Showing 354001 words to 357000 words out of 429394 words

Chapter 119 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

954

haka zalika banyarda wani yazo gidannan gurinta ba, sannan zata bani wayarta" Abban ya fada yana kallon Umaimah data sunkuyar da kanta qasa tana hawaye, takaicin yanda gaba daya kowa ya tsaneta ya kamata, babu wanda ya dubi halin da ta tsinci kanta a ciki ita ta rasa Khalil a maimakon su tausaya mata suyi qoqarin kwato mata haqqinta se suka bige da tsanarta kamar ta aikata musu wani mugun laifi.

Tana jin Abban ya gama maganarsa, zancen ba zata fita ba ko ba za'a zo gunta ba be dameta ba kamar na karbe mata waya. Idan ya rabata da wayarta ta ina zata samu damar magana da Khalil harsu daidaita ta koma dakinta? Tsawar da Mama ta daka mata ceta sakata miqewa da sauri dan dakko wayar, tana hawaye kamar yarinya ta bashi wayar tata ya karba a gabanta ya zare layin ya ballashi biyu kafin ya sake kallonta yace
"Abu na gaba
daga yau duk wani aiki na cikin gidan nan ya dawo hannunki, ina nufin daga kan shara girki wanke wanke da duk wasu sauran ayyukan tsakar gida ke zaki cigaba da yinsu har wankin kayanku idan kuna da buqata ku bata tayi muku dan ba zan ringa ciyar da ke a banza ba tunda kinqi zaman aure kiyi na Farilla ki samu lada zakiyi Mustahabi anan. Idan har na kamaki da laifin saba daya daga cikin sharuddan nan ina me tabbatar miki da cewar sekin gane kuskurenki tabbas".

Da sauri ta daga kai ta kalli Abban bakinta na rawa alamar son yin magana amma mugun kallon da Mama ta aika mata dashi yasa ta kasa cewa komai ta maida kanta qasa hawaye suka sake balle mata kamar famfo.
"Rayuwar da kika zabarwa kanki kenan zaman gida ba gaki ga gidannan se kici uwar da kika ajiye a ciki. Kinsan dai ba zamu zauna muna goga kafada dake a cikin gidan nan ba mu dafa mu baki kici ki ajiye kwano mu share guri ki zauna na iya lokacin da aka miki ma Allah ya bamu lada dan haka dolenki kiyi aiki in har kina son zaman lafiya damu koda yake ma bata bakina nakeyi saboda na manta da kin rigada kin zama yar kanki kiyi duk yanda yayi miki Umaimah babu wanda zesake tilasta ki akan kiyi daidai amma kin sani matuqar kika qi ji ba zaki qi gani ba kuma kinji abinda Mahaifinki duk ya fada se ki zaba zama lafiya kibi abinda yace ko ki fara neman wani gidan uban da zakije kici gaba da yanda kika ga dama" Mama ta fada cikin fushi ita dai Umaimah kanta na qasa in banda hawaye babu abinda takeyi.

Shiru sukayi na kusan Minti goma babu wanda ya sake cewa komai se Abban ya yunqura ze tashi Mama da Antyn suka miqe a tare suma dan taimaka masa ganin Anty tafi kusa dashi yasa Maman ta tsaya ita kuma ta kamashi suka shige cikin dakin
"Idan baqin cikin ki ya kashe shi se ki zuba ruwa a qasa kisha" Mama ta sake cewa kafin ta juya ta fice daga falon ta barta tana kuka da tunanin ita me tayi kuma da za'ace baqin cikinta ze kashe Abba? Haka taja qafafunta da suka sake yin tsami saboda zama ta fita daga, a bakin qofa sukaci karo da Sharifa zata shiga da Flask qarami a hannunta ta kalli Umaiman tayi tsaki qasa qasa tace
"Wlh mutum ya kashe mana Uba ba yarda zamuyi ba se munyi shari'a dashi" tayi gaba a hasale Umaiman ta fincikota baya tareda watsa mata maridukda ba wai taji abinda ta fada bane saboda ta sauke fushin su da take cike dashi tace
"Dan uwarki ni sa'arkice da zaki mun qunquni?"

Kuka Sharifan ta fasa, Nuratu data taho da Kwanuka tayi saurin direwa a qasa ta fincike hannun Umaiman data shaqe Sharifan tana cewa
"Karki sake gigin taba lafiyar wani daga cikinsu"
"Ke kuma ina ruwanki ai ban saka ki a ciki ba balle ki shiga" ta sake zaburowa Nuratun seta daga mata hannu tace
"Karki kuskura kice zaki zageni dan nima kinsan ba sa'arki bace ba, kuma iskancin da kika sabayi a baya muna daga miki qafa yanzu kinyi kadan wlh duk wanda kika nemi ki taka se ya mayar miki da raddi dan haka ki kama tsumman rayuwarki kija sauran mutunchin daya rage miki, mtsww" taja tsaki ta dauki kwanon data ajiye tayi cikin falon Sharifa ta faki idon Umaimah tayi mata gwalo kafin tabi bayan Nuratu da sauri.

Kamar yar yarinya haka ta wuce dakin Mama tana kuka da hawaye shabe shabe zata shiga ta tuna da Gargadin data mata dan haka ta coge daga bakin qofa cikin kuka ta kalli Maman da suke magana da Anty Hafsa da Maman Asad tace
"Wlh Mama kiyi mun tsakani da Nuratu karta sake shiga shirgina akan me yarinya zata mun rashin kunya na hukuntata sannan tazo ta bada ni a gabanta ta gaya mun magana wlh karta sake idan ba haka ba..."
"Idan ba haka ba me Umaimah?" Mama ta dakatar da ita kafin taci gaba da cewa
"Ke har kina da kunya ma da zakiji haushi dan wani ya miki fitsara? Yanzu maganar da kika zo kina mun a sama kamar yarki ki ai ladabi da Biyayya ne ya jawo haka ko to kici gaba karki fasa"

Seta juya tayi dakinta tana ci gaba da kuka haushin kanta ya kamata data kaiwa Mama qarar ma bayan tasan ba goyon bayanta zatayi ba. Yanzu zaman nan da taga sunyi ma Allah kadai yasan abinda suke fada akanta ita dai Allah na kallo duk Wanda yaci namanta ta barshi dashi.
Kwanciya tayi tana ci gaba kuka baqin cikin ganin da tayiwa Khalil jiya naci gaba sa nuqurqusarta gashi Abba ya kwace mata waya abinda ta qudura yau zata bawa Yasir kudi ya siyo mata sabon Layi tunda yayi blocking wanda yasanta dashi gashi yanzu babu wayar ba ta san yanda zatayi ba kuma tasan a cikin gidan babu me bata tashi wayar. Tana tsaka da Tunanin Sharifa ta daga labule ba tareda ta shiga ba baki a tunzure tace mata
"Kizo inji Mama kuma tace karki bata mata lokaci"
"Wlh se naci uwarki idan na riqeki zaki san ni kikewa fitsara shegiya sa a haihuwar Kaji nayi Jika dake ko Salman wanki na biyu na girmeshi ballantana ke qaramar mara mutunchi" Umaiman ta fada tana miqewa ita dai tayi gaba abinta saboda son ta qara bata rai harda daga murya tana waqa
"Ruwa yaci garin maqiya ashe dai mune da guri na kwana se inga tsiya".

Kwafa Umaimah tayi a ranta tana ayyana zasu gamu ne. Seda ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da tayi luhu luhu gefen idonta da dukan jiya ya sama ya tashi dukda maganin da me chemist ya bata ta shafa. A qofar Kitchen ta tarar da Maman ta qarasa gurin ta tsaya Maman ta nuna mata Kayan Miya dake ajiye a qasa tace
"Gashi nan ki debi wanda ze isa ragowar kisaka a Fridzer akwai Nama a ciki ki dauki qulli uku Jollop din shinkafa zakiyi lokaci ya qure bare ayi me Miya".

Galala ta saki baki tana kallon Maman da kuma kayan Miyar da ta nuna mata ita kuwa bata ma sake kallonta ba tana gama fada mata abubuwan da zatayi ta juya ta bar gurin ta koma dakinta suka ci gaba da tattauna abinda ya dame su ita da yayanta. Umaimah kuwa tafi qarfin minti goma a tsaye tana ayyana wai da gaske ake ita zata ringa girki a gidan? Girkin da ko zamanin yammatanci idan da abinda ta tsana ace tayi shine girki balle yanzu data qara sanin dadin jikinta komai tana daga kwance ake mata shine za'a ce ta dora tukunyar Abincin kusan mutum Ashirin gaskiya ba zata iya ba.

Ganin tsayuwar da takeyi ba zata bata mafita ba yasa taja qafafunta ta wuce dakin Anty danta gaya mata ita fa ba zata iya ba gara ma a san me dafa abincin tun wuri. Tareda Fatima qanwarta ta tarar dasu bata san sanda tazo ba, qerere tayi musu akai ba tareda ta gaida Fatiman ba saboda a ganinta Sa'ar Nuratu ce ba wani girmarta tayi da yawa ba da zata gaisheta. Anty ta daga kai ta kalleta ranta babu dadi tace
"Ya akayi?"
"Mama ce tace wai naje na dora girki ni kuma gaskiya banida lafiya bazan iya ba" ta bata amsa kafin Antyn tayi magana qanwarta ta rigata tace
"Ai se kije ki gayawa Maman data sakaki ko dan saboda itace marainiyar wayonki zakizo ki fada mata?"

"Ya haka Fatima?" Anty ta tareta kafin ta kalli Umaimah cikin yanayin qosawa da Halinta tace
"Ba girki na bane kinga bani da damar cewa karkiyi, kije ki gayawa Maman baki da lafiya zuwa kiji sauqi seki karbi aikin" bata ko tsaya taji me zata kuma fada ba taja fuu tayi waje tana jin Fatiman na cewa
"Wlh Anty ke kika bawa yar iskar yarinyar nan dama take taka ki a gidan nan, kin gama shan wahalarta tun tana yar mitsitsiya ta tafi yanzu ta kuma dawowa zata ci gaba da Addaba miki tun wuri idan zaki tashi ki kwatarwa kanki yanci kiyi" bataji Me Antyn tace ba tayi kwafa a fili tace
"Shegiya me suffar munafukai shiyasa aka sakoki saboda halinki ai"
"Ina fata da kanki kike" taji muryar Nuratu a bayanta ta galla mata harara amma batace komai ba. Kitchen din ta koma dan dai ko hauka take bata isa tajewa Mama da raini a wannan gabar da suke ba.

Ta shiga ta duba Gas ta kunna taga da akwai tayi hamdala a ranta, tsabar dorawa kai Jidali ga Gas Allah ya rufa musu Asiri be hanasu kudin Refilling ba amma a ringa kunna itace a gidan. Store ta shiga ta dakko Industrial Gas dinsu ta hada dan tukunyar ba zata hau kan wancan ba Haka ta debi kayan miyar diban wulaqanci ba tareda ta wanke sauran ba ta zuba a Freezer yanda Maman tace ta barsu a gun ta hau aikinta. Ita kanta data gama dafa abincin seda gabanta ya fadi kan tunanin abinda ze biyo baya amma haka ta daure ta juye shinkafar a babbar kular da ake zuba abinci fara tas da ita tun a ido idan ka kalleta babu sha'awa ta debi tata a Qaramin Flask ta qara mai a ciki dan bata saka yanda ze wadata ba ta samu leda ta kwashe musu rabin Yajin dake cikin Roba ta qulle tayi dakinta ko zuwa tace musu ta gama batayi ba.

Kukan yunwar da qananan yaransu Nuratun suka fara ya sakata zuwa ta duba abincin, ta kalli Kitchen din da yayi kaca kaca kamar anyi gasar girki a ciki, kwanukan data bata duk ta barsu a nan ga ledar Maggi ta watsar hatta da ledar data cire Nama nan cikin kitchen din ta yar dasu, kada kai Nuratu tayi taqarasa kan kular ta bude
"Kan bala'i" ta fada a fili tana bin shinkafar da kallo se kace a gidan prison ga qamshin kayan Miya alamar basu soyuwa yana tashi seta dakko cokali ta debi kadan ta kai bakinta bata iya taunawa ba ta furzar da ita saboda Azababben Yajin daya ratsa bakinta wato duk fato faton Jajjagen data gani a ciki zallar Attaruhu ne kenan da alama kwano dayan ta juye duka. Plate ta dauka bayan data sha ruwa ta zuba shinkafar ta fita, a gaban Mama dake kan Sallaya tunda ta idar da Sallar Azahar ta ajiye ta kalli abincinta kalleta se tace
"Abincin ne ta gama". Shiru Mama tayi tana bin shinkafar da kallo ranta na baci, na farko Umaiman ta sani basa saka jajjage a abinci indai Abba zeci sedai a markada kayan miyan dakyau ko babu wuta se an kai Inji sannan wannan fari fat din da shinkafar tayi ina laifinta zuba Kori tunda bataji zata saka wadataccen kayan hadi da ze canza mata kala ba"

"To me zanyi da ita da kika ajiye mun se ku zuba kuci Abbanku dai nasan ba zeci wannan abun ba bari naje na tafasa masa ko Taliya ce tunda inada sauran Miya" Mamanta fada tana miqewa, tsakaninta da Umaimah dai sedai tace Allah ya shiryeta dan ba zata mata baki ba iya bacin ran da take sakata ma Allah ya yafe mata.
"Mama mi dandana kiji ban sani ba ko bakina ne beji daidai ba" Nuratun ta sake fada se Maman ta dakata ta debi lokaci daya ta kai bakinta, dakyar ta tauna ta hadiye lokaci daya idonta yayi jajir saboda bacin rai ta kalli Nuratu tace
"Dakko mun Kular Abincin".

Salman daya shigo ta cewa ya kama mata suka kaiwa Maman ta bude ta kalli uwar Shinkafar data dafa ta zarce awon Abincin da suke sakawa koda ace duk yaran gidan da iyalansu suna nan ga girkin babu kai bare qafa, Babu mai a ciki yaji kamar yayi magana sannan bata tsammanin ta saka Maggi salam yanda kasan girkin Asibiti na masu Hawan Jini ko ciwon Sugar.
"Kirawo mun ita" Mamanta fada cikin tsananin bacin rai, se Anty Amina tayi saurin cewa
"Dan girman Allah Mama ki kyaleta, ta rigada tayi abinda take so zuwan ta nan babu abinda ze canza illah ya qara miki bacin rai da damuwa shiyasa nace ki bari muyi girkin amma yanzun ma Kiyi haquri bari na tashi na dora ko Taliya ce aci ki barta dan Allah".

Badan Maman taso ba ta barsu suka fita su ukun suka fara kiciniyar dora sabon girki, Nuratu ta gyaro Kitchen din ta fito da kwanuka ta taresu gurin wanke wanke su kuma suka hura wuta suka dora Sanwa suna aikinsu suna yan hirarraki dan basu bari Abinda Umaimah tayi ya bata musu rai ba, nan da nan suka gama tsaf suka raba kowa aka saka masa Nasa, Maman Asadta kaiwa Anty nata daki suka gaisa cikin mutuntawa da Fatiman dake ta zubawa yar uwarta qorafi akan Umaimah suka sallami duk sauran yaran kafin suka saka nasu a babban Try sukaci. Bayan sun gama Nuratu ta hado kan ragowar kwanukan zata wanke Mama ta dakatar da ita. Da kanta ta wuce dakin Umaimah, tana kwance daidai a Gado cikinta na juya mata saboda yajin data nada gana abinci ga wanda ta qara dan ta samu abincin ya ciwu mata Mama ta shiga da Sallama ta tsaya akanta tace
"Tashi kije ki wanke kwanukan da aka bata".

Bata musa ba ta biyo bayan Maman ta kalli uban tulin kwanukan a bakin famfo ga wata babbar tukunya bayan wadda tayi girki da ita ta tabe baki ta zauna tana shafa kwanukan kamar me wasa, tun ana dab da kiran La'asar ta fara ba ita ta gama wanke wanken ba se ana Haramar shiga Magrba shima ganin Laqai laqai din nata na mafita bace yasa ta ware ta shigayi tana hawaye tsabar wulaqanci tanayi ana qaro mata wasu seda ta Zagi Salman daya shigo da kwanuka daga dakinsa wasu ma da gani sunfi Sati ba'a wanke ba dan har wari suke ko a jikinsa ya ajiye mata aiko ta ware su gefe ta rantse ba zata wanke ba. Duk tana zaune yayyenta kowacce tayi Harama ta tafi gidanta. Bayan ta gama dakyar ta tashi daga gurin ta bar kwanukan. Seda ta watsa ruwan Zafi ta gasa jikinta dan an kawo wuta kafin ta iya yin Sallar La'asar da Magriba tana shirin aje haqarqarinta ta huce gajiyar girki da Wanke wanke Sharifa ta sake shiga fuskarta a washe da alama tana jin dadin aiken zuwa kiran Umaiman tace

"Mama tace ki fito ki dora Tuwan dare"
"Na rantse da Allah se naci kutumar ubanki idan na riqeki" ta fada cikin tsananin fushi tana tashi zaune muryar Abba ta jiyo daga waje yana cewa
"Gani a kusa fito kici uban nata kuma karki fito kiyi abinda tace kinji".
Kuka daya riga ya zema mata jiki ta fasa amma bame qara irin na jiya ba, jikinta kamar ana sarata haka take ji bata warke daga jinyar dukan data ci jiyan ba ga Azabar aiki an tasota a gaba. Harta sauke tuwon tana kuka, Miyar dai yanzu ta saka musu maggi dukda bata dan dana taji yanda yayi ba gurin kadin ne daman ita hannunta baya yauqi dan haka kubewar ta tsinke kamar Romo, ta Jibge Tuwon a Kula gaba daya ba tareda ta Malmala ba danma na Semovita ne amma dukda haka jikinta ya gaya mata gurin tuqin tana gamawa ta tsallake komai a inda yake ta wuce daki harda kwanukan data wanke tun dazun bata kau dasu ba. Seda ta shiga dakin Mama dake lura da duk abinda takeyi ta fito.

Ta bude tukunyar Miyar ta dandana, kai kawai ta girgiza ta maidata kan wuta ta qara abinda ya kamata ta kuma daureta sannan ta sauke ta shiga rabon tuwon dan Goma ake nema a lokacin daman badan Abba daya ce setayi girkin ba batayi niyar sake jira ta kwashi takaicin Umaimah ba da tuni ta gama girkinta.

Guraren sha daya tuni tayi nisa a bacci dan tana shiga dakin ta kife tana kukan takaici a haka baccin ya kwasheta kiran sunanta taji anayi tareda bubbuga qafarta ta bude ido dakyar dan bata da Nauyin bacci taga Ummu-Salma tsaye, seda ta tashi zaune da kyar kafin Ummu-Salman tace
"Anty Umaimah kije inji Abba"
"Inje kuma Me zanyi masa?" Umaiman ta fada tamkar zata fasa kuka wannan wane kalar bala'ine?
Ita dai Ummu-Salma na tsaye a gefe, bata dade da shigowa gidan ba ta taho daga makaranta Dutse take FUD tana Final Semester dinta Motarsu ta lalace se goma ta iso tana shirin kwanciya Abban ya ce ta kirawo masa Umaiman.

Seda ta gama qunquninta da qananun hawaye kafin ta miqe tana layi ta fita, tsoronta karya sake mata irin dukan jiya da babu inda zata wlh haka ta isa falon Abban suna zaune tareda Mama da Anty ga Kular abincin ranar da tayi a gabansa tana kallon fuskarsa gabanta ya fadi saboda fushin data gani akanta wai shi da Bashi da lafiya dan Allah baze sararawa zuciyarsa haka ya dena fushi ba? Qasa ta samu ta rabe idonta har sannan yana yajin bacci Abban ya fara magana cikin fada yana cewa
"Wato saboda ki nuna ke bakya ji duk kuma abinda aka ce kiyi sekin bata wa mutane rai shiyasa kikayi haka ko? To bari kiji daga yau kamar yanda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login