Showing 315001 words to 318000 words out of 429394 words

Chapter 106 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

938

ta fara fiddo da kayan cikin jakar tana kallon Umaimah tace
"In gaya miki jiya naga Suleiman namun wani gani gani na sakashi abu ya qiyi shine fa yau babu shiri na bazama ina zan zauna kallon ruwa kwado yayi mun qafa?
Kedai ai duniya ta samu hankalinki ya kwanta Khalil ya dawo hannunki se yanda kikayi dashi, to kema ga saqonki inji Malam wannan turaren ne kuma yace na jaddada miki ki kula dashi karki kuma nemansa ki rasa" Safina ta fada tana bata wani dan qullin baqar leda. Drawer gefen gadonta taja ta saka a ciki daga nan suka ci gaba dayi, Mu'ayyadya shiga dakin da Sallama yana tafiya a hankali, seda ya gaida Safina kafin ya qarasa jikin Umaimah ya jingina ta dagoshi jin jikinsa da zafi tace
"Zazzabin ne ya dawo?"
Kai ya daga mata kafin ta sake cewa
"Toh me yasa baka kwanta a gurin Hajiya ba ka fito?"
"Hayaniya akeyi Momy duk su Momyn Sharada ne sukazo harda su Maman Kaduna ma su da yawa" ya bata amsa yana kwanciya akan gadon. Mamaki ya kamata jin yace mutane a bangaren Hajiya, su Jalilah ba baqi bane daman kullum suna tafe amma Maman Kaduna Maman su Lubna kenan dayace sunzo da yawa su kuma me ya kawosu?

"Kaga tashi kaje dakinku ka kwanta kaga nan ma hira mukeyi karmu dameka" ta fada ganin yana shirin yin bacci se Safina tayi saurin tareta tace
"Ki barshi mana mu se mu koma falo ai na gama bude kayan duk da ba zama zanyi bama gara inje in aikata abinda ya kamata" ta fada tana miqewa tsaye. Falon suka koma, suna zama tayi qasa da murya tana kallon Umaimah tace
"Kinga ga dama kin samu duk suna gidan dangi na kusa dana nesa yanzu ki tashi kiyi turaren nan kowa ta shaqa shikenan fa kin gama dasu tsakaninki da dangin Khalil se yanda kikace haka za'ayi"
"Kuma fa hakane, bari to ina tashi" Umaimah tayi na'am da zancen babu bata lokaci ta shiga kitchen ta kunna coal ta saka a kasko ta fito falon, seda ta dakko maganin ta kwance zata zuba Safina tayi saurin tareta tana cewa
"Ke uwar hankali waya ce miki haka zakiyi? Ai se kin je can kin ajiye kaskon a inda kika san idan kin zuba duk zasu shaqi hayaqin sannan ki zuba ki bar gurin. Ki samu kamar bayan windown falon ki saka a can zefi samunsu kuma ki tabbata babu wanda yaga sanda kika zuba maganin haka qa'idar aikin take".

Harararta Umaimah tayi kafin ta dauki kaskon ta fita, harta zagaya ta bayan falon babu wanda ta hadu dashi, tana jiyo hayaniya da shewarsu daga ciki dukda bata tantance abinda suke cewa ta tabe baki a ranta tana tunanin ko taron uban me sukeyi haka se Allah. Seda ta samu guri me kyau ta ajiye kaskonta ta kwance qullin ta debi turaren bayan ta dauke numfashi ta zuba, murmushi ta saki ganin yanda iska take kadawa ta bangaren da haqin yake bi kai tsaye tana sake ingizashi zuwa cikin falon
"Me kikeyi haka Umaimah" taji Muryar Mama kamar a mafarki a bayanta.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 70

"Meye wannan kika zuba?" Maman ta sake fada tana matsawa kusa da ita Umaimah ta saki ragowar qullin hannu ta a qasa saboda kidima cikin rawar baki tace
"Mammma yaushe kika zo ya kika biyo ta nan?"
"Ba wannan na tambayeki ba me kika zuba a cikin kaskon nan nace?" Maman ta sake fada tana qarasawa kusa da ita ta kalli kaskon dake bulbula uban hayaqi mara dadi ta kalli Umaimah da alamun rashin gaskiya suka gama bayyana a jikinta cikin in ina tace
"Am Mama maganin Miyagu ne aka bani"
"Kuma maganin se akace kibi gida gaba daya ki saka musu kuma a boye?" Maman ta sake tambayarta tana tsareta da ido se Umaimaha ta zumbura baki tana kallon gefe tace
"Toh ai Mama haka me maganin yace Mayun na gida ne kuma idan suka sani ba zasu bari na saka ba dan kwanaki ma da aka bani daukewa sukayi na neme shi na rasa"

"Dauki kaskon muje" Maman ta sake fada tana girgiza kai Mamakin Umaiman yana kamata dan ta yarda da gaske maganin Miyagun ne mamakinta kawai yanda tace wai Mayun na gida ne kenan Mijinta ma Mayen ne da Yayanta tunda dai a Barayin uwarsa take kunna maganin itace mayyar kenan.
Umaimah kuwa babu yanda ta iya haka ta dauki kasko gudun kar Maman ta zargi wani abu, addu'arta daya Allah yasa bataga sanda ta zuba maganin ba inda bata gani ba toh ai magana ta qare hayaqin ya shiga kuma ko yaya ne ya gauraya da iskar gidan duk sun shaqa.

A bakin qofa suka ci karo da Safina da uwar jakarta ta rungumo,ta gaida Mama data bita da kallo tana cewa Umaimah zasuyi waya, suka shiga ciki tana gaba Maman na binta a baya. Anty Laure na zaune kan kujera tana girgiza qafa kana ganinta kasan bala'i nacinta Umaimah dai ta wuce Kitchen ta juye garwashin a sink ta kashe kafin ta koma falon gabanta na faduwa wannan zuwan na Mama babu sanarwa tasan ba Alkhairi bane, qila wani sharrin aka qullo mata shine maman ta taddota har gida kenan zata ci mata mutunchi.

A qasa ta zauna ta gaishe su, Anty alaure bata amsa ba Mama dai ta amsa a sanyaye tana kallon Umaiman tunanin yanda zata isar mata da wannan saqo me nauyi take yi. Ruqayya ta fito daga kitchen da Babban Try ta doro Ruwa da Lemo ta ajiye ta gaida Mama cikin girmamawa ta sake komawa ta dakko Babban Bowl data zubo dambun nama, jiya Khalil ya shiga dashi ko Umaiman ma ta manta bata gayawa na se yanzu ta tuna dashi. Seda ta ajiye musu duk wani kalar kayan dadi da suke dashi a gidan kafin ta koka kitchen ta shiga shirin dora abincin rana na Alfarma duk saboda zuwan Hajiya Mama.

Duk kayan da Ruqayya ta ajiye musu babu abinda suka taba, Mama ta kalli Umaimah da duk ta fita a kamanninta tace
"Umaimah haka ciki ya mayar dake? Yaushe ne lokacin haihuwar taki wai?"
"Nima ban sani ba Mama amma sunce na kusa" ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba se Mama ta sauke ajiyar zuciya kafin ta sake cewa
"Khalil yana gidan ne?"
"Ya fita tun safe amma nasan qila yana hanyar dawowa saboda yau be cika fita bama indai ba da wani babban dalili ba"

"Toh yayi Allah ya dawo dashi lafiya" Maman ta sake fada se sukayi shiru gaba daya kusan minti biyar Umaimah ta kalli Anty Laure tace
"Anty ya Babanmu ina ta cewa zanzo gashi kin rigani zuwa"
"Kiyi ta kanki yarinya ahto kiji da abinda yake a gabanki ba gulma" Anty Laure ta fada, shirun suka sakeyi, gaba daya Umaimah ta tsargu da yanayin Mama. Da ace laifi tayi fada zata fara mata amma yanda ta ganta a sanyaye gashi se kallon ta takeyi yasa hankalinta ya fara tashi, kodai wani abu ne ya faru a gida? Amma idan haka ne ai ba Mama ce zatazo da kanta ba wani za'a turo to ko qararta Khalil yakai shi kuma me tayi masa kai babu ma wata qara da ze kai da can ma baya kai qararta gida balle yanzu da ya sake zamar mata Mijin tace qila dai wani abun ne na daban ya kawo Maman. Maganar Mama ce ta katse mata tunani jin tana cewa

Cike da qarfin Hali Mama tace
"Ni kam ya maganar qarin auran Mijin ko?"
Tamkar saukar aradu haka taji maganar, seta muskuta tana kallon Maman tace
"Toh ya gaya miki kenan, to ni ina ruwana na hanashi yayi aurene da zeje ya hadani dake? Yayi auransa mana ai ba akaina matar zata zauna ba".
Yanda tayi maganar seka rantse da Allah har ranta kamar yanda ta fada abin be dameta ba, cike da samun kwarin guiwa Mama tace
"Haka ne kam ba akanki zata zauna ba kuma na godewa Allah da kika fahimci hakan in har da gaske kikeyi kenan" Mama ta fada seta gyara zama sosai kafin ta kira sunan Umaiman cikin muryar dake nuna muhimmancin maganar da take so tayi mata.

"A matsayinki na Musulma kinsan cewar Imaninki baze cika ba har se kin yarda da Qaddara me kyau ko Mara kyau haka ne ko ba haka ba?"
A hankali Umaimah ta bude baki tace
"Hakane Mama"
"Toh ina so ki bude kunnenki da kyau ki saurari abinda zan gaya miki sannan ina so kiyiwa maganata kyakykyawar fahimta" Maman ta sake fada Umaimah dai kallonta kawai takeyi tana jin gabanta yana faduwa. A hankali kuma cikin hikima Mama ta fara mata Nasiha irin wadda duk taurin zuciyar mutum seta raunana tayi laushi, seda ta tabbatar da jikin Umaiman yayi sanyi qalau ta yanda ko motsi ta gagarayi daga zaunen da take kafin ta sake gyara zama tana dauke idonta daga kallonta. Cikin nutsuwa ta warware mata zare da abawar abinda yake faruwa ta rufe da cewa
"Kiyita maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel har se kin samu gamsashshiyar nutsuwa, karki yarda ki bawa Shaidan damar shiga zuciyarki yayi wasa, ubangiji ne yayi hukuncinsa kar kice zakiyi fito na fito da umarnin ubangiji Umaimah kiyi addu'a Allah yasa hakan ya zamo muku Alkhairi baki daya, Mijinki yana sonki na tabbatar kuma babu abinda ze canza hakan daga zuciyarsa. Haqurin da zakiyi da juriya su zasu qara girmama soyayyarki da martabarki a zuciyarsa".

Shiru falon ya dauka kamar babu abu me rai a ciki kafin Umaimah da tayi mutuwar zaune ta ja numfashinta daya bar jikinta na wani lokaci, babu yabo babu fallasa ta kalli Maman tace
"Toh Mama nagode da Nasiha ina kuma addu'ar kar Allah ya tabbatar da wannan mafarkin naki"
"Mafarki Umaimah, duk maganganun da na gama yi miki a mafarki kika daukesu?" Mama ta fada cikin mamaki se Umaimah ta miqe tsaye tana kallon Maman tace
"To idan ba mafarki bane Mama tatsuniya ce ko kuma makuwar tunani kima samu da har kikayi irin wannan hasashen?"

A hasale Anty Laure tace mata "Ke shagga idan zaki hada hankalinki guri daya tun wuri kiyi ki fuskanci abinda yake a gabanki, munafunci ne an rigada anyi ruwanki ki maida musu da aniyarsu ruwanki kiyi hauka su samu yanda suke so suyita yawo dake a duniya suna yadaki zabi ya rage naki yanzu ita dai Kishiya kafin ta shigo ne kake yin barazana ko hakan ze sa a fasa idan kuma ta rigada ta shigo sedai kayi yaqin tsira da mutunchi dan ko kin koreta a banza ta rigada ta kafa tarihi ko magana aka tashi se an jinginaki da ita ace tsohuwar Kishiyarki to gara ki rungumi qaddararki kawai ki zauna lafiya ki kuma bawa munafukai kunya dan gasu can sun cika gida suna jiran suga yanda zakiyi".

Wata dariya Umaimah tayi tana girgiza kai tace
"Toh inaga ba Mama kadai ta rikice ba harda ke Anty Laure shiyasa she na ganku wani iri kamar an muku mutuwa to gaskiya ya kamata ku nemi magani tunda wuri kar abin ya zarce haka. Idan ba rashin lafiya ba taya ma tunaninku ze fara baku wai Khalil yayi aure kuma ace ban sani ba? Ai wlh ko na mutu ina cikin kabari na tabbata idan Khalil zeyi aure se yaje kan kabarina ya fada mun saboda kar na tashi na ringa yi musu fatalwa ballantana ace da raina ina zaune cikin gidan nan yaje yayi aure hhhhhh" ta sake yin wata dariya duk se suka saki baki suna kallonta Anty Laure tace

"Eh lallai babu shakka Umaimah kai tsaye kice hauka mukeyi kawai meye wani sakayawa kice bamu da lafiya? Toh karma ki kidina kanki a banza kiyi kamar baki san me muke fada ba, Khalil dai yayi aure bakuma yanda kika iya" bata tsaya qarasa jin abinda Anty Lauren take fada ba ta shige dakinta da sauri ta kullo qofar dan karma su bita cikin. Wayarta ta dauka bayan data zauna gefen gado ko kusa taqi ta bawa kwakwalwarta damar daukar abinda suka fada ballan tana har tayi tunani akai.

Kwanciyarta tayi kusada Mu'ayyad tana jin ana buga qofar dakin tayi banza dasu har suka gaji suka bari daga wajen tana jiyo Anty Laure na qunduma mata zagi ko a jikinta sema ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta rufe ido babu dadewa kuwa bacci ya kwasheta bata farka ba se bayan Azahar shima dalilin bugun qofarta da ake tayi babu qaqqautawa.

MAMA
Da ido tabi Umaimah harta shige daki ta bugo musu qofa. Anty Laure ta kwashi salati tana tafa hannu tace
"Yaya kina kallon abinda yar iskar yarinyar nan tayi mana? Mu ta kira da mahaukata sannan ta shige daki ta barmu a zaune kamar wasu gantalallu to dan kanta kuma ni wlh yanzu naji dadin kishiyar da akayi mata yar banza me baqin hali da bamu san a inda ta gado ba"

"Laure ni duk ba wannan ya dameni ba, yarinyar nan fa bata yarda da abunda muke fada ba. Ina tsoron abinda ze biyo baya idan ta farga"
"Toh ba ita ta sani ba Yaya ina cewa tayi bamu da lafiya ita da take lafiyayyar ai shikenan idan taji ana ta matsa za'a shigo da Amarya ai a sannan zata sha jinin jikinta wawiyar yarinya da babu abinda ta sani se hauka da rashin hankali nidai tafiya zanyi idan zaki tafi muje idan kuma se kin zauna kin fahimtar da ita Allah ya bamu Alkhairi ni nayi nan" Anty Laure ta fada tana figar jakarta zata fita se Mama ta miqe a sanyaye itama tabi bayanta.

Gidan Maman suka wuce a can suka tarar da Maman Asad tun kafin ma ta tambayi ba'asi akan ganin yanayin Maman Anty Laure ta kwaza mata zance, Anty na tsakar gida tana aikace aikace da yake cikin daga murya Anty Laure take maganar dan haka taji komai a kidime ta saki tsintsiyar hannunta ta dafe qirji babu shiri ta afka dakin. Maman Asad kuwa sunan zaune tayi, seda ta kwashi wasu mintoci kafin ta iya bude baki tace
"Tashin hankali da ba'a saka masa rana toh yanzu Anty Laure ya zamuyi?"

"Ya zamuyi Hajiyayye ko ya zatayi? Meye namu a ciki ya wuce mu koma gefe musha kallo ba cewa tayi bamu da lafiya ba se mu jira muga yanda tata rashin lafiyar zata bayyana aure dai an rigada an daura"

"Amma tsakani da Allah babu Adalci a cikin wannan abun, yama za'ayi ace Khalil yayi aure ba tareda Umaimah ta sani ba kawai saboda ya jazawa mutane da wanda yaji da wanda beji ba duk jidalinta ya shafe su gaskiya ba'a kyauta ba" Anty ta fada kamar zatayi kuka, ita dai Mama tayi shiru tana jinsu kawai kafin ta nisa ta kalli Maman Asad tace
"Hajiyayye ki kira Nuratu da Hafsa qila ku fimu dabarar da zaku fahimtar da ita ta gane bana son azo ana tashin hankali daga baya gara yanzu duk abinda zatayi ta gama kafin tarewar Amaryar. Bari na shiga ciki na kwanta kaina yana mun ciwo".

Ita dai Maman Asad ta rasa abin cewa se Anty Laure keta bala'i Anty Saratu kuma ta rafka tagumi tana wasiqar jaki. Hasashen abinda ze faru daga sanda Umaimah ta fahimci dagaske Khalil yayi aure.

UMAIMAH
Bacci tasha da gaske dan bata farka ba se kusan qarfe uku na rana dalilin buga mata qofa da akayi. Seda ta wanko fuskarta da bakinta tukunna ta bude qofar jin me bugun har sannan be haqura ba. Fuska a hade ta bude qofar tayi tozali da Lubna, rabonda su hadu ido da ido tun haihuwar Mu'ayyad da sukazo suna.

Wani kallon banza suka aikawa junansu Umaimah ta harde hannu a qirji tana qarewa Lubna Kallo kamar yanda itama take kallonta kafin Lubnan taja tsaki cike da mugun kishin da yake nuqurqusarta na rasa Khalil a karo na biyu tace
"An fito da kaya za'a tafi kaiwa nace be kamata ace uwar gida bata gani ba dan haka ki fito ki saka albarka amma se kin daure fa dan nasan lokacinki baki samu kamarsu ba"

Gajeran murmushi Umaiman tayi kafin ta turo qofar tana cewa
"Kece baquwar saka sutura da har Lefe zeyi intimidating naki, koda yake ba'a taba kawo miki ba shiyasa" tana gama fadar haka ta maido qofarta ta rufe, Lubna ta ciji yatsa cikeda takaici ta daga murya tace
"A banza dai wlh kuma ki shirya duk wano Alqadarinko Allah ya kawo mi karyashi sati i war haka kin zama bora a gidan nan kina ji kina gani Khalil ze ringa ririta yar babynsa sedai bakin ciki ya qumeki kiyi bunga".

Haka suka kwashi Akwatunan suka fita dasu daga gidan ba tareda Umaimah tasan me akeyi bama, da Magriba Bibi take mata surutun biki za'ayi taga Akwati da yawa kuma an ce na Dady ne ko kusa bata maida hankali na, bama wannan ba hatta da zuwan Mama ma ta manta da anyi seda Ruqayya take tambayarta me zata ci, ta gaya mata akwai abincin data hadawa su Hajiya dazu kuma suka tafi basuci ba se a sannan ma ta tuna da zuwan nasu da abinda Maman ta gaya mata.
"Uhm Mama da Mafarkanta mara sa kan gado wanna karon kumai kaina suka fada" ta fada qasa qasa tana taunar Chewing gum.

Kiran wayar Safina ya shigo mata, suka gaisa Safina na tambayarta yaya dazun kuwa ta saka
"To wama ya sani ne na dai saka ban sani ba ko Mama ta gani dan jin muryarta kawai akaina, zan dai sake turara ragowar gobe inma sun shaqa su qara" Umaimah ta fada se Safina ta kwashe da dariyar shaqiyanci tana cewa
"Ke matar nan gara dai ki jira ki gani karki qara guma musu su susuce gaba daya"
"To meya ruwana ciki in ma zaucewa zasuyi su ta shafa gonata suka shiga kuma dole na hukuntasu ko dan su kiyaye faruwar hakan a gaba. Ke ni ba wannan bama kinsan wai Mama zuwan da tayi wai gaya mun takeyi Khalil yayi aure ko zeyi aurene ma ni ban gane kan abin ba"

"Halan Mama nada hawan jini ko kin san idan yayi yawa yana saka mutum ya ringa tunanin abubuwa ba daidai ba, se su ringa tunanin abu suna gani kamar a gaske ya faru Illusion ake kiran abun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login