Showing 348001 words to 351000 words out of 429394 words

Chapter 117 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

980

yace

"Kinyi mun hallaci da yawa Humaira ina fatan ubangiji ya ara mun damar da zan maida miki, Nagode da kika yarda zaki zauna dani a yanayin da ba kowacce Mace ce zata iya haquri dashi ba sannanna miki Alqawari zanje ko inane a fadin duniya na nemi lafiyata, idan har Allah ya lamunce mun na warke zan miki biyan bashinda ke da kanki zaki goge sunan Mugubta da kika laqaba mata ki canza mata da sunan Abin dadi" ya qarasa maganar a kunnenta yana dora hannunta a jikinsa.

Ta zabura ta fasa ihu kamar wadda ya saka wa wuta Khalil ya riqeta da kyau yana dariya yace
"Ki rufa mun Asiri karki jirkita mun Baby na" seta shiga kai masa duka yana karewa harta gaji ta fada jikinsa tana kukan shagwaba, Bayyanar cikin yasa ya fahimci nata laulayin itama irin na Umaimah ne me qara mata buqata zeyi iyakar qoqarinsa gurin ganin be gaza ba, godiyar da yayiwa Allahdaya sa bata rigada ta san dadin abin ba ballantana rashinsa ya dameta iyakar abubuwan da yake mata ya tabbatar zasu wadatar da ita.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 76

Tun daga wannan rana ya daura aniyar riritata tamkar kwai kamar yanda take riritashi take jiyar dashi dadin da besan akwaishi a duniyar aure ba. A yanzu ne ya sake gasgata Nutsuwa ita ce Aure abinda yake dauka a matsayin jin dadin auran a baya ake wulaqanta shi akansa gashi yanzu baya ko jin sha'awar sa koda ace Mace zata tube a gabansa baya jin komai game da ita amma irin dadi da nutsuwar da yakeji har cikin ransa ba zata Misaltu ba, idan ze fita har ya shiga Mota tana binsa da dadadan Addu'oin fatan nasara, wuni guda ta ringa binsa da Text messages din da harya dawo yana murmushi da dokin son ya dawo ya tarar da ita sannan idan yazo gida ya tarar da ita tayi kwalliyar da take kusan zauta tunaninsa ga girki me tsinka harshe tsabar dadi ga Shagwaba idan ta fara masa manta kansa yakeyi gaba daya yakance me yasa ba'a haifeki tuntuni kin girma munyi aure ba idan ya fadi haka sedai tayi dariya kawai tuni ta mantar dashi Umaimah da duk abinda ya shafeta. Idan ba yaga wani abu nata a cikin gidan ba ko yaran sun ambaci Momynsu baya tunata a haka ya shirya musu Tafiya India bayan Mansur ya hadashi da wani likita daya kware a bangaren Matsalarsa.

Watansu daya a can duk kuma wani bincike da ya kamata sunyi masa suka canza masa magani akan wanda yake sha a Nan kamar dai yanda Likitocin nan din suka gaya masa suma haka suka maimaita masa, ba zasu ce masa ya nakasa gaba daya ba haka ba zasu bashi tabbacin samun lafiya ba ko kuma ga lokacin da hakan ze samu kawai yaci gaba da Shan magani yana addu'a haka suka koma gida bayan sun biya Dubai sunyi sati daya a can da yar babynsa da cikinsu dake cikin watanni na biyar a sannan. Haka rayuwa taci gaba da gurgurawa, bayan zuwansu India ya sake zuwa Egypt ganin Likita duk kuma dai Amsa daya yake samu a gurin su, qarfafawar guiwar da yake samu a gurin Humairan yasa ya haqura kamar yanda suka ce ya zubawa saurautar Allah ido yana fatanya kawo masa sauqi a sanda yafiye masa Alkhairi a cikin haka har cikin Humairan ya isa haihuwa ta haifi Danta daya dakko farinta kamar balarabe amma kamarshi daya da Khalil kamar sauran yan uwansa. Fadar irin murnar da Familyn biyu sukayi bata bakine da yawa kuma abin yazo musu a bazata dan ba kowa ne yasan tana da cikin ba se Haihuwa sukaji daga sama da yawa fadi sukeyi rabo ne da ace Umaimah ta matsanta da yawa qila da se ta mutu kuma ayi auran Allah ya taqaita mata ya tsaya a mutuwar aurenta.

Se bayan da akayi suna yaro yaci sunan Mahaifin Humairan Auwal suna kiransa da Aryaan, Gida ta koma tayi sahihin wanka Maman ta kula da ita sosai kuma taji dadi yanda a zaman Kwana Arba'in din dukta yanda zatayi ta bigi cikinta taji ko tanada wata matsala akan zaman da takeyi ta nuna babu, dukda tana so ace Humairan tayi Yaya da yawa saboda ita kadai iyayenta suka haifa amma ko iya haka ta qarasa rayuwarta da Khalil ta bar baya ba lallai se ta qara wata haihuwar ba zasu ci gaba da lallaba rayuwarsu a haka. Seda suka kwana hamsin kafin ta koma dan har Taraba seda sukaje yawon Arba'in, kiran da Khalil ya ringayi da zaryar da yakewa Maman tasa ta tattara masa matasa suka koma dan be qara sanin tasirinta a rayuwarsa ba seda ta tafi wankan gidan, jin sa ya ringayi kamar wani Maraya Hajiya kanta seda ta ringa tsokanarsa idan taga ya zauna ya rafka tagumi tace ya tashi ya tafi gidan Hajiya Hauwa mana sedai yayi dariya ya sunkuyar da kai dan shi kadai yasan me yake ji akan rashin matarsa kusa dashi.

Kwanci tashi akace asarar me rai se gashi Shekara ta cika, watanni goma sha biyu da Khalil ya nemi Alfarmar Umaimah ta shayar masa da Malika da suke kira da Iman sun cika. Zullumi ya shiga akan karbo yarinyar, tausayinta yake ji sosai saboda za'a rabata da mahaifiyarta tun bata san kanta ba amma hakan ya zama dole, yasan kafiya da Nacin Umaimah, tunda ta fada da kanta ba zata riqeta ba gara ya karbi yarsa cikin girma da Arziqi ya hadata da sauran yan uwanta shi kansa yana kewarta dan rabon da ya sakata a idonsa tun tana kwanaki a duniya. Ba'a taba kawota ba kamar yanda suma basu taba kai musu su Mu'ayyad ba tun bayan rabuwarsu kowanne bangate sun kama kansu sun zauna inda Allah ya ajiye su. A gurin Khalifa yake ganin hotunanta duk sanda yaje kaiwa Umaimah kayan abinci qarshen wata ze dauki yarinyar yayi mata hotuna ya nunawa Hajiya a nan shima yake samu ya ganta ta girka tayi wayo sosai kamanninta da Mahaifiyarta sun sake fita sedai kamar yanda kowa yake fada baya fatan Allah yasa ta kwaso zuciya irin ta Umaimah wadda sam babu salama a cikinta.

Yana kwance kan Gadonsa yayi nisa cikin tunani Humaira ta shiga dakin, qamshinta ne ya fara sanar masa da ita ce, ya bude ido ya kalleta tayi kyau harta gaji cikin doguwar rigar Atamfar data saka ga daurin nan ta kawo gaban goshi Umaimah ta fado masa, Humaira da Umaimah suna kamanceceniya ta wasu halayen kamar bangaren kwalliya da tarairaya idan fa yan mutunchinta suna kusa kenan sabanin Humaira da a kullum haka take cikin kyautata masa dayin duk abinda tasan ze faranta masa rai badan tana buqatar wani abu daga gurinsa ba. Ta qarasa ta zauna gefen Gadon tana murmushi tace
"Wai kana kwance har yanzu? Ka tashi kayi wanka ga abinci nan yana jiranka"

Mirginawa yayi kusada ita ya jata ta fada jikinsa yana kallon idon ta yace
"Kinyi kyau".
Yanda tayi farr da ido kamar Umaimah a duk sanda yayi complimenting nata seya miqe yana cewa
"Bari nayi wankan ki kawo mun abincin nan qyuyar fita nake ji"
"An gama ranka ya dade" ta fada tana miqewa ya rakata da ido yana murmushi seda ta kulle qofar sannan ya wuce ya shiga wanka yana yi yana tunanin karbo Malika, Hajiya bazata iya da hidimar yaran ba saboda shekaru da yanayin lafiya da tayi mata qaranci daman Habiba ce qarfin Kula dasu to yanzu ana maganar saura watanni biyu Bikinta data bar gidan kulawar yaransa zata koma kacokan hannun me aiki kenan dan baze iya bawa Jalilah ita ba kamar yanda take haqon in an dakko yarinyar ita zata karbeta, indai zeyi haka to gara ya barta a hannun Mahaifiyarta shi kuwa yana so ya hada kan Yaransa su tashi tare a gabansa.

Duk wannan abun uwarsu taja musu da tayi haquri da yanzu suna tare bashi da tunanin ya zeyi dasu, shawarar daya yanke ita ce ze kira Nuratu tunda ita ta kawo musu Ruqayya ta dawo taci gaba da Aikinta ya yaba da Qoqarinta yasan kuma bazata cutar masa da yara ba saboda ko a lokacin baya duk sanda suke a nan bangaren ita take musu duk wata hidima sun saba da ita.
Tsaf ya shirya, yana fesa turare Humaira ta shigo da qaton Try yayi saurin ajiyewa ya kama mata yana cewa
"Bakya tsoronsu zube kika hado kaya haka?"

"Ba gashi na kawo ba ai ba zasu zube ba" ta fada tana sauke kwanukan qasa ya koma yaci gaba da taje Sajensa ita kuma ta bude Warmer ta shiga zuba masa hadadden Dambun cous cous din da tayi. Ta mudubi ya kalli abimcin yawunsa ya tsinke ga wani qamshi na musamman daya karade dakin take yunwar da yake ji ta qara qarfi ya ajiye Comb dinya dawo kan Carpet din inda ta zuba abincinya tankwashe qafa yana cewa
"Gaskiya a bani a baki bazan iya ci da kaina ba"
"Da ze yuwu ma base ka tauna da bakinka ba kawai sedai kaji cikin ka ya qoshi amma babu komai Allah ya kaimu Aljanna" ta fada tana kai masa abincin baki. Haka ta ringa feeding nasa kamar wani qaramin yaro yana ci yana sakin murmushin da shikansa be san na menene ba kawai dai yasan dadi har ya masa yawa. Seda ya qoshi sannan ta barshi ta kwashe komai ta fita dasu kafin ta sake dawowa ta tarar dashi yana saka hula ta qarasa gyara masa zamanta tana cewa
"Kayi kyau da yawa Allah sa kar wata mace ta kalleka sau biyu idan ka fita" seya ja dogon hancinta yace
"Babu wadda zata kallar miki ni, muje ki rakani nasan Anwar na can yana jirana".
Haka suka fita ta rakashi har gaban motarsa tana masa Addu'a, se bayanya fita ya tuna da yanaso yayi mata maganar dauko Malikan dukda ta sani amma ya kamata ya sake tuna mata kar ta ganshi da yarinya kawai. Da dare suna kwance yake mata maganar nan tace tare zasuje, daman su Mu'ayyad nata cewa suna so suje gurin Momynsu, bata son masa maganar ne saboda taga duk sanda suka tambayeshi da kansu se ya nuna bacin rai dan haka yayi haquri ya tafi tareda su su ganta
"Yaya baze yuwu kace zaka rabasu da Mahaifiyarsu ba Alhalin tana raye, koni dana rasa tawa hat abada wani lokacin nakanji dama ta dawo badan na rasa komai ba sedai kawai dan ita uwa batada madadi" Humairan ta fada a hankali seya sake janta jikinsa sosai ya rungumeta ba tareda yace mata komai ba.

Ranar kuwa da tayi daidai da cikar Iman shekara daya bayanya dawo daga Masallaci yace mata su shirya ita da yara zasuje dakko Iman, irin Ihu da murnar da yaran suka ringayi ya sanyaya masa jiki matuqa saboda kiran yau zasuga Momy kawai suke suna tsalle. Tsaf Humairan ta shirya su cikin kyakykyawar shiga Mu'ayyad ya saka shadda irin ta Mahaifinsa ita kuma Bibi ta saka mata Gown kalar Lace din da ta saka a jikinta se suka fito kamar wasu furen fulawa da baza'a iya dauke kai daga kallonsu ba. Seda sukayiwa Hajiya sallama kafin suka kama hanya, kamar yanda ya saba duk lokacin da zeje gidan su Umaiman a wani super Market ya tsaya yayi musu siyayya sosai kafin suka dauki hanya yaran nata surutu suna gayawa Humaira wadanda zata tarar a gidan idan sunje a haka suka qarasa gidan su Umaimah.

UMAIMAH

Tana kwance a dakinta tana sana'ar ta ta danna waya dan bata aikin fari balle na baqi illa taci tayi wanka ta kwanta tana latsa waya. Tana nan kwance Anty ta shigo tana tambayarta rigunan sanyin Iman da Naziyya ta aiko mata dasu ta nunaww Antyn inda ta ajiyesu ta wuce ta dauka Umaiman ta bita da kallo dan tun jiya taga Anty nata kai komon har hada kayayyakin Iman, ko a jikinta bata nemi jin ba'asin dalilin hada kayan ba dan kusan wata biyu kenan data yaye yarinyar gaba daya ta sallamawa Antyn koda yake daman tsakaninta da ita shan Nono ne wanda shima se taga dama tsakanin Anty da sauran yaran gidan take gararanba har zuwa kan Mama da daga baya ta sauke fushin daya shafi harda Iman din ta rungumi yarinyar ganin cewar Uwarta tayi nisa a lamarin Duniya, duk abinda Anty zatayi mata kuwa karace ita din ce a haqqu datayi mata dan haka taja ta a jikinta sosai ya zamana sun raba hidimarta ita da Anty.

Tunda satin ya kama daman Hajiyar Khalil da sukanyo waya jefi jefi da Maman ta kira akan ranar Juma'a ne cikar Malikan shekara daya kuma kamar yanda suka Alqawarta zasu karbeta su hada da sauran yan uwanta a lokacin taji kamar ta cewa Hajiyar suyi haquri su bar musu yarinyar domin tana jinta a ranta ta maye mata gurin Uwarta data rigada ta sallama sedai nauyi da kunyar Hajiyar ya hanata furta hakan suka rabu akan zata sanarda Mahaifinsu Umaimah a ranar kuwa bayan Abban ya dawo ta gaya masa ta ce
"Amma da zaka roqar mana Alfarmu su Alhaji su bar mana yarinyar nan kaga mun saba da ita"

"Karma ki saka wannan a ranki Malika zasu karbi yarsu su hadata da sauran yan uwanta abu daya dai zan kira Hajiyar da kaina na roqi sassaucin janye mana ragowar yaran da sukayi, badan uwarsu ba kodan kasancewar su din jininmu ne su barsu su ringa zuwa muna ganinsu koda ace ba da kwana ba dan Kwanaki da akayi hutu Nuratu ta sanar mun ta kira Khalil din akan tana so ta dauki yaran suje gurinta yace Aa to sassaucin kadai da zan iya nema kenan ita kuma daman lokaci nake jira na zuba mata ido ne naga ko zata hankaltu tayi nadamar abinda ta aikata ta kuma dauki abinda ya sameta a matsayin darasi amma naga sam babu alamar hakan a tattare da ita, zan dauki mataki me tsauri akanta" Abbaya fada se Maman tayi shiru dan harga Allah ta shaqu da Iman din kuma zata so a bar yarinyar amma ya ta iya haka ta sanarwa da Anty nan suka shiga tattara mata duk wani abu da yake nata a gidan, kafin ranar Juma'ar sun hada mata komai tsaf yaran gidan duk sun shiga Alhinin tafiyar Iman din banda Uwarta da bata san dawar garin ba hidimarta kawai takeyi ba kuma ta damu da tambayar hada kayan da akeyi na menene ba.

Misalin qarfe hudu na yamma suka karbi baquncin Khalil da Humaira tareda yaransu. Cikin yanayin jin nauyi, kunya da kuma murnar ganinsu Anty da Maman suka tarbesu a falon Maman dan ko kusa basu kawo cewar da kansa ze zo karbar Iman din ba. Mama ta ringa satar kallon Khalil da yayi wata canzawa da Mamaki. Yayi kyau ya qara cika da girma Alamun nutsuwa da Jin dadi sun bayyana tare dashi kana kallon sa kasan bashida wata damuwa tsayin shekara daya kenan rabon da ta saka shi a idonta tun yana Asibiti dan gara Abba yakan je lokaci lokacin har gidan ya duba shi amma ita ta gaza yin hakan ta kance kunyar Hajiya Aisha ba zata barta iya sake hada ido da ita ba.

Anty ta kasa zama har seda ta cika musu gaba da duk nau'in kayan ciye ciye da suke dasu a gidan danma basu san da zuwansu ba. Cikin girma da mutuntawar daya saba yi musu ya gaida Mama da Antyn, Humaira dake zaune a qasa itama ta gaida su Babu yanda basuyi da ita ba akan ta hau kan kujera ta zauna taqi, Mama dai se kallon Dan Baby dake hannunta take yi gashi nan tamkar Balarabe saboda haske tamkar Uwarsa da itama ta canza ta zama babbar Mace. Anty ta miqa hannu ta karbi Aryaan tana cewa
"Kawo megidan na gani anya kuwa bazan saki na qarfen ba daman ba awo ba cefane wannan kuwa ko babu komai na kalli farar fata naji dadi".
Mu'ayyad ya tura bakin shagwaba dan shi take cewa na qarfen yana kuma jin dadin sunan se ya zura hannu a Aljihu ya ciro dari biyun da Khalil ya bashi kudin Juma'a ya miqawa Antyn yana cewa
"To gashi kiyi cefanen".

Dariya suka saka gaba daya ganin abinda yayin, Anty ta ci gaba da juya yaron tana yaba girma da wayonsa kamar ba dan wata uku ba Mama dai da Khalil surukuta sukeyi ita dai se murmushi take tana kallon rabon daya rabo Umaimah daga gidan Khalil a hannun Antyn shi kuma nauyinta ne ya hanashi sakewa se yanzu yake jin yayi kuskuren zuwa da kansa, daya sani Khalifa ya turo irin yanayin daya ganta ya tabbatar da har yanzu tana cikin radadin zafin abinda ya faru. Dakyar ya iya tambayar Abba suka sanar masa be dawo daga Kasuwa ba amma duk inda yake yana hanya dan ranar Juma'ar da wuri yake dawowa.

Sun zauna kusan Minti sha biyar Anty nata jan Humaira da hira ita dai se murmushi takeyi Khalil kuwa wayarsa yake dannawa Mama kuma tayi shiru tana ta tunani yaran dama sun fice gurin su Momynsu ganin bata dakinta yasa sukayi waje nan suka ci karo da Yasir Autan Anty da yana shigowa ya gansu ya buga tsallen murna ya kwashe su sukayi waje gurin Abokanan sa.
"Amma dai a nan zaku bar mana su suyi week end ko? Munata zuba ido anyi hutu kusan sau nawa ba'a kawo su ba" Anty ta sake katse musu zaman shirun da sukayi se yayi yaqe yace
"Za'a kawo su in sha Allah yanzun dai basu taho da kaya ba"
"Toh ai shikenan Allah ya kaimu toh, Amarya zo muje can kafin a dawo da yar taki wai kitso Sharifa ta tafi kaita tun dazu kinji su shiru" Anty ta sake fada tana miqewa dan su bawa Mama da Khalil din guri tasan ba zasu rasa abinda zasu tattauna ba Humaira tabi bayanta suka fita. A tsakar gida suka ci karo da Umaimah Anty ta kalleta ganin da Hijab a jikinta tace
"Ke kuma se ina"?
"Kati zan karbo gurin Ilu" ta bata amsa tana kallon Humaira

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login