Showing 273001 words to 276000 words out of 429394 words

Chapter 92 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1010

matsalarta bace koda Rufaida ta dawo kamar yanda tayi alqawari taje gidan se kawai tace mata babu komai, daman abu ne ya taso mata kuma ta rigada tayi daman bata sake bi takan Safinah ba dan ita shawararta a gunta ba mafita bace.

Lafiya lau take ci gaba da zuba mulkinta, yanda Khalil din yake ta tata yana tarairayarta ya sake tabbatar mata da cewar babu waccen magana ta rusata dan haka ta saki ranta take sabgoginta. Hajiya ce dai ta dauke mata wuta ba kamar yanda suke a da ba tunda ta fahimci da hadin bakinta aka so ayi mata qullalliya shikenan ta qullaceta shigar da takeyi part dinta ta dena sau daya take leqawa ta gaisheta ba kuma ta zama suyi hira kamar yanda suka saba zata koma bangarenta su kansu yaran yanzu janye su takeyi da sun dawo daga makaranta suka shiga bazata barsu su koma part din Hajiyar ba se kwanciya bacci shima din saboda ba zata iya zirga zirgar tashi sakasu fitsari ba ne amma ta qudurce a ranta data haihu zata tattaro yaranta gaba daya su dawo gurinta tunda itama fuska biyu ce da Hajiyan toh su zuba su gani.

A bangaren Hajiya ma kwana tayi tana juya maganganun Khalil din, har ga Allah ita dai bata son qarin auran nan daya dakko ba kuma dan komai ba se dan gudun tashin hankalin da ze iya faruwa a gidan. Iya abubuwan da suka faru a baya sun isa ishara a sannan ma hasashene ya saka Umaiman aikata abinda tayi ballantana a yanzu da zancen auran na gaske ke shirin qulluwa, ita duk ba wannan ba yarinyar daya dakko yake son auran kanta abar tausayice bata yi kwarin da za'a hadata kishi da mace kamar Umaimah ba banda ma abu irin na Namiji idan auran yake so meze hana yaj ya nemo babbar Mace amma ya dage se wannanyar yarinyar. Haka ta ringa juye tana saqa yanda abubuwan zasu kasance, a yanda ya bude baki har yake mata magana ta tabbatar da har zuci yake son auran nan kuma idan tace zatayi amfani da qarfinta na Uwa ta tauye shi batayi masa Adalci ba dan haka dole ta haqura ta barshi yayi, amma badai ya auri wanann yarinyar ba sedai yaje can ya samo wadda zata iya gogawa da Umaiman dan idan ta bari akayi wannan hadin tamkar daukar Alhaki ne. Ita kanta Hajiya Hauwan tayi mamaki data yarda da wannan hadi amma zuwa da safe zata kiraya suyi magana ta fahimta ta yanda su da kansu zasu fasa bashi auran ta haka komai zero warware ba tareda yayi zargin ita ta hana ba. Da wannan shawara tayi Na'am ta kiran Hajiya Hauwa amma kafin nan zata tara sauran yaranta mata dan taji shawarar su akan wannan al'amari kafin ta yanke hukunci.

Washe gari kuwa da safe ta kira Amina ta shaida mata tana son ganinsu gaba daya yau, babu bata lokaci kuwa Aminan ta kira Jamila da Jalilah ta gaya musu daman Habiba na gida dan haka kafin qarfe tara na safe gaba daya sun hallara a gidan saboda amsa kiran Hajiyar kowacce zuciyarta cike da son jin ba'asin wannan kiran gaggawa haka.

A taqaice Hajiyar tayi musu bayanin dalilin kiran nasu da tayi, Jalilah taja kabbara harda daga hannaye tace
"Alhamdulillahi Allah na gode maka daka nuna mun wannan rana da raina ban mutu ba, ai wallahi na dade da wannan qudurin kuma koda ace Khalil be nemo aure ba ni da kaina zan nemo masa to gashi yayiwa kansa tunani me kyau kai wallahi naji dadi, Allah ya tabbatar da Alkhairi ya nuna mana lokaci"

Jamila da tayi tagumi ce ta janye tana cewa
"Toni abin ne na rasa me zanyi, murna ce ko kuma fargaba? Yin auran abu ne me kyau amma ni tashin hankalin da matarsa zatayi shi nake tsoro wallahi"
"Kamar kin shiga raina Jamila ni kaina abinda kawai nake hasasowa kenan, gashi Hajiua tace yarinya ce qarama idan da ace ma wata babbace da zasu iya gogawa da sauqi amma yanzu ya auro yarinyar mutane tayita azabtar da ita ai anyi ba ayi ba kenan" Anty Amina ta goyi da bayan Jamilan, Hajiya na shirin magana Jalilah ta taresu da cewa
"Oh saboda ana gudun Jidalinta shikenan shikenan se yayita zama yana tauye kansa shi bazeji dadin aure ba to ko jaririya ya nemo haka ze aurota kuma babu abinda ta isa tayi mata da ikon Allah taci zamaninta yanzu kuwa sedai ta zama yar kallo a gidan Khalil. Ni bari na kirashi ma yazo muji yanda za'ayi da batun hada lefe gara ayi komai da wuri bana son bata lokaci".

Duk ta yanda suka so kawo suka akan lamarin auran seda tabi ta kanainaye musamman da Khalifa ya shigo shima ya mara mata baya seda suka san yanda suka ja ra'ayin Jamila da Aminan suka Aminta da zancen auran dukda daman su bawai basa so yayin bane, Aa Jidalin Umaimah suke tunani da kuma tausayin ita wadda akace yana so ze aura din suna ganin tayi qanqanta a hadata kishi da Umaimah. Hajiya da tunda suka fara bata ce musu komai ba tayi ajiyar numfashi tace
"Yanzu meye matsayarku akan maganar nan? Nidai har ga zuciyata bawai bana son auran nan ba Aa tunanin abinda zeje ya dawo nakeyi, bana son tashin hankali musamman a matsayin da yarinyar nan take ciki gata da taohon ciki kuma daman tun samuwar cikin ake ta turka turka daga wannan se wannan bana son abinda ze zo ya taba lafiyarta ko ta abinda yake cikinta amma kuma bazan so na zama me son kai ba shima Babana na tauyeshi, dan haka mecece shawararku ta qarshe akan abinda ya kamata muyi?"

Anty Amina ce tayi magana tace
"Nidai Hajiya ina ganin tunda har Khalil ya furta yana so yayi aure ki barshi yayi ki kuma bishi da Addu'a Allah yasa hakan ya zama Alkhairi ya kuma bashi ikon yin Adalci a tsakaninsu. Amma yanzu yayi haquri ya dakata da maganar auran har zuwa Umaimah ta haihu saboda kowa yasan halinta, bazata dubi halin da take ciki ba tsaf zata illata kanta ta illata abinda ke cikinta a banza saboda haukan kishi dan haka yaci gaba da naman auransa a hankali har zuwa sanda Allah ze tabbatar".

Jalilah da Jamila sunyi Na'am da maganarta amma seda Jalilan ta qara da cewa
"Amma kamar yanda yace iyayenta sunce ya tura idan da gaske yake to ya kamata ayi hakan kinga shine shaidar yana nema manya su shiga cikin magana, daga nan za'a iya jan lokaci ta fara makaranta ma zuwa sannan ta qara wayo da sanin yanda duniya take kafin azo ga batun aure ko ba haka ba?"

Da wannan suka rufe zaman, kuma basu tashi ba seda Hajiyan ta kira Baba Abu ta sanar masa kuma shima yayi na'am da al'amarin har yana cewa
"Ai Hajiya Ibrahim me haquri ne wallahi saboda tunda naji halayyar yarinyar nan a bakin iyayenta na tabbatar da ba qaramin haquri yake dashi ba da aka dauki wannan lokaci babu wanda yaji kansu kinga kuwa yanzu tunda ya nuna yana da buqatar qari babu me hanashi, zan samu Alhaji Garba da Alhaji Shehu se muji ta bakin Ibrahim din inda za'aje masa neman auran, Allah ya tabbatar da Alkairi yasa zamu gani".

Guraren sha daya da rabi Jamia ta miqe zata tafi dan tana da duty a Asibiti sha biyu zata karba, tare suka fita da Anty Amina datace itama zata koma gida dan babu abinda tayi kafin ta fito nan suka bar Jalilah da zata wuni tana sake jaddada musu kowa ta hado gudummawarta su fara hada lefe Jamila na mata tsiyar ita da yar dakin nata yau kuma itace ja gaba a kan qaro mata abokiyar zama suka fita suna dariya.
Turus sukayi a compound gurin da Khalil yake ajiye motoci, cikin kaduwa Anty Amina ta shiga kwalawa Sammani kira se gashi nan kamar an jefoshi ya fado gurin.

KHALIL
Tun qarfe bakwai ya shirya saboda zeje Qunchi, suna aikin gina makarantar kwaleji ya manta shaf be sanar mata da fitar safe zeyi ba dan haka bayan ya gama shirinsa dakansa ya tafasa ruwan zafi ya hada shayi yasha da sauran Gurasar jiya da sukayi ya dumamata. Yana cikin karyawar Ruqayya ta shiga kitchen din, cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa yana tambayarta ko Umaiman ta tashi tace masa Eh yanzun ma ita zata damawa Kunun Gyada dan haka ya fita daga kitchen din ya wuce dakinta na qasa. Tana zaune akan gadon ta jingine bayanta da Allon gadon tana danna waya ya shiga ta dago ta kalle shi tareda amsa sallamar da yayi kafin ta mayar da kai tana ci gaba da danna wayar.

A gaban mudubi ya tsaya yana kallonta, gani yayi ta kumbura tun daga fuskarta har zuwa yatsun qafarta dan haka ya matsa kan gadon ya danna qafarta da yatsun hannunsa ta janye qafar tana ya mutsa fuska kafin ta gaidashi a hankali. Be amsa ba ya zauna gefenta yana cewa
"Meya sameki haka, kinga yanda kika kumbura gaba daya kuwa? Amma jiya da dare naga ba haka kike ba".

Baki ta dan tabe kafin tace
"Nima haka na tashi na ganni ai"
"Kuma shine kike zaune ba zaki kirani muje Asibiti ba, ina ne yake miki ciwo?" Ya fada yana miqewa tsaye seta kalle shi tace
"Nifa lafiya ta qalau inda ina jin wani ciwo ai da na tafi Asibitin da kaina, kuma kumburi daman in ciki ya tsufa ai mutum yana yi ba wani sabon abu bane"

"Amma ba irin wannan ba, duk cikin da kikayi baki taba kumbura haka ba ki tashi kawai muje Asibiti su duba ki idan sun tabbatar da babu wata matsala sannan zan yarda" ya sake fada yana janyo Hijabinta da tayi sallah ta bari akan Sallayar. Baki ta zumbura tana zaune bata da niyyar tashi kuma bata ce masa komai ba se ya ja tsaki yana kallonta cikin bacin rai yace
"Kina da matsala, lafiyar jikinki ma baki damu da ita ba komai se kin saka shirme da shiririta a cikinsa ki tashi nace tun ban bata miki rai ba saboda kin san ni bama wasa da duk abinda ya shafi lafiya".

Dole ta miqe badan taso ba, dakyar taken daga qafa saboda yanda jikinta yayi nauyi, ita kanta tasan kumburin ya zarce na yanda ta saba amma saboda bataji wani ciwo ba kuma da rashin daukar abu da muhimmanci kamar yanda yace din yasa tayi zamanta. A hanya yana ta faman yi mata mita ita kuwa ta doni baki gaba kamar zata tabo glass din motar, daidai zasu shiga Gate din Asibitin watarsa dake ajiye tayi qara, yanda kasan ita aka kira ta kalli wayar da sauri 'Shatunah' sunan data gani yana yawo kenan akan screen din wayar ta kalli Khalil???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? wanda shima kallo daya yayiwa wayar ya dauke kai tamkar bashi ake kira ba a haka ya nemi guri yayi parking motar ya kashe kafin ya dauki wayar tasa da Wallet kuma har sannan yaqi yarda su hada ido da Umaimah data kafa masa nata idanun kamar wata sabuwar Mayya.

Seda ya kusa shiga Reception din Asibitin ya lura da bata biyo shi ba, yawu ya hadiye kafin ya qara hade fuska ya juya gurin Motar, tana ciki hat sannan ta hada uban zuba kamar me naquda se numfarfashi takeyi yanda kasan ana tsira mata allura zata fashe saboda fushi.
"Ki fito muje" ya fada cikin tsare gida kamar tana jiransa kuwa tace
"Bazan fito ba, idan kuma ka isa kazo ka fiddani ta qarfi".

Kallonta yayi ganin yanda fuskarta tayi ya tabbatar da ba abinda ya mata zafi yanzu zata tara masa mutane ta zubar masa da mutunchi a gurin dan haka ya bude sit dinsa ya shiga seda ya kulle motar kafin ya kalleta babu yabo babu fallasa yace
"Ki yi haquri muje a dubaki bayan nan koma menene idan muka koma gida se muyi magana akai".

"Ashe kasan akwai abinda zamuyi magana akai kenan, to jikina ne kuma lafiyata ko nace bazan shiga ba, ko ka gaya mun wace yar iska ce ta kiraka da har kake dangantata da taka ko kuma wallahi yanzu a nan gurin nayi maka Tijarar da baka zata ba" Umaiman ta fada tana kallonsa Khalil dayaji ransa ya baci nan da nan saboda yar iska data kira Humairansa da shi yasaka shima cikin fushi yace mata
"Kin dade bakiyi Tijara ba ko kuwa an gaya miki ina tsoron haukanki ne? Jiki kuma kamar yanda kika fada nakine lafiyarki ce duk abinda ya sameki ke kadai ya shafa bani ba dan nan bada dadewa ba zan dakko wata dake ko babu ke rayuwata zanyi bani da Asara" yana gama fadar haka ya tada motar a tsiyace ya fizgeta ya fice daga Asibitin Umaimah da tayi suman zaune saboda jin abubuwan da yake fada fizgar da yayiwa motar ce ta tabbatar mata da cewar a Raye take kuma gaske ne ba mafarki ba Khalil ne yake fada mata wadannan maganganun.

"Dake ko babu ke zanyi rayuwata bani da Asara" maganar ta caki zuciyarta kamar shigar mashi, cikin azamar da bata san tana da ita ba ta kaiwa Sitiyarin cafka suka shiga kokawa yana qoqarin riqe kan motar tana fizgewa, abin yazo masa a bazata gashi sun rigada sun hau titi cikin taimakon Allah ya hankadeta ya samu ya riqe kan motar daya kwace masa saura qiris su afkawa murhun wata me qosai ga mutane a gurin sun baibayeta dan har seda ya ture mutum biyu Allah ya rufa asiri basu ji ciwo ba suka miqe da sauri suka matsa daga gurin. Motar na tsayawa ya kasheta gaba daya ya zare muqullin kafin ya juya ya zabga mata wani lafiyayyen mari da seda jinta da ganinta suka dauke na wani lokaci kafin ta fasa qara saboda gigitaccen zafin daya ziyarci kwakwalwarta.

"Ke wace irin mahaukaciya ce Umaimah, me kike shirin yi? Kashe mu kike so kiyi kome akan Titi zaki gwada wannan haukar?" Ya fada cikin fushi yana kallonta tuni idanunsa sunyi jaa saboda bacin rai haka jijiyar kansa sun tashi rudu rudu alamun ya kai qololuwar bacin rai kenan. Umaimah ko bata iya bashi amsa ba kururuwa kawai takeyi saboda radadin Azabar marin daya kwasa mata, yaja tsaki kamar ze tsinke harshensa kafin ya balle murfin motar ya fita. Be bi takan masu motocin da suka tsatstsaya wasu na zaginsa wasu na neman jin ba'asin abinda ya faru ba ya wuce Gurin mutanen daya afkawa sunyi cirko cirko suna kallon motar tsabar bacin rai ya kasa bude baki yayi musu magana se hade hannayensa biyu yayi alamar ban haquri, wani dan dattijo da yazo siyan qosan ya matsa kusa dashi, ya daga kafadarsa. Akan idonsa ta kama Sitiyarin dan yana daya tsallaken lokacin cikin tausasa murya yace

"Kayi haquri kaji Dana, su Mata wani lokacin ka kan rasa inda hankali da tunaninsu yake tafiya, dukda bansan meya hadaku ba amma tayi wauta. Ka jaku a hankali ku tafi gida koma menene ku warware ka kuma kula karka bari ta sake samun damar maimaita abinda tayi yanzu domin ba daban Allah ya taqaita ba qila da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba Allah kadai yasan Adadin mutanen da hatsarin nan ze ritsa dasu".

Dakya ya iya cewa mutumin
"Nagode Baba" kafin ya juya ya shiga motar, Umaimah dake kuka kamar wadda ake zarewa rai ta dago ta kalleshi, ya kunna motar yana fara tafiya ta sake yunqura zata kama sitiyarin be bata lokaci ba ya riqe motar da hannu daya ya sake zabga mata wani marin da daya hannun
"Na rantse da Allah kika sake kwata mun hauka sena nuna miki na fiki rashin hankali, budeki zanyi ki fada kan Titin mota tabi ta kanki kowa ya huta tunda abinda kike nema kenan" ya fada cikin bacin rai ba tareda ya kalleta ba.

Cikin kukan radadin Azabar Marin data sha tace
"Ai wallahi sedai mu mutu tare dan na grantse da Allah babu wata mace data isa ka hadani da ita, duk kuma wadda tayi gigin shigowa rayuwarmu ka tabbata cikin biyu se daya ta faru, ko dai ita ta mutu ko kai ka mutu idan yaso gaba dayan mu muyi Asara" taci gaba da kuka wiwi dan jin fuskarta takeyi kamar ya watsa mata tafasashshen ruwan zafi. Khalil kuwa dariya ma maganar tata ta bashi dan haka ya dara kadan kafin ya kalleta yace

"To kuwa seki shirya saboda nan bada dadewa ba wadda tafiki cancanta data zamo matata zata karbe gurbinta, idan kinga dama ki nutsu ku zauna lafiya idan ba baki ga dama ba kiyi duk abinda zuciyarki take ayyana miki da kiyin aurene babu fashi se nayi idan yaso ki kasheni ko ki kasheta kamar yanda kike fada se mu gani ke idan zaki zauna kiyi gadin duniya ne" daga nan yaja bakinsa yayi shiru duk irin ihu da kururuwar da takeyi tana zaginsa da iyayensa harda Mahaifinsa dake kwance a kabari bata manta dashi ba seda ta zaga yayi mata shiru be tanka mata ba, tafasa kawai zuciyarsa takeyi ya tabbata idan ya biyewa abinda zuciyarsa takr saqa masa to fa sedai ya maida gawarta gida dan se yayi mata dukan mutuwa a motar kafin su isa amma haka ya daure har suka je gida.

A bakin get ya tsaya ya kalleta da idanunsa da sukayi jajir ita kanta duk rashin mutunchin da taken zazzaga masa suna hada ido seda ta dauke wuta ta matsa can jikin qofar motar, cikin wani irin Amo yace ta sauka, bude bako tayi da niyyar gaya masa magana ya daka mata tsawar da har seda abinda yake cikinta ya wuntsila, babu shiri ta balle murfin ta fice tana haki, a bakin get din ta tsaya tabi motarsa daya fizga da gudu ya bar layin da kallo nan ta shiga tunanin me zatayi masa. Ta rantse da abinda ze kasheta Khalil yayi kadan dashi da duk ma wanda suke goya masa baya akan yayi auran za kuma ta tabbatar musu da ita Umaimah warkice daidai da qugun kowanne dan iska.

Haka taja qafa ta shiga compound din, idonta ya sauka akan sabuwar motarsa Marsandi daya siya ko cikakken wata biyu batayi ba gaba daya zata iya qirga sau nawa ya hauta dan ita

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login