Showing 156001 words to 159000 words out of 429394 words

Chapter 53 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1007

anyi shiru wacece?"
"Yi haquri baiwar Allah, na tura miki da saqo ne ta WhatsApp naga baki bude ba shi yasa na kiraki, amma kije ki bude idan kinga abinda yake ciki seki kirani muyi magana" matar ta bata amsa daga dayan bagaren kafin ta samu damar magana ta kashe wayar.

Shiru tayi tana nazari, sam muryarta batayi mata kama data wanda ta sani ba amma haka nan zuciyarta ta kwadaitu dason ganin saqon menene da har zata kirata suyi magana bayan ta gani. Zeta koma kan Kujera ta zauna dakyau ta shiga WhatsApp din babu bata lokaci ta bude chat din nata hotunan sun rigada sun bude saboda wayar a auto download daman take.

Wata irin zabura tayi ta miqe tsaye kai bazakace ciki ne a jikinta daya tasanma wata bakwai ba hannunta har rawa yakeyi tana bin hotunan gaba daya ma ta gagara gane abinda take gani kamar idanunta suna mata gizo haka tabi su daidai tana kallo har zuwa kan Video da shine na qarshe ta kunna take numfashinta ya tsaya na wani lokaci kunnenta yayi mata duuummmm, a dukka sauran hotunan bata gama yarda ba amma a video ta tabbatar da Khalil ne dan bayan fuskarsa ga muryarsa nan yana gayawa wata cewar ze aureta.

Bata san wayar ta subuce a hannunta ba seda taji Ummu-salma tana cewa
"Yah Umaimah zaki fasa wayarki fa kuma babu screen guard akai"

Bata kulata ba tabi wayar ta dauka ta riqe kawai dan ta rasa ta ina zata fara a lokacin, Khalil zata kira ko kuwa seta fara binciko wace wadda ta gaji da zaman duniyarce ta shigo duniyar Mijinta.

Kira ne ya shigo ta daga da sauri kafin tayi magana aka ce
"Nasan zuwa yanzu kinga saqon dana tura miki ko? Zan tura miki da Address, number waya da duk wani abu da zaki buqata gurin binciko wadda take qoqarin shigowa gidanki. Amma karkiyi gaggawar nunawa Mijinki kinsan abinda yake shiryawa ki bari harse bayan kin gama tattara duk wasu hujjoji da kike da buqata dan kinsan maza yana iya qaryatawa sedai kiji ya shammaceki, na barki lafiya" ta kashe wayar.

Kamar wata sokuwa haka Umaimah ta tsaya ta kasa aiwatar da komai seda taji qarar shigowar Message kafin ta bude. Kamar yanda tace kuwa Number wayar ce da Address da duk wani bayani da zata nemi sani akan Hadizan harda Address din gurin aikita.

Hijabin da tayi sallah dashi ta figa ta saka, bata damu da lokaci ba dan a lokaci qarfe biyar ta gota tayi waje, seda taje qofar gida suka ci karo da Salman daya shigo yana kallonta yace
"Aa ina zakije haka da Hijabi a baibai?" Seta kalli jikinta sannan nema ta tuna da babu ko sisi a hannunta da zatayi kudin mota, kallonsa tayi tace

"Key din Motar Abba yana hannunka?"
"Eh gashi nan yace naje na shawo masa mai gobe ze dawo ai" Salman ya bata amsa yana daga muqullin seta juya zuwa inda motar take tana cewa
"Yawwa muje dan Allah ka kaini in mun dawo zan baka kudi ka qara wani Man"

"Ina, wai Asibiti?" Ya tambayeta yana bin bayanta dan abinda zuciyarsa ta ayyana masa kenan bata da lafiya idan ba haka ba me ze sakata fitowa haka a rikice kamar wadda aka koro amma ina mutanen gidan kuma?
Tsawar data buga masa ta saka shi bude motar ya suka shiga yana kallo ta, seda ya fita daga layinsu suka dauki hanya kafin tace masa
"Na'ibawa zaka kaini"

"Na'ibawa kuma Yah Umaimah, ba Jambulo Asibitin da kike zuwa yake ba?"

"Zaka kaini ko kuma na sauka na hau Adaidaita" ta katsa masa wata tsawar seya juya kan motar ya tafi inda tace a ransa yana tunanin ina zataje.
Address din ta bashi ya ringa dubawa inda basu gane ba suyi tambaya tiryan tiryan se gasu a qofar gidan su Hadiza.

"Ka jirani a nan ina zuwa" ta fada kafin ta balle murfin motar ta fita Salman ya rakata da ido harta qarasa inda wasu Samari suke zaune, tambayarsu tayi suka nuna mata gidan bata jira komai ba ta fada babu sallama Maman Hadiza na zaune tsakar gida tana Alwalar sallar Magribar da ake dab da kira se ganin mace tayi a kanta fuska babu alamar Rahama.
*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 41

"A'uzubillahi" Maman Hadiza ta fada a firgice dan sam bataji shigowarta ba se dagowa tayi taga mace da uban Hijabi a tsaye akanta

"Kece shaidaniyar daya kamata a nemi tsari dake" Umaimah ta fada tana jifanta da wani mugun kallo kafin taci gaba da cewa
"Koda yake ba gurinki nazo ba, ina ita karuwar yar taki me bin Mazan mutane ita nake nema?"

"Baiwar Allah wacece ke, ya zaki shigo mun gida babu neman izini kizo kina zagina?" Maman Hadiza ta fada tana miqewa tsaye, Umaimah ta yatsina fuska tace
"Ita sallama anayinta a inda ya kamata ne ba irin gidan nan ba, kinga tsohuwa na gaya miki ba gurinki nazo ba, ki kama kanki ki kiramun wadda nazo gurinta idan ba haka ba na zazzage duk wani buhun rashin mutunchi dana zo dashi akanki".

"Amma dai duk daga inda kika fito ke ba yar arziqi bace ba, haka dai gaki nan harda ciki za'a saka miki ran cewar matar aure ce ke ta kirki amma shine zakizo har muhallina ki tarar dani ki zage ni akan me?" Maman Hadiza ta fada, se Umaimah ta gyara tsayuwarta tace

"Kece tsohuwar banza da kika haifi karuwa da take yawo kwararo kwararo tana kwartanci da bin mazan mutane, to wallahi a wannan karon ta janyo abinda yafi qarfinta tunda ta bi Khalil, sena wulaqantata yanda ko sunan Namiji idan taji seta gudu daga gurin balle ta sake kallon Mijin wata".

Shiru Maman Hadiza tayi idanunta suka ciko da kwallar, cikin raunin murya tace
"Ba laifinki bane, Hadiza taja mun da bata fita tana zubar mana da mutunchi da qima ba da baki samu damar zuwa har gida ki ci mun mutunchi ba. Zan roqe ki kiyi haquri ki tafi, nayi miki alqawari babu Hadiza babu Mijinki daga yau..."

"Lallai ma, ai wallahi idan kinga na dara qafata daga nan gurin toh mun kece raini nida ita ta banbance Aya da tsakuwa, har zaki yi mun wata fuskar tausayi bayan nasan bakinku daya waya sani ko dake da itan duk sana'ar ku daya kema yawon bin...."

Jinta ne ya dauke na wani lokaci kafin ta ankare da abinda ya faru se jin ruwa tayi yana bin hancinta ta saka hannu ta sha fo se ganin jini tayi lokaci daya kuma radadin Marin bazatan da aka falla mata ya ziyarceta ta fasa ihu tayi baya Allah ya taimaka bango ya tareta, Hannu Isma'il ya sake dagawa ze zabga mata wani Marin Maman ta riqe shi tana cewa

"A kul Isma'il karka qara tabata, waya aikeka ka daki mace da ciki idan wani abu ya same ta fa?"

"Wallahi Mama ba'a haifi wani Da a duniya daya isa ya ratso har cikin gidan mu ya zagi Mahaifiyata ba ko labari naji ba akan ido na ba sena sauke masa haqora ballantana wannan tazo har gabanki tana kiranko da" seya kasa qarasawa idanunsa sun kada sunyi jajir jikinsa har rawa yakeyi saboda tsabar baqin cikin da yakeji. Tundaga qofar gida yake jiyo tashin muryar Umaiman yana shigowa kunnuwansa suka jiyo masa tana kiran Yar uwarsa da Mahaifiyarsa karuwa.

"Ki tafi nayi miki Alqawarin Hadiza zata rabu da Mijinki" Maman ta sake fada tana matsawa inda Umaimah ke zunduma ihu tana riqe da hancinta da jini yake zuba.

"Wallahi bazan yarda ba, na rantse da Allah seka san ka dakeni se an bimun haqqina a kurkuku zaka qare rayuwarka shegu jinin masifa jinin bala'i yayan Karuwa" Umaimah ta fada cikin Kuka se ya sake zabura zeyi kanta Maman ta shiga tsakani tana cewa
"Na haneka Isma'il duk abinda tayi mana Hadiza taja, da bata fita tayi abinda takeyi ba babu wanda ya isa ya zo ya zage mu amma shikenan ita ta ja mana" Maman ta qarasa tana fashewa da kuka

"Wallahi idan bata fita daga gidan ba sena Halakata sedai duk abinda za'ayi mun ayi" Isma'il din ya sake zabura Maman ta tare shi tana kuka ta juya kan Umaimah data gama tsorata tace
"Ki tafi baiwar Allah ki fita dan Allah kodan cikin jikinki karki sake jaza manata wata Masifar" bata ma qarasa ba Umaimah ta kwashi qafafunta daman tun sanda ya mareta ta cire takalma haka ta fita daga gidan kamar wadda aka harbo Salman na hangota ya taso daga majalisar daya zauna cikin tashin hankali ya shiga tambayarta meya faru. Bata amsa shi ba ta shige mota, seda suka fita daga layin ta sake fashewa da wani kuka cikin ihu tace

"Wallahi tallahi bazan yarda ba, qanwarsa tabi mun Miji sannan yazo ya dake ni na rantse da Allah se nayi qararsa se an bi mun haqqina" Kuka takeyi kamar zata qarar da Hawayenta shidai Salman yama rasa abinyi. Fuskarta ta kumbura suntum ga jini faca faca akai, so yake ya tambayeta gida zasu ko Asibiti amma yana tsoron karta huce a kansa dan haka ya kama hanyar gida kawai.

Motar su Umaimah na fita daga layin Adaidaita ya dire Hadiza, tun daga soro ta fara jiyo Kukan Mahaifiyarta ga Muryar Yaya Isma'il yana maimaita "kiyi haquri Mama kar kiyi mata baki"
Gabanta ya yanke ya fadi, yau kuma wane sabon tashin hankalin Khausar ta hada mata? Take ta tuna da abinda ta gaya mata dazu da safe

"Kin dauka na qyaleki ne ko to ba haka bane na barku ne se kun sakan kance kafin na sake kunno muku da wani sabon tashin hankalin. Keda kwanciyar hankali a rayuwarki Hadiza se ranar da na samu cikar burina da kika dade kina wargaza mun, na dade ina dakon wannan lokacin, kuma yanzu na samu wadda zata aiwatar mun da komai ta daidaita rayuwarki hankali kwance".

Gabanta ya yanke ya fadi ta shiga karanto duk addu'ar data zo bakinta, kasa shiga gidan tayi ta tsaya a Soron, tsoron abinda zata tarar ya cika mata zuciya amma idan bata shiga ba ina zataje? Zata qara wa kanta wani laifi da zargi a zuciyar Maman ne dan ko a yanzun tunda ta taho cikin taraddadi take dan ta zarta lokacin tasowarta daga aiki saboda wani case da sukaje kashewa a wani gida.

Shahada kawai tayi ta shiga gidan da Sallama, Mama da Isma'il suka dago a tare suka kalleta ba tareda sun amsa mata ba. Jiki a sanyaye ta qarasa gabansu ta durqusa kan guiwoyinta bakinta na rawa ta bude da niyyar magana Isma'il ya daka mata wata tsawa yana cewa
"Wacece waccen kika janyo tazo taci mutunchin mahaifiyar, Matar waye a cikin Yan iskan da kike bi" ya qarasa a tsawace se tayi saurin ja da baya tana girgiza kanta ya taso daga gaban Maman ya biyota yana cewa

"Ba magana nake miki ba Matar waye waccen"
"Wallahi ban santa ba Yaya, shigowata kenan banga kowa a qofar gida ba" ta fada a gigice ganin yana nufota fuskarsa babu rahama
"Matar Khalil, haka naji ta ambaci sunansa" Mama ta fada daga inda take se Hadiza tayi sak a fili ta maimaita
"Khalil kuma, me matarsa zatazo yi a godan nan?"

"Ubanki tazoyi, wato da nace ki rabu dashi ba auranki zeyi ba ashe baki barshi ba kuna ci gaba da yawon shashancinku ko? To a kanki zan huce zagin da tazo tayiwa Mahaifiyarmu har cikin gida" Isma'il ya fada kafin ta yi yunqurin tashi ya kai mata qafa ta koma ta zauna tareda fashewa da kuka

"Ka barta Isma'il duniya ce idan bataji maganar mu ba zataji tata" Mama ta fada cikin kuka itama seya juya ya fice daga gidan yana huci kamar sabon zaki, da ace zoo sake ganin yarinyar nan seya mata dukan mutuwa sedai duk uban da ze faru ya faru. Hadiza kuwa yana fita ta rarrafa gaban Mama tana cewa

"Wallahi Allah shine shaidata Mama ban taba aikata duk abinda kike zargina dashi ba Khausar bata ni takeyi a gurinki ko yanzu ita ta turo wannan matar saboda kafin yanzu ma taso ta hada mana wata qullin Allah yafi qarfinta shine ta sake qulla wani, amma wallahi Mama bana tareda Khalil, na rabu dashi tun sanda kuka umarce ni wallahi sharrin Khausar ne ita take hada komai"

"Ki tashi ki bani guri Hadiza tun kafin kisa zuciya ta debeni na furta miki abinda bazaki so ba" Maman ta fada seta miqe tsam ta wuce daki tana ci gaba da kukan da yake nuna quncin da zuciyarta take ciki. Me tayiwa Khausar a rayuwa da take saka mata da haka?
A iya saninta tsakaninsu babu komai se Alkhairi, qawarta ce tare duk sukayi fadi tashin rayuwa tundaga secondary har Jami'a zuwa yanzu da suke aiki guri daya a duk tunaninta bata hango wani abu data tabayiwa Khausar da har zata nemi ramuwarsa yanzu ba.

Wayarta ta ciro a jaka ta shiga neman layin Khalil amma kamar koda yaushe bata shiga, dabarar yi masa magana a WhatsApp tazo mata se tayi saurin kunna Data, da lambarta da take WhatsApp kan abinda ya shafi aiki tayi masa magana cikin Sa'a yana Online.
"Matarka tazo gidan mu yau, me ya kawota?" Ta tura masa ta zauna zaman jira shiru shiru har kusan minti Ashirin be duba ba dukda har sannan yana Online din se kawai ta ajiye wayar jiki a sanyaya ta fita tayo Alwala. Ta dade tana kaiwa Allah kukanta akan ya wanketa a gurin Mama ya kuma tonawa duk me nufinta da sharri Asiri.

Umaimah.
Hijabin kanta taja ta rufe fuskarta ta shiga gidan, Mama da Anty harda sauran yaran na tsaye cirko cirko a tsakar gida tana shiga Mama tace
"Ahaf me na gaya miki yawonta ta tafi gashi nan ta dawo duk kun tada hankulanku a banza" ita dai bata saurara na ta shige daki, kai tsaye bandaki ta shiga ta cire Hijabin jikinta ta tsaya gaban mudubi tana qarewa fuskarta data canza kamanni tashi daya kallo. Kuka ta sake fashewa dashi idonta kansa radadi yakeyi mata musamman bangaren da ya mareta bangaren ya kumbura suntum idon yayi ciki.

Seda tasha kukan ta sannan ta kunna ruwa ta fara wanke fuskar, ganin bazata fishsheta ba ya sakata fita ta window ta kwalawa Salma kira tace ta dora mata ruwan wanka ta koma kan Gado ta zauna tana ci gaba da share Hawaye zuciyarta ta ayyana matakai sunfi dubu da zata dauka akan Hadiza da Ahalinta amma duk wanda ta hasaso se taga ai yayi kadan akan abinda suka mata. Ta bibiyar mata Miji kuma taje jin ba'asi wanta ya daketa wallahi basu isa ba.

Ummu-salma ta kawo mata Ruwan ta tsaya tana kallonta ta falla mata harara tareda daka mata tsawa ta fita daga dakin da sauri
"Munafuka" ta fada tana sakin tsaki kafin ta tashi dakyar ta shige bandakin tayi wanka. Sosai ta gasa jikinta da fuskarta da ruwan ta kuma samu sauqin kumburin amma fa ba duka ba ta fito ta saka doguwar Riga ta tada sallar Magriba da Isha.

Ummu-Salma na fita jiki na rawa ta tafi dakin Mama, a can ta tarar da Salman da shima shigowarsa kenan dan ya koma ya shawo Man da dazu be samu zuwa ba ganin Maman suna magana yasa ta juya seta dakatar da ita tace
"Salma ya akayi?"
"Am bari naje Mama ku gama se na dawo" ta fada tana juyawa saboda hararar da Salman din yake aika mata. Yasan sarai munafunci ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login