Showing 24001 words to 27000 words out of 429394 words

Chapter 9 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

931

dagaske yana da wata ashe ba Nabila ce zata fara qirga kwanakin ta ba itace lokacin ta yayi.

Ganin da yayi dagaske fa take Kukan yasa ya sassauta murya ya shiga bata haquri,
"Wasa nake miki, kuma ko jiyan nan da kika ganmu ba dagaske nake miki ba Abokina Mansur na raka duba Maman budurwarsa bata da lafiya shine kwalliyar da kika ga munyi".

Dagowa tayi ta kalle shi irin kallon " ka tabbata?"
Da ido ya mayar mata da amsar "kiyarda dani" dole tayi qasa da kanta dan bazata iya jurewa kallon cikin idonsa ba, a haka ma tana ji kamar ta mutu saboda shi inaga yana mata wannan kallon me narkar da zuciya.

"Nifa bani da budurwa, gashi Hajiya ta takuramun aure take so nayi. Ranar fa da kika je gidan mu shikenan Hajiya ta saka ni a gaba akan ki ita a dole ke budurwa tace. Harfa ta gama gayawa sisters dina nayi mata. Harfa gurin Sister ki taje akan taso tazo nan gidan tayi magana kafin a turo maza dakyar fa na fahimtar da ita ni babu komai tsakanin mu, ta yarda amma ta kafa mun sharadin kafin qarshen shekarar nan dole nayi aure gashi ni ko budurwa bani da ita yanzu bansan yanda zanyi ba, ko kina da qawa ko qanwa data shirya aure ki hada ni da ita? Ni kinga tsoron yammata nake ban taba zuwa nace wa wata ina sonta ba".

PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI

*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 8


Yanayin kallon data watsa masa ya sakashi daga hannaye sama yace "Allah ya baki haquri, ki barshi base kin samo mun ba", gani yayi kamar Almutsutsan nata zasu motsa dan sak kallon data masa jiya kafin ta fadi.

Buda baki tayi zatayi magana ya sake tareta yana miqa mata kofin daya zuba ze sha yace " karbi kisha zuciyarki tayi sanyi kinji Umaimah, maida wuqar mantawa nayi daman ance mata kishi ne daku bakazu iyayiwa abokin ku budurwa ba"

Khalil da neman magana yake, se yayi kamar yana rarrashin ta se kuma ya sake soko wata maganar Ita kuwa se aikin asarar hawaye takeyi. Ganin dai abin nata bana qaro bane ya saka shi daidaita nutsuwarsa yace

"Umaimah ya isa, me yasa kike asarar hawayenki bayan kin san masu tsada ne, wai kukan me kikeyi ne ma? Indai magana tace ta saka ki kuka toh kiyi haquri kinji ni wasa nakeyi"

"Dagaske baka da budurwa?" Umaimah ta fada bayan data dan tsagaita da kukanta, se ya dago ya kalli cikin idanunta, irin abinda yake gani a ciki ya wuce ya misaltashi. Tsakanin shi da ita besan wanda yafi wani mutuwa a soyayyar wani ba, yana fatan wannan hadin nasu ya zama Alkhairi.

"Dagaske nakeyi sedai idan yanzu zaki zama budurwar tawa" ya sake fada yana kallonta.

Qasa tayi da kanta tana sakin wani murmushi ji takeyi kamar ta taka rawa Alhamdulillahi Allah ya cika mata burinta.

"Kinyi shiru ko bakya sona ne?" Ya fada yana leqen fuskarta, seta dago tareda gintse fuska tace
"Bayan kace kayi soyayya da Nabila kuma kace kana Sona"

"Wacece Nabila?" Ya tambaya, yanayin da yayi magana ya tabbatar mata da cewa besan Nabilan ba.
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta shi kuma yana qare mata kallo harta gaji ta kalle shi da hararar wasa tace

"Kallon fa ya isa haka"
"Bazan iya dena kallonki ba, tun a ranar farko danafara ganinki kika sace mun zuciyata ban kuma samu sukuni ba se a yanzu dana furta miki muradin zuciyata, dan Allah Umaimah ki soni har qarshen rayuwata kinji, ban taba soyayya ba na tabbata kuma abinda nake ji akanki ya zarce So Qauna ce" ya fada cikin wani sanyi daya ratsa duk ilahirin jikinta.

"Ina da tsananin kishi akan abinda nake so da har ake mun kallon me matsala a kwakwalwa, idan har ka tayani kare duk abinda ze jawo motsuwar kishina zaka same ni yanda bakayi tunani ba" ta samu kanta da furtawa ba tareda tayi niyya ba. Haka kawai take jin bazata boye masa komai a kanta ba, gara ta gaya masa ko ita wacece saboda gudun wata rana yaga wani abu daban da beyi zato ba wani abu ya faru.

"Kice ni dan gata ne tunda dan gata shi yake samu ma har a damu dashi ayi kishin sa. In dai nine baki da matsala, bazan taba baki wata dama da har zuciyarki zata baci akai na ba"

A nan gurin soyaya me qarfin gaske ta samu matsuguni a zukatan Umaimah da Khalil, Musayar kalamai suka ci gaba dayi har basu san lokaci ya tafi ba, seda Salman Qanin ta ya leqa akan Abba yace ya tafi dare yayi kafin yayi mata sallama ya wuce kamar karya tafi.

Folder takaddunta da ledar jiyan ya bawa Salmanun ya shigar mata dasu harda qarin wata ledar me dauke da Turare da tundaga jikin ledar kake jin qamshinsa.

Basu haqura ba, kusan raba dare sukayi bayan tafiyar sa suna waya, ya bayyana mata komai akan sa duk wani abu daya shafe shi daya kamata ta sani ya gaya mata. Ya kuma sanar mata da cewar shi ba da wasa yake ba aurenta yake so yayi, kuma a yanda yake hasashe baya so abin ya wuce qarshen shekara dan haka tayi tunani akan sa ta gani, idan har ta amince dashi a shirye yake ze turo magabatansa a tsayar da magana dan burin Hajiyarsa kenan a koda yaushe.

Itama a nata bangaren tayi amanna dari bisa dari dashi, kamar yanda yayi mata bayanin kansa haka ita ma ta zayyana masa komai bata boye masa ba hatta da auranta da aka fasa karo uku seda ta fada masa.

"Amma menene dalilin daya saka aka fasa?" Ya tambayeta,
"Sunce kishina yayi yawa" ta bashi amsa. Mamaki ne yake kama Khalil idan tayi maganar Kishi dan abu kadan seta sake jaddada masa batun ita fa tana da kishi,

"Wai Umaimah wane irin kishi ne dake haka da har ze saka mutum uku su fasa auranki?" Khalil ya fada a ransa yana juya maganar wane kakar Kishi ne da har zesa a fasa auran Mace.

"Ba zasu iya tsayawa akan mace guda daya ba se sunyi biye biye ni kuma bazan jure hakan ace Mijin da zan aura yana kula wata mace a waje bayan ni ba shine idan nayi magana suke zabar dasu fasa amma ni na dauka hakan lokaci na ne beyi ba, duk ranar da Mijin aurena yazo zanyi".

"Basu dace dake bane shiyasa Allah yake kawo dalilai na rabuwarku saboda ke rabo na ce" Khalil ya bata amsa cikin tabbatarwa, kamar tana gabansa ta sunkuyar da kai cikin qaramin sauti tace
"Allah yasa".

Haka suka ringa aikawa da junansu dadadan kalamai masu sanyaya zuciya har suka gaji sukayi bacci zuciyar Umainah fes tana jin kamar an saka Hypo an wanke mata ita. Baccinta na ranar kuwa cike yake Mafarkai masu dadi na gata sunyi aure da Khalil har sun haifi kyawawan yara suna rayuwa cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

*MAFARIN SOYAYYAR UMAIMAH DA KHALIL (QADDARARSU)*

Yanda ta farka washe garin ranar cikin walwala da farin ciki ya bawa kowa Mamaki banda Mama da tasan za'a rina saboda tun a daren da Abban ya shaida mata sunan wanda yazo gurin Umaiman ta tuna da dramer su ta kwanaki ta kuma gane shine dai yaron da yazo jiya da Magriba.

Fatan Alkhairi tayi musu da fata Allah yasa qarshen damuwarta kenan danta yaba danutsuwa da hankalin yaron,tana kumada kyakykyawan yaqini na cewar Umaiman zata samu kulawa da jin dadi a gurinsa.

A cikin sati daya daya biyo baya abubuwa sun chanza sosai wanda suka hada da dawowar walwalar kowa na gidan saboda Farin ciki ko akasin haka na gidan ya ta'allaqa da Umaimah ne, a yanzu kuwa babu wanda ya kaita walwala da farin ciki, saboda yanda a kullum take samun sabuwar kulawa da tattali daga Sabon Habibin nata Khalil.

Wannan dalilin yasa ko da satiya zagayo suka manta da batun zuwan su Aminu Kano yin cika makon Gwajin kwakwalwar da za'ayi mata har seda Dr Kabiru ya kira yayi wa Abba tuni ya kuna sanar masa da sakamakon gurinsu sun fito, yana jira a kawo wancan dinne yayi Nazarin su gaba daya hakan yasa dole suka je Asibitin akayi dukda Umaimah bata so ba, toh daman ita tasan matsalarta kuma ga magani ta samu ina dalilin da zaa ringa kaita ana soka mata qarafuna a kai.

Sakamako ukun duk da suka fito sun nuna cikakkiyar lafiya da kwakwalwarta take dashi, bata taredada wani ciwo ko damuwa illah irin saqon gaggawa na tashin hankali da take aikawa da kwakwalwar tata nema yake neman ya jawo mata ciwon damuwa wanda a gwajin qarshe ma babu alamar hakan dan haka Dr Kabiru yayi mata gargadi sosai tareda bata shawarwari akan ta kula da lafiyar ta dan itace gaba da komai.


BAYAN WATA UKU

A cikin wannan lokacin abubuwa da dama sun faru na jin dadi ciki kuwa harda tsayar da ranar auran Umajmah da Khalil da akayi. Watan su daya da fara soyayya Mahaifiyarsa tazo da kanta suka gana da Mama ta jadda mata irin so da qaunar da sukeyiwa Umaiman, sosai Maman taji dadi ta kuma godewa Allah daya azurya Umaimah da samun suruka ta gari me kuma qaunarta, ba'a rufa sati ba iyayensa maza sukaje da kudin aure da saka ranar su watanni biyar masu zuwa kamar yanda Khalil dinda Umaimah suka tsara wanda yayi daidai da saka ra ar Nuratu da Angonta Dr Sabi'u.

Rikici da hauragiyar Umaimah ya zama tarihi dan tun daga declarationna soyayyartada Khalil wani abu na rashin jin dadi be sake faruwa ba, Khalil na matuqar taka tsantsan da duk wani abu daze bata mata rai har ya kai ga motsawar Matsalarta dan a lokacin da yaje gaishe da Abban ta be rufe shi ba, yayi masa kyakykyawan bayani game da Umaimah da HALIN KISHIN ta.

Hatta da Gurin Malami da Asibi da aka kaita seda ya gaya masa ya kuma Nuna masa takaddun Asibiti da suka nuna shaidar lafiyarta.
"Umaimah yarinyace da duk wanda ya zauna da ita ze sota, banda halinta na rashin sanin yanda zata sarrafa kanta acikin Fushi bata da wata matsala. Nasan zakaji matuqar dadin zama da ita idan har ka kiyaye duk wani abu da ze janyo motsawar rikicinta saboda idan tana son abu, tana kula dashi ne da dukka rayuwarta" Kalaman Abba da ya riqe kenan yake kuma amfani dasu.

Shi da kansa ya shaida Umaimah tana sonsa har wani lokacin ya kanyi mamakin tsakanin shi da ita waya fi wani son wani atsakanin su. Yanda take riritashi da tattalinsa yana saka shi yaji kamar yafi kowanne Namiji sa'a a rayuwarsa, yana yawan hasaso yanda rayuwar auransu zata kasance.? Irin soyayyar da zasu shimfida me tsafta, yayan da zasu haifa a kullum ya zauna shiru lissafinsa kenan.

A farko farko ne ma suka fara samun sabani wanda tunda yayi wa tufkar hanci komai ya koma musu daidai. Abinda ya faru wata rana ya dakkota daga gidan Yayarta Nasiba, suna tafe a hanya Abokiyar tagwaitakarsa? Jalila da yayi sabin Numberta da 'Rabin jiki' ta kirashi'.

Tunda Umaimah ta kyalla ido taga kiran wayar yanayinta ya chanza daga murmushin da takeyi zuwa fuskar bacin ran da yayi mata dirar mikiya lokaci daya.

Har ya kammala wayar sa ya ajiye be lura da yanayinta ba seda ya kashe wayar yake ce mata "Kinji Jalila ko, wai mata wayonku yayi muku yawa wallahi. Tana gidan Mijinta amma duk idan tana da buqatar kudi se taci tudu biyu, mijinta yayi mata nima nayi mata dan Allah ba wayo bane wannan? Koda yake nima dai na kusa ajiye tawa matar dole a ringa daga mun qafa tunda yanzu inda uzurin da zanyi da Kudi" ya qarasa yana kallon fuskar jin harya gama maganar bata ce komai ba.

Umaimah kuwa wani irin daci ne ya taso mata kamar zatayi amai saboda tsabar dacin da maganganunsa sukayi mata. Ya iya duban tsabar idanunta yake gaya mata tsohuwar budurwarsa ta kirashi tana neman kudi a hannunsa babu kunya babu tsoron Allah,

"Kinyi shiru, lafiya dai naga fuskarki ta chanza" ya fada yana qare mata kallo ganin yanda ta hade fuskar tam har wani ja ja yaga fuskar tayi. A fusace ta bude baki tace

"Toh ni ina ruwana can ta shafe ku kaida ita, amma dai ka sani yanda kake magana da matar wani kaima se Allah ya sakawa mijinta anyi da taka. Ita kuma ballagaza mara kamun kai tana gidan wani tana waya da tsohon saurayi zataje ta tarar da Allah, wai Rabin jiki idan ma gangar jikince kai ka sani ai baka burge ba tunda har ka bari wani ya aureta idan kuma da auranta kuka hadu kake neman ta ma duk matsalar kuce ba tawa ba" ta qarasa a mugun fusace kamar zata kai masa mari.

Gefen hanya ya gangara ya faka motar ya tsaya kawai yana kallonta dan gaba daya ya rasa mamakin kalamanta zeyi ko kuwa tsoron yanda ta birkice gaba daya tana jifansa da maganganu zeyi?

"Wato ga mahaukaciya tana magana ka sakani gaba kana kallona ba? Ai wallahi bansan haka kake ba Khalil kuma ka bani mamaki, ka rasa wa zakayi tarayya da ita se matar aure to wallahi kaida Allah za kuma kaga sakayy....."
"Shut up Umaimah ya isheki" ya daka mata tsawar da ta sakat yin shiru ba tareda ta shirya ba. Cigaba yayi da cewa

"Kina hankalin ki kuwa kin san me kike fada? Wai ma dakata duk akan me kike wadannan maganganun har kina nema ki jefeni da abinda bana fatan Allah ya jarabceni da aikatawa ba. Bari kiji, ni mace idanba yar gidanmu ba babu abinda yake hada ni da ita balle har muyi magana a waya kece mace ta farko a tsahon rayuwata da wata doguwar magana me muhimmanci ta shiga tsakanin mu.

Idan kuma duk saboda Jalila kike wannan babatun" ya dauki wayar ya shiga whatsapp ya kirata video call tana dagawa yace
"Ina gayawa yayarki banason mace ta fiya qiba shine na kira mata ke video call taga yanda kika saki jiki kika zama shirgegiya waye za'a cewa ke qanwata ce ya yarda" ya fada cikin tsokana.

Daga cikin wayar ta amsa da cewar "Wallahi Khalil ka raina ni, minti daya fa ba kadan bane amma ka ringa cewa ni qanwarkace karma ka saka ta yarda wallahi nice Hassana ni nake gaba da kai kulkum se Hajiya ta raba mana Musun nan amma kaki ka dena cemun qanwarka".

"Gata ki fada mata toh amma dai bazan taba yarda ba nine Hassan ke kuma Usaina kawai muje a haka" ya fada yana juya wayar saitin Umaimah da tayi sak tun sanda ya ambaci sunan Jalilan, a sanyaye suka gaisa ko ba'a fada ba kamannin sa dake fuskar Jalilan sun isa su gasgata alaqar jini da take a tsakaninsu. Tsokanar ta ta ri gayi Umaimah na dan murmushi tana satar Kallon Khalil daya zuba mata ido kawai a ransa yana tunani.

"Nice Hassanarsa nasan ya ce miki shine Hassan ko, son girma irin na Khalil qila ya gaya miki ya girmi Jamila ma to Yayar muce ita amma ni na karbi qanqantar na bar muku girman kinji Matar Yaya, ki kula mana dashi da kyau" Jalilan ta fada bayan da suka gama gaisawa.

Janta take da hira amma ta kasa sakewa, qarshe sukayi sallama ta miqawa Khalil wayar,karba yayi ya kashe still yana kallonta yace

"Ko dan gaba karki sake jifana da irin zargin da kika darsa a zuciyarki kuma banyi tsammanin haka daga gare ki ba amma nayi miki uzuri a yanzu ya wuce" kafin ya tada motar suka cigaba da tafiya.

"Amma ai kaine ka saka abinda zesa nayi zargi akai,? bakaga da sunan da kayi saving number ba ai da sunanta ka saka ko Sister zan gane ammaka saka wani rabin jiki" ta fada tana tura baki dan ba wai hakan ya saka ta naba'a bane, dukda jikinta yayi sanyi da abinda ta aikata din ta kuma ji kunya dan sam ta manta da sunan Hassanar sa kenan Jalila dan tun a wayarsu ta farko ya gaya mata duk sunayen yan uwansa ciki daya da kuma Jamila wadda ita kadai ce suka Uba daya Mamanta ta rasu itama a hannun Hajiyar su ta tashi.

Shiru ya mata har ya kaita gida basu sake cewa komai ba dan sosai ransa ya sosu da abinda tayin, yanzu ace ma da wata can yake waya ba Jalilan bace beyi zaton zata iya masa magana da irin lafazin da tayi amfani dasu ba sam basu dace ba, amma yayi mata uzuri tunda karo na farko ne.

Umaimah na faman bata rai ta sauka daga motar, a cukulece tayi masa sallama har tayi gaba kuma se ta dawo shidai yana tsaye yana mamakin sabon halin nata na yau tace
"Kuma dai gaskiya ka canza sunan da kayi saving number in dai ba kana so zuciya ta ta buga ba idan ina ganin sunan a wayar ka" tana gama fada ta shige gida ta barshi zaune cikin mota yana tunani. Shikam yau abubuwan nata daure masa kai sukeyi, wannan shine Kishin da take fada daman? Idan kuwa haka ne wannan ai shirme takeyi, duk kishin da zesa ka kasa banbance daidai da rashin daidai ai ya zama shirme.

Seda suka kwana biyu tana fizge fizgr, sam shi ya manta ma me akayi kawai dayaga take taken ta ya dauki hakan a matsayin yanayi da kowanne dan Adam yana iya riskar kansa a ciki na damuwa ko rashin jin dadin wani abu, ya tambayeta ko da wata matsala ne ta nuna babu komai se kawai ya shareta. Daman lokacin shima ayyuka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login