Showing 339001 words to 342000 words out of 429394 words

Chapter 114 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

937

bude baki da sunan yiwa bayani daga gaisuwa shikenan idan mutum ya gaji da zaman gulmarsa ya tashi ya tafi. Daga Mama har Abba kuwa yini sukayi a dakunansu suna jinyar jiki data zuciya. Ruwan shayi kadai suka ringa iya kurba bisa tirsasawar Yayansu har kuma suka fita zuwa Asibitin a cikin Mama da Abban babu wanda ya sake tayar da maganar.

Jikinta yayi mata nauyin da ko bakinta ta gagara budewa tayi magana se binsu takeyi da kallo kawai, so takeyi ta tambayesu ina Khalil, ta tabbatar da yana raye ko kuwa da gaske ya mutu? Idan har ya zama Khalil ya mutu kuwa tasanbata da sauran amfani a duniya binsa zatayi. Seda Likita yazo ya sake duddubata ya tabbatar da komai normal kafin ya fita yana sake jaddada musuda su barta ta huta kar su sakata magana ko yin wani dogon yunquri Likitan na fita gaba dayansu suka miqe da niyyar tafiya. Babu wadda ta kula Umaiman a cikinsu haka itama ta rakasu da ido suka bar dakin Anty Hafsa ta rakasu a hanyarta ta dawowa suka hadu da Jalilah da Humaira sun dawo Asibitin suka gaisa babu yabo babu fallasa ta tambayesu jikin Khalil kafin ta juya jiki a sanyaye ta koma dakin da Umaiman take.

Kujera ta samu ta zauna ba taredata kulata ba itama, Umaimah tayi qarfin halin bude baki ta kira sunanta tayi mata banza seda ta sake maimaitawa kafin a hasale Anty Hafsan tace
"Karki kuskura kice zaki matsawa rayuwata saboda kin ganni anan, banda ina tsoron Allah ya kamani da laifin watsar da zumunchi da wlh Umaimah baki isa na sake kallon koda inuwarki ba, kiyi ta kanki kawai ni bana zauna bane saboda nayi hira dake ko wani Ahto".

Kallon Anty Hafsan ta ringayi harta gama sababinta kafin a hankali idonta ya ciko da kwalla tace
"Idan kin kwantarda hankalinki ma Anty hafsa ni nasan tawa ta qare a duniyar dan idanhar Khalil ya mutu da gaske nima mutuwa zanyi"
"Dallah rufe mun baki maqaryaciyar banza, Idan Khalil ya mutu zaki mutu sannan har ki nemi ransa da hannunki saboda kin rainawa kanki hankali to idanso kikeyi ki tabbatar da qudurinki to bakici nasara be mutu ba yana nan da ransa Allahya kubutar dashi daga sharrinki ya kuma raba shi da Uqubar auranki. Kaiconki Umaimah, tunda kika yiwa kanki sanadin rabuwa da nagartaccen Mutum kamar Khalil har ki mutu ba zaki maida makwafinsa ba idan kuma baki tubarwa Allah ba haqqinsa baze taba barinki ki zauna lafiya ba" Anty Hafsa ta sake hayayyaqo mata cikin daga murya da har seda wata Nurse ta shigo tana cewa
"Haba baiwar Allah ya zaki ringa yi mata ihu akai bayan an gaya miki tana da buqatar hutu da kwanciyar hankali a yanzu? Idan ba zaki iya kulawa da ita ba ki tafi wata tazo amma ba zakizo kina ma patient dinmu ihu akai ba"

Banza tayiwa Nurse din data matsa gurin Umaimah dake kuka a hankali tana rarrashinta da abin ya isheta ta fita ta bar musu dakin badan Mama cetace ta zauna ba bataga abinda ze saka tayi jinyar Umaimah ba.
Umaimah kuwa dakyar Nurse ta lallabata tayi shiru, ta kalli Nurse dinda idonta da yayi jage jage da hawaye tace
"Nurse Dan Allah ki taimakmun ki kaini naga halinda Mijina yake ciki shine kadai abinda ze saka hankalina kwanciya dan Allah"
"Kiyi haquri kinga yanzu kika farka jikinki na buqatar hutu ko magana da kikeyi yanzu da yawa be kamata ba ki yi haquri zuwa gobe idan kika ji qarfin jikinki se a kaiki ki ganshi" Nurse dinta fada mata cikin lallashi.

Washe gari da Safe ta kwarzabi Nurse akan seta kaita taga Khalil, jijjiga gadon da take kai ta shigayi saboda tsabar takaici daman Anty Hafsa fita ta sakeyi ta bar musu dakin Nurse din ganin Umaiman na neman ta janyo musu sabon Aiki bisa tilas ta kirawo Dr, jijjigar qarya ta shigayi babu shiri ya basu Umarnin su turata akan Wheel chair su kaita dakin da Khalil yake, haka Nurses din suka fita da ita cike da zumudin ganinshi take, kwata kwata bata tuna wani abu makamancin saki ya gifta tsakaninsu Allah Allah take ta ganshi taga lafiyarsa a haka suka shiga dakin da aka kwantar da Khalil din a bangaren VVIP.

Yana zaune akan Gadon ya jingina bayansa da Pillow da aka saka masa dan ya bashi support Humaira na zaune a gabansa da bowl me dauke da Quaker oat tana bashi a hankali wani kalar tsadadden murmushi ne akan fuskarsa yake jifanta dashi a wannan yanayin Umaimah ta riske su wani abu me kama da saukar Aradu ya dirar mata a zuciya take komai ya tsaya mata wani tuquqin baqin ciki ya tokare mata maqoshi ta kasa cewa komai nan da nan hawaye suka balle mata.

Khalil daya ga shigowarsu lokaci daya murmushin dake kan fuskarsa ya disashe. Ya zuba mata ido yana kallonta wani abu me kama da tsanarta yana mamaye tarin soyayyar da yake mata a baya. Ganinya zubawa bakin qofa ido ya saka Humaira kallon gurin itama a tsorace ta saki Bowl din hannunta a qasa abinda yake ciki ya zube Jikinta ya dauki rawa saboda ganin Umaimah hannu biyu Khalil ya saka ya kama kafadunta yajata ta fada jikinsa ya lumshe idanunsa da suka fara canza kala saboda bacin ran ganin Umaimah.
"Ku fita da ita" ya fada a hankali ba tareda ya bude idonsa ba Nurses din da suka zama hoto suka shiga tura Umaiman dake kuka kamar ana zare mata rai, baqin cikin abinda Khalil din yayi a gabanta kamar ya kasheta da ace zata iya tashi tsaye kan qafafunta da babu abunda ze hana ta janyo yarinyar nan daga jikinsa tayi mata dukan mutuwa. Wai me yasama ba ita ta kwalawa abun akai ba ta mutu kowa ya huta?

Da wannan tunanin suka maida ta dakin da take, Anty Hafsa taja tsaki ba tareda tace musu komai ba. Nurse nagama maidawa Umaimah drip Jalilah ta shigo dakin kamar an korota ta nuna Umaiman da yatsa tace
"Ki kama sauran mutunchin daya rage miki karki kuskura ki sake rabar dan uwana. Aurene ya hadaku kuma ya sawwaqe miki Ubangiji ya sake gajarta tarayyarku ya yanke Miki iddarsa kinga babu sauran Kare bin damo idan kuma ba so kikeyi ki hasalamu mu dauki matakin daya kamata a akanki ba ki fita daga rayuwarmu Umaimah, iya daukar Alhakinmu da kikayi Allah yabi mana haqqinmu amma bama buqatar ki sake rabarmu har abada" tana gama fadar haka ta juya ta fita Umaimah ta bita da kallo cikin kaduwa da kalamanta.

Tabbas bata manta Khalil ya saketa ba amma bata yarda cewar aure ya qare a tsakaninsu ba. Ta sani Khalil yana sonta itama tana sonsa duk abinda ya faru tursasashi akayi amma badan ra'ayinsa ya saketa ba kuma tasan baze taba haqura da ita ba duk ma a yaya ze dawo su ci gaba da rayuwarsu. Ranar wuni tayi zuciyarta babu dadi, idanta tuna wai babu igiyar auran Khalil akanta se taji kamar tayita kurma ihu. Ita dai Anty Hafsa tafi ki mutu batace mata, idan kaji tayi magana yan dubiya ne sukazo wanda da yawa tsurku ne yake kawo su saboda irin labarun da suke ta yawo a gari.

Randa suka cika kwana uku a kwance ranar Abba da Mama suka sake komawa duba Khalil, Hajiyarsa ma an sallameta tun washegarin ranar ta koma gida shida Umaimah ne a kwanceda jaririyarsu da itama a ranar aka fito da ita dan Alhamdulillah jikinta ya murmure ta samu sauqi. Jalilah ce ta karbota kai tsaye ta wuce da ita dakinda aka kwantar da Khalil din yana zaune bayan Humaira ta gama bashi abinci sun tafi gidada Jamila saboda ita ta kwana dashi ranar Khalifa ya tafi wani aiki ta shiga da Babyn ta miqa masa ya karbeta yana kallon kyakykyawar fuskarta sak Umaimah.

"Kamar uwarta tayi kaki suna bani ita nayi addu'a na tofa Mata Allah yasa ta tsaya a iya kamannin karta kwaso baqin hali irin na uwarta" Jalilan ta fada Khalil dai kallon yarinyar yakeyi wata irin qaunarta me zafi tana shigarsa. Sallamarsu Abban ce ta katsewa Jalilah Mitar da takeyi, cikin girmamawa ta gaishesu dan duk abinta ba zata zargi Iyayen Umaimah da saka hannu a cikin abinda yarsu take aikatawa ba. Dattijai ne gaske da suka nuna hakan a cikin al'amuransu. Iyakacin jajaircewar da sukayi gurin tabbatar da samuwar yancin Khalil ya isa ya qara siya musu qima da mutunchi a idon kowa.

Ta karbi Babyn daga hannunsa ta bawa Mama ta karbeta tana kallonta itama tausayin yarinyar ya kamata ta fado a yanayi mara dadiz tazo a ranar da Uwa da Ubanta suka raba hanya.
"Masha Allahu Allah yasa ko dakko Haliyyar kwarai ta mahaifinki tunda kinyi karar dakko fuskar mahaifiyarki" Abba ya fada har zuciyarsa bayan da Mama ta miqa masa yarinyar ya sake kallon Khalil bayan yayi masa ya jiki yace
"Wane suna kukayi mata huduba dashi"
"Daman sunan Mama za'a saka mata ba'a rigada dai anyi hudubar ba" Khalil ya fada a sanyaye se Abba ya dagata yana cewa
"Allah ya raya yayi akbarka yasa ki gaji me sunanki gurin haquri" Jalila da Khalil suka amsa da Amin. Sun jima sosai a dakin suna sake tattaunawa har zuwa sanda wasu Abonana Khalil suka zo dubashi kafin suka fita har sannan yarinyar na hannun Abba.

Bisa tursasawarsa Mama ta bishi dakinda Umaimah take, tana kwance kan gado ta zubawa Bango ido dan ta mayar da kanta kurmar qarfi da yaji, jinyar zuciyarta kawai takeyi ta daga kai ta kalli Mama da Abban da suka shigo da Sallama Nuratu da Anty Hafsa suka amsa tareda basu gurin zama suka shiga gaishe su. Seda Umaimah ta dauke hawayen daya zubo mata kafin cikin rawar murya ta shiga gaida iyayen nata. Abba ya amsa a gajarce Mama kuwa daman ko kallon inda take batayi baya miqawa Nuratu yarinyar yana cewa
"Ga ta Mahaifiyarku yayiwa takwara"

"Ni bana so sanda na ce ya saka mun ai be saka ba ya je ya canza mata suna infact ni bazan riqe masa yarsa badai ya sakeni ba yaje ya kaiwa Hajiyar ita ko matarsa su riqe masa amma wlh bazan shayar masa da Ya ba" Umaimah da basu saka ta cikin maganarsu ba tayi tsugul ta amshe tana gama fada ta rushe da kuka me sauti kamar daman jiran dalilin yinsa takeyi. Kallonta sukayi gaba daya, Abba ya sauke ajiyar zuciya Mama kuwa sake maida kai tayi tana kallon qofar fita badan tana kokawa da shaidan dake mata hububar tsiya ba da qila tsinewa Umaimah zatayi tabi duniya kawai kowa ya huta. Ganin tana neman caza musu kwakwalwa babu gaira babu dalili gaba daya suka fice suka barta a dakin tana kuka tamkar ranta zefita. Turo qofar akayi ta daga kai bazato suka hada ido da Safina data shigo dakin a kidime kamar an jefota.

Gajiya tayi da kiran Umaimah a waya bata samu yau taje gidan Sammani ya shaida mata Umaiman tana Asibiti bata da lafiya hankali tashe ta nufo wajenta ta taki sa'a Umaimah na neman wanda zata kwance sauran haukan daya rage mata a kwakwalwa.

Fadar irin tashin hankalin da sukayi da Safina bata baki ne, ta manta da zancen wani dinki da yake a jikinta da qarfin da kowa yayi mamakin inda ta samoshi saboda ganin tunda ta farka bata iya wani motsa jikinta dakyau se gashi ta kama Safina ta sakata a kwana ta ringa kilarta aka rasa me kwatarta saboda kowa yana tsoron ya shiga ta hada dashi.
Ta zagi Safina da kafatanin danginta ta kuma tsinewa Malaman Safina da Ahalin su gaba daya ta kuma jaddada mata da ta nemo mata duk kudadenta data san ta karba ta kaiwa Malamai idan ba haka ba se tayi mata abinda harta mutu baza'a sake hada baki da ita a yaudari wani ba. Dakanta ta ringa shelanta irin abubuwan Safinan ta kaita tasa akayi mata ashe duk yaudara ce tunda gashi nan har Khalil din yayi aure bata sani ba qarshe ta karbi tukuicin Saki sanadin wannan uwar sabada da akaci seda dinkin jikinta ya bude aka sake maida mata da wani jiki ya dawo danye sati daya ya kamata a sallameta amma seda ta shafe sati biyu a Asibitin cikin wani mawuyacin hali kaf??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in suka sallamesu gaba daya ta koma gida da Babynta Malika wadda ta karbeta bisa tirsasawar Abba da yayi rantsuwa akan in har bata karbi yarba kamar yanda take iqirari sedai ta nemi wani gidan uban badai nasa ba.

Ta karbeta dukda seda suka qulla yarjejeniya akan Idan Malikan ta cika shekara daya Khal ze karbi yarsa, kuma yace ya dauki Alhakin samar musu da duk abun buqata har zuwa wannan wa'adin, zaman Asibitin da tayi kaf shiya biya kudin sannan yan uwansa basuyi qyashin siyan duk wani abu da Jaririyar zata buqata ba sun kai gidansu Umaimah, dukda zafinta da sukeji be shafi yarsu ba. Sun yi mata ragon suna da duk wani abu da akeyi lokaci kawai suke jira shekarar da aka diba ta cika daga nansu karbi yarsu su hada da Sauran saboda koda ace Umaimah ce ta buqaci su bar mata yaran babu yanda za'ayi su yarda ballantana da har ta budi baki tace bata qaunar ganinsu, yanda Ubansu ya fitar da ita daga rayuwarsa itama ta bar masa dunda daman bada su taje ba.

Mamakin da lamarinta yake bawa mutane kadan ne, daman sunsan dacewar zata iya aikata abinda yafi haka ma amma da yawa sunyi zaton rabuwarsu da Khalil din da yanda abubuwa suka wakana zasu ladabtar da ita ta koma cikin saiti sedai ko kusa a lissafin Umaimah ba haka bane, ta qulla a ranta duk aje a dawo Khalil baze taba rayuwa babu ita ba kuma tana zaune ze dawo gareta a lokacin zata jashi aqasa ta rama duk wani wulaqanci data fuskanta a dalilinsa shi yasa sam hankalinta beyi wani qololuwar tashi ba dukda idanta tuna yana tare da wata macen ba ita ba se taji kamar ta hadiye zuciya ta mutu amma tasan na dan lokaci ne matsawar da zatayi daga kusa dashi kuma ze qara bata damar tsara ta yanda zata magance komai a lokaci daya.

KHALIL

A bangaren Khalil kuwa Sakamakon gwajin da akayi masa ya fito kuma ya tabbatar da ya samu Nakasa a al'aurarsa a gurin sa abun be zo masa a bazata ba domin ya rigada ya sakawa ransa faruwar hakan tashin hankalin da kadai ya fuskanta shine rashin iya controlling fitsari da yakeyi, daman tun bayan da aka kaishi suka saka masa robar Fitsari shika dai ne fargabarsa ace ze dawwama yana amfani dashi bayaga haka duk wani qalubale da ze bibiyeshi me sauqi ne yana kuma roqon Allah daya bashi ikon Jurewa kuma cikin ikon Allah randa ya cika sati daya suka cire masa robar kuma be fuskanci wata matsala ba, abunda kadai ya rage masa ciwon mara da yake fama dashi lokaci zuwa lokaci wanda likitan yace yaci gaba da shan magani da yardar Allah ze rabu dashi maganar samun daidaituwar lafiyarsa ce wannan ya fawwalawa Allah domin shine meyin yanda yaso, kai tsaye baze ce masa ya samu tawaya ta har Abada ba domin babu yanda Allah baya iya juya lamarinsa amma mawuyacin abune koda ace ya warke lafiyarsa bazata dawo gaba daya ba haka suka sallameshi ya koma gida sedai ya ringa zuwa check up lokaci lokaci.

Ya koma gida ya cigaba da Jinya cike da zullumi da tausayin Humaira da ko kadan bata gajiya da kulawa dashi tun ya na gadon Asibiti har zuwa sanda aka sallamo shi haka yan uwanta sun nuna masa karamci, su suke qara qarfafa mata guiwa tareda sake nuna mata dumbin ladan dake tattare da aikin jinyarsa da takeyi. Idan ya kalleta tausayinta da soyyarta suna qara nunkuwa a zuciyarsa amma ya qudurwa ransa baze taba bari son zuciyarsa ya sa ya cutar da ita ba, ze yi mata adalci ya kuma yiwa kansa Adalci shekarunta sunyi qanqantar da ze tauyeta ta zauna dashi da lalurar sa baze yarda ya zama me son zuciya ba ze sallameta taje ta auri wani tayi rayuwarta shi kuma ya rungumi qaddarar sa a yanda tazo masa. Dangane da Umaimah kuwa da abinda tayi masa ya fawwalawa Allah komai ya kuma dauki abinda ya same shi a matsayin qaddararsa yana kuma roqa mata sassauci a gurin Allah sannan yana mata fatan Alkhairi akan duk rayuwar da zata fuskanta a gaba. Baze qullace ta ba kuma yayi mata uzuri saboda yasan duk abinda ta aikata Soyayyarsa ce sila, haka ya fawwalawa Allah komai be sare ba dan haka ya shiga neman Asibitoci a qasashen qetare da suke da kwararru akan matsalarsa zeje ya gani saboda shi magani baka san inda zaka dace.

UMAIMAH

Umaimah ta sake koma gidansu amma wannan karon a Matsayin Bazawara, dakinsu na yammatanci ta gyara ta shiga kimanin watanni uku da rabuwarsu da Khalil kenan amma gani takeyi kamar ba gaskiya bane, dauka takeyi ireiren sabanin da suka saba samune ta taho gida bayan wani lokaci ze huce ya dawo ya maida ta dakinta Musamman irin yanayin da take ciki na cewar babu abinda ta nema ta rasa se kulawarsa data yan uwanta. Tunda ta dawo gidan bata qara samun wayarsa ba kai ba shikadai ba hatta Hajiya idan ta gwada kiranta wayar bata shiga harta gaji ta dena bayan dawowarta gida dai Khalilfa yaje sau daya ya kai musu saqo dukda be shiga gidan ba a waje ya tsaya ya bawa yara tulin uban siyya duk wani kayan amfani daga kan naci zuwa na tsafta seda ya siya ya aika mata dashi kamar yanda yayi alqawari sannan ya dora mata da dubu Ashirin a kan kayan.

Sanda yara suka shiga dashi Mama na zaune a tsakar gidan ta tambayesu daga ina suka ce mata wani Khalifa ne yace a kawo. Bata sake ce musu komai ba suka gama ajiyewa suka fita dan da Umaimah da duk wani abu daya shafeta ta dade da jingine su a gefe. Tsakaninta da ita ido idan sun hadu kenan tayi mata iyaka da shigar mata daki kuma bisa dukkan alamu abun be dameta ba dan bata nuna ba sabgoginta kawai takeyi wuni guda tana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login