Showing 60001 words to 63000 words out of 429394 words

Chapter 21 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

974

wuce mata mazaunai, hannun vest ne da ita ga qirjin ta da akayi da Lace tasan babu abinda zata kare seta ajiye tana cewa
"Tabdi ni zan saka wannan abun ma kenan? Yanzu kuma idan ban saka ba se yaji haushi, bari na saka sena dora Hijabi akai" ita kadai tayi kidanta tayi rawarta.

Sanda ta saka rigar ita kanta juyawa ta ringayi tana kallon kanta, tayi mata kyau ta kuma karbi jikinta, bugun qofar da taji yanayi ya sakat saurin rarumar Hijab ta saka kamar mara gaskiya ta bude qofar.

"Muje" ya fada bayan daya shaqi daddadan qamshin da dakin yakeyi, ya nuna mata qofa tayi gaba yana binta a baya zuciyarta kamar zata fito waje saboda tsorio.

Dakin da yake mazaunin nasa suka shiga, se taga gadon ciki har yafi na dakinta ma kyau ta tura baki tana qarewa dakin kallo
"Lafiya" ya fada yana kama hannunta, seda ta kuna shagwabe fuska kafin tace
"Gani nayi gadonka yafi nawa kyau"

"Gadon mu dai, nan shine dakin mu ni da Umaimatah" ya fada yana yi mata peck a baki ta sunkyar da kai dan ita fa kunya abun yake bata.

Sallah yaja su raka'a biyu bayan sun idar ya dafa kanta ya yi musu addu'a, duk tambayoyin daya kamata yayi mata akan addini ya mata kuma Alhamdulillah ta bashi amsa daidai saninta bayan sun shafa addu'ar yace ta hau gado ta kwanta shi kuma ya fice daga dakin, kusan minti biyar da fitarsa har idonta ya fara rufewa saboda dagaske ta gaji tana buqatar hutu taji an turo qofar.

Jallabiyyar dake jikinsa ya cire ya ajiye kafin Kai tsaye ya nufi kan gadon Umaimah na ganin ya taho ta buga tsalle ta koma gefe, ita fa da yace ta kwanta harga Allah ta zata ita kadai zata kwana bata ankare ba se ji tayi fit ya zare mata hijabin da take ta faman nuqu nuqu dashi da fasa qara saboda yanda ya sake kunna ragowar fitilun dakin masu haske yana qarewa rigar jikinta kallo, zillo tayi zata sauka daga gadon ya kamota da hannu daya ya saka dayan ya kashe fitilu, ganin bata san dare ba ita ta ware baki tana masa ihu yayiwuf ya hade bakinsu guri daya daga nan labari ya chanza salo.

Asuba ta gari Mr and Mrs Bayero


PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
PAGE 18


A hankali ta zame jikinta daga nashi ta tashi zaune tareda jingina bayanta da Allon fuskar gadon tana qarewa Khalil kallo yana sharar baccinsa harda munshari. Badan kartayi qarya ba se tace har wani kyau da kyalli fuskarsa ta qara, kamata yayi ace taji haushinsa akan al'amarin daya farun a daren jiyan tsakaninsu wanda ya girmi tunanin kwakwalwarta ballantana harshen ta ya iya furtawa.

Yanda Khalil din ya gigice mata ya ringa sarrafata kamar ya samu pencil da takadda yana zane abinda yafi kwarewa akai sannan bakinsa ya kasa rufuwa daga surutan da idan ta tunosu ma seta rufe ido tsabar kunya abinda yafi tsaya mata a rai yanda ya ringa maimaita kalmar yana sonta yana qaunar ta da irin ruwan Albarkatun daya ringa zuba mata su suka taru suka wanke gingimemen laifin lallasa mata jiki da yayi.

Sauke qafafunta tayi qasa a nutse ta miqe cikin takatsantsan gudun kartayi wani motsi me qarfi ta jigata jikinta da a daren jiya ta ringaji kamar tayi hatsari sedai lafiya lau ta ringa takawa har tabar dakin bayan ta kulle masa qofar a hankali.

Dakinta ta koma, irin ruwan daya hada mata cikin dare ya wanketa dakansa ta sake hadawa ta shiga ciki ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.
Khalil qarshene gurin tattalin mace ta shaida hakan a qasa da awa ashirin da hudu da zuwanta gidansa.

Yanda ya ringa lallabata yana tarairayarta a daren jiya bayan da komai ya kammala a tsakaninsu take tunawa, ya tara ruwa duk noqewa da rakin da take haka ya sakata ciki yana diba yana gasa mata jikinta seda ya canza ruwa uku kafin ya barta tayi wankan tsarki ta dawo dakin da har ya canza bedsheet ta sake kwanci.

Be barta haka ba ya sake tada ta, madara me sanyi ya cika cup da ita ya bata ta shanye sannan ya ballo mata pain killers tasha ya ringa bubbuga bayanta yana fada mata kalamai masu dadi har ta koma bacci kafin shima ya kwanta.

Da asuba me seda ya saka ta sake gasa jikinta kafin ya tafi masallaci ya barta bayan ya kulleta ta waje dan kamar ya sani niyya tayi yana fita ta gudu dakinta saboda cewar da yayi idanya dawo za'a qara tunda yaga ta warke shiyasa tana idar da sallah ta haye gadon ta qudundune kamar me bacci bawan Allah kuwa be tada ita ba se kwanciya yayi shima a bayanta ya rungumeta a jikinsa, tun tana jin motsinsa har baccin gaske ya dauketa se gurin qarfe tara ta farka.

Jin ruwan da take ciki ya salamce ya sakata fita daga bahon ta bude rariya ruwan ya tsiyaya, har ta tara wani ruwan zatayi wanka ta tuna da wani Kwandon turaruka da Rumasa'u ta bata jiya a matsayin gudummawarta tace turarukan wanka ne, seta dauki towel ta daura ta fita.

Kwance ledar da aka lullube su tayi ta juye Manya da qananan robobin akan gado wani irin cakudadden qamshin su me shegen dadi ya daki hancinta seta dauki guda daya ta duba sunan dake rubuce jikin sticker *MEERAH_PERFUMES_MORE* kamar ta san sunan, tabbas wanna sunan Matar da Akayi musu turaren wutar da aka jera musu a Show glass a gurinta ne lallai dole ma suyi kyau.

Dubawa ta shigayi ta kwashe wadanda aka rubuta *Bath Mist* ajiki ta wuce dasu bandakin, ita kadai ta ringa sakin murmushi sanda ta zuzzubasu a ruwan wankan wani irin Exotic qamshi me sanyi da kwantar da hankali sukeyi haka tayi wankanta ta fito kamar kar ruwan ya qare amma babu komai kuma ta samu nayi.

A gaban mirror ta zauna tana shanshana fatarta dake kyalli da walwalin ingantaccen gyaran da Anty tayi mata ga wani kata'in qamshi da takeyi na Birth mist din *MEERAH_PERFUMES_MORE*.
Seda ta dauko Manzaitun me kyau da Anty Hafsa ta ajiye mata jiya ta zuba a hannunta ta shafe qasanta dashi kafin ta janyo lotion ta shiga shafawa a jikinta, ragowar qananan kwalaben *MEERAH_PERFUMES_MORE* ta duba ilai kuwa ta samu body oil ta budeshi ta kai hancinta seda ta rufe ido ta bude saboda qamshinsa.

Da dan tsinke dake ciki ta ringa dangwala ta shafa a bayan kunnenta, wuya, saman cibiyarta, matsi matsin cinyarta baya ta goge ragowar akan cinyarta tana murmushi saboda yanda qamshin yake ratsata ta tabbatar idan Khalil yaji dole ya yaba.

Wardrobe ta bude, kai sufa yan gata ne dan hatta da kayan sawarsu an jera musu, riga da skirt ta ciro na wata farar Atamfa me adon ja. Tunda aka dinka take cin burin sakata saboda yanda dinkin ya fita, seda ta saka undies kafin ta zura skirt din dakyar ya zugu saboda yanda mazaunanta suka cikashi taf ta juya ta sake juyawa a fili tace

"Fatabarakallah ina ma yan ciki baqi na kusa sedai suyi bunga" ta saki dariyar iya shege ita kadai kafin ta dauki rigar ta saka. Daurin ture kaga tsiya tayi bayan ta barbada farar powder ta saka kwalli da lipglose me kyalli dan ita daman ba gwanar kwalliya a fuska bace. Turaren ta na dindindin Kalta Maryam ta sake fesawa ta ringa juyi a gaban mudubi ita kadai tana ihu kamar mara abin yi can kuma meta tuna ta zabura ta shiga tattare kayayyakin data yi amfani dasu kafin ta nufi palour jin cikinta ya fara kukan Yunwa.

Seda ta kai tsakiyar palour ta tuna da ashe fa ba ita kadai ba, gaskiya zataji kunya Khalil ya ganta da wadannan damammun kayan seta juya dakin, jan mayafi ta dakko ta sake fita, palour qal babu dattin komai se ta wuce inda aka jera turarukan wuta ta dauki kasko ta bude qofar palour ta wuce kitchen.

Seda ta kunno Magic coal ta koma dakin, a kasko biyu ta saka ta harhada kalolin turarukan wuta ta zuba a kowanne kasko ta shige da daya dakinta ta bar dayan a nan palour bayab ta kunna Ac kafin ta koma kitchen.

Ganin akwai kusan komai na amfani dan daidai da kayan miya ta tarar a freezer ga nama nan da kifi haka cikin store akwai dankali da doya harda plantain ga kuma garar Abinci nan da aka hado su da ita se kawai ta debi dankalin ta shiga ferewa.

A nuts take aikinta tana yan waqoqinta, tana tsaye gaban Gas tana jiran Dankalin data zuba a mai ya qarasa soyuwa ta kwashe sam bataji shigowar mutum ba se hucin numfashi taji agefen kunnenta babu bata lokaci ta fasa qara tayi gefe saura qiris ta tunkude kaskon man dake kan wuta Khalil ya riqota yana cewa

"Kiyi a hankali karki jima kanki ciwo fa"
"Ba kaine ka bani tsoro ba banji tafiya ba kawai naji numfashi a kunnena" ta fada a shagwabe tana kai masa dukan wasa, seya riqe hannayenta yana murmushi yace

"Kice dai kina ta waqa amma ni har sallama nayi kece dai baki jini ba". Janye hannun tayi saboda hango dankalin ta ya fara ja alamar ya kusa qonewa tayi saurin saka ludayi tanakwashe wa tace
"Ka gani ko gashi nan kasa dankalina ya qone Allah idan yayi ba dadi bazan yadda ba"

"My strong woman, wayace miki Amarya tana shiga kitchen irin yau? koda yake alama kike mun ta kin warke, bari mu koma daga ciki toh muci gaba dan kinsan ban qoshi ba kawai na dan tausaya miki ne yanda kika ringa kuka kina kiran Mama jiya" Khalil daya sakata a tsakiya rungumeta ta baya ya fada cikin kunnenta, kunya kamar qasa ta tsage Umaimah ta shige se qoqarin kwacewa take amma ya hanata sema qara cusa kansa yake a wuyanta yana cewa

"Wow Babe wane turare kika saka haka i love the scent, its really amazing and erotic".

"Khalil bazaka kasheni da raina ba" ta fada a zuciyarta tana qoqarin yakice shi daga jikinta jin ya fara lasar mata kunne kamar wani tsohon maye, qara janyota yayi ta fasa kukan qarya tace

"Wallahi yunwa nakeji ka barni na qarasa hada abinci" se ya saketa yaja da baya ya jingina da cabinet yace

"Ok na barki, kije ki zauna bari na qarasa miki ma"
"Aa" ta fada tana noqe kafada, Tumatir da Attaruhu da Albasar data wanke zata soya kwai ta shiga yankawa gaba daya jikinta rawa yakeyi, ta fasa kwai a qaramin bowl ta ajiye kafin ta dora wani kaskon ta zuba Mai se taja ta tsaya saboda yanda take jin idanunsa a jikinta ta tabbatar in ta ci gaba da aikin za'a samu matsa, in ma ta qona kanta ko kuma ta qona abinda take dafawa.

Gas din ta kashe ta juya ta kalleshi tace
"Ni gaskiya ka fita duk ka sakamun ido na kasa yin komai...." Be barta ta qarasa saboda cafkar da yayiwa bakinta ya shiga kissing dinta babu ji babu gani, seda ya gaji dan kansa kafin ya saketa ya juya yana cewa
"Ki qarasa bari nayi wanka" ya fice daga kitchen din

Hajiya Umaimah ido yayi fici fici kamar an jijjiga bera a jarka taja numfashin daya maqale mata tareda tattaro yawu ta hadiye, wannan karatun na Khalil ya girmi kanta taga alamar zata sha wuya kafin ta haddace, amma dole ta bada himma tun kafin ta zama daqiqiyar daliba.

Jiki a mace ta soya kwan, ta zuba komai a kwanuka masu kyau ta ringa dauka tana shiga dasu cikin palour, seda ta ajiye duk abinda tasan zasu buqata kafin ta qarasa inda ta ajiye kaskon turaren wutarta ta dauka tana shirin qarawa dan na ciki ya cinye, yanda qamshinsa yake tashi babu qauri ko kadan irin yanda wasu turaren sukeyi a farko ko idan sun qare ya sake burgeta da Turarukan na *MEERAH_PERFUMES_MORE* tana shirin zubawa Khalil daya fito daga daki ya dakatar da ita yace

"Karki zuba", seta kalle shi da rashin fahimta tace
"Lafiya? Ko qamshin babu dadi ne?"
"No i love the scent qamshin da dadi sosai zaki ma zubamun na kai office na ringa sakawa amma hayaqin ne bana so, idan zaki kunna turare ki ringa sakawa hayaqin ya fita kafin na shiga guri saboda yana damuna a maqogaro sosai wannan sedai ki kaishi cikin daki tunda a nan zamu zauna"

"Noted Sir" ta fada kafin ta dauki kwalbar turaren da kaskon ta shige dakinsa ya rakata da murmushi. Ko ina tsaf dan har gadon ya gyara ta bude toilet nan ma qal dashi da alama ya sake daurayewa bayan da yayi wanka, taji dadin wannan sauqin halin nasa tasan idan ya dore a haka zasu ji dadin zama dan ta dade tana addu'ar samun? irin mijin da yake taya matarsa aiki. Turaren ta zuba ta kullo qofar ta dawo palour, nan suka zauna suka karya abinsu a nutse yana tsokanarta wai meye sirrin yaga ta miqe garau ko daman duk abinda ta ringayi dazu lambo ne saboda ya qyaleta dan haka seta biya bashi ita dai se murmushi take tana sunkuyar da kai dan kunya yake bata idan yana irin maganganun.

Haka suka wuni cikin gidan abinsu gwanin dadi, tun tana zazzamewa idan ya jata jikinsa har ta haqura ta fara sakewa dashi dan ta fahimci irin mazan nan ne masu nanewa Mace duk inda take suna nan dan ko tashi tayi yin wani abun qafarta qafarsa seya bita har bandaki data shiga yin fitsari bin bayanta yayi seda ta nemi saka masa kuka kafin ya haqura ya barta.

Guraren bayan La'asar su Yaya Naziyya sukaje gidan tilas Khalil ya fita ya basu guri badan yaso ba nan suka tasa Umaimah da tsiya kala kala wai har sun chanza daga ita har shi a dare daya abin Allah sega Umaimah wai tana sunkuyar dakai baki ya mutu babu tsiwa bare rashin mutunchi, suka qarasa mata yan gyare gyaren daya kamata suka gyara gidan qal Yaya Naziyya data hada ruwan Mopping Umaimah ta dakko Mata Mopping Mist din *MEERAH_PERFUMES_MORE* ta zuba ta kalleta tace
"Wai ni Umaimah ina kika samo wadannan sirrin qamshin haka, dazu dana shiga bandakinki kamar karna fito wallahi nasan dai ba'a gida aka hado miki kayan nan ba".

Fari da ido tayi tace sirrin *MEERAH_PERFUMES_MORE* wadda Anty findiga ta hado mana turarukan wuta a gurinta ta Yolan nan ce to a gunta qawata Ruma tayo mun wadannan hade haden, kingansu ga *Turaren wanka, body oil, gana kaya, ga air freshner, turaren Mopping, ga Spray na mota ma na boyewa Khalil se randa ze koma aiki zan saka masa a motarsa sannan ga wadannan turarukan hayaqi na daki dana jiki su kin san ingancinsu ma ba se na fada miki ba tunda kun satar mana*"

Duka Naziyya takai mata ta goce tace
"Ke fa baki da mutunci daman wato satar mukayi ai daman ba ku kadai aka ce gidan ku yayi qamshi me dadi ba, dakko mun Roba daya na dauki lambar me turaren nima a hado mun dan sisi zan fara kwanannan nima".
(Domin samun ingantattun turaruka masu sirrin qamshi na musamman ku tuntubi *MEERAH_PERFUMES_MORE 0706 9239573*, tana Adamawa Yola, suna aika kaya ko ina a fadin qasar nan cikin Aminci).

Se bayan magriba suka tafi bayan da suka sakata ta sake falle wanka da sababbin turarukan wankanta data samu kamar ta goyasu ta ringa yawo dasu saboda qauna ta saka dogurar riga yar kanti silk Peach color me dogon hannu ta lafe a jikinta ta fitar mata da shape ta nade a palour tana kallon Tv tana shan lemon kwakwa da dabinon da suka zo mata dashi aka saka a fridge yayi sanyi.

Horn din motar data jiyo a waje ya sakata ajiye cup din ta miqe, seda ta qara gyara fuskarta a daki ta fito lokacin har ya bude Get ya shigo da mota ta fita palour daidai sanda Khalil din ke shigowa da yammata biyu a bayansa dauke da kulolin abinci dan daman ya kirata ya gaya mata kartayi girki tana ganinsu nan da nana fara'ar data fito da ita akan fuskarta dan ta tarbeshi ta gushe.

Kallon yammatan ta shigayi kamar wadda taga kashi, ta gane Habiba Autarsu amma ita dayar me ruwan sadaka yalla fa? Khalil daya cake yana jira tazo ta tareshi yaji shiru se yayi saurin qarasawa kusa da ita saboda hango irin kallon da take jifan qannen nasa dashi tun kafin a kwata wani abun ya rungumeta yana cewa
"Bazakizo kiyi welcoming din ba"

"Wacece waccen?" Ta fada tana kallon cikin idonsa, nan da nan ya hade fuska shima ya juya ya kalli Habiba da daya yarinyar me suna Iman, yar qanwar Hajiyarsu ce, haka kawai suka nace se sun biyo shi wai tun safe suka so zuwa Hajiya ta hana su su dai suna so su gaida Amarya dan washe gari ita Iman din za'a mayar da Ita Minjibir inda take makaranta dan saboda bikin aka dakkota.

"Ku ajiye kwanukan mana kun tsaya kamar wasu sojoji" ya fada yana kallonsu, se suka wuce kan Dining suka ajiye flasan hannunsu, har suna rige rigen gaida Umaimah dake jifansu da irin kallon da suka kasa tantancewa dan dai a ganin da suka mata sau biyu duk irinsa takeyiwa mutane, to kodai idonta ne a haka su dai basu sani ba.

A shaqe ta amsa musu kafin tabi bayan Khalil daya shige daki suka bar su Habiba da baki a bude.
"Habiba me yake damun Amaryar Yaya Khalil ne? Kingafa ko yar murna ta ganmu batayi ba se bata rai takeyi, haka fa ranar kamun nan ta ringa kuka kodai bata son sa auran dole akayi mata?" Iman din ta fada dan irin masu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login