Showing 18001 words to 21000 words out of 429394 words

Chapter 7 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

927

baki dafa ba amma kece farkon ci koh? Toh idan kin gama kije ki gyaramun daki" Maman ta fada tana qare mata kallo.

Ajiyar zuciya tasaki dan a zatonta fada maman zata mata tace toh, seda ta qoshi ta kora da zobonta me sanyi ta huta kafin ta tafi dakin maman.

A palour ta tarar da ita da wata baquwa sun baje kuloli masu kyau suna dubawa da alama talla ta kawo mata dan se koda mata su take, gaishe da baquwar tayi ta shige ciki ta fara gyarowa, tana jiyo baquwar tana cewa Maman

"Hajiya na zata saiti bibbiyu zaki dauka tunda yan matan naki biyu ne ko"

"Aa yanzu dai dayan zan dauka ita wannan da saura idan lokaci yayi a siya" Maman ta bata amsa

"Ai kuwa da kin siya kin huta dan kinsan kullum qara kudi kayan suke abinda ka siya dubu daya yau gobe idan kika koma se kiji daya da dari biyar koma dubu biyu, wannan hauhawar fara shi dai Allah ya mana maganin sa" matar ta sake fada. Murmushi Mama tayi tace

"Yanzu dai bari na dauki na dayar da nayi niyya ita ce me garanti, wannan kinsan sau nawa ina mata tarin kayan kitchen? Da takaici ya isheni fitar dasu nayi na rabawa yan uwanta wasu na biki dasu duk randa Allah yasa ta tsayar da hankalinta ta fitar da Miji a kaita da abinda ya sawwaqa"

"Allah dai ya rufa asiri, in sha Allahu ma tareda yar uwarta zaki saka su a Lalle".

Baki Umaimah ta tunzura gaba, wayasani ma ko irin wadannan maganganun da maman take a kanta ne suka hana mijin tsayuwa ita kullum me laifi ce a idon Maman, Allah dai ya yanke mata ta tafi itama kowa ya huta a sannan zaa gane amfaninta ai.

Haka ta gyaro dakin ta wanke Bandaki tsaf lokacin matar sun gama ta wuce se Maman ita kadai tana waya da wanda yake kawo mata Manja daga Kudu da yake tana siyar da Manja da Mangyada, hannun kujera ta nema ta zauna tana jiranta harta gama.

"Ya akayi?" maman ta tambayeta,
"Na gama gyara ciki saura nan"
"Toh bismillah mana ko na hana kine" Maman ta sake fada, seta miqe ta shiga tattare kwalayen tace
"Ina zaa ajiye wadannan kayan toh"

"Saka su can dakin" Maman ta nuna mata dayan dakinta data mayar dashi na aje shirgi Wanda da Su Umaimah suke ciki kafin Yayyensu suyi aure su koma dakin da suka bari na tsakar gidan. Bude dakin tayi ta shigar dasu,

"Mama duk kayan can Yaya Nuratu zaa jibgawa su? Toh Allah yasa dai ta samu gidan da ze dauka koda yake ma gidan quaters ne ai kin ma san yanda suke sedai idan an a tafi dasu a dawo da wasu a san dai kin mata kaya da yawa kawai" Umaiman ta fada tana kade kujeru, da kallo kawai Maman take binta, a ranta tana nema mata shiriya daga gurin Allah dan lamarin nata kullum qara gaba yake.

Bata damu da shirun da Maman tayi ba taci gaba da cewa
"Qilama ni da bakya ta tawa na fita samun babban gida, kinga lokacin ai a tasheki a tsaye ki rasa yanda zakiyi"

"Allah baze hanani yanda zanyi ba dan ubanki keda bakinki sam besan abinda ze fada ba, fita ki bani guri na fasa gyaran daman idan baki yi niyyar abu ba se kin san yanda kika jangwalo aka ce ki barshi" Maman ta fada kamar zata kai mata duka, Dariya ta sheqe da ita ta shiga cewa

"Haba Hajiyar mu easy mana, nifa wasa nake miki. Yo ko yanzu aka ce a fito Hajiya ai a shirye kike Allah dai ya bar manake Hajjaju".

Ganin da Mama tayi tana neman mayar da ita wata abin tsokana yasa ita ta bar mata dakin ta koma tsakar gida inda inuwa ta dan fara sauka suka shiga hira da Anty Saratu.

Umaimah ko tas ta gyara dakin ta goge ta saka qamshi, tada zafin nama idan ta saka kanta ta iya aiki sosai dan wannan horon Mama ne duk yaranta seda ta tabbatar da ta horasu yanda duk inda sukaje bazata ji kunya ba, daman Umaimace me son jiki a ciki, amma idan ta tashi yin aikin kuma zatayi shi dakyau.

Dakinsu ta koma ta kwanta kafin rana tayi tana so taje kitso, tana hawa kan gadon wayarta dake jikin chaji ta fara qara, kamar bazata daga ba se kuma ta janyo ta ta amsa kiran ba tareda tayi magana ba.

"Amincin Allah ya tabbata a gareki" Aka fada da muryar da tanaji ta gane waye, murmushi ne ya kufce mata,
"Tareda kai, ina fatan kaje gida lafiya?" Ta bashi amsa.

"Ban sani ba, da kin so kiji aike zaki kirani ba se yanzu dana kira zaki tambayeni ba" Khalil ya fada daga dayan bangaren,

"Thats remind me, a ina ka samu number na?" Umaimah ta fada tana gyara kwanciyarta da kyau akan Gadon,

"Baqauya kawai, wayace miki har yanzu ana tambayar ina aka samu number budurwa ne"

"Ni ba baqauyiya bace" ta fada a sakalce tana tura baki, akan me zece mata baqauya, ita da take yar tsakiyar birni bama shi dan bayan badala ba.

"Toh yi haquri yar birni" ya fada yana dariyar yanda tayi maganar kafin yaci gaba da cewa,
"Dadin tuqina ya saka kin manta da folder credentials dinki, kinga da a commercial car ne da yanzu se ki tafi gidan redio cigiyan wanda ya tsinta".

Dafa baki Umaimah tayi tana tashi zaune tace
"Subhanallahi, wallahi na manta shaf kuma ban lura ba. Dase nazo daukar wani abun sannan ne zan ga babu su"

"Daman kinji tuqin babban Driver ina zaki tuna" ya sake fada cikin sigar tsokana, seta mayar masa da cewar

"Babu wani nan, bayan nama fika iya tuqin kanayi a hankali kamar me tsoron hanya"

"Oh haka kike ce? Toh next time idan mun hadu za'a gwada se muga wanda yafi wani iyawa"

"Allah ya kaimu zan kuwa baka mamaki" ta fada cikin tabbatarwa bayan a zahiri inda ake takawa ma mota tayi tafiya bata sani ba, ba kuma dan babu inda zata koya ba Aa koda basu da Mota a gida banda ta Abbansu amma Yayyenta mata masu aure kowacce nada motar hawa, ita dan karambanin nan ma yasa ta hau bata taba ba tafi gane ta kame a kujera a jata.

Hira suka danyi kafin ya mata sallama da cewar idan ya samu dama zuwa dare ze kawo mata, idan kuma bezo yau ba se dai zuwa Litinin dan washe garin juma'a zeyi tafiya zuwa Dutse akwai aikin da sujeyi acan kuma se ranar Lahadi ze dawo.

Wannan waya da sukayi ba qaramin nishadi ta saka Umaimah ba, ta ringa walwala, su kansu mutanen gidan seda suka ringa tambayarta Albishir din me ta samu da take farin ciki haka sedai tayi murmushi tace babu komai.

Be kawo mata a daren ba, ai kuwa baqin ciki ya mata dirar mikiya ya shafe walwalar data wuni a ciki dan tun magriba ta fesa wanka dukda batayi kwalliya ba amma ta saka kaya da suka qara haska tah tayi fes, shiru har akayi isha babu shi babu kiran wayarsa tun tana zuba ido qarshe se jiyo radion da Abba ya kunna tayi a tsakar gida ana wani shirin siyasa da yake ji qarfe Goman dare.

Ita kadai ta ringa zuga tsaki tana juyi a gado, kamar ta kirashi amma in ta tuna daman ya gaya mata ba lallai yazo a yau din ba se ta Kanne, yanzu har se ranar litinin zata sake ganinsa kenan? Wannan abu ya mata ciwo da yawa.

Haka ta cinye weekend gashi ko a waya be kirata ba, sundai yi magana ta whatsapp ta saka status ya duba suka gaisa daga nan be sake ce mata komai ba.

Ranar Litinin bayan magriba suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shiga
"Wai ana sallama da Umaimah a qofar gida" yaron ya fada, se tayi tsam daga abinda takeyi ta kalle shi. Wane dan rainin hankalin ne ze aiko sallama da ita? Tasan dai duk masu zuwa gunta se sun kirata a waya shi wane isashshen ne haka da ze aiko ba tareda tasan da zuwan sa ba.

"Kaje kace ba ta nan" ta fada se Mama tayi saurin dakatar dashi tana hararta tace
"Je ka tambayo wane ne kace tana zuwa"

"Mama fa ni bamuyi da kowa ze zo gurina ba kawai se a aiko kice ace ina zuwa indai mutumin kirki ne ai seya fara sanar dani kafin yazo" ta fada kamar zatayi kuka dan tasan tabbas baze wuce irin yan yawar samarin nan masu bi gida gida suna sallama da yammata ba.

Banza Mama ta mata taci gaba da lazumin da takeyi, sega sallamar yaron ya sake dawo yace "wai Khalil ne, kuma yace sauri yake yi kizo ki karba saqon".

"Khalil?" Ta fada a fili tana kallon yaron kamar shi ze bata amsa kafin ta shiga qarewa kanta kallon, Zani ne da T shirt a jikinta tunda tayi wanka da La'asar ta sakasu se qaurin manja takeyi saboda suyar wainar fulawa take a lokacin. Miqewa tayi ta nufi daki, Mama da tunda akace Khalil ta zuba mata ido tana so ta tuno ina ta taba jin Umaimah ta ambaci sunan tana tunanin Umaiman ta fito ta chanza kayan jikinta zuwa baqar doguqar riga ta yafa mayafinta,

"Mama bari na karbo, credentials dina na manta ranar a makaranta shine ya kawo min" ta fice da sauri.

Su biyu ta gani tsaye jikin mota sunsha kwalliya kamar masu zuwa gurin daurin aure,
"Allah yaso ki kin fito, yanzu na ke shirin neman wani yaron na bashi ya kai miki se fa dana ce wancan ya gaya miki sauri nakeyi" Ya fada bayan data gaishe su, harar wasa tayi masa kafin tace

"Sauri zuwa ina? Kun wani sha shadda kamar masu zuwa tambayar aure"

"Kin canka daidai tambayar aurana zamu je, saurin da nakeyi kenan saboda baban yari yar qarfe 8 yace muzo kinga be kamata tun yanzu na fara sabawa sirikina lokaci ba" Khalil ya fada yana miqa mata Folder da kuma wata farar leda me dan girma.

Idan tace tayi suman wucin gadi batayi qarya ba dan daga can sama ta ringa jin muryarsa yana ce mata
"Ki karba mana, kin tsaya kina kallona karki sa na rage kyau kafin naje gurin Amaryata".

'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' tayi nasarar furtawa a fili kafin ta tafi tamkar zata kifa yayi saurin tarota, a rikice ya shiga jijjigata yana cewa
" Umaimah Umaimah ke Umaimah lafiyar ki kuwa? Mansur shiga gidan na kayi sallama dan Allah muji ko daman bata da lafiya" ya fada ganin tana lumshe ido kamar me shirin tafiya dogon suma.

Abokinsa Mansur daya yi mutuwar tsaye ya zura da gudu zuwa cikin gidab su Umaimah se ganin mutum kawai sukayi, a taqaice ya kalli Nuratu da Salima babbar Yar Anty Saratu yace "kuzo dan Allah" kafin ya juya ya fice,ai gaba daya suka rufa masa baya harda Anty da Maman tunda basu san me ya faru ba.

Hango Umaimah dake riqe a hannun Khalil ya qara daga musu hankali suka isa gurin da sauri, Anty ce ta karbeta Nuratu ta taimaka gurin qara kamota suka riqeta dakyau suna tambayar sa meya faru

"Wallahi Hajiya bamu sani ba, lafiya lau ta fito na miqo mata kayan nan(ya nuna kayan da suka watse a qasa tun daya taro ta kafin yaci gaba da cewa) kawai naga kamar hankalinta baya kaina na sake mata magana se ji kawai mukayi tayi salati ta tafi zata fadi na tareta amma wallahi babu abinda mukayi mata, zaki iya tambayar samarin can dan tunda muka zo suna zaune a gurin" ya qarasa yana nuna mata majalisar su Malam Sadi, kamar kuwa yana jira Malam Sadin ya taso yana cewa

"Ashsha Ashsha mutanenne suka motsa mata ko, daga jin yanda taja dogon salatin nan ina ga gamo tayi ku kamata muje cikin gida" yayi gaba ze shiga gidan Mama data kasa magana ta tareshi da cewa

"Jeka abinka, idan muna da buqatar ka zaa kira ka, Samari mun gode ko ku gaida gida" ta qarasa tana kallonsu Khalil da gaba daya kana kallonsa kasan hankalinsa a tashe yake kafin tabi bayan su Anty da suka shige gida da Umaimah.

Akan babbar tabarmar dake tsakat gidan suka kwantar da ita Nuratu ta shiga daki ta dakko abin auna jini da bugub zuciya ta shiga dubata, ita kuwa Umaimah Abinda take ji yau ya wuce ta dora hannu aka tayi ihu, kukan take amma na zuciya hawaye kadai ke kwaranya a idonta.

"Mama kodai a kirawo Malam Sadin ne ni banga komai daya same ta ba qila abin bana Asibiti bane" Nuratu ta fada tana kallon Mama data zabga tagumi, se ta girgiza mata kai alamar Aa, kafin ta juya ga Umaimah dake Hawaye idonta a rufe ta kira sunan ta tace

"Zo Umaimah, taso ki gaya mun meya same ki" Kamar jira takeyi kuwa ta tashi daga kwanciyar ta fada jikin Maman tareda fashewa da kukan da kana jinsa kasan tundaga qasan zuciyarta yake fitowa.

"Qila gidan su Nabila zeje, dan daman jiya Rumah take cewa ta gansu a hanya sun shigo Kano ashe amma basu kulata ba, qila maganar auran nasu ta kankama da gaske kenan" ta sake rushewa da Kuka kamar Numfashinta ze dauke

Bayanta Mama ta ringa bubbugawa kawai da sigar lallashi gaba daya ranta a jagule yake, dagaske akwai akwai Alamomin Aljanu tattare da Umaimah masu yawa haka wani sa'in tana nuna alamar me motsi a kwakwalwa ya kamata su dauki mataki dan da alama abin kullum gaba yake ba baya ba.

A haka Abba ya shigo ya same su, Nuratu ce ta gaya masa iya abida suka sani da farko yayi kamar ya shareta dan yasan be wuce iskanci ta ne ya motsa ba amma kuma ganin irin kukanda take dole ta baka tausayi, anyi anyi tayi magana taqi, data bude baqi baqin cikin abun yake shaqeta ta kasa magana se sabon kuka ya kufce mata, sun yarda da zancen Malam Sadi na cewar Gamo tayi dan haka suka kwanta da qudurin da sassafe zasu kaita gidan wani babban Malami da Abban suke daukar karatu Asabar da Lahadi.

A bangaren Khalil kuwa kai a kulle suka bar qofar gidan nasu, tsabar yanda ya rikice kasa tuqa motar yayi se Mansur ne ya karba.

"Khalil, dama yarinyar nan nada matsalar Jinnu ne?" Mansur ya katse shirun da sukayi kowa na jimami a zuciyarsa, se Khalil yaja ajiyar zuciya kafin yace

"Wallahi bansani ba. Gaba daya wannan itace haduwa ta da ita ta biyu da mukayi doguwar Magana ban san komai a kanta ba amma naji wannan mutum yana fada qilan ko tana dasu ne"

"Tab ai kuwa da sake dan bazan baka shawarar ka kwasowa kanka shirgin Iska ba, mata masu lafiyar ma yaya aka qare da rigimar su bare kuma gyaran Malam. Tunda dai abu beyi nisa ba gaskiya Dude back out" Mansur ya sake fada daidai sanda yasha kwanar gidan su Budurwar sa, kwalliyar da sukayi zasuje duba Maman Budurwar ne da bata da lafiya.

"Daman matsalar Aljanu tana hana a aure ne maimakon ma kace na nema mata magani, beside mun tabbatar da Aljanu takeyi ko kuma wani health issue ne na daban, kawai ka tayani Addu'ar Allah ya bata lafiya amma maganar na janye ma babu ita dan yanzu na fara Son Umaimah"

"Allah dai ya biya mijin gyaran Malam, se ka koyi ruqiyya saboda tashin dare, dan wallahi Matar Iro Black har kan kwano take hawa, kota kwasa a guje tayi titi, seka shirya yar tsere a layi mutumina" Mansur ya sake fada.

Banza Khalil ya masa har suka qarasa gidan, da farko ma cewa yayi baze shiga ba, seda Mansur din ya nuna bacin rai kafin suka shiga. Yana mata yaya jiki ya fito waje ya baro shi kiwa yana ta sake gwada kiran wayar Umaimah da tun dazu ya jita a kashe abinda ma ya saka yayi aike kenan amma har sannan a kashe.
Yana so yaji lafiyarta amma babu hali, haka ya koma gida bacci kansa rabi da rabi yayi, duk juyin da zeyi seta fado masa a rai Addu'arsa Allah ya bata lafiya zuwa safiya kafin ya wuce aiki zw biya ya ga yaya jikinnata.

*KHALIL DA UMAIMAH SOYAYYA GAMON JINI*
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 7


Washe gari kuwa kamar yanda Abba ya fada qarfe 8 suka isa gidan Babban Malami Sheik Ali Musa. Sun tarar da Malam yana bada karatun safe, dan haka Abban ya zauna a gurin bayan anyiwa Su Umaimah da Mama iso cikin gidan Malam.

Idan kaga yanda ta zabge a dare daya seka yi zaton ta dade tana jinya, akan fuskarta zaka karanci tarin damuwar da take ciki shiyasa koda Mama tace ta shirya zasu fitan batayi musu ba, bazasu fahimceta ba dan haka idan anje gurin suka fada musu bata da wasu Aljanu sa qyaleta ta sarara.

Se gurin qarfe tara Malam ya samu shigowa, a sitting room dinsa suka zauna bayan sun sake gaisawa yana kallon Umaimah data jingina da bango ta tafi duniyar tunani yacewa Abba
"Lafiya dai Alhaji Sabo naganku da sassafe haka?"

"Eh to lafiya ba lafiya ba Akaramakallahu" Abban ya fada kafin ya gyara zaman sa a taqaice ya zayyanowa Malam Ali duk abinda yake faruwa da Umaiman, ya rufe da cewa
"Jiya haka nan ta yanke jiki ta fadi shine har yanzu ta ke aikin koke koke babu magana kuma. Shiyasa nace gara muzo tun kafin abu yayi tsamarin da magance shi zeyi wahala".

Malam Ali da tun fara maganar Abba yake nazarin Umaimah, shidai a iya sanin da ilimin da yake dashi ta bangaren abinda ya shafi aljanu bega wata alama a tattare da ita ba saboda koda ace Aljanun sun barta kafin su shigo gidan ne indai tana da shafar su seya gane amma dai bari ya sake bincikawa tunda shaqiyancin jinnu kullum qaruwa yake, wani lokacin idan sukayi wani alayen badan qarfin Ayar Allah ba bazasu gane ba.

Wani turaren mai ya dauko ya miqawa Mama yace ta shafa mata a goshinta,kunne da kuma qofofin hanci yasan duk inda Aljani ya buya a jikinta idan turaren ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login