Showing 399001 words to 402000 words out of 429394 words

Chapter 134 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1006

ya dena shiru cutar da kansa da ya ringayi lokacin Umaimah yanzu ya gane kuskurensa kuma baze maimaita ba duk wadda ta masa abu seya fada idan yaso ran kowa ya baci. A fusace abinda tayi masa yana sake tunzurashi yace
"Hajiya baki san meta mun ba, turata gidan kawai shine maslaha idan na huce zan dawo da ita"

"Toh yanzu nace kaje ka dawo da itan sedai kuma in ban isa ba seka gaya mun, meta maka? Duk abinda zata maka dai nasan baze kai na wacce ta tsaya a gabanka ta zageni ba toh tunda muka yafe mata banga laifin da za'a mana ya gagara yafuwa ba dan haka ka tashi kaje ka dawo da matarka banda tsabar rashin tunani Yarinyar data rufa maka Asiri ta zauna dakai a halin lalura yanzu daka samu lafiya shine zaka fara gwada mata halinku na Maza ko kuda baku san abin arziqi ba daman"

"Toh saboda ina da lalura shine zata ringa kula wasu Mazan a waje?" Maganar ta subuto daga bakinsa ba tareda ya shirya ba take kuwa Hajiya tayi tsit saga bambamin da takeyi qirjinta ya shiga dokawa ta kalli Khalil da shima yayi tsilli tsilli saboda subul da bakan da yayi, a sanyaye tace
"Babana me kace? Wane mqza take kulawa a waje?"

"Am ni ba haka nace ba, kawai dai ki bar maganar dan Allah Hajiya ta kwana gobe da safe ta dawo shikenan" ya fada yana qoqarin miqewa seta daka masa tsawa tana cewa
"Bana son rashin arziqi, ka dakko magana irin wannan sannan ka tashi kana neman bagarar da ita kasan me kake cewa kuwa? Maza fa naji kayi zancen tana kulawa a waje, koma ka Zauna Khalil ka gaya mun gaskiya ka samu lafiya da gaske kuwa? kuma wane irin zama kukeyi? tun yaushe hakan take faruwa?"

Zaman yayi gaba daya ya rasa me zece mata ganin ta rikice ya tabbata fassarar datayi wa maganar daban da abinda Yakima nufi dole ya tattaro nutsuwarsa jin tana cewa
"Cikin jikinta kuma fa a ina aka sameshi" se yayi saurin cewa
"Haba Hajiya abin be kai nan ba, bafa irin kula Mazan da kike tunani bane nine ban daka miki maganar a yanda zaki fahimta ba daman wannan yaron saurayinta ne yake aiki a Asibitin Al'amin, tun randa muka fara ganinsa naja mata kashedi akan sa amma bataji ba shine yau.." Tiryan tiryan ya labarta mata komai ya qara da cewa
"Ni daman nasan ba wata rashin lafiya kawai ta shirya zuwa ta ganshi ne, na gaya mata ta zaba koni koshi, idanta zabeshi wlh data haihu zan sawwaqe mata taje suyi aure bazan tauyeta ba dan nasan zaman haquri takeyi dani bawai samun yanda take so takeyi ba" yayi maganar kansa a qasa saboda nauyinta.

Hajiya ta sauke numfashi saboda jin abin beyi girman data zata ba amma dukda haka hankalinta be kwanta ba dan ita fitina tana qarama idan ba'a maganceta ba girma takeyi. A hankali tace
"Bata kyauta ba amma kaima kayi saurin yanke hukunci wannan ai abinda za'azo gida a sasantane ba wai seka turata gidansu ba. Sannan shedan ne kawai yake tunzuraka yana qara rura maka wutar kishi amma babu wani abu, aikinsa yakeyi ita kuma kace likita ta turata yin test kaga baze yuwu ai tace ba ze dauki Jininta ba tunda shine a gurin"

"Amma ai bashi kadai bane a gurin Hajiya, data san tsakaninsu akan me zata bashi jikinta har ya wani riqeta yana shafata yana murmushi? Daman ai ya fada mun se ya zama fitina a rayiwarmu to gara kafin muga fitina taje can ta aureshi su qarata ni na haqura" ya sake fada idonsa nayin Jaa dan abin ya bala'in qona masa rai se Hajiya tayi saurin cewa
"Ashsha ka dena cewa haka Mana Babana shaidan ne kawai ya haska maka haka babu tabbacin ma murmushin yakeyi sannan waccen magana daya fada na tabbata a lokacin cikin fushi ne shima bazamuga fitina ba da yardar Allah amma koma yayane kayi haquri tayi kuskure kuma ba za'a sake ba ka daure dan ni badan halin taba ka daukota ta dawo gida karka ja mana abin fada, kana ji har yar uwarka ta fara jifan tsohuwar matarka da cewar Asiri tayi muku to lallaba ka dawo da matarka kafin kasa can itama a fara jefa mata wani zargin, Mace da tsohon ciki haihuwa kowanne lokaci a turata gida ai abin a tambayi ba'asine, zan gayawa Hauwa na tabbata zatayiwa tufkar hanci ba za'a sake yin hakan ba kaji" Hajiya ta shiga lallabashi dole badan yaso na ya tafi ya daukota, harta kwanta Mama ta tasheta akan Khalil yazo ta zare ido tana shirin yin kuka ita dai data barta ta kwana gobe koma me za'ayi ayi amma ya ta iya haka suka kama hanya har sukaje gida be kulata ba. Sum sum ta shige bangarenta shima yayi nasa, yara duk sunyi bacci dan haka itama ta kwanta washe gari kuwa qarfe tara Mama ta dira a gidan dan Hajiya kasa bacci tayi saboda zullumi seda ta kirata ta gaya mata komai.

Irin labaran da take yawan ji akan Tsohon saurayi da budurwa yasa ta kasa samun nutsuwa, bata zargin Humairan da wani banzan hali amma shaidan abin tsoro ne musamman su da suke da baraka yana iya amfani da wannan damar ya kaisu ga abinda ba za'a so ba ga kuma maganar shi yaron da Khalil yace mata ya taba gaya masa tuna shekarun baya na cewar ya jira ya gani, seya zama fitina a rayuwarsu idan har qullin na nan a ransa har yanzu gara ayiwa tufkar hanci da wuri kafin azo ana kukan da an sani.

Tana shiga kafin takai qasa Mama Hauwa ta dauketa da Marin daya gigitata, Khalil dake bayabta ya tareta dan tafiya tayi zata fadi ta kuwa fashe da kuka dan hannun Mama badai zafi ba kamar na maza haka yake. Ta shiga surfa mata bala'i tana zaginta, duk yanda Hajiya taso ta tausheta taqiyin shiru seda tayi mata tatas tana cewa
"Saboda bakida hankali baki saninda yake miki ciwo ba, ke ko a hanya kika ga Nura ya kamata kibi inda yabi yaron daya sha Alwashin lalata rayuwarki shine kike bibiya wato ki bashi damar aiwatar da shirinsa a sauqaqe kenan to ki jini da kyau idan kika kashe auranki sedai ki san inda zaki nufa badai gidana ba tunda ke baki san abin arziqi ba".

"Haba Hajiya abinfa bekai haka ba, na sanar dake ne kawai saboda ya kamata ace kin sani amma badan ki dau abinda zafi ki ringa maganganu haka ba, naga kinada alaqa da uwar yaron zaki iya mata magana taja masa kunne ya fita a sabgarta shikenan ba se anje ga wannan tone tonen ba" Hajiya ta fada, Khalil dai yana riqe da Humaira dake gunsheqar kuka idonsa ya kada yayi jaa shima kamar yayi kukan daya sani be sanarwa da Hajiya ba, beyi tsammanin zata fadawa Mama maganar ba gashi yanzun abin nema yake ya qara girmama.

"Ki barni da mutuniyar banza Hajiya wannan yarinyar da kike gani kunnen qashi ne da ita ai, banda ma abu irin na yaran zamani ina ke ina kula wani tsohon saurayi da auranki duk ba daga nan fitinu suke bullowa ba wai se suce mutunchi mutunchin yaci uwarsa da ubansa ai tunda soyayya ta gifta Shaidan na iya shiga ya taka rawa son ransa yayi abinda yaga dama dan haka kowa ya zauna a iyakarsa babu wani mutunchi da tsohon masoyi ai da ka sani tun jiyan ka fada mun da bazata dawo ba seta zauna a gidan idan yaso ka saketa ta gani idan Nuran ze aureta in ma abind akije saqawa a ranki kenan to sedai ya lalata miki rayuwar kamar yanda yace ya kashe miki aure kuma shi ba auranki zeyi ba dan daman kafin su bar unguwar ya dade yana fadar maganganu akan seya fito dake kuma na auranki zeyi ba sakarya shine har zaki taka kije inda yake. Daga nan shima gidansu zani na samu Hajiya Asaben" Mama ta fada tana miqewa tsaye ta kalli Khalil tace

"Kar kaji komai Khalil in kaga ba zaka iya ba ka sakota duk inada labarin diban Albarkar da take maka ai ta dawo gidan taga idan zawarcin da take sha'awa wasane, abinda take rainawar se naga a gidan ubanda zata same shi".

Kamar qasa ta tsage su shige shida Hunairan, wannan tonon silili da yawa yake dai Mama ta fice Hajiya ta bita rai babu dadi datasan haka zata dauki abin da bata gaya mata ba. Seda ta rakata ta dawo ta sake hadasu su biyun tayi musu fada da Nasiha kafin suka koma bangarensu, fita yayi niyyar yi amma ya haqura ya zauna ta ringa kuka tana bashi haquri da rantsuwar ba abinda yake tsammani bane.
"Wlh bansan a Lab yake ba, kuma danaje duk Matan sunyi sun kasa dubo jijiyar ne" ta miqa masa hannu ta se sannan yaga kumburin da yayi taci gaba da cewa
"Sun kasa ganin jijiyar se caka mun Allura sukeyi shiyasa ya karba yace zeyi amma wlh dana shiga koda na gaishe shima dauke kai yayi be amsa ba"

"To murmushin da yakeyi yana shafa hannunki fa?" Khalil ya sake tambaya dan abin nan ya tsaya masa a rai seta cigaba da kuka tana cewa
"Wlh badani yake ba kuma ba shafawa yakeyi ba jijiya yake dannanwa hirar su sukeyi suna labarin wani abokin aikinsu aida ka kalle su duka dariya sukeyi ba shi kadai bane" se kuma yaji wani iri dan da gaske take dukkansu dariyar sukeyi amma a lokacin dauka yayi su sukewa Dariyar ganin yanda tayi da fuska shi kuma yana mata murmushi, be nuna mata nadamar zaton daya qulla ba ya miqe yana cewa
"To se ki dena kukan haka kuma Test dinna menene gashi ba'ayi ba?"

"Nima ban sani ba na Fitsari dai ta bani dana jini kamar protein dai naji tace" Humairan ta bashi amsa seya fita yana ce mata
"Bari na kira Dr Al'amin in yaso da yamma se muje idan ya zauna. Asibitin ma canza shi zamuyi bazan iya jurewa kuna haduwa dashi na zuciyata zata iya tarwatsewa" ya fice daga dakin.
Seda ya kira Dr Al'amin din, be gaya masa abinda ya faru ba dan dukda baya qaunar Noor baze so ya zama sanadin rasa aikinsa ba dan Dr Al'amin ya masa bayanin nauyin da yake kansa, da ace babu yar tsama a tsakaninsu ma tsab shi me iya taimaka masa ne. Dr ne ya masa bayanin Dr Huriya wadda Humairan ta gani jiya ta sanar masa da sunzo amma sun tafi basu kai mata Test result ba, yana taso ya kirashi ya shafa'a yace masa

"Da daddare kuzo Khalil ayi gwajin ina ga ma in zaka yarda ayi mata CS kawai a cire babyn yafi sauqi"
"CS kuma Dr, da akwai wata matsala ne?" Khalil ya tambaya hankalinsa na tashi daya tuna cikin Imaan da shima yace sedai ayiwa Umaimah CS" cikin son kwantar masa sa hankali Dr Al'amin yace

"Aa fa babu wani Abu Khalil kawai dai babyn ne nake ganin yanada girma, zata iya haifarsa amma zata dan ji jiki kaga idan akayi mata aikin za'a sauqaqa amma shawara ce idan ka yarda itama ta yarda shikenan". Hankalin sa ya dan kwanta sukayi sallama, da daddaren kuwa ya kaita ya kasa ya tsare a Lab din har akayi test din Noor bama ya nan shi ya tashi tuntuni. Dr ya dan rubuta mata magunguna da zasu rage mata ciwon kan da tace tana yana damunta basu bar Asibitin ba seda aka basu appointment na CS din da tace ta yarda ayi mata dan tunda yace mata Babyn yayi girma zata dan sha wahala ta tsorata, Aryaan ma data haifa 2.8kg taji jiki balle wannan da yake cewa ze iya kaiwa 4kg ina zata iya gara a cire kawai Allah ya raba su lafiya. Sati daya ya basu satin na zagayowa kuwa sukaje ko Hajiya be sanarwa da za'ayi aikin ba se bayan da aka ciro mata Qaton Babynta fari tas dashi shima aka kaita dakin Hutu kafin ya kira Hajiya ya gaya mata. Ta ringa fada kamar zata aro baki Mama dai da taji tace ai auna arziqi tunda anyi aikin lafiya an gama. Haka tayi kwana uku cikin kyakykyawar kulawa kafin aka sallameta ta wuce gidan Mama kamar yanda Hajiya tace. Sau daya suka hadu da Noor yaje karbar Sample a ward din da take kansa a qasa ya kasa ko kallon qofar dakin nasu da yake a bude sosai Mama taje tayi musu Tijara a gida Ummansa har kuka tayi tana roqon ya fita a sabgar Humaira ya barsu su zauna lafiya ya ringa rantse mata akan shi wlh babu wani abu tsakaninsu tun tuni ya cire komai, ko a baya hankali be gama masa jiki bane shiyasa yake wasu tunanuka amma yanzu babu komai game da ita a ransa illah mutunchi tunda dai shiya hadasu ba rashin mutunchi ba.

Yanda yake sunkuyar dakai Maman da kanta ta kirashi ya shiga dakin, ta bashi dan da biyu tana cewa
"Ga danku kaga na farin can" ta nuna masa Aryaan dake cinyar Jamila yana shan Yoghurt tace
"Kana ganinsu kasan namijin gaske ya haifesu" shidai yayi yaqe ya musu Addu'ar Allah ya raya ya kama gabansa, to shi ko qaddara ta fito da Humaira ai yasan ba sa'ar auransa bace dan bashida abinda ze riqeta dashi ta saba da rayuwar jin dadi me zatayi dashi da har yanzu neman madafa yakeyi babu abinda ya ajiye.

Ranar Suna yaro yaci sunan Mukhtar sunan Mahaifin Mansur Amininsa kuma Mijin Mama mariqiyar Humaira kenan. Har kuka Maman tayi da wannan kara daya musu, kullum burin Mansur kenan a haifar masa Namiji ya saka sunan Mahaifinsa yayansa biyar yanzu duk mata Khalil be gaya musu sunan yaron ba har se ranar sunan da Safe dan data dameshi da tambaya cewa yayi kawai ta samar masa Laqabi se ranar suna zataji, aiko Yayan Mama sunji dadin wannan kara a gidan Hajiya kuwa ana fadar sunan Jalilah tayi tsallen Arbarka tace qarya yake, sunan Abban Umaimah ya saka. Hajiya ta riqe baki tana cewa
"Jalilah jidalinki yawa ne dashi, yanzu sunan ma se kin janyo magana akai"
"To idan qarya nakeyi Hajiya ya fada mana, babu wani sunan Baba me Mota daya saka (haka suke kiransa da suna yara) sunan tsohon sirikinsa ya saka ze wani fake da haka"

"Toh Jalilah ko sunan Abba na saka ai babu aibu a ciki dan Abba uba nane kuma ya isa da nayi masa takwara, karki tunzurani idan ta sake haihuwa na sake maimaita Mukhtar" ya fada mata kaitsaye ta tafa hannaye tana cewa
"Eh lallai Allah ya tsamoka Khalil a kwale kwalen Asiri kake yawo babu kuma wani ka sake sakawa daman shi ka saka kuma sena zuga Humairan akan me za'a saka mata sunan uban kishiya, kishiyar ma yar iska mara mutunchi"

"Kiyita rage mata zunubi kina jibgawa kanki" ya fada yana ficewa dan inya zauna se sun haura sauran yan uwan kuwa dariya suke musu kawai dramar tagwayen bata qarewa su basu ganin sun girma sun haura Arba'in inji Jamila amma kullum kamar wasu yan sha takwas, mita ta dira akan me za'a saka sunanda Hajiya ta gaji tace

"Ke dai in baki sararawa kanki ba ciwon damuwa ne ze kasheki kafin lokacinki yayi, ni banga dalilin dorawa kai damuwar wani ba taka ba. Umaimar nan fa baki isa ki kankareta daga cikinmu ba, yaya uku ta haifawa dan uwanki gasu nan duk inda akaje aka dawo fa an hadu babu yanda za'ayi a rabu kuma Alhaji Sabo Dattijo ne kuma in ma shiya saka banga laifinsa ba dan ya masa abinda uba yakewa Dansa haba ki rage wannan zazzafar qiyayyar taki Yayanta suna girmamaki karki bari su fahimci qin da kikewa uwarsu ba zasuji dadi ba kuma kema zasu iya qinki a dalilin haka dan duk yanda uwa take Yayanta suna sonta.
*HALIN KISHI*

*NA MAR?????!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!"YAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 85

Sha tara ta arqizi iyalan gidan Alhaji Sabo suka hada na kayan barka bisa karamchin da suka ce an musu na maida sunan mahaifinsu. Mama da Anty suka shirya Khalifa ya kaisu gidan Hajiya, Mama ta ringa kallon gidan abubuwan da suka faru a ranar data saka qafarta na qarshe na dawo mata shekaru kusan biyar kenan kota layin bata sake biyowa ba se yau din nan tunanin yanda zata sake kallon idon Hajiya takeyi a haka akayi musu iso cikin falon Hajiyar daya sake qawatuwa fiye da da.

Hajiya rasa inda zata sakasu tayi saboda murna, tasa aka ringa kawo musu abubuwan motsa baki yanda take haba haba dasu duk yasa kunya ta sake dabaibayesu jikinsu ya qarara sanyaya da lamarin karamchi irin nata. Tabbas Umaimah tayi asarar Sirikar kirki da samun irinta keda matuqar wahala a wannan zamani. Seda ta gama cika musu gaba da abubuwan ciye ciye kafin ta zauna suka shiga gaisawa. Da suka tado zancen baya ma hade fuska tayi ta nuna musu ita a gurinta komai ya wyce, ashe qullatarsu sukayi shiyasa suka yanke zumunchi dasu Mama da Anty suka hau rantse rantsen ba haka bane yanda suka rude yasa tayi dariya tace

"Komai ya wuce wlh kuma kamar yanda nasha fada miki nayiwa Umaimaha uzuri ba halinta bane kuskure aka samu tareda zugar shaidan data mugayen qawaye amma komai ya wuce sedai muyi fatan hakan ya zama Alkhairi a rayuwarsu gaba daya, Allah kuma ya fito mata da wani Mijin idan kuma da rabon daidaitawa se kiga an koma".

Daga Anty har Maman kasa amsa mata maganar qarshen sukayi dan basu da tabbacin har zuci tayita seta sako musu wata hirar tun suna dararewa har suka saki jiki akayi ta labarin duniya. Duk abinda aka ajiye musu Mama dai Lemo kadai tasha se Dubulan Anty kuwa ta zage taci abinda ya mata dan daman ita bata iya fulako ba. Sun jima kafin Hajiya ta shirya tace suje can gidan su Humairan suga Baby tunda bata dawo ba, a compound suka hadu da Khalil daya dawo daga Abuja saukarsa kenan ya shigo gidan suka hadu ya ringa sunkuyar da kai qasa kamar ze kwanta musu saboda ladabi ya gaida su Maman, ta amsa tana murmushi Anty ce tadan jashi da wasan data saba yi masa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login