Showing 195001 words to 198000 words out of 429394 words

Chapter 66 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

998

bazata sake faruwa ba kuma ko a yanzu Abban Mu'ayyad yaga damar qara aure a shirye nake dana bashi goyon baya dari bisa dari idan har ya samo macen da tayi daidai dashi.

Kuma dan Allah Hajiya ki tayani bashi haquri dan tunda abin nan ya faru yaqi bani damar da zamuyi magana ballanatana har na nemi yafiyarsa. Fushi yake dani me tsanani baya ko kirana a waya se idan na kirashi nan ma ba wata magana muke ba daga gaisuwa yake kashewa" ta qarasa tana fashewa da wani munafukin kuka. Hajiya ta dauki salati tana cewa

"Amma Babana anyi shakiyyin yaro wato baqar zuciyar tasa ce ta motsa koh? Waye baya kuskure a rayuwa, Allah ma muke masa laifi ya yafe mana yacigaba da wadata mu da dukkan ni'ima da mun roqa da bamu roqa na se shi?
Daman ni jikina ya bani wannan tafiyar da yayi ya share guri ya zauna da walakin to kuwa zeci gidansu" haka ta ringa rarrashinta tareda bata assurance na seta ci qaniyar Khalil, da kansa ze dawo ya lallabata su koma.

Ran Umaimah qal ta bar gidan Hajiya. Suna tafiya ta cewa Salman su biya ta Alpen zata siyi Mai da turare, a mota tabarwa Salman Bibi ta shiga dantafi sauri, tana cikin duba wasu Turaruka taga wata ta wuce kamar Rufaida, saurin bin bayanta tayi tana kiran sunanta amma bata waigo ba seta dauka kawai kamace ta juya da niyyar tafiya daidai sannan Ma'aruf ya qaraso gurin tana jinsa yana cewa
"Naji kamar ana kiran sunanki ko ke baki ji ba?"

Tabe baki Rufaida tayi tace
"Banji ba, ko kuna bani din ake kira ba"
"Yanzu saboda wulaqanci kna jina kenan daman kikaqi juyowa" Umaimah ta fada a fusace tana qarasawa gaban Rufaidan, qugu Rufaida ta riqe tace
"Toh se akayi Yaya najiki din banyi niyyar amsawa ba ko kuwa cewa akayi dole sena kulaki? Wai ni bana ja miki kashedin babu ni babu ke ba, akan me iya bala'in da kika jamun na kwana a Cell be isheki ba me kuma kike nema a gurina?
Daga yau ko a hanya kika ganni karma ki nuna kin sanni wallahi idan ba haka ba se na baki mamaki Mtsw" taja tsaki tareda aikawa Umaiman wata muguwar Harara tayi gaba bata ko saurari Ma'aruf dake faman ce mata
"Meye haka Rufaida, ya zaki ringa yiwa mutane hayaniya gashinan har kin tara muku Jama'a".

Kallon Umaimah da tayi suman tsaye yayi yace
"Kiyi haquri kinji" ya juya yabi bayanta.

Jiki babu kwari Umaimah ta juya ga mutane da suke ta kallonsu kamar sun damu Tv, tana jin wata tana cewa
"Baki gane su ba? Sune fa sukayi wata sharrin Lesbian aka kamasu har aka sa sukayi video ban haquri" seta yi saurin ajiye kayan data diba, shopping din da batayi ba kenan ta fice daga gurin saboda zamanin nan yanzu kana tafe salin alin ma video ake maka ayita yawo da kai a Social media inaga ita da tayi qaurin suna har an samu wanda suka gane fuskarta dukda a Video sun chanza saboda wuyar da suka sha.

Rufaida kuwa a mota har fada seda sukayi da Ma'aruf akan yana mata magana abinda tayi bata kyauta ba.
"Ina ruwanka, Kai ka hadamu ko kuwa da yanzu rabuwar mu zata dameka? Malam kayi ta kanka kawai saboda bakai tajazawa kwanan cell ba shiyasa ai har kake so na kulata" ta fada a fusace kafin ta juya masa qeya. Mugun haushin Umaiman takeji, bayan kwanan Cell data ja mata ga Asarar dubban followers dinta na Tiktok data sha wahalar tarasu, dab take da Tiktok su fara biyanta wannan abun da sukayi ya jawo mata kuma shine zata sake kukata? Allah ya sawwaqe.

Umaimah ko gida suka wuce Mama ta ringa musu fada ace tun safe su fita se yanzu kusan Tara zasu dawo ina suka tsaya Salman ya rantse mata gidan Hajiya suka wuni se yanzu suka taho ita kuwa oganniyar daki ta shige ba tareda ta bada amsa ba. Da ta saka damuwar abinda Rufaidan tayi mata se kuma ta yakice, a fili ta furta
"Ita ta rasa, daman ita take amfana dani ai ballantana na damu dan ta dena kulani nima hutu nane".
Washe gari da safe sega Kiran Khalil a wayarta, kamar yanda ya kona mata magana a dake tun sabaninsu da Hadiza yau dinma haka suka gaisa yake gaya mata ta shirya a cikin satin nan ze dawo bata ja maganar ba tace masa Allah ya nuna mana suka kashe wayar.

Ko a jkinta ta fara shirye shiryenta dan daman tasan tunda Hajiya tace zata kirashi to zata kirashin qarshe dai fada ne zeyi yace ta kuma kai qarar sa to anci Sa'a be mayi fadan ba. Anty ta sanarwa da zancen dawowar tasa nan kuwa ta shiga yi mata gyara na musamman dukda bayan ta haihu ta danyi kadan tace ta bari se goshin dawowar Khalil din sannan suci gaba dan haka kuwa suka tashi da haiqanba dare ba rana qalqaleta take ciki da waje. Idanda dan halin Umaimah ne ba zata mata ba amma a kaf yaran Maman haka kawai Allah ya dora mata sonta dukda tasan duk cikinsun babu wadda ta tsaneta kamarta ta shanye gashi yanzu komai ya wuce tunda tana mata rana, abu da yawa nata kafin Mama ta sani ta gaya mata.

Ranar Lahadi yace ze dawo bayan sun sake yin waya dan haka ranar Alhamis sukaje gidan tareda Maman Asad da Ummu-Salma sukayi gyare gyare, bayan sun dawo Maman Asad take cewa Mama
"Mama da da hali da an chanzawa Umaimah ko iya kujeru ne wadannan din sun fara jin jiki"
"Kema kinsan da kudina bazan canzawa Umaimah komai ba dan ba sanin darajar su tayi ba idan banda shegiyar qazanta ya za'ayi ace kayanta duk kyansu da kwarinsu basu cika shekara uku cif bafa ace sun lalace? Ga dakin Nuratu nan kulllum ka shiga fes kamar yau aka jera su, se ta chanza da kudinta idan tana so amma ni bazan yi asarar kudina bata sake kashe su a banza kuma nan kusa ai chanza gida zasuyi, idan Mijin yaga dama ya mata wasu mudai munyi namu na farillah" Mamanta bata amsa ita se a sannan ma ta san da zancen canjin gidannasu dan haka tace

"Ai banma sani ba tunda haka ne seta fara tanadi kafin lokacin dan dai ba zata tare sabon gida da wadannan kayan ba, bafa ki ga yadin ba duk ya dafe daga Fari ya koma Ash"

"Daman ai kuna sane kuka saka akayi mata kala me Haske, ni baqi nace ai mata ai taje ta qaraci qazantarta" Mama ta sake fada Maman Asad ta fashe da darita tana cewa

"Kai Mama ina kika taba ganin baqaqen kujeru idan ba Lether sit ba? Ai baqi sema yafi nuna datti a leda ne kawai yake kyau tunda su basa nuna qura"

"Ku kuka sani" Mamanta bata amsa kafin taci gaba da abinda takeyi se ta miqe ita kuma ta wuce palour Anty inda akeyiwa Umaimah kitso. Zama tayi suna dan taba hira kafin a gama mata dan itama kitson take so ayi matan, u guwar da suka koma babu me kitso idanba tazo gida kamar haka ba bata samu tayi daman. Ana gamawa Umaimah ta shige daki ta hau mulke jikinta da hadin Dilkar da Anty tayi mata, seda ta bushe tayi wanka ta saka Salma ta debo mata garwashi ta turara hayaqi na tsugunno dana jiki tanayi tana murmushi ita kanta dadin jikinta takeji yanda tayi kyau tayi mulmul abinta Jegon ya bala'in karbarta har yafi na fari tasan idan sukayi arba da Khalil manta komai zeyi su sha soyayyar su, tayi missing dinsa over wallahi.

"Ke kuma lafiya kike ta zuba murmushi kamar wata sauna" Maman Asad data shiga ta fada tana kallonta, dariya ta saki ta zauna akan gado tana cewa
"Tunanin irin love din da zamu kashe da Habibi idan ya dawo nakeyi mana"

"Sefa Habibi, to dai kafin kiyi tunanin kashe love ya kamata ki fara tunanin yanda zaki wanke laifinki a gurinsa, ki samu ku fahimci juna kafin Live dinta tafi yanda ake so" Maman Asad ta fada. Se Umaimah ta gyara zama tace

"Baki san Khalil ba, duk fushinsa fa shi dana kawo dauri gaban goshi na fesa turare an gama magana manta komai yakeyi in gaya miki" se Hajiyayye ta zauna dan abin yafi qarfin tsayuwa tace

"Na yarda Umaimah bakida hankali ashe, wato daukar sakarai kike masa saboda kawai yana biye miki ya yafe duk haukar da kike masa ko? To wallahi ki kiyayi kanki da fushin me haquri, ranar daya tashi fashe miki sekin raina kanki. Ke yanzu har kina zaton Daura dankwali da turare zasu saka ya manta tozarcin da kika ja masa ko? Ke bashi ba ko mu yan uwanko dan bamu da yanda zamuyi dake ne yasa muka ci gaba da kulaki amma wallahi abinda kikayi har yau idan ta juyo zagin mu akeyi dan gani ake duk da sa hannunmu kikayi ai kin auna arziqi wallahi dabe baki tukuicin Saki ba ya barki kikayi zaman gida kawai danna tabbatar idan Bashir ne da yanzu na gama Iddah na fara zawarci dan bazan ma kuskura na kama hanyar gidansa ba daga Station din nan.

To tunda har Allah ya dubeki ya baki me iya daukar halinki seki taimaki kanki kiwa kanki gata ki nutsu Umaimah, karki dauka kinyi wannan kinci banza dukda har yanzu ba ace haka amma nasan tsaf zaki iya gaba kice zaki maimaita ina jiye miki abinda ze biyo, kuma kibi Mijinki a hankali ki kwantar dakai ki nuna masa kinyi nadama ta gaskr ba tuban muzurun da kika sabayi ba.

Daman base n miki magana akan Maqociyarki ba, idan kinga dama ki koma kuci gaba da jaye jayen bala'i tare jiki magayi, kuma ki nemi Islamiyya ta matan aure Umaimah ki shiga dan Allah kije ki qara sanin menene aure dan karatun da kikayi a baya banida tabbacin kin san me aka koya miki ki koma ki sake tilawa dan da kina amfani da Duk Litattafan da muka karanta da nutsuwarki tafi haka, ita kanta bokon idan da hali ki koma Degree, ko bazakiyi karatun ba ki shiga cikin mutane ki qara samun wayewa ta zaman takewa dan ita Jami'a amfanin ba iya kayi karatun boko bane harda koyon karatun zaman duniya dan zaka shiga ka zauna da mutane kala kala".

Kumbure fuska Umaiman tayi, da farko tana sauraron nasihar tata amma tunda aka zo gabar ta koma makaranta ta hade rai wato kallon baqidajiya mara Ilimi ma suke mata kenan, se kuwa tace

"Lallai ma Yah Hajiyayyen nan wato ma daukata kike a mara Ilimi wadda akayi a sarar kudin tara ko? Naga dai a gidannan idan za'a dakko takaddu a duba har ita Nuratun da take wani ji ita ga likita na fita qoqari kawai dan banyi niyyar inyi irin abinda tayi bane ya saka kuma ko a Islamiyya wallahi nafi qarfinace mun jaka danhar yau da hotona kafe a office din Headmaster kowa yasan ni me qoqari ce"

"Dallah rufe mun baki shashasha ai ga gidadancin nan kina aikatawa, ce miki akayi sakamakon jarabawa shine tabbacin mutum yasan abinda yake koyo? Mutum nawane irinki masu karatu dan kuci jarabawa amma idan za'a tsare ki da wuqa ba zaki kawo abinda kika rubuta na.

Qarara Ayyukanki sunfi kama dana wadda bata taba shiga Aji ba Umaimah dan wallahi Mace yar secondary data san kanta ba zatayi haukan da kikeyi ba, kiji ko kar kiji ke kika sani gaskiya ce bakya so kuma se mun fada miki in kinga dama ki gyara in kinga dama kici gaba da yanda kike dukkanin mu a gidajen aure muke kuma Alhamdulillah cikin rufin asuri da kwanciyar hankali da dadi babu dadi babu Wanda yasan ya muke rayuwa sabaninke da kaf matsalar gidan auranki a titi, ruwanki ki gyara ruwanki karki gyara n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i nan ba abinda ya shalleni haqqine na sauke na yan uwanta ka kuma bawai dole bane dan haka kinga tafiyata" ta fice ta barta a zaune tana cizon yatsa, gaskiya ta gama cinta wasa amma zasu gamu ai tasan bata isa tayi mata wannan cin mutunchinta barta haka kawia ba bari dai ta samu daidaito da Habibinta sannan zatayi lokacin kowa ma.

Ranar Asabar ta tattara yanata yanata ta koma gidan Khalil bayan dogon fada, Nasiha da gargadin data sha. Daren ranar gani tayi yayi mata tsayi da yawa saboda zumudi, tuni ta fara rage aikin abubuwan da zata masa ta tarba gwada tafiya da magana kuwa ita da kanta seda ta ringa yiwa kanta dariya dan kamar ta zare, gaskiya kewar Khalil na dab da zarar da ita.



HALIN KISHI

49


*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 49

KHALIL
Kiransa Hajiya tayi ta rufeshi da fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba taqi bashi ko damar ya gaisheta har seda ta kao aya kafin ta kashe wayarta, yasan baze wuce Umaimah taje ta gaya mata qarya da gaskiyar data saba bane shine zata hau kansa ba tareda shi taji ta bakinsa ba haka ya tashi shirin tahowa dan ce masa tayi ko ya dawo ko Umaiman ta bishi shi kuwa daman ba zaman wani abu yake ba aikin ma da suke gaba daya an kusa kammalashi kuma ya gama bangarensa tuntuni kawai wasu harkokin kasuwanci ya sake samu a can da taimakon wani Co-Architect da sukayi aiki tare shi ya nuna masa hanya ta irin abubuwan da suke tafiya a can wanda basu dashi se an shigar musu daga wasu qasashenda kuma namu na nan da suke da sauqi acan nan da nanya fantsama harkar shigowa da fitar da kayayyaki kuma da Allah ya saka albarka a abin yana ganin haske, ga harkar Gold da yake da sauqi sosai a can, sunq ulla Bashir, danye yake siya su kai Dubai a canza shi zuwa abubuwa da dama wannan hidimomin ne suka dauke masa hankali gaba daya har mamakin kansa yake ta yanda ya iya share tsahon lokacin ba tareda Mace ba kuma baya jin wata damuwa kodanbaya kawo abin a ransa ne yana fushi dame abun sabanin da da ko muryarta yaji yanzu jikinsa ze amsa?

Shidakansa yasan zazzafar soyayar da yakewa Umaimah ta dishashe ba kuma ya zaton zata sake samun matsayi irin wanda take dashi a da cikin zuciyarsa ta rigada ta barar da damarta.

Ranar Lahadi kamar yanda ya fada qarfe sha biyun Rana tayi masa a gidan Hajiya. Dakyar ta barshi yayi sallar Azahar banda ruwa ba abinda yasha ta korashi wanda be so haka ba, so yayi ko ze koma gidan se cikin dare amma haka ya tafi yana ta doka tsaki Mu'ayyad nata kukan ze bishi aka lallabashi da kyar akan se an kwana biyu za'a maida musu shi. A Mota Khalifa dai sedai ya juya ya kalle shi ya dauke kai, tunawa yakeyi lokuta baya idan yayi tafiya ya dawo yanda yake doki da zumudin komawa gidan ya ringa Azalzalarsa da yayi sauri kenan amma yau har fada yake masa wai yana gudu da motar. Har cikin gidan ya shigar masa da mota ya fita yayi masa sallama ba tareda ya tsaya sun gaisa da Umaimah ba.

Numfashi yaja ya fitar kansa na kallon qofar palour da aka liqa wata sticker me qyalqyali an rubuta
'WELCOME HOME HABIBI" A jiki. Waiwayawa yayi ya kalli qaramin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login