayenki" saurin goge fuskarta ta shigayi jin za'a siya mata wata ta dane cinyar Khalil din tana qoqarin taba takaddun zanen dake gabansa ya janye su yana cewa Umaimah
"Kije dasu dan Allah na samu na qarasa aikin nan yau"

"Uhm kafi sati kullum haka kake cewa yau zaka gama, ni na fara gajiya da wannan aikin me cinyewa mutane lokacinsu" ta fada tana zumbura baki, seya daga wata takadda ya nuna mata yana cikin tsokana yake cewa
"1 Billion contract ake gaya miki yarinya, kedai kiyita salati kina mana addu'a idan harkar nan ta fada ai ke kanki zaki sha mai Hajiyata"

"Toh Allah yasa" ta fada tana miqewa ta bawa Mu'ayyad kwanon ita kuma ta kama hannun Bibi suka fita ya bita da kallo yana wa tafiyarta data fara canzawa kallo. Watanninsu Shida da tarewa a Sabon gida kuma watannin cikinta tsarabar Sabon gida. An tare lafiya kuma tun sannan zaman lafiya ya sake jaddaduwa a gidan idan ka cire qananan sabani da kowanne gidan aure ake samun su musamman ma da akayi katari da Khalil din me dauke kaine abinda yake qarawa zaman nasu Armashi kenan dan ko tsiyatakunta sonso motsawa baya kulata yanzu.

A bangaren Alaqarta da Hajiya kuwa se abinda ya qaru saboda qaruwar kusancinsu yasa ta sake siye zuciyar Hajiyan da mugun ladabi da biyayya. Kusan koda yaushe tana bangaren Hajiyar, da safiya tayi Khalil ya fita ta gama abinda zatayi zata wuce can. Habiba ta shiga jami'a dan haka yanzu itake duk wani abu daya shafi Hajiya harda Abinci dan sauda yawa can take girki seta debar musu dan dama yaran kusan ko yaushe suna can, Mu'ayyad ya fara zuwa makaranta se Bibi ce kawai a gida.

Da sallama ta shiga palour Hajiyar Jalilah da zuwanta kenan ta dago suka kalli juna kowacce ta watsar da yar uwarta. Tun case dinsu da Hadiza Jalilan ta fita a sabgarta. Haduwa seta zama dole gaisuwa ko se akan idon Hajiya in ba haka ba babu meyiwa wata kallon arziqi.

Ita Umaimah gani takeyi Jalilah ke zuga Khalil, ita kuwa abinda Umaiman tayi ne ya saka ta fitar mata akai ga kuma wannan rainin da tayi mata tunda ai ko banza ta girmeta tayi qanwa ta kusan nawa da ita bataga dalilin da ze saka ta fara kulata ba.
"Aa, Umaimah kin shigo yanzu yau Weekend dinma bazaki zauna ki huta ba ai Habiba tana gida" Hajiya data fito daga kitchen ta fada cikin fara'a, Umaimah ta zame qasa ta shiga gaisheta ta amsa tana tambayarta jiki jiki ta amsa harda satar kallon Jalilah data sakawa waya Ido kamar ma bata parlour. Kwanon hannunta ta ajiye Hajiyan tana cewa

"Dambun kaza na miki tun jiya Hajiya shi nace bari na kawo miki yanzu"
"Toh Madallah na gode kwarai Allah yayi miki albarka kamar kuwa kinsan bakin yana kwadayi, bana so na sakaki aiki ne ga nauyin jiki shi yasa na saka Habiba kin ganshi can na kasa ci duk ta qonashi ka shegeb qarni daga ji bata saka kayan qamshi a kazar ba"

"Kai Hajiya kawai dan kin saba cin na Anty Umaimah ne amma wallahi abuna yayi dadi, dan Allah Anty ci kiji" Habiba data taho da kwanon dambunta ta miqawa Jalilah. Ta dibi kadan ta saka a baki tace
"Aiko yayi dadi kuma ni banji wani qarni ba Hajiya se qamshin spices ma yakeyi"

"Oho duk ta zuba wasu abu masu warin kyankyaso ba ni nafi son abu na haka daga citta se Tafarnuwa ci kiji banbancinsa da wannan" Hajiyan ta fada tana miqa mata kwanon Umaimah seta miqe tana cewa
"Kedai kici abinki tunda ya fi miki dadi" Umaimah ta harareta qasa qasa yanda baza'a lura ba amma tsaf Jalilan ta gani a ranta tace
"Da haka kika shanye mana uwa kenan ai kuwa zamuyi maganinki".

Miqewa Umaimah tayi tana cewa
"Bari naje Hajiya, Anty Jalilah amma yai dai zaki shigo mana dan ina lissafe tun ranar tariyar mu baki sake leqa bangaren ba".
Yanda take murmushi seka rantse har zuciya tayi maganar, Jalilah ta mayar mata da martanin murmushinta tace
"Zan shigo, ki gayawa dan qanina ina nan zuwa" da haka ta juya ta bar sashen.

Ta tarar da Khalil ya tashi daga aikin da yakeyi, wayarsa dake ajiye akan centre Table ta dauka,seda ta leqa dakinsa, qarar zubar ruwa dataji yasa ta gane wanka yakeyi dan haka ta dawao palour ta bude wayar ta shiga yi masa binciken data mayar dabi'arta. A sabuwar Islamiyyar data chanza a nan cikin unguwar saboda tasu tada tayi mata nisa daga nan dukda yanzu tana jan mota babu inda bata shiga amma akwai tazara sosai to a Islamiyyar tayi wata sabuwar qawa wai ita Safina ana kiranta da Maman Halima.

Qawance suka qulla tamkar sanda suke da Rufaida, Rufaidanda saboda qin Allah yanzu take so ta dawo mata suci gaba da qawance saboda ganin cewa Allah ya sake dagata Mijinta ya samu budi sosai ga tangamemen gida na kerewa Sa'a tana ciki se gata ta debi zugar yan unguwa su Maman Hauwa wai sunje yi mata Allah sanya Alkhairi dukda bata fada musu zata tashi ba se a bakin Maman Hibban sukaji dan suna hulda da ita har yanzu ita kadaice bata ji hudubar Rufaida ta dena kulata ba se Ramatu kishiyar Maman Hauwa.

Ita Safina ita ta qara mata sabon course na binciken wayar Miji. Dukda daman sa'i da lokaci takanyi amma yanzun da Safina ta karanto mata wasu gurbatattun tunani ta dasa mata zargi a ranta ya sa ta maidashi sana'a a cewar Safina Maza yanzu gaba daya yan iska ne kawai wasu ne suka fi wasu iya taku shiyasa ba'a gane su amma in kika zurfafa bincike da wayo se kin gano duk abinda Mijinki yake aikatawa a boye. Ba iya binciken waya ta koya mata ba harda Mota.

Haka kawai zata ce ya bata Aron mota ta fita ta samu guri ta bincike masa mota tsaf tun Khalil baya lura har ya fara gane idan ya ajiye takaddu ana canza musu tsari ya fara zargin ko a office ne wani yake masa haka se daga baya wata rana ya kamata,ta ari motar ta fita can qasan ta tsaya tayi parking shi kuma fitar gaggawa ta same shi dan haka ya dauki motarta ya fita. Ya dade yana mamakin me take nema, be nuna ya ganta ba ya tafi sabgarsa bayan ya dawo ya duba motar tsaf dan a ranar akwai tsabar kudi naira miliyan biyar daya karbo daga banki ze kai wani guri ya barsu a motar zuciyarsa ta darsa masa ko kudin zata dauka amma ya qaryata hakan dan a zamansu naira biyar dinsa be taba nema ya rasa ba idan ze aje abu ya shekara ze dawo ya tarar dashi batta idan tana da buqata zata uzzura masa ya bata amma bazata taba taba masa kudi idan bashi ya dauka ya bata ba

Bayan ta ajiye motar ya koma ya duba kamar yanda ya tsammata komai yana nan inda yake ko tsinke bata dauka a ciki ba dan yana da lura haka idanya ajiye abu be fiya mantuwa ba kuma ko ya aka taba seya gane shiyasa yasan komai dake cikin motar da kuma yanda suke tanbayar da yake yawan yiwa kansa itace me take nema? Se daga baya ya samu amsarsa randa ya taba jinta tana waya take gayawa wadda besan ko wacece ba ita Mijinta Dabanne da sauran Maza kuma baya cin Amanarta dan babu inda bata bincika ba har dirar mikiya data tsiri yi masa a Office se yana tsaka da Aiki zataje kuma bata taba kamashi da wata alama ta rashin gaskiya ba. A nan ya gane ashe duk wannan binciken na neman hujjar yana cin Amanarta ne kai Mata se a barsu.

Tsaye Khalil yayi a bayanta yana kallon yanda take bincika masa waya kamar wani danta, messages ta gama dubawa ta bude WhatsApp kenan ya fuzge wayar dan akwai abinda baze so ta gani ba, badan yana tsoron komai ha sedan kawai yanzu yana da buqatar nutsuwa wata kwangila yake nema yana kan Tsara papee work din ne kafin yayi presenting idan yayi ayi awarding nasu yanzu idan ta shigar Masa WhatsApp sabuwar chapter bala'i zasu bude a gidan kuma be shirya asarar wannan kwangilar ba.

"Wai sau nawa zan miki magana akan ki dena yi mun bincike a waya ne?" Ya fada cikin fushi, Umaimah data zabura dan sam bata san yana wajen ba ta dauka wanka yakeyi ashe ruwa ya tara be shiga wankan ba, hade rai itama tayi tace
"Idan mutum yana da gaskiy ai baze damu ba in an duba masa wayar ammaji yanda ka wani zabura ka kwace da alama wani abun kake boyewa a ciki"

"Ni dan ki ne da zaki ringa mun bincike dukma abinda nake boyewa ina ruwanki? Ki shiga hankalinki wallahi bana son shirme kinsan sarai yanzu da da ba daya bane bazan dauki ko wanne rashin hankalinki ba" Khalil din ya fada a hasale se kuwa ta riqe qugu tana cewa

"Lallai Khalil, ni kake kira mara hankali ko saboda na kusa na bankado Asirin abinda kake aikatawa a waje ko? To mu zuba mu gani, ni din dai nice Umaimah ba janzawa nayi ba kuma zan tabbatar maka da hakan duk wadda ta shirya siyan tashin hankali da kudinta taci gaba da kulaka" tana gama fadar haka ta haye sama fuuuu ta barshi a tsaye.

Bayanta yabi da kallo, shikenan Aljannun da aka saka a batta tun mutuwar Yaya Aminu sun balle bala'i ya dawo kai wannan yarinya shaidan yana jinjinawa Umaimah. Zama yayi akan kujera ya shiga WhatsApp din nasa ya bude, kamar yanda yayi tunani kuwa message dinta ne a farko ga saqon data turo na qarshe ya fito ras I love you da manyan baqi harda Jajayen heart emoji. Beko bude ba yayi deleting chat din gaba daya yana zauke numfashi, Zahra nema take seta saka shi a bala'i, shidai Addu'arsa Allah ya taimake shi kwangilar nan ta samu daga nan ba kare bin damo kowa ya kama hanyar sa amma kafin nan dole ya lallaba wannan yar Tijarar ya samu ta barshi ya kammala abinda yake gabansa.

Umaimah ko kasa zama tayi sanda ta shiga dakinta, tabbas akwai abinda Khalil yake boyewa kuma ko menene seta bankadoshi idan ba haka ba me yasa ze fuzge wayar bayan a baya kota dauka ya kamata sedai ya mata fada kawai amma baya wannan rikicewar,to wallahi ya tarowa kansa abinda baze iya ba kuwa in har ta kamashi da laifin cin Amana ba zata saurara masa ba.

Kayanta ta cire ta shiga wanka, fita zatayi tanaso taje gida ta duba Anty ance tayi targade a hannu ta manta ma se yanzu abin ya fado mata daga nan ta biya gidan Safina ta bata wannan labari lallai ta yarda da tace Khalil ya iya taku ne kawai amma babu yanda za'ayi ace Matashi da kudi kamarsa ya rasa Yammata ko be nema ba dole su bishi ai.

Sanda ta gama shirinta bata tarar da Khalil ba ya rigata fita, tayi kwafa wato baze mata sallama bama waya sani ko gurin Matan ya tafi. Motarta ta hau ta fice, a babban Get suka hadu da Jalilah da Habiba da alama fita zasuyi suma amma ba nisa zasuyi ba dan slippers ne a qafar Habiban ko kallonsu batayiba ta bawa mota wuta ta fice a sittin.

Bata jima a gidansu ba ta tafi musamman da Mama ta fara mata fadan Yawo dan a Satin sau uku yan ganin sabon gida da basu samu zuwa ba se yanzu dangin Abba na Qarayeda sukazo biki gidan Baba Abdullahi da akayi wancan satin zuwan su uku bata nan, jiya juma'a ne kawai ta zauna gashi yau ma ta sake fita.

A parlour Safina ta yada mayafin Abayar data saka bayantasha ruwan sanyin data kawo mata ta zauna a qasa dantafi jin dadi Safina na kallonta tace
"Na ganki ke kadai, ina yaran?"
"Ki rabani da wasu yara dallah akwai matsala wallahi" Umaimah ta faa se Safina ta gyara zama tana cewa
"Matsala a ina meya faru?"

Labarin yanda sukayi ta bata, Safina ta shiga tafa hannu tana cewa
"Tab Umaimah kinyi sake wallahi an gama dake kina me har haka ta faru? Kawai ma kice abu yayi nisa sedai fatan Allah ya kiyaye"

"Ni ba surutu nazo kimun ba mafita nake nema" ta katse Safina, seta gyara zama tace
"Kinga yanzu dai ki fara gano wace tsinanniya ce ko tsinannu ma tukunna ne zamu san ta inda zamu bullo. Ba kwanaki nake gaya miki naje gidan su budurwar Baban Halima na zage shegiya tas ba? Wai ko wancan satin naje gidan Hajiyarsa se ji nayi suna yada zance wai ai satin nan Kabir zekai kudin aure, nayi dariya, daga gidan in gaya miki na wuce Sharp Sharp. Jiya ina nan kwance ya shigo wurgai wurgai dashi sedaga baya Rabi take gaya mun ashe yarinya da mamanta harda Wanta wai sunje gidan Hajiyar sun kai kashedi akan ya fita a sabgar yarsu ba zata aure shi ba. To ina zan iya wahala ga inda zan kai kudina a share mun hawaye".

"Nifa na gaya miki babu wani shege da zan kaiwa kudi yana zaune yaci, yawwa bala'ina ma yafi duk wani Asiri da baya dorewa idan kuma kika hadu da wadda tafiki iya bin malaman fa ta shigo da qarfin tsiya ya za'ayi?" Umaimah ta fada cikin qosawa da zancen Malamai da kullum aikin Safina kenan, taje ta kai kudi ayi mata aiki kullum a tafe shiyasa ga ta nan sedai qaton gidan amma babu abinda ta ajiye suturar Arziqi se tayi da gaske take dinkawa badan Mijin baya mata ba sedan ta qulla zubin Adashin da babu kwasa.

"Yanzu dai kiyi qoqari wayar tazo hannunki ki dauko lambar shegiya daga nan zamu san abinyi" Safina ta jaddada mata. Nan ta kusan wuni seda tazo tafiya ta dakko wata jigida ta bata tana cewa
"Gata an kawo amma fa ta qara kudi dubu goma sha biyar dakyar ta bari a sha uku saboda ma nace ta hado miki sauran kayan ne suma wani

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login