Showing 87001 words to 90000 words out of 429394 words

Chapter 30 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

988

a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 25

Kallonta kawai Khalil yakeyi ya kasa cewa komai saboda tsabar mamakin rashin mutunchi da tsaurin idonta dakyar ya iya bude baki yace mata
"Umaimah, uwa da uban Lubna kika zaga kin san matsayinsu a gurina?"

Zumbura baki tayi gaba tareda matsawa gefen kujerar da take kai ya zamana sun qara samun tazara a tsakaninsu kafin tace

"Oho nidan koma suwaye uban yarinya zanci idan ta sake shiga sabgata gara ma ka gaya mata wallahi"

"Lallai zaki iya zagin Hajiya koda yake ma kin zageta dan da ita da Kawu Najib da Anty Dubu abu daya ne a gurina, toh bari kiji kinyi na farko kinyi na qarshe duk ranar da da wasa kika sake kuskuren gayawa wani nawa maganar banza ma ballantana ta kai ga zagi se na baki mamaki Umaimah dan nasan darajar iyayena bakuma ayi macen da zata wulaqantasu ko ta zage a gabana ba" Khalil ya fada cikin matuqar bacin rai yana miqewa tsaye, dakinsa ya nufa se kuma ya fasa shiga ya juya da niyyar fita yana jin qunquninta tana cewa

"Oho dai kuma na daki banza, ai baka burgeni ba da baka rama mata dukan ko zagin ba"

"Ni nasan mutunchi da qimar iyaye bazan zagi naki ba, duka kuma kibi a sannu duk ranar da kika tiqeni zaki gane ba tsoronki nakeyi ba da ya saka nake raga miki" ya sake fada yana aika mata da wani irin kallo daya saka qirjinta bugawa.
Fita yayi saga gidan ya samu kan wani dakali daga can gefe ya zauna yayi shiru, shi kuma tasa qaddarar akan aure, wayar sa datayi qara ce ta katse masa tunani ya cirota daga Aljihunsa ya daga ganin Hajiya ce take kira.

Tiryan tiryan ta fada masa abinda su Habiba suka gaya mata ya faru a gidan,
"Ni daman nasan qarya takeyi Umaimah bazata aikata abinda tace tayi mata ba tareda dalili ba kuma ni tayi mun daidai data zaneta tunda bata da kunya idan ba haka ba taje har cikin gidan ta tace zata mata rashin kunya ai idan bata dubi darajar matarka ce ba ta dubi na tazarar shekarun da ta bata, Allah ya rufa asiri ka bawa Umaiman haquri dukda nima zan kirata" Hajiya ta fada se Khalil ya saki murmushin takaici a ransa yace
"Almura, duk mugun halin ta babu me yarda se wanda ya gani da idonsa" a fili kuwa yace

"Koma menene abinda Lubna tayi be kamata ace Umaimah ta daketa ba, me yasa bazata kirani ni ta gaya mun na dauki mataki ba kawai seta kama yarinya da duka" ya fada cikin bacin rai se Hajiya ta tare shi da cewa

"Akul Khalil karka kuskura ka zama cikin irin mazan da suke goyon bayan qannensu sama da matansu koda kuwa sune da gaskiya, yanda kake da damar hukunta na qasa da kai idan sunyi laifi haka matarka matsayin ku daya kaida ita a gurinsu kar kuma ka kuskura ka basu qofar da zasu rainata dan kai kanka bazaka ji dadi ba, saura kuma naji wani abu daban" daga haka ta kashe wayar tana jin haushin son kan da Khalil din yake neman nunawa, a zatonta da yaji kan labarin zece ze qarawa Lubnan wani dukan ne se taji akasin haka, maza dai Allah ya shirya su da son kai.

Khalil kuwa cikeda qarin takaici ya maida wayarsa Aljihu yanzu idanya gayawa Hajiya zagin da tayiwa yan uwanta cewa zatayi qarya ne saboda makauniyar soyayyar da takeyiwa Umaimah shidai yana fatan Allah karya kawo ranar da notin kan Umaimah ze goce a gaban Hajiya ko inda zata samu labari dan besanyanda zata kaya ba. A gurin yaci gaba da zama har aka kira sallar magriba kafin ya wuce masallacin cikin layin nasu yayi sallah, har ya zauna dan baya son kowama gidan ta qara bata masa rai se kuma ya tuna da ya taho da wani aiki da zeyi dan haka ya miqe ya tafi gidan.

Tana zaune tayi daidai akan daddumar da tayi sallah ga faranti a gabanta ta yankakken mangwaro da gani me qanqarane, kallo daya yayi mata bayan da yayi sallama ciki ciki ya dauke kai, ya ja mata kunne akan shan sanyi amma taqi ji, be kukata ba ya wuce cikin dakinsa ya kunna Laptop ganin chajinta yayi qasa ya saka shi neman chaja amma be ganta ba, daga cikin dakin ya kwalawa Umaimah kira, tana jinsa sarai amma tayi banza har seda ya gaji ya fita ya tsaya a qofar dakin yana kallonta, yasan taji shi sarai wulaqanci ne ya hanata amsawa amma bashi da lokacinta a yanzu.

A dake ya ce mata
"Ina kika saka mun Chager Laptop dina?"
Wani kallo ta watsa masa me kama da harara kafin ta tura baki gaba tace

"Ni ka bani ajiya ne ka duba a inda ka saba ajiyewa mana". Seda ya hadiye abinda ya tsaya masa a maqoshi kafin ya sake ce mata

"Idan tana gurin da nake ajiyewar ai da banzo na tambayeki ba, ki taso malama ki dakko mun ina da abunyi"
Yanda yayi maganar babu wasa ya sakata miqewa dole ta wuce shi tana qunquni, magana takeyi sarai kuma ya jita tace

"Haka kawai ayi mun laifi dan na dauki mataki kuma ya zama abin fushi toh ko kububuwa mutum ya zama ba abinda ya shafeni wallahi yarinya ta sake zuwa tayi mun hauka naci ubanta na kuma daketa na daki banza babu abinda za'a iya" ta shige ta dakko Chager data saka a cikin drawer sabanin saman drawer daya saba ajiyewa. Akan gado ta dora masa ta fice tana juya jiki Khalil ya bita da kallo ya saki murmushin zallar takaici kafin ya jona chager ya shiga aikin da zeyi

Qunquninta ne ya ringa dawo masa haka kawai yaji ransa yana qara baci wato babu abinda ya isa yayi mata koh wai wane irin raini Umaimah take dashi haka ace mace har mace amma babu ladabi harshenta babu linzami? Yaga alamar dauke kai da yakeyi yana kyaleta a maimakon tayi hankali iskancinnata qara gaba yakeyi, dole ya dauki mataki tunda shi ta rainashi ai akwai na gaba da ita da take shakka.

Wayarsa ya janyo ya shiga kiran Yaya Aminu dan yasan shine maganinta ba kuma yaso kai tsaye ace ya kai qararta gida ko ya kira daya daga cikin yayyenta mata gara Aminun ze iya musu maganin matsalar ba tareda Mama ko Abba sunji ba.
A mutunce suka gaisa ya tambayeshi yana gida ne zasu shiga yace Eh har yana masa tsiyar tunda sukaje musu bangajiya ai basu sake leqawa ba har ita Umaiman daman dai ba gwanarzuwa gidansa bace dan ba wani shiri sukeyi da Mamy matarsa ba.

Bayan ya kashe wayar yaci gaba da aikin da yakeyi har aka kira Isha kafin ya fita masallaci, tana zaune tana aikin danna waya ya wuceta, seda ya kai qofa ya juyo yace mata
"Ki shirya idan na dawo zamu fita"

"Ai kuwa babu inda zani zakazo kana wani ciccin magani saboda na daki budurwarka, ai dana sani ma na balla qafar shegiya se inga ta tsiya, mtsw" taja tsaki duk a cikin kunnen Khalil daya dakata dan yasan se tayi magana ita kuwa daman ba tsoron yajin takeyi ba shiyasa ko qunqunin zatayi a fili take abinta duk abinda ze faru ya faru ai kuwa har yaje sallah ya dawo tana zaune inda ya barta dan ko sallar ita bata tashi tayi ba.
Wuceta yayi ya shiga daki ya chanza kaya ya dakko muqullin mota ya fito, a maimakon zaunen da take da ta kwanta ne akan carpet tana waya ya fito ya tsaya akanta amma bata nuna ko kusa tasan da tsayuwarsa bama.

Ya kao bango da rashin mutunchinta dan haka ya fizge wayar yayi jifa da ita take ta rotse a gurin Umaimah ta tashi zaune tana cewa
"Lalala, ka fasa mun waya? koda yake ina ruwana ma kudinka ai ba nawa ba" ta juya zata sake kwanciya ya saka hannu ya fizgota a mugun tsorace ta miqe hatta da dan cikinta seda ya hantsila ta shiga raba ido tana kallonsa yace

"Wuce ki dakko Hijabinki" ya saketa tayi taga taga zata fadi ta samu ta dafe kujera, yanda taga fuskarsa ta tsorata dole ta kama hanya ta shige daki sum sum ta dakko Hijabin a ranta tan tunanin toh ina zasuje koda yake tasan baze wuce gidan Hajiyarsa ba.

Qarar rufe Get da taji ya tabbatar mata da har ya fita seta zura takalmanta taja qofar palour ta fita itama. Yanda yake fizgar motar ya tabbatar mata da zuciyarsa a wuya take seta kama kanta, ganin sun hau kan State road ta sake tabbatar da gidan Hajiya zasuje, ai kuwa a shirye take da ta sake gurzar bakin yarinya a gaban Hajiyar idan tayi mata sharri ehe sedai ayi wacce za'ayi, ganin ya dauke hanya yayi Hotoro ya sakata shan jinin jikinta, a saninta bashida wani dan uwa a hotoron da zasuje gidansa a daren, Jalila ce kuma basa Kano suna Warri inda mijinta yake aiki se anyi hutu suke zuwa kanon.

Bata qarasa shiga tasku ba seda taga yayi parking a qofar gidan Yaya Aminu. Cikin ta ya bada qululu ta waiwaya ta kalleshi daidai sanda ya kashe motar yana qoqarin fita irin yanda ya hade rai bata da ma qwarin guiwar yi masa magana amma Khalil ya isa mugu, yanzu daga wannan dan qaramin abun shine ze kawo qarar ta gurin Yaya Aminu?

Lissafin yanda zatayi take har ya shige gidan ya barta a mota dan tuni Ummi babbar Yar Yayan ta bude masa qofa, seta balle murfin ta fita cikin mutuwar jiki, abinda yake dan kwantar mata da hankali tasan a yanzu dai bazata doku a gurin Yaya Aminun ba, ai koshi Khalil din baze bari ba ko badan aure ba ai a qyaleta dan abinda ke cikinta haka ta shiga gidan kamar munafuka tayi sallama Ummin tazo ta rungumeta tana mata oyoyo Anty Mami ta fito daga palourta tana cewa

"Wata sabon gani yau Umaimah a gidanmu lallai za'ayi ruwa da qanqara". Yaqi tayi ta shiga gaisheta ta tareta tana cewa
"Haba kamar za'a gudu, mu shiga ciki mana ma gaisa a nutse" tayi gaba Umaimah da Ummi suka bita a baya a ran Umaimah ko zaginta take tana cewa

"Algunguma me makon da kikaji ya kawo qarar tawa ki kirani ki gaya mun karna bishi ko ina yau shine yanzu zaki wani ringa yaqe mun baki toh Allah ya isa".

A palour Yaya Aminu ta tarar da shida Khalil suna hira kamar bashi ne suka taho yanzu fuska a daure kamar yaci kashi ba, gefw ta samu ta rabe ta gaida Yayan nata ya amsa yana karantarta Anty Mami na janta amma taqi sakewa se satar kallon Khalil takeyi tana marairaice masa fuska fatanta ya fahimci roqon da takeyi masa na karya fadawa Yayan komai dan tasan da ace ya rigada ya gaya masa bazata samu fara'ar da yayi mata yanzu ba amma sam Khalil yaqi bari ma su hada ido seya duba agogon hannunsa ya kalli Yaya Aminu yace

"Gurinka muka zo Yaya"
"Toh Allah yasa lafiya, koda yake daga yanda naga idon wannna shaqiyyar tana sunne kai nasan da abin tsiyar data shuka" se Mamy ta miqe tana cewa

"Haba dai ai ta girma yanzu ko Umaimah, bari na baku guri toh taso muje can" ta fada tana kallon Umaimah data miqe kamar me jira se Yayan ya dakatar da ita yace
"Jeki zatazo idan tayi free" Mamy ta saka dariya ta fice.

A taqaice Khalil ya zayyanowa Yaya Aminu kokensa akan Umaiman, abu biyune zuwa uku qorafinsa yanda sam babu ladabi a tsakaninsu ba kuma ta tauna magana duk dacinta haka zata yaba masa ita se kuma rigimar da sukayi da Lubna yau a gidan dukda be gaya masa zagin da tayiwa Kawun nasa da Goggonsa ba ya dai qare da cewa

"Kullum abun qara gaba yakeyi shiyasa naga gara ka shiga ciki qila kai idan kayi mata magana taji, yanzu dan Allah Ya dace ace daga zuwan baquwa gidanta koma me tayi mata ta kamata da duka ita kwata kwata bata da aji bata san abinda ya kamata ba a ko ina tace zatayi dambe da mutane haba dan Allah"

Caraf Umaimah da ta kasa kunne duk tana jin qararrakin nata daya kawo ta karbe zancen tace
"Ai idan gaskiya ce seka gaya masa matsayin wacce na daka din a gurinka, budurwarsa cefa Yaya tazo har cikin gidana zatamun rashin kunya saboda bata da tarbiyya harda cewa fa zata dakeni shine ni kuma na saita mata zama yanda gobe ko layin gidan saurayinta ba...." Bata qarasa ba saboda marin da Yaya Aminun ya dauketa dashi da ya saka kunnenta toshewa na wani lokaci bata dawo saiti ba ya qara mata wani ta kuwa dage ta fasa ihu tareda zabura tayi kan Khalil be haqura ya sake duma mata dundu a baya ta gantsare ta sake fasa wani ihun tana
"Wayyo cikina bayana"

A rikice Khalil ya riqota yana cewa
"Innalillahi Yaya abin be kai da duka ba ka manta ba ita kadai bace" ya rungumota jikinsa ta fizge Yaya Aminu ya daka mata tsawa yace

"Zauna a nan ki kuma rufe mun baki kafin na dakko bulala na hada miki jikinki a nan mutuniyar banza kawai, ke har kike kiran wata da mara tarbiyya ga rashin tarbiyya nan qarara kina nunawa? Ai gara ki tabbatar masa da babu wanda ya isa dake idan ma ya kawo qararki ne dan a miki fada toh kinfi qarfin kowa".

Kuka Umaimah take mara qara tana sosa bayanta Khalil na tayata kamar shima ze fasa kukan, cike da takaici Yaya Aminu yaci gaba da cewa

"Ni daman nasan shirun da akaji Allah kadai yasan iskancin da kike shukawa ilai kuwa gashi da shukar ta isa girbi an gani toh karki fasa duk abinda kikeyi kinji ina daidai da duk wani iskanci da lalatar ki, kai kuma" ya juya kan Khalil yaci gaba da cewa

"Kaine babban me laifi da har ka bari wannan abar da batafi ka hadiyeta ba take gaya maka maganar banza baka saba mata kamanni ba, daga yau ko kallon banza ta sakeyi maka dakata ni na sakaka saboda ita tun asali idan har ba an taba lafiyarta ba ba'a daidaitawa da ita. Bata jin Nasiha ko fada se taji a jikinta sannan take nutsuwa".

Kamar Khalik zeyi kuka ya sake rungumo Umaimah jikinsa yace
"Amma Yaya Umaimah yanzu ai ta wuce duka a gurin ku ma ballantana ni a matsayin mijinta na daketa, nasihar dai ita ya kamata ayi mata musamman yanzu a yanayin da take ciki tana buqatar kulawa ne ba damuqa ba".

Harara Yaya Aminu ya maka masa yace
"An dame tan dan ubanta da kasan bakaso ayi mata fada meya kawoku? Ai dole ma ta rainaka ka zauna kamar sakarai kana wani rarrashinta bayan ita ce tayi maka laifi toh tunda wuri ka tashi kasan abinda kakeyi idan ba haka ba wannan seta maida kai abinda bakayi tsammani na, dan zuma ce ita da wuta ake cinta, a haka dai gaka nan kamar namijin gaske amma ka zauna wannan abar tana gigitaka, zaki miqe ne ko kuwa sena qara miki wani dundun makira zaki narke saboda kiyimun sharri" Yaya Aminun ya sake fada yana zaburo mata se gata kuwa ta zaune dungurgur akan kujera dan da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????se malele kuwa take a jikin Khalil din tana riqe baya.

Fada sosai Yaya Aminun ya hada daga ita har Khalil din yayi musu dan daga baya ma laifin kansa ya koma yace shi ya bata fuskar da take masa kowanne iskanci dan gashi yanzu ma a gabansa ya gani to kuwa tunda ya bari tasan lagonsa haka zata ringa wana shi gaba gaba kuma tafi qarfinsa bazata lankwasu ba zasu zama sedai shi ya bita ba ita ta bishi ba. Yayi musu tatas kafin ya dora da nasiha basu bar gidan ba se Goma saura Umaimah ko kallon qofar Mamy batayi ba ta fice daga gidan dan Khalil da Yaya Aminun sun tsaya yana sake jaddada masa ya tashi tsaye akanta idanba haka ba kar yayi kuka da kowa ya kuka da kansa a gaba.

Suna shiga mota ta barke da kukan da bata samu damar yi a gidan ba, kuka me hade da ihu ta ringa kurma masa duk yanda yaso ya daure kamar yanda Yaya Aminun ya jaddada masa kasawa yayi ya faka motar ya shiga lallashinta nan ta botsarewa kuwa ta baje kolin sabon rashin mutunchi tana cewa ai yana sane ya kaita aka ci zalinta, ya ringa bata baki yana lallashinta amma a banza qara watse wa takeyi seda ya gaji ya dauki wayarsa yana cewa

"Bari na kirashi na gaya masa tunda daman yace duk abinda kikayi na gaya masa ze zo har gida ya mun maganinki" ya shiga dannan kiran Yaya Aminu ta wafce wayar tana cewa

"Saboda bakai ya daka ba ai wallahi se Allah ya sakamun da kai dashi duka ba yafewa zanyi ba".

Abinda yafi qarfinka aka ce seka mayar dashi wasa haka ce ta kasance da Khalil tunda dai ya fuskanci bakin ne babu linzami unguwar zoma bata gasa mata shi ba gara ya lallabata su rabu lafiya, haka suka qarasa gida ranar dai baccinsa ragagge ne saboda kuka da tashin hankalin data ringayi na zallar Jidali dan yayi zaton zatayi kukan ciwon baya amma kamar ma ta manta da an daketa a gurin, fuskarta ce dai ta tashi taji hannun Maza a haka suka lallaba suka kai safiya, da wurwuri ya bar mata gidan saboda sabuwar tijarar data dira da safiyar Allah ta'ala shikam dai tasa Jarabawar akan mace akai masa.

Umaimah kuwa Khalil na fita ta shiga ta fesa wanka ta hada shayinta me kauri tasha. Duk Dramar tana sane tayi abarta ta kuma yi alqawarin seta tayar masa da hankali gwargwadon zafin mari da dundun daya kaita aka mata. Tana gamawa ta kwanta ramuwar baccin da bata samu tayi cikin dare ba, wunin ranar haka tayi shi har Yamma tana nade a gado sedai idan an kira sallah ta sauka tayi ta kuma komawa ranar se bayan magriba Khalil ya dawo saboda baqi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login