Showing 183001 words to 186000 words out of 429394 words

Chapter 62 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1030

zuciyarta su zasu kaita su barota a inda ba zata iya fiddo da kanta ba. Idan ba Mahaukaci ba wa ake cewa yayi barna kuma yayi ba tateda tunanin me hakan ze janyo masa daga baya ba.

Tsaki yaja yana qoqarin kulle qofar ya tuna da ba lallai a ya smau magananin a ciki ba dole seya fita dan haka ya koma dakko muqullin mota. Har ya shiga ya juyo da baya saboda gilmawar wata daya gani kamar Khausar. Saurin mayar da qofar yayi ya kulle ganin sunfara sauka daga benen sunyi qasa a hankali yabi bayansu, tana gaba wani Dogon saurayi fari na binta a baya waya ce kare a kunnenta daga yanayin fuskarta ya karanci cikin tashin hankali take da alama ta samu saqon anje nemanta ne.

Bin bayansu yayi har suka fita yana ganin sun nufi wata mota yayi saurin yin inda ya ajiye tasa motar ya dauka, seda ya bari sunfita kafin yabi bayansu, a sannu yake binsu cikin kwarewar da shi kansa besan yana da ita ba ta yanda babu yanda za'ayi su fahimci ana binsu a baya. Dukda Gajiya da mugun ciwon da kansa yakeyi masa haka ya daure yaci gaba da binsu, Hadeja road yaga sun dauka, to ina zasuje? lissafinsa dai yasan ba zasu bar Kano a daren nan ba,
Amma koma inane baze taba bari su tsere masa ba.

Wani gidan mai daya ga babu kowa ya tsaya ya qara saboda gudun karya qare masa a hanya man motar yayi qasa. Gudu ya ringa shararawa a Titi ko tsoron dare ba yayi da yanayin hanyar da take Titi daya ya ringa tafiya amma ko qyallin motarsu be hango ba, be sare ba yaci gaba da tafiya, yasan dai babu wata hanya da zasu dauke subi indai ba kuma cikin qauyuka suka shiga ba Titin dai yaci gaba da bi harya kai Munjibur basu gamu ba ya gama saddaqarwa sunyi masa nisan da baze iya taddasu ba danhar idan tafiya sukeyi kuma Titin nan suka bi a irin gudun da yayi da ya tarar dasu a hanyar.
Baze yuwu ya juyo Kano a sannan ba dan Goma har ta gota ga muguwar yunwa da ciwon kan da suke damunsa se kawai ya dauki hanyar Munjibur park, canze kwana zuwa da safe ya koma cikin gari.

Yana tafe yana cizon yatsa da dana sanin tsayawar da yayi gashi yanzu Allah kadai yasan inda suka tsere, wata nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke daidai sanda ya shigar da motarsa gurin parking yayi arangama da Motar da yake bi. Gaggauce ya shiga ciki, ya ringa baza ido a reception ko ze gansu amma shiru seda ya biya kudi aka bashi muqullin daki ya shiga kafin tunanin kiran Yaya Aminu yazo masa. A taqaice yayi masa bayanin komai da kuma inda yake a yanzu Yaya Aminu ya bashi tabbacin zasu dauki mataki dan yanzu haka ma yana office be tafi gida ba saboda wani pending case da basu qarasa na.

Dakyar ya iya shan coffee a cafeteria dukda baqar yunwar da yakeji ya koma can bakin qofar gurin ya kafa ya tsare duk wani me shiga da fita akan idonsa har zuwa sanda Yaya Aminu ya sake kiransa akan gasu sun shigo Munjibur, yayi mamakin yanda suka fito operation din da daren nan, yanda kasan wanda sukazo kama wata qasurgumar yar fashi haka suka zagaye gurin, a cikin daren akayi Nasarar damqe Khausar dake can cikin daki ita da saurayinta Nasman suna shirya yanda za'ayi ta fece daga Kano har zuwa sanda abubuwa zasu lafa. Shiya takura akan su tsaya a nan su kwana kafin da safe su wuce dan daman sun hadu kenan zasu tafi yawon sheqe ayarsu ta samu kira daga gidansu cewar Jami'an DSS sunje nemanta kuma an baza nemanta a duk inda aka san tana zuwa suna fakonta shiyasa babu shiri tace su tafi, shi kuwa ya rigada yayi caji dalilin da yasaka yace su kwana anan kenan ya samu ya rage zafi kafin da safe ya gudu ya barta dan baze saka kansa a rigimar da be san mafarinta ba haka kawai.

Kwanan da Khalil beyi a can ba kenan ya biyo su suka dawo Kano, tunda ya kife akan gadon dakin Hotel din daya koma be farka na se qarfe goma da Rabi na safe shima saboda bugun qofar da ake tayi daga waje. Dakyar ya tashi ya zauna yana dafe kansa, labulen window a dage suke hasken rana ya cika dakin abinda ya ankarar dashi cewar gari ya waye kenan ya miqe a hankali yana jin kamar iska zata kwashe shi saboda rashin kwarin jiki ya bude qofar.

Room service neda kayan shara, ya sanar dashi ya dade yana bugu dan har ya fara zaton ko ba lafiya ba tunda an tabbatar da mutum a ciki Khalil ya daga masa hannu yace yaje, idan ya gama abinda yakeyi ya fita se yazo yayi aikinsa Mutumin ya juya yana waigensa yanayinsa yayi masa kama da wanda yasha tafi qarfinsa dan dakyar yake iya bude idonsa haka tsayuwa seda ya jingina da qofa.

Wanka ya farayi tareda Alwala yayi sallar Asubar da ta kufce masa. Ta Landline yayi order abinda za'a kawo masa abinci tuli a hakan ma gani yake kamar bazasu qosar dashi ba dan rabonsa da Abinci tun wanda yaci a Jirgi se Coffee daya sha da daddare tas kuwa ya tada abincin nan sunfi kala uku yasha ruwa yayi qyatsa sannan ya fara fahimtar abubuwa dakyau. Kan Gado ya koma ya miqe bayan ya cire jallabiyyar jikinsa, wayarsa ya lalubo tana cikin Aljihun rigar daya fita da ita da daren Tarin Missed calls din daya gani akai sunfi Hamsin duk ya share ya tafi kan na qarshe wanda Yaya Aminu ne ya kirashi. Sanar masa yayi da tun dazu suna CID shikadai ne bezo ba har yan gidansu Hadiza gasu nan harda ita ya bashi haquri akan baccine yaci qarfinsa amma gashi nan zuwa ya kashe daga nan ya kira Jalilah da itama ta kirashi sau ba Adadi.

Muryar Hajiya yaji ita ta dauki wayar, cikin tsananin bacin rai tace
"Ibrahim kana ina? Duk abinda kakeyi ka bari kazo nan inason ganinka kaji ko?"
Da "Toh" kadai ya iya amsa mata danyasan tunda ta kirashi da Ibrahim yau ranta a Asalin bace yake.
A gurguje ya shirya ya fita, gidan Hajiyar ya fara zuwa ko zama bata barshi yayi ba tace su tafi ya daga kai ya kalleta ya Kalli Jalilah da Anty Amina da suke zaune duk sun sunkuyar da kawuna cikin son qarin bayani amma babu wadda tayi magana.

"Ka tashi mu tafi Office din yan sandan, saboda rashin Imani a hada baki dakai a dauki yarinya da tsohon ciki a kukketa a Cell baka ko tsoron wani abun ya sameta sannan a rasa cikinku Wanda ze sanar dani badan wannan yaron Munzali Abokin Khalifa ya ganku acan ba ya gaya masa da sedai mugun labari kake so naji ko me? Kun hada kai da uwarka Jalilah abu na faruwa kun boye mun har ka dawo qasar nan ban sani ba ai shikenan" Hajiya ta ringa sababi a mota gaba dayansu dai suka mata shiru babu wanda yace komai har suka isa.

Sun tarar da Abban su Umaimah tareda qaninsa Baba Abdullahi fuskar Abban kadai zaka kalla kasan yana cikin tsananin damuwa. Tun a daren Jiya da Mama ta sanar dashi bayan ya dawo seda hawan jininsa ya tashi jiri ya debe shi badan Allah ya taqaita ba ya zauna a kujera da ba'asan abinda ze faru ba, ya ringa sauke ajiyar zuciya yana nanata hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarsa kafin yaji dama dama har ya iya miqewa ya tafi dakinsa. A daren kwana yayi da ciwon rai, Asuba nayi ya kira dan uwansa ya shaida masa se gashi kuwa tun gari be gama haske ba ya ringa fadan me yasa tun a jiyan su Maman basu kirashi ba ya za'ayi su barta ta kwana a can haka suka dungumo gaba daya suka tafi amma ko kallon arziqi basu samu ba dan a sannan bangaren Hadizan basu rigada sun qaraso ba.

Daidai isowarsu Khalil a sannan kowa ya hallara bangare hudu harda yan gidansu Rufaida Babban yayansu da Mijin Yayarta da shima Jami'in tsarone aka hadu ana ta jajantawa juna ga Babansu Khausar daya iso a rikice shima dan katsahan a safiyar mugun labari ya riskeshi.

A daya daga cikin ofisoshin gurin suka hallara, sega Umaimah, Rufaida da Khausar an taso qeyarsu cikin dare daya sun zama abin tausayi karma Khausar taji labari. Ita Umaimah da Rufaida tsabar Azabar cizon sauro da zafi ga warin da gurin yakeyi ne ya gigitasu. Maganin sauron da Khalil ya kai musu masu gadinsu ne suka kwace harda bargon Rufaidah Umaiman cema suka dan tausaya mata suka bar mata nata haka sukayi kwanan zaune suna make maken sauri jikinsu kuwa yayi rudu rudu kamar wanda Sukayi birgima a gidan tururuwa Umaimah tayi Amai yafi sau goma daga daren zuwa safiya shiyasa ta sake jigata tafiya ma seda wata ta ruqota sannan take iya daga qafarta.

Khausar kuwa abin nata yafi muni, daman sanda suka kamata sun tarar dasu a daki bayan sun gama sheqe ayarsu suna kora kwayoyi saboda su samu nutsuwar bacci a cewarsu, tun a hanya ta ringayi musu shirme da masifar me tayi da zasu kamata rabi cikin hankalinta rabi a maye dan haka suna zuwa a maimakon waddata taho da ita ta sakata Cell din su Umaimah seta jefata cikin Matan nan da dama cike suke da haushin su Umaimah da suke ganin suna da gata. Tana shiga ta taka daya daga ciki bata yi wata wata ba ta hankadata Khausar na daidaita tsayuwarta dan ta kusa ta fadi ta kwashe mata da mari nan fa sauran sukace dawa Allah ya hadasu suka rufu akanta sukayi mata dukan kawo wuqa masu ganin na kallonsu babu wadda ta kai mata dauki.

Kaca kaca sukayi mata fuska ta kumbure baki kamar ta boye fanke saboda yanda ta tashi kamar ma sun cire mata haqori ne oho sannan tun farar safiya aka jefata a dakin tuhuna. Kamar masu jin haushinta seda suka fara lallasata abinda ba'ayiwa su Umaimah ba kafin suka fara mata tambayoyi. Da farko tayi gardama, dukda wayarta dakw hannunsu sun binciko duk wata shaida da suke buqata harda ma abinda be shafi case din ba sun qara tara wani chages din akanta amma dukda haka tayi qememe taqi amsa laifinta.

Dukan mutuwa suka mata har daya daga ciki na cewa a bashi belt ya shaqw mata wuya kawai ta mutu su huta dan sun fahimci yanzu tura nasu laifi Kotu bata lokaci ne kawai dan idan sunada hanya se kaga shari'ar bata wani kasancewa yanda ya kamata ake sallamarsu amma idan suka kasheta anan sun kashe banza qarshenta suce sun wayi gari sun tarar da gawarta shikenan ai kafin ma ya kai aya jiki na rawa Khausar tace zatayi magana. A gaba suka sakata suna mata video ta amsa duk abinda ake tuhumarta dashi harda dalilan ta da ya sakata aikata komai daga nan suka mayarda ita se yanzu aka sake dakko su.

Kowacce na ganin idon iyayenta ta fashe da sabon Kuka, Hajiyar Khalil ta shiga tafa hannu kwalla ta kawo mata tana cewa
"Na shiga uku ni Aisha kalli yanda kuka mayar da yarinya a dare daya fisabiliklahi bakuda tausayine baku ganin halin da take ciki me tayi muku?"

"Idan baki rufe mana baki ba Hajiya zaki fita daga nan, ita ce bata tausayin kanta da har ta jefa kanta a wannan halin kinga kuwa babu abinda ya shafe mu" daya daga cikin Jami'an ya fadawa Hajiyar a dake dole ta kama bakinta tana share kwallar tausayin Umaimah.

Bayani Detective Adnan ya farayi akan bincike ya kammala ga kuma sakamakon da suka samu dan hak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a yanzu sun gama cike duk wasu takaddau da suka kamaya zasu turasu kotu kowanne yaje ya nemi lauya dannan zasu ci gaba da tsare su ne a hannunsu ba wai zasu barsu su tafi gida ba. A tare Su Umaimah suka fashe da mugun kuka kowacce ita kadai tasan azabar data dandana adare dayan nan inaga ace zasu ci gaba da zama anan kawai mutuwa zasuyi.

"Dan girman Allah Khalil ka saka baki ka bata haquri wallahi ni ba laifina bane gata nan wannan ce ta sakani ni banma taba ganinta ba se yau itace ta shirya komai tunda an ganta su kyale mu, wallahi na qara kwana a nan mutuwa zanyi, daman nasan dan cikina ya mutu dan tun jiya na dena jin motsinsa" Umainah ta da cikin matsanancin Kuka tana kallon Khalil da shi kuma Hadiza yake kallo wadda itama kukan takeyi tana jingine jikin Hajiya Barira.

"Ballantana kuma ni da bansan komai ba ai tsakanina dake Umaimah se Allah ya mana hisabi kuma bazan taba yafe miki ba, dan Allah Yaya Abubakar kasa baki a barni na tafi tunda dai ni babu ruwana tsautsayine kawai ya shigar dani" Rufaida ta fada itama cikin kuka, Khausar dai babu baki kanta yana qasa ta kasa hada ido da kowa a gurin. Tsawa Detective ya daga musu sukayi shiru gaba daya ya kalli Musa Kallah yace
"Yanzu magana tana hannunku, kamar yanda na fada mun gama cike takaddu gobe zamu turaku koto. Kuma duk wata shaida da ake da buqata muna da ita a hannu ya rage nasu su nemi masu kare su ko akasin haka dan haka ina ganin mun gama wannan zaman kowa ze iya tafiya" Kafin Musa Kallah yace wani abu sukaji muryar Hadiza cikin kuka tana cewa

"Indai har saboda ni ne da abinda sukayi mun na yafe musu har gaban Abada ku barsu su tafi gida"
"Akan me zakice kin yafe musu, beside ai bama ke kika shigar da qara ba ballantana kice zaki janye" Yaya Isma'il ya fada a fusace kamar ze kai mata duka. Tun a hanya ya ringa kafa mata kashedin karta kuskura tayi wata magana indai bata neman haqqinta ba daman Mama bata biyosu ba tareda Hajiya Barira suka zo shine yanzu zatace ta yafe ai kuwa baze sabu ba.

"Amma duk abinda mukeyi saboda ita ne kuma tana da damar da zata janye ko jaddada qarar nan dan haka idan tace ta yafe musun magana ta zauna za'a janye qara, sedai idan akwai wani bangare da abinda suka aikata ya taba ko ya janyo masa wani damage to wannan suna iya shigar da qara tareda hujjoji na gaske" Musa Kallah ya fada yana kallon Hadizan seta sake daga kai tace

"Na yafe musu nidai"
"To wallahi bazasu tafi haka kawai ba, bacin sunan da suka jawo mana se sun koma duk inda suka bata ta sun wanke abinda sukayi su fada da bakinsu cewar Qazafi sukayi mata" Yaya Isma'il ya sake fada cikin hasala yana hararasu su ukun, gaba dayan mutanen gurin da suka cika da tausayin da Mamakin Hadiza bisa wannan abu da tayi sukayi na'am da maganarsa. Kafewa yayi akan sedai a kira taron yan jarida su dauki komai Musa Kallah yace Aa, kamar yanda suka yada wancan a waya ya zaga ko ina yanzun ma haka zasu maimaita da bakunansu ta hanyar video bama rubutu irin wancanba nan take aka kawo Camera da professional me hoto ya fara daukar video.

Babu bakin musawa dan a iya adalci sun san anyi musu su ukun suka jeru kowacce aka dauketa tana bayanin duk abinda ya faru da role din da tayi playing a cikin lamarin. Kasa rufe bako Hajiyar Khalil tayi sanda take jin kan zancen na gaskiya dan ita Abokin Khalifa gaya mata yayi wai fada sukayi da maqociyarta shine aka kamasu ta girgiza kwarai da jin lamarin, badan da kunnenta take ji Umaiman tana maimaitawa abinda ya faru ba da wallahi ba zata taba yarda zatayi haka ba. Haka aka gama daukarsu Video akayi rubutu kowanne bangare suka saka hannu na anyi musu tsakani babu au babu Hadizan. A take aka sallami Umaimah da Rufaidah babu wadda ta kalli Yar uwarta kowa tayi ta kanta Khausar kuwa ciki suka maidata saboda sun bude mata sabon case ita da saurayinta da yake can a garqame Wanda ashe qundumemen case ne akansa ana suspecting informa ne na yan Kidnapping kuma an dade ana bibiyarsa se yau Allah ya basu sa'a akansa a ka kamoshi ba tareda yayi zato ba.

Mahaifinta yanke jiki yayi ya fadi dajin wannan sabon tashin hankali, ragowar kowa ya kama gabansa banda Isma'il da be bar gurin ba seda aka tura masa copy na video confession dinsu Umaimah be kuwa bata lokaci ba gurin uploading nasa a Media kan kace kwabo labari ya yadu a ko ina.

Daga CID Asibiti aka zarce da Umaimah, Hajiyarsu Khalil dai kasa magana tayi haka shima ya zama kurman dole ya rasa abinda yake ji a ransa. Yaji dadin wanke Hadiza daga zarginda ake mata da akayi amma yayi baqin ciki da takaicin wai matarsa ce aka dauki video ta tana fadar abinda ta aikata idan ya tuno abinji yakeyi kamar yayi bindiga ya fashe shi yasa koda suka tashi tafiya ya dauki su Hajiya kamar yanda sukazo ita kuma yan gidansu suka tafi da ita. Be taba nadamar auran Umaimah ba irinna yau, yayi nadamar zuwansa gurin Nasir da har ya janyo haduwarsa da ita amma qaddara ta riga fata. Yanzu babu abinda yake ganin zeyi ya goge baqin cikin data qunsa masa ya kuma biya Hadiza bacin sunan data ja mata kamar ya auro ta su zauna tareda Umaimah kuma babu yanda ta iya da ita.

Yana ajiye su Hajiya be tsaya na ya juya dan be samu damar magana da Hadiza ba a can gurin qudurinsa kuma baya so ha dauki lokaci idanso samune kafinya koma SA yake so a daura musu aure su tafi tare idan yaso kafin ya dawo Umaimah tayi bunga ta mutu tsabar baqinciki. Hanyar gidansu Hadizanya dauka a ransa yana addu'ar Allah yasa ta aminta da maganar sa ba taredabata lokaci ba.
"Zama ta amince saboda Hadiza tana tsananin Sona" ya bawa kansa tabbaci da kwarin guiwa.

Acan Asibiti kuwa Emergency aka karbi Umaimah, Ruwa suka fara daura mata kafin suka bata duk wani taimako da takeda buqata sun kuma tabbatar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login