Showing 270001 words to 273000 words out of 429394 words

Chapter 91 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

922

ta kula shi ba. Haka ta qarasa daren cikin shirya irin rashin mutunchin da zataje tayi a gidansu Mansur kafin daga bisani ta dawo kan uban gayyar dan ba raga masa zatayi ba.

Washe gari fuska a washe ta farka abinda ya matuqar daurewa Khalil kai ganin da kanta ta shirya masa abin kari kai bazaka ce wani abu ya faru jiya ba. Kallon abincin ya ringayi ya kasa ci, kwanaki yaji an ce wata ta sakawa mijinta maganin bera a abinci sabida ze mata kishiya wannan tunanin ya hanashi taba duk abinda ta ajiye din har seda ta zauna ta zuba nata ta zubawa yara suka fara ci kafin ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga shima.

"An jima zamu fita, yau zumunchi nake ji zamuje mu gaida Hajiyar su Mansur wlh na manta rabon da naje gidan tun jiya kawai take fado mun a rai" ya ji maganarta a tsakiyar kansa ai be san sanda ya kware ba ya shiga tari baji ba gani Umaimah na tsaye kansa harya lafa zagi ta dura masa su a zuciyarta sunfi kala dubu, ya dago ya kalleta da idonsa da sukayi ja saboda kwarewar da yayi yace
"Gidansu Mansur kuma yau? Sau nawa nake ce miki kije ki gaishetan kike qi se yau zakije zakije?"
"Toh dai qorafi ya qare yanzu dai yau zanje kuma daga yanzu in sha Allah zan ringa leqawa ina gaidata ai Mama nada kirki nice ma da naqi Sakin jiki da ita" ta bashi amsa tana komawa gurin zamanta. Shiru yayi, yasan dai baze yuwu ace tasan wadda yake nema ba amma kuma baze so taje gidan ba saboda gujewa sammatsi yanzu idan ya hanata nan na ya saka kansa a matsa dole tabi ba'asin dalilin hanawar to shi yaya zeyi yanzu?

Haka ya qarasa tuttura dankalin data zuba masa ya fita tareda yara da ze sauke a makaranta bayan ya bata kudi akan ta bawa Maman idan taje.

Ko Awa daya beyi da fita ba itama ta fice bata kuma zame ko ina ba se gidan su Mansur. Mama na zaune A tsakar gida ta kunna Radion ta tana ji Humaira na kitchen tana hada musu abin karyawa Umaiman ta fada musu kamar dirar Kirsimeti.
"Subhanallahi waye haka?" Mama da yanda a bugo qofa ya tsoratat ta fada tana miqewa, ganin Umaimah tsaye yasa ta saki ajiyar zuciya tace
"Au kece tafe da safiyar nan qaraso ciki mana kika kafe a bakin qofa".

"Ba zama ya kawo ni ba baqar Annamimiya mara tsoron Allah, wato saboda tsabar son zuciya da kwadayi dan kinga Allah ya horewa Mijina abin duniya shi yasa kike so ki laqaba masa wata shegiya da ba'asan Asalinta ba ko ku dandali arziqi? Bautar da Ubansa yayi muku da wadda shima yayi da Danki duk bata isheki ba se kin hadashi aure da yarki? To bari kiji Hauwa na rantse da wanda yake busa mun numfashi babu wanda ya isa yayi wannan hadin, idan kuma kince se anyi to ki tabbata kin hado ta da Likkafani da duka sauran kayan jana'iza dan kuwa daren da aka kaita cikin gidan Khalil a kabari zata qarasa shi".

Qarar kwanuka da suka zube ta saka Mama da Umaiman waiwayawa suka kalli Humaira dake tsaye qofar kitchen ta zubar da kwanukan data fito dasu saboda tsorata da ganin yanayin Umaimah da kuma maganganun da take fada jikinta se rawa yake kamar wadda Sanyi yake kadawa.
Wani banzan kallo Umaimah ta bita dashi sama da qasa kafin ta tabe baki tace
"Da alama wannan kazar kike shirin liqawa Mijina? To ki bar murna aikin Bokanki yaci dan nasan idan ba Asiri ba babu abinda ze burge Khalil a jikin wannan abar me kama da Muciya a tsaye ina tabbatar miki da duk abinda kikayi sena warwareshi, ke kuma idan kina son kanki da lafiya wallahi ko a mafarki karki qara tunanin Mijina dan idan ba haka ba ni nan se na zama Ajalinki, sena lalata na balbalta rayuwarki ta yanda har ki mutu kina danasanin sanin Khalil a duniya kiji da kunnenki ni nan Umaimah na isheki" tana kaiwa nan taja wani matsiyacin tsaki ta juya zata fita Mama ta tareta da cewa

"Mungode kwarai da ziyara, amma ina so ki sani shi aure lamarin ubangiji ne duk kuma wanda yace ze dakatar da faruwarsa rabo yana iya kashe shi ayi ko bayan ransa, ke yarinya ce har yanzu baki gama sani inda yake miki ciwo ba a rayuwa dan haka kibi a sannu" tana gama fadar haka ta kalli Humaira da Hawaye su ke mata zarya a fuska tace
"Wuce muje ciki" nan suka bar Umaimah tsaye kamar wadda aka dasa kafin taja qwafa ta sake ficewa fuuu tana shan alwashi kala kala akan Maman da Yarinyar, abun da yazo mata a rai shine fuskarta ta rudeshi dan haka dole ta dauki matakin lalatata ta haka ne zata sake kareshi daga dukkan wasu Mata ko Iyayen yara masu kawo masa tallan Yayansu.

A cikin gidan kuwa suna shiga palour Mama ta kalli Humaira dake kuka tana yarfe hannaye tace
"Yi mun shiru sakarya, idan wannan dan kurarin nata ya firgitaki ta ya zaki iya zama da ita a matsayin kishita kuma a cikin gida daya? Dole ki bude baki ki kuma cire duk wani tsoro da sokonci daga ranki ki kwatarwa kanki yanci dan daga sanda tasan kina tsoronta ta samu hanyar Azabtar dake".

"Ni wlh Mama bazan aure shi ba daman na gaya miki kece kika dage akan sena na amsa masa kin gani yanzu tun ma ba'ayi auran ba tazo tana cewa zata kasheni idan kuma aka kaini can daga ni se ita fa baki san abinda zata mun ba sedai kawai a kiraki ace kizo ki dauki gawata" Humaira ta fada tana sake rushewa da kukan tashin hankali. Tsaki Maman taja ta zauna akan kujera tayi shiru tana tunani, tabbas seta koyawa Umaimah hankali kuma zata tabbatar bata zageta a banza ba, setayi mata bazatan da zata girgiza har ta kusa rasa hankalinta. Ganin Humairan nata kuka yasa ta janyota jikinta ta shiga lallashinta.

"Kiyi shiru kinji auta karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki kishi ne yake damunta amma babu abinda zatayi mki. Kuma ma ai ba gida daya ze ajiye ku ba na sani kinga babu ruwan kowa da yar uwarta balle har wani abu ya hadaku ma kedai kawai kici gaba da Addu'a Allah ya tabbatar miki da Alkhairi tunda kina sonsa yana sonki ai magana ta qare babu ruwanki da wata matarsa" Maman ta fada tana shafa kanta seta dago da guntun Hawaye tace

"Nidai Mama na haqura ni daman ba wani sonsa nake ba gara na auri Noor dina na zauna ni kadai babu me daga mun hankali"
"Humaira kenan, shikenan tunda kince haka amma kina da tabbacin idan kin auri Noor din shima wata rana baze qaro miki wata irinta ba? Koma bashi ba duk Wanda kika aura dayan biyu ne ko ki tarar ko tazo ta tarar dake kuma baki sna Mijin ba ko ya zamana matar ce takr juyashi kinga wahala zaki sha. Wannan kuwa kin sanshi kin san komai nasa na tabbatar baze taba bari ta cutar dake ba kefa da kanki kike bani labarin Yanda Ibrahim yake riritaki da alqawarin da yake miki idan kunyi aure"

Saurin rufe ido tayi alamar kunya, duk hirar da sukayi seta bawa Maman labari dan haka ta koya mata ta dauke ta kamar qawa tana hira da ita a haka take sanin duk abinsa take ciki na daidai ta qara dorata akai na kuskure ta gyara mata.
"Toh kin gani shine kuma kike so ki bar mata ita kadai ta shanye duk soyayyar nan da akayi miki alqawariz ita kanta kishin da takeyi kenan bata so kizo kiji dadin da takeji a gidan shiyasa fa take wannan kururuwar ba wani abu ba so take ta tsorata ki ki bar mata mijinta ita kadai kuma duk mata haka sukeyi amma da anyi auran zaki ga ta saduda ta haqura tunda babu yanda zatayi".

Haka taci gaba da lallabata tana bata baki tareda qara mata qarfin guiwa tana bata misalai akan wasu mutanen sannan taja mata kunne akan koda wasa karta gayawa Khalil zancen zuwan Umaiman gidan. Sefmda ta saki ranta kafin ta fita ta gyara barin da tayi ta shiga hada musu wani sabon abin karin amma fa can qasan ranta cike yake fal da tsoron Umaiman. Bata son Hayaniya a rayuwarta ita bata iya fada ba sannan ace za'a hadata kishi da wannan matar da take cewa zata kasheta gaskiya bazata yarda ba kawai tayi shiru ne bata musawa Maman ba amma dole daga baya a san abinyi tana son rayuwarta bazata kai kanta Mahallaka tana sane ba.


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 62

HUMAIRAH
Duk yanda taso ta gujewa Khalil din da auransa ya gagara saboda wata irin sabuwar kulawa da tattali da yakeyi mata suka rufe mata ido take jinbazata iya rabuwa dashi ba. Soyayya yake gwada mata irin wadda take mafarkin samu a gurin Noor dinta, kuma kamar yanda takejin ana fada idanka auri Yaro kafi samun soyayya sabanin babba da ze ringa ganin kamar bata lokaci ne sedai a yanzu da ta hadu da Khalil ta qaryata hakan. Kamar yanda Mama ta kwabeta da karta gaya masa zancen zuwan Umaimah gidan haka kuwa akayi bata gaya masa ba, shi ya ringa insisting akan ta yardar masa yaje can Jalingo ya gaida Dangin Mahaifinta dana Mahaifiyarta amma taqi saboda ita duk lissafinta fa babu maganar aure a yanzu, so take su ci gaba da soyayya kawai yana lallabata yana sangartata har zuwa ta shiga Jami'a ta gama Kafin sannan Noor dinta shima ya samu abinyi se suyi auransu dan fa bajin zata auri Mijin Umaimah ta kasheta a banza tayiwa Iyayrnta a sarar meyi musu Addu'a bayan ita kadai suka haifa.

Ranar da yamma suna zaune da Mama a tsakar gida suna shan iska saboda garin ya dauri da zafi gashi babu wuta, a kishingidr take suna chat da Khalil da ya tafi Anambra yana tsokanarta wai zeyo mata tsabar garin kwaki da kwakwar manja tana dariya Mama ta kalleta tace
"Wai ni dariyar me kikeyine tun dazu kamar wata tababbiya kina danna waya?'
Seda ta bashi amsa kafin ta tashi zaune sosai tana kallon Maman fuskarta da murmushi tace
"Nida Yah Khalil ne Mama, wai tsarabar Garin kwaki zeyi mun shine nace bana so".

"Kiji sokuwa aikensa kikayi da zece ze kawo miki abu kice bakyaso in banda rashin wayo aiko qasar garin tax and qullo a leda ya kawo miki godiya zaki masa ba kushewa ba. Ni da ace ma magana tayi qarfi ai inaga gidan Unaizatu zaki tafi ki zauna can tayi miki karatun aure da zama da kishiya dan da wannan salubancin naki kam wuya zakije kisha Mijin ma baki san yanda zaki tarairayeshi ki kula dashi ba balle azo ga batun kishiya" Mama ta fada tana kallonta, seta tura baki tace
"Nifa Mama ki dena mun fatan zama da wata kishiya, shiyasa ma da Yah Khalil din yake ta wani cewa zeje Jalingo nace masa ba yanzu ba, haka kawai ni jira nake Noor ya samu aiki kawai muyi auranmu bazan iya ba taje ta zauna da Mijinta ita kadai".

Kallonta Maman take harta kai qarshe kafin ta girgiza kai tayi kwafa kawai bata ce mata komai ba. Noor din da tun ran da wancan abun ya faru be sake zuwa gidan ba tana lura da ita kuma kullum ta kirashi baya dauka har takadda ta bawa Amir yaron maqontansu ya kai masa jiya tana zaune Humairan ta fita Islamiyya ya dawo da ita wai yaqi karba shine take lissafi akansa ko to zataci qaniyarta kuwa tunda ita ta hana Khalil din zuwa to da kanta ita zata bashi umarnin yaje ya nemi auran kawai dan ta qudurcr seta nunawa Umaimah ba ita kadai bace yar banza, kuma ita shirme takeyi da hauka aure da yardar ubangiji se anyi shi se dai in ta hadiyi zuciya ta mutu.

Washe garin ranar kuwa da dare sega Khalil yak gurin Humairan, da Maman suka fara gaisawa ba kuma tayi qasa a guiwa ba ta bude masa magana akan idan da gaske yakeyi tofa ya kamata manya su shiga ciki harta qara masa da cewar a can garin nasu akwai Yayan dangi da ake so ayi musu hadin zumunta da Humairan dan haka idan ya tsaya sanya ze iya rasawa da wannan maganar ya bar gidan yana fita ya shiga kiran Mansur da tunda maganar sa da Humairan ta fita ya shiga gaba dashi. Takanas ya kirashi ya gaya masa magana akan ya kyale musu qanwa baze aureta ba tun kuma daga wannan wayar idan ya kirashi ma baya dagawa dan ya gaya masa in dai ba ya janye ba tofa zasu samu matsala dan baze zuba ido a hada yarinya da Umaimah ta lahanta ta ba.

Gida ya wuce, dukda dare yayi dan goma ta wuce amma ya shiga bangaren Hajiyarsa. Habiba ya tarar a palour da Halima me aikinsu suna kallo ga Mu'ayyad na bacci a qasan carpet suka gashe shi gaba daya ya amsa yana tambayarta Hajiya fa tace tana daki jin haka yayi tunanin tayi bacci seya juya Habiba ta tareshi tana cewa
"Ba bacci take ba Yaya yanzu na kai mata shayi zata bawa Bibi idonsu biyu".
Juyawa yayi ya hau saman. A dakin ya samu Hajiyar ta gama bawa Bibi shayin harta kwanta ita kuma tana ninke kayan data cire da alama itama kwanciyar zatayi.

A kan one sitter dake dakin ya zauna yana sake gaisheta ta ajiye kayan hannunta ta zauna tana cewa
"Babana baka kwanta ba, da alama ma yanzu ka shigo gidan?"

Kansa ya shafa yace
"Eh wlh Hajiya naje gurin Humaira ne daga can kuma na tsaya wani guri s yanzu na shigo"
"Toh ya suke? Ya Hajiya Hauwan? Kaga inata zuci zucin na kirata tun ranar nan da mukayi magana Allah beyi ba ni da naji shiru daga bangarenka dana Matarka ma.na zata kun daidaita maganar ta wuce ne ashe kana kan bakanka" Hajiya ta fada seya dagao ya kalleta yace

"Wace magana kenan Hajiya?"
"Maganar auran naka mana tun waccan ranar bata sake tada maganar ba kuma naga ta shiga sabgoginta kamar babu abinda ya faru"

"Toh nima dai haka na gani kuma bata sake mun magana ba, dukda dai gaskiya nima tun waccen ranar ban sake tada mata da maganar ba yanzu ne dai nake so nayi mata saboda dazun da naje Mama tace mun ya kamata Nayi magana idan da gaske nake aje a samu iyayen Humairan abinda ya kawoni yanzu ma kenan na gaya miki saboda ki sanarwa dasu Baba Abu se su saka ranar da zasuje ayi shirye shirye kinga tafiyar da nisa".

Kallonsa Hajiya ta ringayi har ya kai qarshe kafin ta sauke ajiyar zuciya tace
"Babana dagask dai kake da maganar aurannan, ni da zaka bi ta tawa da ka haqura da matarka ita kadai yanzu kuna zamanku lafiya so kakeyi ka dakko wata da zata zo ta jawo maka tashin hankali da damuwa...."
"Hajiya" ya kira sunanta cikin marairaicewa abinda yasa ta dakata da maganar da takeyi kafin yaci gaba da cewa
"Dan Allah Hajiya na roqeki da ko saka albarka a abun nan ki dena yi mun fatan tashin hankali ko damuwa. Hajiya ni nake zaune da Umaimah ni nasan dadinta ko akasin haka tunda har nazo miki da buqatar ina son qari ki barni dan Allah".

"Shikenan Allah ubangiji ya tabbatar da Alkhairi yasa ayi a sa'a, amma ina so kafin a kai ga yin magana ka fara sanar da matarka tukunna, idan ta karbi abun ta fuskar limana shikenan idan kuma ba haka ba dole a qara lokaci zuwa sanda abubuwa zasu qara sauqaqa kaga ita ma kafin nan yarinyar ta qara girma se ayi komai cikin dadin rai da kwanciyar hankali" Hajiyan ta sak fada, ajiyar zuciya yayi yana kallon qasa yace mata
"In sha Allahu babu abinda zero faru is Alkhairi, yanzu dai ki sanarwa da Baba Abun duk abunda suka yanke shikenan" ya sak jaddada mata dan gaba daya kalaman na Hajiya yau jinsu yakeyi akwai son kai a ciki, yanda kasan Umaimah ta haifa ba shi ba yanzu tana nufin kenan seda Amincewar Umaimah zeyi aure idan ba haka ba sedai a fasa kenan.

Sallama yayi mata ya wuce bangarensu, a falon qasan ya tarar da Umaimah tana kwance a qasa tana danna waya. Ba yabo ba fallasa ta amsa sallamarsa tareda yi masa sannu da zuwa, daga kwancen ta nuna masa Dining inda abincinsa yake ya wuce ya zauna yana duba abinda suka dafa. Gurasa ce da gasashshan nama se kunun Aya ga Qaramin flask na Tea dinsa an ajiye ya zuba abinda ze iya ci yayi bismillah ya fara lokaci lokaci yana kallon Umaiman dake kwance har sannan a zuciyarsa yana ayyana ta yanda ze sanar mata da zancen auran har ya gama ya tashi daga gurin. Kusada ita ya koma ya zauan ya dauki remote ya chanza tasha zuwa labarai ya tsurawa Tv ido badan yana fuskantar abinda ake cewa a ciki ba yana nan zaune se ji yayi tana masa sallama zata shige daki, miqewa tsaye yayi shima gaba daya bakinsa ya masa nauyi yana nan tunanin me zece mata harta shige ta kullo qofarta seya sauke ajiyar zuciya ya kashe Tv ya haye sama shima dan tuni Ruqayya ta kwashe kayan abincin daya gama.

A daren kasa bacci yayi, kwana yayi yana saqa da warwarar yanda ze gayawa Umaimah zancen auran nasa daga qarshe ya yanke shawarar komawa ya sake samun Hajiya ya lallabata ita ta gaya mata dan gaskiya yana shakkar kallon idonta yazo mata da wannan zance be san a yanda zata dauki al'amarin ba yasan idan Hajiyar ce zata fi fahimtarta akansa.

UMAIMAH
Tun bayan da taje tayi tijara a gidansu Humairah ta kwantar da hankalinta dan gani takeyi barazanar da tayi musu ta isa ta saka a fasa auran musamman da Khalil beyi mata maganar ba kenan sunji tsoro basu gaya masa ba qila dai an rusa maganar to koma dai menene ita dai tayi abinda tayi cansu gane ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login