Showing 363001 words to 366000 words out of 429394 words

Chapter 122 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

956

cikin sanyi tace mata
"Ki samu Robobi ki juye ki saka a Freezer idan ta kitchen din bata dauke ba ki kawo nan ki saka a Fridge dare yayi yanzu da Safe maga yanda za'ayi" daga haka ta shige daki ta barta babu yanda ta iya ta koma ta dakko Kular abincin tayi yanda Maman tace dan tasan idan ma ta barshi ya lalace qarin laifi ne a gurinta. Seda ta gama Adana abincin tas ta kwashe kwanukan wanke wanken data bari bakin famfo ta shigar dasu kitchen kafin ta koma daki tana ci gaba da kuka, daren bata iya runtsawa ba tunanin yanda zata cinye shinkafar nan safe rana dare harta qare takeyi idan Abban be haqura ba seda Asuba ta gabato bacci ya fara fizgarta, motsin shigowar Abba dasu Salman daga Masallaci ya farkar da ita kamar wadda aka koro fit ta fice daga dakin ta tsaya gaban Abban tana muzurai so takeyi ta sake kafa masa magiya amma yanda taga fuskarsa a daure ya hanata iya bude baki tace masa komai se hawaye suka fara mata tsere Abba kuwa yayi wucewarsa ciki ba tareda yabi ta kanta ba indai juninta rashin ji yana da hanyoyin dafata cikin ruwan sanyi har tayi laushi kuwa.

Ciki ta koma tana sharar kwalla tayi Alwala tayi sallah, harta kishingida tana ci gaba da share Hawayen ta tuna da zancen girke seta fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa musamman data tuna itace zata hura kai wannan bala'i da me yayi kama? Sanda tana gidanta iyanzu tana kan Royal Bed cikin Turkish Duvet ga sanyin Ac da qamshin freshner suna ratsata, tana kwance Ruqayya zata shigo mata da abin kari har kan gado ta shiga Jacuzzi tayo wanka taci a yangance ta sake kwanciya amma yanzu Murhune yake jiranta da Itace kai Allah ka kawo mata dauki. Kuka tasha bana wasa ba kafin ta lallabi kanta ta fita dan zaman ba amfani ze mata ba bandama ta sake ja wa kanta wata shiga ukun.

A qofar falon Mama ta durqusa ta gaisheta ta daga mata kai kawai a hakan ma taji dadi dan tunda ta dawo Maman bata taba amsa gaisuwarta ba, murya na rawa tace
"Me za'a dafa Mama?"
"Kunun tsamiya da Alala, wake yana nan an jiqa seki wanki ki bawa Yasir ya kai markade shima qullin kunun yana nan a Kitchen idan kinga dama ki bata ke zakiyi taci harsu qare" Maman ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba harta miqe kuma ta koma murya na rawa tace
"Mama kinsan idan na dama kunu tsinkewa yakeyi, sedai na dafa Abba kuma baya so a dafa".

Shiru Maman tayi kamar ba zata ce mata komai ba se kuma ta numfasa tace
"Idan ruwan ya tafasa kizo ki gaya ki debi kwai ki dafa a saka a cikin Alalan" daga haka taci gaba da jan carbinta Umaimah ta ja qafafunta ta wuce Kitchen din. Waken ta fara dubawa ta sauke ajiyar zuciya ganin gyararrene har ya juqu ma dan haka ta wanke shi ta dubo Attaruhu da Albasa ta zuba cikin takatsan tsan, sedata hada markadan tsaf kafin ta wuce qofar dakin Anty ta kwankwasa dan babu wanda ya fito a yaran Lahadi ce kuma an musu hutun Tahfiz ga garin yanayin sanyi ya fara shigowa tasan suna nade a bargo se ita da uwarta bata sonta ce take gararanba a tsakar gida da farar safiya. Tafi Minti biyar tana bugu kafin Antyn ta bude fuska babu yabo babu fallasa tana kallonta, kamar karta gaisheta saboda qin roqar mata da Abba da batayi ba jiya amma ta dake tace mata ina kwana.

"Mama ce tace Yasir yazo ya kai markaden Alala" ta fada a cukule itama Antyn murya babu walwala tace
"Yasir ya tashi da Zazzabi sedai ko Sharifa dan Firdausi ma tabi Fatima jiya". Jin cewar se Sharifa yasa ta juya ba tareda ta cewa Antyn komai ba dan indai yar iskar yarinyar nan ce qarshe seta jawo mata wani laifin ace bata gama da wuri ba sawunta a likafa ta wuce ta kunna wuta danma itacen busashshene tana yi tana hawaye wai ita Umaimah ce ta sake dawowa girkin itace? Seda ta hada wutar ta dora ruwan kunu kafin ta leqa waje ta samo Almajiri ya kai mata markaden a ranta tana Mamakin duk Almajiran da suke musu hidima a gidan suna ina tunda satin ya kama ta dena ganinsu ko saboda an shirya maida ita boyi boyi yasa aka sallamesu.

Ta kalli tsakar gidan ta tabbatar kuma ita din ce dai me sharewa duk dan saboda a jance zancen cin shinkafa ta tattara kwanukan da aka fito dasu na wanke wanke a gefe ta hau shara, kafin ta gama bayanta ya riqe dakyar ta iya miqewa saboda Azabar ciwon daya dauka ta wuce dakin Mama tana kuka kamar yarinya dan ruwan ya tafasa Mama ta kalleta kawai bata ce komai ba, ganin Almajirin ya kawo markaden ta kama hada Alalan tana yi tana diga musu Hawayen daya kasa tsayar mata a ciki Mama dai ta dama kununta tafi ki mutu bata ce mata ba se sanann Anty ta fito suka gaisa ta kawo Flask din da ake saka musu Kunun Maman ta zubawa kowa nasa ta koma dakinta. Umaimah na zaune tana jiran Alalal ta dafu tana aikin kuka kamar matar Mamaci har yayi ta kwashe ta hada kwanukan ta hau wanke wanke. Tana kallo kowa ya debi abin karinsa yaci kamar kwayar idonta zata fita saboda kuka yanzu duk ta gama wahalar nan ba zataci ba kenan ake nufi haka ta wuce daki ta kwanta dakyar saboda ciwon jiki tana kuka data ci shinkafar nan ta gwammace yunwa ta kasheta kawai kowa ma ya huta tunda an tsaneta. Sha biyun rana Mama ta kwala mata kira, ta yunqura dakyar ta fita jikinta kamar wadda ta fado daga kan bishiya saboda ciwo ta tsaya tana kallon Zogalen dake jibge a qasa ba'a tsinke shi ba ta kalli Mama dake cewa
"Gashi nan Dambu zakiyi tsakin kwano biyu zaki auna dan za'a kai nan baya gidan Malam Bala anyi Rasuwa dazu ga Madambaci nan nasa a aro na gidan su Harira shi babbane sosai in kika hada da wannan zaki fi sauri".

"Dambu" ta maimaita tamkar bata san kalmar ba, ta waiwaya jin Yaro yayi sallama da wani uban rafkeken madambaci ya ajiye take ta tuno da zuwansu gidan Qawarta Abu Maman Nihal a irinsa suka tarar da ita tana dambu shikenan ta shiga ukun ta ta lalace. Cikin kuka tace
"Wlh yunwa nakeji Mama bazan iya aikin dambu yanzu ba"
"Ga shinkafarki can ai ki diba ki dumama kici kuma ki hanzarta ki dora da wuri dan Abbanku yana gida kin san kuma Azahar nayi ze nemi Abinci" Maman ta bata amsa cikin ko in kula kafin ta zura Hijabin dake hannunta tana cewa
"Idan kin gama bamu dawowa ba ga Kwano nan(ta nuna mata wata fanteka) indai kinyi awon daidai ragowar ze cika wannan bayan ki debar mana na gida se bawa Ko Salman ne ya miqa gidan rasuwar se Mundawo" tana gama fada tayi gaba sega Anty ta fito da fitsararriyar yarta inji Umaimah a bayanta da alama tare zasu tafi suka rankaya suka barta a tsaye ta rasa abinyi se hawaye takeyi.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 78

Zama tayi gaban zogalen tana kukan daya aureta, Abba ya fito daga bangarensa yayi mata kallo daya ya wuce abinsa ko amsa Adawo lafiyar datayi masa a shaqe beyi ba yana fita Ummu-Salma dake labe ta fito daga dakinsu. Tausayin Umaiman ya cikata, tun jiya da dare Sharifa ta bata labarin ance ita zata ringa aikin komai ta tausaya mata dan abin yayi mata yawa musamman da bata sababa ko sharar gidan aka bar mutum da ita aiki ce balle ga wanke wanke Ina laifin ace ta ringayin iya girki? A hankali ta qarasa kusada ita tace
"Kiyi haquri Anty Umaimah nasan Abba ze huce ya sassauta miki yanzu dame zan kama miki kinga lokaci yana tafiya?".

Fuska shabe shabe kamar wata yar Yaye ta kalli Ummu-Salma tace
"Yunwa nake ji bazan ma iya aikin ba idan banci Abinci ba"
"To bari na dakko Miki akwai ragoqar Kunu da Alala a dakin mu se kici" Salma ta fada harta miqe Umaimah ta tuna da maganar Abba ta dakatar da ita tace ta bari. Shinkafar dai da bata so ta debo, Ummu-Salma ta karba nan da nan ta hada jajjagen zallar tumatir da Albasa tayi mata Sauce ta dumama mata shinkafar tana nan zaune gefe kamar me shirin gangarawa ta kai mata Abincin harda Baqin Shayi kafin kace me kuwa ta tadashi ko tuna rashin dadin shinkafar batayi ba ta cinye ta tsaf tasha ruwa sa'annan ta fara gani daidai dan yunwar ta mata karo, Da rana jiyan bata wani ci dayawa ba kuma haka ta kwanta bata ci tuwon ba ga safiya tayi har sha biyu sannan ta sakawa cikinta Abinci.

Tareda Ummu-Salman sukayi aikin Dambun nan da nan suka gama ta rabashi kamar yanda Maman tace, seda suka gyara tsakar gidan tas suka wanke kwanuka kafin ta shige daki jikinta na nuqurqusa. Ba daban Salma ba da yau bata san yanda zatayi da ranta ba ta shige bandaki tana qunar rai, Dambun yayi kyau duk kuma wahalar data sha babu rabonta a ciki se hawaye haka tayi wanka ta fito tana ci gaba da tsane hawayen. Tayi sallah saboda baqin ciki a gurin ta kwanta cikin Sa'a bacci yayi awon gaba da ita bata farka ba se ana idar da Sallar La'asar. Fuska a kumbure dalilin kuka da bacci ga gajiyar dake tare da ita ta fita tsakar gidan bayan tayi sallah, babu kowa se tashin murya da take jiyowa daga falon Mama seta nufi can, Anty Laure ce da Anty Uwani. Daga bakin qofar ta durqusa ta gaishesu Anty Uwanin ta amsa Anty Laure kuwa sama ta dage kanta, Mama ta kalleta tace

"Ya akayi?"
"Dama tambaya zanyi me za'a dafa!" Ta fada muryarta na rawa se Maman ta nuna mata wani farin bokiti me dan girma tace
"Ga Awara nan ita za'a soya se ki damawa Abbanku Kunun gyada shikenan". Da 'toh' ta amsa ta shiga falon a darare ta Kinkimi bokitin zata fita Anty Laure tace
"Wai ni Umaimah takaba kikeyi ko qaqa? Tun dawowarki gidan nan kike fama da wadannan shegun rigunan bana jin sun kai goma Zawarci hauka ne ko kuwa Qazantar ce har yau baki dena ba duk ina uban jibgin suturunki da bazaki ringa sakawa?"

Seta rasa amsar da zata bata ta kalli Mama kawai dan dai tun dawowarta gidan kayan datayi amfani dasu zaman Asibiti ne taketa dirza basu fi goman ba ta bakin Anty Laure ita kuma ganin ba inda taken zuwa yasa bata damu da bin ba'asin kayanta ba, Mama ce ta nunawa Anty Laure Dayan dakin dake cikin Falon ta tace
"Suna ciki Akwati sun kusa Ashirin ni har Mamakin uban suturun da suka debo da sunan nata na ringayi dan da tana gidan nasa ma ba sawa takeyi ba. Tun tana Gadon Asibiti su Nuratu suka debo mata kayan katako ne Alhaji yace a barsu tunda daman shi yayi"

"Aa shi kuma Yaya wace irin magana ce haka kamar yaya shi yayi? Ai ba haka nan aka kaita babu komai ba babu abinda ba'a sai mata ba na aure canji ya mata kuma ko bataje da komai ba wadannan da ya matan sun zama nata ai kyutace saboda baqin hali shine kuma da akace ya barsu ya riqe din" Anty Laure ta fada se Mama ta muskuta tace
"Aa fa ba laifinsu bane babu yanda basuyi ba akan a diba Alhaji yace Aa yace ya tattara ya siyar ya rage Asarorin data masa dan ashe har Mota me tsada yarinyar nan ta fasa masa bamu sani ba se daga baya"
"Kuma haka ne fa ai shikenan kinga kinyi zaman shekara bakwai a banza baki tsira da komai ba randa kika tashi yin aure kina ruwa dan mun rigada mun miki na fari ke ba sana'a ba ke ba aiki ba toh Allah ya rufa Asiri".

Ita dai Umaimah tuni ta fice daga tsakar gida take jiyo sababin Anty laure, ta rafka tagumi wato duk lokacin nan an debo mata kayanta amma babu Wanda yace mata gasu ta tambaya kuma cibi ya zama qari saboda tsabar an tsaneta kayan dakin ma bar masa akayi ai shikenan. Haka ta shiga yanka Awara ta gama ta jere duk kayan da zatayi Amfani dasu cikinta se kiran ciroma yake amma ta qudurce ko zata yi me ba zata sake cin shinkafar ba, ta dazu ma yunwa ce babu yanda zatayi ga yar kwaskwarimar da Ummu-Salma tayi mata toh yanzu saboda mugunta suna dawowa Anty ta aiketa wai gidan Yayarta tasan kuma dan karta tayata aikine ai Allahya kaimu gobe da yake girkin Antyn sedai ta fito tayi abinta dan bayi zatayi ba.

Tana shirin Hura wuta Yasir ya shigo da barkono da alama aikensa Akayi ya siyo ya ajiye mata harda kayan Maggi ta kalle shi ta kalli barkonon, ko zamanin yarinta bata daka dan da tayi hannu ta zeyi kanti seta dade tana jinyarsa kafin ya warke ko tuqin tuwo tayi me yawa hala yake mata shine yanzu za'a kawo mata wani yaji kusan kwano guda ta daka me za'ayi dashi? Yasir kuwa yana aje mata ya wuce dakin Mama ya fito da ledar citta da Tafarnuwa ya ajiye mata yana cewa
"Mama tace ko raba barkonon biyu kuma kar ki saka farin Maggi iya dunqule da gish??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????iri za'a saka". Seta wai waya ta kalli dakunan kafin tayi qasa da murya tace

"Kana ji ka dauka ka kaiwa Maman Nana kace nace ta bayar a daka yanzu ka kawo mun in ka dawo zan baka dari biyar maza ka boye kar ka bari wani ya gani" jin zata bashi cin hanci ya tattari kayan ya fice dasu Umaimah kuma ta shiga qoqarin kunna wuta a ranta tana ayyana kota kunna Gas tunda Abban baya nan sega Yasir ya dawo da barkono ya dire mata yana cewa
"Abba yace a dawo dashi". Bata iya amsashi ba saboda takaici, kenan Abban na waje. Seta miqe da sauri ganin An kawo wuta, a Blander ta hada ta warwatsa musu yajin tana kuma sane da Abban yafi son dakan hannu dan Maman Asad na siyar da su Spices da Yaji idan ta kawo niqan Inji baya ci sedai a daka masa a turmi.

Ba yanda ta iya ta shiga suyar Awara, tana cikin tsame kaskon farko Salman da Abokansa biyu suka shigo gidan da sallama. Ahmad daya daga cikinsu irin mutanen nan ne nan masu shegiyar zolaya ya kalli Umaimah harda bude baki irin na mamakin nan yace
"Kai Salman dama Yah Umaimah na siyar da Awara shine baka gaya mana munzo mun yi mata cikini ki ba? Dan Allah kalli yankan manya manya ba irin na Rabin bakin layi ba Yah Umaimah a samun ta dari a kyauta mun saboda naje majalisa nayi miki tallah" tsabar wulaqanci Salman da dayan yaron suka kalleta suka tuntsure da dariya harda duqawa qasa saboda yanda bilhaqqi tayi kama da me siyar da Awarar gasken.

Zuciya ta zowa Umaiman wuya kamar zata yi Amanta ta kalleshi tace
"Uwarka ce me suyar Awara bani ba shege dan masu..."
"Akul dinki da yi mana zagi a cikin gidannan idan ba haka ba sena gurje bakinki, aida Awarar kike soyawa ma da kin samu abinyi" Abba daya shigo ya dakatar da ita, seta fashe da kuka babu shiri tana cewa
"Haba Abba ku kumin sannan wasu su shigo sumin ku goya musu baya wannan wane irin abu ne?"
"Halinki yaja miki da ace kin zauna inda Allah ya ajiyeki da babu wanda ze ganki ya zageki amma tsarin da kika dauka kenan ai shikenan" ya fada yana wucewa ciki dan ana shirin shiga sallar Magriba ne. Salman da Abokansa kuwa jiki a sanyaye suka fice daga gidan Umaimah ta ringa kuka tana suyar Awara, wlh da Ace yaron nanya matso kusada ita seta dulmiya kansa a kaskon dan ubansa sedai duk yanda za'ayi ayi. Haka ta gama suyar wata danya danya wata ko harta qoneta ta bar musu a gaban kaskon ta shige daki tana ci gana da gursheqan kuka. Waiita me tayi data cancanci wannan qasqanci haka?
Idan laifinta suke gani ai ba ita ta kashe auranta ba su suka ce a sakota akan me kuma za'a kafa mata qahon zuqa idan ba'a dubi cin Amanar da Khalil din yayi mata ba kuma ai ba a qullaceta ba inma taqamarsu abinda ta masa ba gashi nan ya warke ba yana yawonsa ita fa illar daya mata ai harta mutu ba zata warke daga ciwon cin Amanar daya mata ba. Yayi aure a bayan idonta sannan ya bita da tukuicin saki. Haka ta sake kwanciya bata ci komai ba dan tunda ta shiga dakin bata sake fitowa ba kuma babu Wanda yabi ta kanta da safe kuwa dakyar ta ke zama saboda yanda jikinta yake rawa dalilin Yunwa. Yanda ta fito tana bin bango ga fuskarta data jeme a dare daya ya sa Mama kama aikin abin kari saboda yan makaranta da Abbazeyi fada shima daya ga Umaiman yayi shiru duk sun san yunwa ce take rarakarta, ta gama bin bango kamar qadangaruwa Mama ta daga Ruwan shayi dan tun dare an siyo biredi suka hada da ragowar Awarar kowa ya kama inda zashi ganin babu sarki se Allah yunwa na neman halakata yasa ta farwa shinkafarta da qanqararta da komai ta hau ci.

Seda taci taci se Amai kuma ta tafi bakin famfo ta ringayi gaba daya jikinta yayi laushi dakyar ta iya kuskure baki ta tashi ta koma qofar dakinta ta zauna jikinta na kaf kaf kamar zazzabi na shirin rufeta. Duk yanda Mama taso ta dauke kai seta kasa ta tafi dakin Abban ya zaune yana karyawa ta zauna a kujerar dake kusa dashi a sanyaye tace
"Alhaji kayiwa Allah ka sassautawa yarinyar nan akan batun Abinci kar yunwa ta illa tata"
"To se me? Mu illoli nawa tayi mana?" Abba ya fada ba tareda ya kalleta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login