Showing 222001 words to 225000 words out of 429394 words

Chapter 75 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

955

din baya ya ajiye babbar Ledar daya taho da ita ya shiga mazaunin sa ya dora mata wata qarama a jiki yana cewa
"Anwar matsala ne, wai Icecream zasu sha kamar wasu mata dan Allah, ni banma san gurin nan abinda suke siyarwa ba kenan se yau, bari zamu samu lokaci muzo da su Bibi bakiga ciki ba yayi kyau sosai"

"Allah ya kaimu" kawai ta iya cewa ta sauke ledar daya dora mata a qasa, har suka isa Salon din bata sake magana ba shima ya kama kansa ganin kamar ta fusata kome aka mata oho. Dubu goma ya zaro a Aljihunsa ya bata, ta karba ba tareda tace komai ba dan in ta bude baki tsaf zata rusa shirinta ta bude murfin motar ta fice ba tareda ta dauki ledar Icecream din ba ta shige gurin.

Khalil na tsaye har seda yaga ta shiga an rufe qofar, seda ya qara minti biyar a tsaye haka nan yakeji gabansa na faduwa ya dai daure ya tayar da mota dan yana jin wayarsa dake aljihu se vibrating takeyi yasan kuma Zahra ce take kira.

Yana Juya kan motar Umaimah dake tsaye tuntuni ta fito sanye da dogon Hijabi har qasa ta dora Niqab akai,tsayuwar da yayi ya bata lokaci tayi mata amfani dan ta samu ta shirya duda daman tana shiga ta kira Harun tace ya saka mata ido akan motar Khalil din, idan ma ya tafi ya bishi zasuyi waya duk inda suka nufa zata biyo su. Da sauri ta shige Napep din tace yabi bayansa. A sannu a sannu Harun ke binsa ta yanda baze taba gane cewar wani na biye dashi ba har suka isa unguwar YanKaba ya karya kwanar wani layi data ga an rubuta 'Dr Sabitu Bashir Street' a jikin wani dan Allo take cikakken sunan Zahran data gani a truecaller ya dawo mata.

A farkon Layin tace ya tsaya, ta sauka ta taka da qafa ta shiga a qofar wani katafaren gida ta hango motar Khalil din a ajiye taci gaba da tafiya harta wuce gidan Get din yana kulle dan haka bata ga komi ba ta wuce qarshen layin inda ta hango Hasumiya da alama Masallacine a gurin.
A qofar masallacin ta zauna, mutum biyu ta hango a ciki suna karatu ta zauna shiru gaba daya kwakwalwarta ma ta tsaya cak ta dena aiki. Tunani takeyi ta shiga gidan ne suyi aran gama taji abinda ze gaya mata ko kuwa ta jira ya gama abinda yakeyi ya tafi kafin ta shiga taci uwar yarinyar?

Tayi zurfi a tunani Samarin dake karatu a masallaci suka fito, daya ya kalleta yace
"Malama lafiya kuwa tun dazu kike zaune anan?"
Niqab din fuskarta ta daga dan kar suyi mata zargin rashin gaskiya, wani gida data gota taga kwado a Get din ta nuna musu tace
"Can gidan nazo kuma nayi rashin sa'a basa nan shine na zauna nake hutawa anan"

"Ayya halan bakuyi waya ba, ai bana jin sunyi cikakkiyar awa da tafiya garinsu ma sannu kuma da alama daga nesa kike?" Wanda ya fara mata maganar ya sake fada da ganinsa yana da surutu, se Umaimah ta yamutsa fuska kamar gaske tace
"Kash wallahi ban kiraba dake babu waya a hannuna kuma daga Kura nake"
"Tab sannu gashi kin daki gurbi, seki daure ki tashi ga magriba ta kawo kai yanzu za'a fara shigowa masallaci" dayan da beyi magana ba ya fada me surutun na shirin cewa wani abu yajashi suka tafi. Umaimah ta rakasu da ido daidai nan taga an bude Get din gidan su Zahra ai bata san sanda ta miqe tsaye ba ta nufi gurin.

Khalil ne ya fito wata zuqeqiyar yarinya da a halitta bazata gwada mata komai ba ta biyo bayansa fuskarsu washe suna dariya daga inda take tana jin yarinyar na cewa
"Amma Dear naji dadin zuwanka, harfa su Sury sunyi fushi zasu tafi na ringa lallabasu kaga yanzu ai haka yafi kunga juna kun gaisa ba se lokacin biki yazo ba".

Khalil dake kallonta yana murmushi like an idiot yace
"Ai kuwa dai nima naji dadin haduwa dasu sosai shikenan dai yanzu qorafi ya qare ko?" Ya fada yana aika mata da wani kallo da Umaimah ta zata ita kadai yake yiwa irinsa.

"Baiwar Allah yi a hankali fa karki fadi" taji muryar saurayin dazu ya fada se a sannan ta lura da a guri daya take a tsaye tana kallonsu Khalil din jiri ke neman kadata ta dafe bangon kusada ita shine yake mata magana. Kai ta daga masa ta shiga jan qafarta dakyar numfashinta na mata wuyar shaqa. Khalil da Zahra suka bita da kallo, qirjinsa ya buga da qarfin gaske sanda suka hada ido da matar kafin ta dauke kai taci gaba da tafiya tana cira qafarta dakyar.

Kamar idon Umaimah haka ya gani haka tafiyarta da yanayin jikin sunyi masa kama da nata amma me ze kawota nan? Kuma ya tabbata idan itace tabbas Allah kadai yasan abinda ze faru a gurin. Muryar Zahra yaji tana cewa samarin
"Kai Aliyu wacece wannan din da kuka bari ta shigowa mutane layi da magriban nan da wannan shigar, kunsan dai yanda criminals sukayi yawa ko?" Se wanda ta kira da Aliyu ya bata amsa da cewa
"Gidan Barrister tazo kuma basa nan shine ta zauna gurin masallaci ta huta"

"Dear kaima baka yarda da ita ba ko?" Zahra dataga ya zubawa inda Umaiman tabi ido ta fada se yayi firgigit ya kalleta yana cewa
"An Bari naje na bar Madam a Salon tana jirana zan dauketa".

Fuska ta bata bata ce masa komai ba yayi mata murmushi ya shiga motarsa yana daga mata hannu, hannun itama ta daga masa daga nan yaja ya tafi har sannan zuciyarsa na masa wasi wasi akan wacce ya gani din.
Kiran daya shigo wayarsa ya sakashi dubawa, Umaimah ce, muryarta babu yabo babu fallasa tace
"Base ka biyo daukana ba na wuce gida ban samu kitson ba"
Ajiyar zuciya ya sauke jin cewar ta tafi gida kenab dagaske ba itan bace, lallai tsoron da yakewa Umaimah har ta kai ta fara masa gizo.

UMAIMAH
Dakyar ta iya maida kanta imda Harun yake jiranta, ta zauna a Napep din tana jan numfashi jikinta na wata irin rawa. Harun ya kalleta yace
"Anty lafiya kuwa?"
"Maidani gida" ta fada dakyar kafin ta dora kanta akan qarfen adaidaitan tayi shiru dan ta kasa tunanin komai.
Khalil ya iya yi mata qarya ya taho gurin wata ko?
Wani tunani ne ya fado mata nan ta shiga jan numfashi tana fesarwa har seda taji ta samu nutsuwa kadan kafin ta dauki wayarta ta kirashi ta gaya masa ta wuce gida, gara taje tashirya yanda zataci ubansa a ruwan sanyi. Se yayi danasanin munafuntarta yayi mata qarya wallahi kafin ta juya kan ita qaramar Shegiyar. Wato saboda tsabar ya shirya ci mata mutunchi seda ya samo daidai da ita dan ita da kanta ta yarda ba zata gwadawa Zahran komai ba a halitta sema dai ita ta fita dan ba zaka hada jikin budurwa da Wadda ta haihu har biyu ba.

Bata san ko nawa ta zaro ta bawa Harun ba ta shige gida kai tsaye kan gadon dakinta ta fada wasu hawaye masu dumi suka shiga tsere akan fuskarta idan ta tuna yanda Khalil yake kallon yarinyar yana mata murmushi se taji kamar ta shaqe kanta saboda baqin ciki. Wai meya shiga kanta daya hana ta tsaya tayi musu tijara a gurin? Yanzu meye amfanin dawowar da tayi tazo tana kuka anan?
Wani ihu ta kwara kafin ta miqe ta watso da duk tarin kwalabe da robobin dake kan Mirror dinta, tamkar farin shigan hauka haka ta shiga dukan duk abinda hannu ta ya kai kafin wani lokaci tayi wa dakin rotse hannayenta bada zubar jini babu abinda sukeyi.

A haka Khalil ya dawo gidan, tunda yayi arangama da Hijab da Niqab a kan kujerar palour yaji lakar jikinsa na tsiyayewa, kasa gaba yayi balle baya qirjinsa ya ringa bugawa a sittin wato dai ta tabbata Umaimah ce, kenan bin bayansa tayi, tayi badda kama dan taga inda zeje me yasa sam tunanin zata iya aikata hakan be zo masa ba tun Sanda tace zata bishi ya kamata ace ya zargi wani abu kai tun farko ma shirun da tayi masa yasan ai ba haka kawai ba dole akwai abinda take shiryawa, bashida mafita a yanzu illah yayi mata bayanin komai ko Allah ze sa ta fahimce shi dukda yasan abune me wahala amma ze gwada.


*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 53

Kamar wani mara gaskiya haka ya tura qofar dakinta da sallama, Umaimah dake zaune a qasa ta dago ta kalleshi da jajayen idanunta dan ba qaramin kuka tasha ba. Yawu ya hade ya shiga qarewa dakin data sauyawa kamanni kallo, besan da me tayi aikin ba amma duk wani abi da yake na glass a dakin ta fasashi kuma tana zaune a cikin gilasan kanta yayi buzu buzu kamar wata hauka sabon kamu. A hankali ya shiga takawa zuwa inda take yana kuma qara baza idonsa dan ya tabbatar da babu wani makami a kusa sa da ita da zata iya yi masa lahani dashi a haka har ya isa gabanta ya durqusa dan tunda tayi masa kallo daya ta maida kanta qasa tana jan Ajiyar zuciya.

"Umaimah" ya kira sunanta a tausashe bata amsaba kuma bata dago ta kalle shi ba dan haka ya qara matsarta yana qoqarin kama hannunta daya ga jini ya bata yana cewa
"Umaimah please..."
"Karka kuskura ka tabani Khalil idan ba haka ba wallahi sena baka mamaki" ta fada tana fizge hannunta tareda tashi tsaye sam ko nauyin cikin jikinta bataji, miqewa yayi shima da saurin ganin tana qoqarin taka kwalaben dake zube a qasa dan ko shi da yake sanye da takalmi da taka tsantsan ya tsalleke su, ruqota yayi ta fizge ta tafi baya saura qiris ta fadi ya sake tareta be bi takan dukan datake kai masa ba ya dagata cak suka fice daga dakin

"Ka ajiye ni Khalil ka ajiyeni dan kutumar ubanka" ta fada cikin wani irin sauti ai kafin ta kai qarshe ma ya direta a qasa yana bin bakinta data qunduma masa Ashar dashi da kallo.
"Ni kike zagi Umaimah?" Ya fada cikin mamaki yana nuna kansa, idon ta cikin nasa tace
"Na zageka maqaryaci maci Amana, taron da zakuyi da su Anwar din kenan ka tafi gidan su Budurwa a Yankaba, saboda ka mayar dani bansan abinda nakeyi ka dauka akwai wata qarya da zakayi mun ban gane ba? Wallahi kar nake kallonka Khalil, kuma tun ranar dana fahimci kana cin Amanata na dana maka tarko, duk wani motsinka akan ido na kakeyinsa ban kuma tabbatar daka cika qasurgumin maqaryaci ba se yau da har ka iya tsara zance ba tareda ka koji tsoron Allah ba ka yaudareni".

Kallonta kawai yakeyi har ta kai aya, jikinsa ya qarasa mutuwa, yanzu shi Umaimah ta zaga haka kai tsaye ba tareda shayin komai ba? Lallai abinta ci gaba yakeyi ba kuwa ze dauka ba, baze taba zama sakarai a gabansa mace ta zage shi ba dan haka nan take shima ya hade fuska yana kallonta yace
"Eh naje gurin budurwa se akayi yaya? Ajiyarki aka bani da zaki ringa bibiyar rayuwata ki daka mun ido ko kuwa? Sannan da izinin wa kika je, ba Salon na ajiyeki ba amma saboda baki dauki aure a bakin komai ba kina ganin zaki iya duk abinda kika ga dama shiyasa kika bini ai, kuma gashi nan a garin bin diddiginki ki tono abinda ze hana ki zaman lafiya dan da banyi niyyar sanar dake ba se komai ya kammala saboda kar hankalinki ya tashi amma yanzu tunda kin sani shikenan, auranta zanyi ita yarinyar da kika ganmu tare kuma baze dauki lokaci ba dan dakyar za'a ci wata daya nan gaba" ya fada da wani kalar expression akan fuskarsa.

Umaimah da tayi kasaqe tana kallon sa lokaci daya tayi kansa tana cewa
"Qarya kakeyi wallahi Khalil, baka isa kayi aure ba kai nawa ne ni kadai babu macen data isa ta shigo rayuwar mu. Idan kuma ka shirya ja mata bala'i shikenan karka manta da abinda ya samu Hadiza wallahi se nayi mata ninkinsa se ta zama mujiya a cikin mutane ba ita ba har iyayenta se sun zama abin tausayi".

Tsaki yayi ya wuce dakinsa ransa yana bala'in zafi, Ya rasa Umaimah wace irin mutum ce da idan ranta ya baci hankalinta yake gushewa. Ganin ta sauka qasa da sauri ya saka shi juyawa yabi bayanta amma kafin ya tarar da ita har ta fice daga palour seya qara sauri yana kiran sunanta ganin a yanayin da take kuma ta fita a hakan Umaimah kuwa ganin ya biyo ta ma se ta saka gudu, a parlour Hajiya ta zubr tana wani irin kuka ga numfashinta na qoqarin daukewa. Hajiya data idar da sallar Isha tana zaune a saqon kujera ta miqe a gigice tayi kanta tana tambayar lafiya? Koda yake babu alamarta a tattareda ita. Yanda take a hargitse ga jikinta duk jini ya bada amsar abinda yake faruwa.

"Khalil ne" ta fada cikin jan numfashi, Hajiya ta dafe qirji tace
"Dukanki yayi? Shaye shaye ya fara kome?" Daidai nan ya shigo shima kamar an jefo shi Hajiya ta miqe da sauri tana cewa
"Me kayiwa yar mutane Khalil, me tayi da zaka aikata mata wannan mugun abun?"

"Wallahi Hajiya babu abinda nayi mata nima dawowa nayi na tarar ta fasa komai na dakinta ni ban mata komai ba" ya fada da sauri ganin Hajiya na neman laqaba masa abinda beyi ba. Umaimah dake kwance lakadan saboda wani azababben ciwo da mararta ta dauka ta bude baki dakyar tace
"Qarya yakeyi Hajiya ya san me yayi mun, ki gaya masa ko ya fasa abinda yayi niyya ko na kashe kaina wallahi".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Umaimah wace irin magana kike haka kamar ba musulma ba? Ki kashe kanki a saboda me saboda damuwar duniya? Kar na sake ji, kai kuma kamata mu tafi Asibiti kalli, innalillahi wainna ilaihi raji'un" Hajiyan ta sake fada tana zare ido ganin jinin na bin qafafun Umaiman. A rikice yayi kanta ya dagota, hankalinta ya fara nisa daga jikinta shiyasa ta gagara hanashi bata san yanda akayi ba se farkawa tayi ta ganta a Gadon Asibiti gefenta Khalil na zaune ya dora kansa akan gadon da take kwance.
Abinda ya faru ne suka fara dawo mata, murmushin da yakeyiwa Zahra ta hango bata san sanda ta saka hannunta da ba'a daura mata ruwa ba ta kwada masa mari a qeya.

A gigice Khalil ya farka yana zare ido, tun daren jiya da aka kawo ta be runtsa ba se yanzu da safe bayan su Hajiya sun tafi gida aka barshi shi kadai koda yake yace ze zauna da ita.
Kama hannunta yayi ganin tana qoqarin fizge qarin ruwan da aka saka mata ta juyo a fusace tace masa
"Ka sake ni karka sake tabani Khalil"
"Ki nutsu Umaimah ba'aso kiyi wani dogon motsi dan Allah saboda jijjiga jikinki da kikayi jiya seda akayi miki daurin bakin Mahaifa saboda babyn tana nema ta fito lokacinta baiyi ba ki koma ki kwanta" Khalil ya fada cikin muryarsa da bata fita dakyau saboda bacci da gajiya ga ciwon kai. Bata ko saurara na ta zare allurar, jini ya fara zuba daga hannun ko a jikinta ta dire qafarta qasa tana yunqurawa zafi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login