Showing 324001 words to 327000 words out of 429394 words

Chapter 109 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1049

duba lambar Hajiya Malika ki kirata dan Allah su taima suzo"

"Amma Hajiya.."
"Kiyi abinda kawai na sakaki Jalilah" Hajiya ta dakatar da ita, wani mugun kallo ta watsawa Umaimah data tsaya taja jiran wani cikinsu ya qarasa ta sauke masa kafada tayi kafin ta juya ta sauka qasa suka bar Hajiya tsaye dan tuni Jamila ta tafi dakko wayar Hajiyar itama.
"Ki bisu idan kina son ranki da lafiyarki" Umaimah ta fada mata cikin hargagi se Hajiyan ta juya da sauri ta bar saman, Umaimah kuwa dukan qofa taci gaba dayi so kawai takeyi ta bude ta qarasa aikin data fara kafin ta ragargaza Angon ta kumaje ta ragargaza Amaryar kamar yanda tayi mata alqawari, seda ta gaji da dukan qofar amma taqi buduwa ta haqura ta sauka, bazata iya misalta abinda take ji ba a taqaice ma zata iya cewa bata tantance komai ita dai tasan tana da rai kuma tana numfashi sauran abunda takeyi umarnin zuciyarta kawai take bi badan tasan abinda take aikatawa ba. Abu daya take ji a kunnenta kuma take gani Lokacin da Mama take gaya mata Khalil yayi aure se kuma hotonsa da waccen yarinyar da yake mata yawo a ido.

Qofar part dinsu ta dawo ta tsaya, Hajiya da yayanta na tsaye daga tasu qofar da alama jiran masu kawo dauki sukeyi akayi horn Sammani ya bude Get da gudu motar Khalil ta danno cikin gidan, kamar walqiya haka ta miqe tadurfafi motar da gudu, Khalil dabe lura da tahowarta ba dan waya yakeyi da Amaryarsa daya baro yanzu zuwan da yayi gidan kaya yazo ya canza danta kafa rigimar ko bazeje gurin Kamu ba to yazo suyi hotuna dan haka yazo ya saka babbar riga,duk uban kiran da Jalilah ta ringa masa be daga ba saboda zatonsa maganar Bikin zata masa yana qoqarinfaka mota se ganin mata yayi kamar an jefota Allah ya taimaka ya riqe motar yana salati kafin ya qarasa gane abinda yake faruwa qarar fashewar glass din gefen da yake zaune ta cika gurin cikin Azama ya durqusa dukda haka seda wani ya yanke shi a gefen fuska, ya balle murfin motar da bala'in sauri ya fice ganin ta sunkuya daukar kokarar data yi masa aika aikar da ita ta fadi.

Qoqari yakeyi ya gane me yake faruwa a gidan dan shi bema gane Umaimah bace so yake yaga wace mahaukaciya Sammani ya bari ta shigo musu saukar dutse yaji a goshinsa se a sannan kuma idonsa ya gane masa Umaimah datayi biji biji kamar wadda ta tsumu a cikin hauka ta sauke masa Kokarar a qeyarsa Dafe be ko tsaya takan Zugin Azabar daya ziyarceshi ba yayi baya ganin ta sake durfafoshi ido rufe, baya buqatar wani qarin bayani abin boyene ya fito fili qila se yanzu kwakwalwarta ta gama fassara mata duk maganganun da ake gaya mata ko kuma yanzu ne ta samu gamsashshiyar hujja data saka ta yarda da, amma ita daya baro a Asibiti meya kawota gida?

Ganin tana qoqarin qara loda masa itace a duk inda Allah ya bata sa'a ya saka qarfi ya murde hannunta ya kwace Kokarar ya jefata gefe Sammani yabi da gudu ya dauke, Umaimah kuwa ganin ya rabata da makamin ta cakumi kwalarsa ta shiga kai masa duka kota ita da hannayenta se a sannan ta fashe da matsanancin Kuka tana cewa
"Allah ya isa tsakanina dakai Khalil Dan iska macuci maci Amana Azzalumi mayaudari ma ha'inci wallahi Allah baze barka ba yanda ka cuceni ka yaudareni se Allah ya bimun haqqina akan ka kaida munafukar uwarka data tayaka kuka yaudareni wallahi se kunga sakayya akan abinda kukayi mun".

"Relax Umaimah relax" ya iya fada yana qoqarin riqe hannayenta amma ina qarfin data samu yau din ya zarce misali gashi shi kuma dukan datayi masa a qeya ba qaramin shigarsa yayi ba dan daga tsayen da yake jiri yake ji kamar ze kadashi, ya waiwaya ya kalli su Hajiya da sukayi cirko cirko aka rasa me kai masa agaji a cikinsu kowa ka kalla fuskarsa ta nuna zallar tashin hankali, kome ta tuna a sukwane Umaimahn ta saki kwalarsa tayi part dinsu tana ci gaba da kuka kamar ranta ze fita Khalil ya bita a baya yana kiran sunanta, a duniya bayan ranar da ze mutu wannan ce rana ta biyu da tun faruwar al'amarin yake taraddadin zuwanta domin be san a yanda zata zo masa ba. A tsakiyar falon yaci birki ganin ta fito daga kitchen da sharbebiyar wuqa a hannu ta se kyalli takeyi ya bude ido dakyau yana kallonta ganin shi ta durfafa da wuqar ai tuni ya manta da wani jiri da zafin da qeyar sa takeyi ya kwasa a dari da sittin ya fita waje Umaimah ta mara masa baya tana kuka tana fadin

"Na gaya maka duk ranar daka kuskura ka hada soyayyata data wata sena kashe ka na kasheta sannan na kashe kaina baka ji ba yau zan nuna maka da gaske nakeyi wallahi Khalil sena kashe ka da dai ka hadani da wata mace gara na rasaka har abada" ta fada tana binsa da wuqa tsirara hankalin su Hajiya ya qara tashi gaba daya suka rude suna kiran sunanta amma ina bata ji se bin Khalil take tana kuka shi kuma yana gudu hankali tashe dan babu yanda za'ayi ya tsaya be san me zata aikata masa ba.
Get ya nufa da gudu ta bishi, yana qoqarin bude qofar aka turo ya saki ajiyar zuciya ganin Mama cikin tashin hankali Salman na bayanta da AbdulBasit dan Yayanta jikinsa sanye da Uniform dinsa na police da alama daga gurin aiki yake, ko a jikin Umaimah babu abinda ta fasa saboda ganinsu kai tsaye ta sake durfafar Khalil daya maqale jikin Get yana raba ido dake da qeya, Qafa AbdulBasit din ya saka mata ta tafi kamar zata fadi kafinta kai qasa ta tareta wuqar hannunta ta fadi Salman ya dauki yayi waje da sauri.

"Ka sakeni, ku bani wuqata in kashe shi wlh sena kashe shi ai na gaya masa amma beji ba ku rabu dani" Umaimah ta fada tamkar me maye lokaci daya numfashinta yana sarqewa idanunta suka qaqqafe kafin suyi wani yunquri jikinta ya saki gaba daya Abdilbasit ya gyara ruqon da yayi mata yana cewa Khalil
"Kama munita mu sakata a mota akaita Asibiti ta suma" se Khalil din yayi gaba ya dawo baya saboda yanda gaba daya tunaninsa ya rimice ga wani mugun ciwo da kansa yake masa sakamon dukan datayiwa qeyarsa. Su Hajiya suka qarasa bakin Get din Jamila ce tayi qarfin Halin matsawa ta kama masa Umaiman tana cewa
"Baze iya ba, shima ba a hayyacinsa yake ba abu ta buga masa akai"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha" Mama ta fada gaba daya ta rikice ta rasa abinyi, haka suka taru suka ciccibata aka sakata a motar dasu Maman suka zo su kuma suka shiga motar Khalil banda Jalila da tace babu inda zataje, Asibiti suka nufa.

Emergency aka karbi Umaiman, suna dorata akan Gado ta farka da wani mugun qarfi ta zabura zata sauka Nurses uku suka hadu suka danneta, tana bige bige tana zaginsu maganganu takeyi marasa kan gado da su basu fahimci abinda take magana akai ba abu daya suke iya fahimta kalmar seta kashe da take ta nanawata a haka Likitan yayi mata allurar bacci wadda seda akayi da gaske kafin ta dauketa.

A can reception kuwa gaba daya sukayi cirko cirko banda Khalil daya zauna a qasa ya dafe kansa da yake ji kamar ana girki a ciki tsabar zafin da yayi masa, Abba da Mama ta kira tun suna hanya ya qaraso Asibitin tareda Anty hankalinsu a mutuqar tashe, a taqaice suka gaya masa abinda ya faru suna nan tsaye suna jajantawa Wata Nurse ta fito da gudu daga ward din da aka kwantar da Umaimah tana kiran Dr,
"Wannan patient din da aka kawo Dr inaga tana da tabin hankali gata can ko 29 mins ba'ayi dayi mata allura ba ta farka tana ta buga kanta a bango tana kuka mun rasa ya zamuyi da ita" Nurse ta fada jikinta na rawa dan tunda take a Asibiti bata taba cin karo da psychiatric patient ba se yau kuma shahararre da haukansa yayi nisa irin na Umaimah.

A fusace Abba yabi bayan Dr zuwa dakin, Umaimah na tsaye tana zugawa Nurses din zagi na tsamar nama akan su bude mata qofa ta fita sunqi Dr ya bude ta waje suka shiga tana ganinsa ta yunqura da niyyar fita Abba dake bayanaa ya zabga mata marin daya sa tayi gefe ta tsaya babu shiri
"Ki nutsu ki shiga hankalinki wlh tun kafin kija nayi miki abinda zanzo ina nadama daga baya. Ke wace irin kafaffiyar yarinya ce da baki san Annabi ya faku ba? A rayuwarki baki san komai se tashin hankali da bala'i ke baki zauna lafiya ba mu baki barmu munsamu nutsuwa ba kashe mu kike so kiyi kome Umaimah?"

"Ni babu ruwanku dani Abba babu wanda nace ya shiga sabgata baku ga abinda akayi mun ba Aure fa Khalil yayi Abba ya munafunceni ban sani ba se yau sannan kuma ku hanani hukuntashi wannan ai ba adalci bane nidai tunda babu me qaunata duk ba zaku iya kwatarmun haqqina ba se ku barni daman nasan ba sona kuke yi ba na sani ma da hadin bakinku yayi shi yasa Mma dasu Anty Hafsa suka ringa zuwa suna fadamun maganganu ashe kunsan abinda kuka shirya nidai Allah ya isa kuma an cuceni Allah yana kallo bazan yafe ba duk wanda yake sa hadin baki a maganar nan Allah ya bi mun haqqina" Umaiman ta fada cikin matsanancin kuka Abba da baqin ciki ya qumeshi ya sake niyyar kai mata Mari ta goce yayi taga taga ze fadi saboda jirin daya taho masa Likita ya riqeshi yana cewa

"Yi a hankali Alhaji karka fadi kayi haquri ka kwantar da hankalinka".
Cikin bacin rai ya kalli Umaimah da har sannan take kuka yace
"Kaiconki Umaimah kaicon zuciya irin taki, ashe ke ba zaki taba yarda da cewar duk abinda ya samu bawa daga Allah bane? Ba zaki iya haquri da duk jarabawar data sameki a rayuwa ba?
Iya wannan auran idan kinada hankali ya isheki ishara amma a maimakon ki dauki darashi ki nutsu sema sake bude babin hauka kikayi ko to kiji da kunnenki karki fasa duk abinda kika yi niyya zan kuma sake jaddada miki Khalil yayi aure babu kuma abinda ya isa ya tada wannan aure se ikon Allah kuma ko kinso ko baki so ba a yau ba se gobe ba ze tare da Matarsa a cikin gidanki a dakinki tunda kin Lalata abinda iyayenta suka saka mata idan yaso baqin ciki yasa ko hadiyi zuciya ki mutu kowa ya huta yar banza me zuciya irinta kafiranfarko" yana gama fadar haka ya sa kai ya fice daga dakin zuciyarsa na wani irin tuquqi, badan karya butulcewa Allah ba daya yi nadamar kasancewar Umaimah jininsa.

Cak ta tsaya da kukan kalamansa sukayi mata dirar Mikiya wai Abba ne yake gaya mata Khalil ze tare da wata mace yau a dakinta akan Gadonta? Seta miqe da wani irin sauri a take kuma kamar wadda aka mayar ta fadi yaraf a gurin kamar me farfadiya tana jijjiga Likitan yayi kanta da sauri Nurses suka rufa masa baya, seda suka mayar da ita kan gadon kafin suka shiga bata taimakon gaggawa sun kwashe sama da minti talatin akanta kafin jijjigar ta tsaya jikinta ya saki gaba daya numfashinta kansa se a hankali dole suka saka mata oxygen bayan Likitan ya mata duk abinda ya kamata yayi suka fita daga dakin aka barta da Nurse guda daya.

Reception din ya koma yana dafe kansa da jarabar Umaimah tasa ya fara maaa ciwo, suna zaune kamar ana zaman makoki sabanin da yanzu su Nuratu sun qaru da wasu daga bangaren Hajiyar dan tuni Lubna ta dake maqale a daki tunda tasha matsa ta kai labari Family group dinsu. Suna ganin Likitan Hajiya da Anty sukamiqe da sauri suna tambayarsa jikinta cikeda qosawa yace musu
"Da sauqi amma kuyi haquri yanzu ku barta kar wanda ya shiga inda take saboda tana da buqatar hutu sosai"

"Toh likita cikin jikinta fa, daman ba kunce gobe zaku mata aiki ba meze hana ayi yanzu saboda gudun kar wani abu ya same shi" Hajiya ta fada se likitan ya girgiza kai yace
"Baze yuwu ba Hajiya, maganar gaskiya a yanzu haka ta sake Suma sannan jininta ya hau har ya wuce qa'ida baze yuwu muyi mata Allurar Anesthesia ba saboda idan abun yazo da tsautsayi zata iya zarcewa dole se mun jira ta farka sannan jininta ya daidaita kafin koma menene ya biyo baya, nidai roqon da zanyi muku ku barta ta huta dan Allah zuciyarta da kwakwalwarta su samu hutu sosai, Ina Mijinta ya biyo ni ina son magana dashi" daga haka ya wuce office ya barsu nan a tsaye.

Khalil ya fito daga wani office dayaga likita shima ya auna BP sa ya rubuta masa magani yace yasha ya samu yayi bacci ciwon kan nasa ze sauka, seda yaje gurin likitan daya duba Umaimah ya sake masa bayanin daya musu kafin ya fito yaje pharmacy ya siyi maganin da aka rubuta masa a gurin ya sha ya sake dawowa reception din ya tarar dasu, Abbane ya kirashi suka fita tare. Duk su biyun idan ka kallesu kasan babu me nutsuwa a cikinsu, can gurin wata bishiya suka tsaya Abban ya kalli Khalil da shi kuma yake kallon qasa yace
"Ibrahim kayi haquri ka qara akan wanda kakeyi dukda dai Allah ya sani ban rufeka ba tun kafin na baka auran Umaimah seda na zaunar dakai na gaya maka wacece ita kuma a hakan kace kaji ka gani kana sonta na tabbata a sannan baka san cewar Jidalinta ya kai har haka ba, bamu tara sani da ikon Allah kuma ita qaddarar mutum baya kauce mata badan da qila yanzu kana gudanar da rayuwarka cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. A taqaice abinda nake so na gaya maka shine karka dauki wannan abun da tayi a matsayin wani abu da ze tsorata ka kota dakatar dakai daga yin duk abinda kayi niyya. Naji ance ta lalatawa Amarya dakinta kuma gobe ya kamata ta tare ko?"

Khalil ya gyada kai kawai se Abban yaci gaba da cewa
"Shikenan amma hakan baze canza komai ba, ka dauki dakinta da take ciki da komai ka bawa Amaryar ita kuma idan ta warke ta shere inda ta lalata ta koma ciki ban kuma yarda naji ka ce ba haka na Umarni na baka idan har ka daukeni a matsayin Uba sannan kamar yanda aka tsara tarewar Amarya a gobe idan Allah ya kaimu zan kira Kawunka nida shi zamu dakko Maka Amaryarka mu kawo maka ita idan Allah ya yarda".

Kallon Abban yayi yana so yayi magana amma ya sake katse shi da cewa
"Bana so naji komai sannan maganar nan ta tsaya tsakanin nida kai ko Mahaifiyarka karka fada mata nida kaina zanyi mata bayani babu abi da za'a jira kuma yarinya zata tare a dakinta ita kuma Allah ya kaimu ta tashi zanyi maganinta in Allah ya yarda.

Se Magriba suka watse daga Asibitin aka bar Mama da Anty Hafsa har sannan kuma Umaimah bata kuma farkawa ba sedai likita yana shiga ya dubata ya kuma tabbatar musu babu damuwa zuwa dare zata farka suna fatan kuma kafin sannan komai ya daidaita.
Guraren goma Khalil ya koma Asibitin dan tun bayan da suka gama magana da Abba ya wuce gida Adaidaita ma ya hau ya kaishi be zata ze iya bacci ba nan da sati daya ma se gashi da taimakon maganin daya sha yayi bacci sosai har bayan Isha sannan ya tashi bayan yayi wanka ya rama salloli ya leqa Dakin Humaira yaga barnar da Umaimah tayi, gaba daya gidan Qamshin Humarar da suka malale a qasa yakeyi ya maida qofar ya rufe yana tunanin abinyi ya wuce bangaren Hajiya a canya tarar da Jalilah ta kafa daba sun dawo daga gidan biki dan duk wannan tashin hankalin da aka sha seda taje da mutanenta Jamila ce kadai bata je ba suna Asibiti tare dasu Hajiya sunje sun sha bidirinsu dan basu gaya musu abinda ya faru ba suma kuma yan jeren da yake ba masu surutu bane basu fadi abinda akayi ba Mama kadai Sumayyan ta gayawa ita kuwa da dama tasan za'a rina batayi mamaki ba.

A daki suka qule da Hajiya take gaya masa zancen kawo Amarya gobe da Baban Umaimah yayi,
"Babana ina jin tsoro, nayi nayi Alhaji ya fahimceni amma yaqi ya kum samu goyon bayan Baban ku Abubakar sun kafe akan gobe zasu dakko Amarya dan har ma sunyi magana da Kawun nanta su kuma sun sanar da Hajiya Hauwan dazu ta kirani take ce mun babu komai hakan ma yayi ai suma iyayenta ne daga baya duk me son zuwa yaga daki se yazo, nidai ban gaya mata halin da ake ciki ba gaskiya dan bansan ta inda zan fara mata bayani ba" Hajiya tayi maganar cikin jimami, se Khalil yace

"In sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi Hajiya"
"Toh Allah yasa" daga nan yayi mata sallama ya koma Asibitin. A canma dai maganar suka sakeyi da Mama da Anty Amina suna sake qarfafa masa guiwa, har gurin sha biyu yana can kafin yayi musu sallama ya tafi har sannan kuma Umaiman bata farka ba.

Kamar yanda Abba da Baba Abu sukayi Alqawari washe gari aka kawowa Khalil Amaryarsa, sedai basu je da kansu ba kamar yanda suka tsara daga baya suka canza shawara dan haka Aka wakilta Mata guda uku daya daga bangaren Mahaifinsa daya qanwar Hajiya se Aminiyarta daya suka dakko masa Amarya ta iso da rakiyar nata iyayen guda hudu suma. A bangaren Hajiya aka tarbesu kuma anan suka barta suka wuce suna yi musu fatan zaman lafiya.

Khalil na Asibiti aka kawo Amaryar dan wunin ranar gaba daya acan yayi shi kuma tun jiya da rana da suka rabu akan zeje ya canza kaya ya koma suyi hoto basu sake yin waya ba wayar tasa ma a motar ya barta be dauka ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login