Showing 69001 words to 72000 words out of 429394 words

Chapter 24 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

994

data tabbatar da baccin Khalil din yayi nisa.
Palour ta koma ta kwanta ta hau WhatsApp lokacin qarfe goma da yan mintina a sannan kasuwar gidan Qasaitacciyar Mace ta faraci.

Hira tayi dadi ita da ta fito da niyyar tadan duba abinda aka tattauna ta koma se gashi ta shantake se jin muryar Khalil tayi a kanta yana tambayar me takeyi a nan cikin daren nan?


Assalamu Alaikum mutanen Kwarai=?M?
Shin kina son kwarewa fannin girke girken zamani,snacks da sauransu
Hajiya ta=؃? ga dama ta samu Mun bude online class wanda zamu koyar da girkin zamani yanda ake sarrafasu ta hanyoyi da dama& Akan kudi qalilan 200 ga mutane 10& daga bisano ze koma 300 kacal kedai kawai tura kudin ki ta wann acct din& ..
1509536481
Rabiatu Nuhu Aliyu
Access bank
https://chat.whatsapp.com/IL3QnKmFxojAATF6WkzGxK

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 21

"Na kasa bacci, shine na fito nan saboda bana so na tashe ka kaga zakayi Driving da safe" ta fada tana tura wayarta qasan pillow. Se daya karanci yanayinta na wasu seconds kafin ya qarasa kusa da ita yana cewa

"Shine zaki fito cikin dare ki zauna ke kadai kina dariya? Me yasa baki tashe ni ba ko ki zauna a cikin dakin?"

"Bana so na katse maka baccinka kuma kwanciyar ce naji bazan iya ba shiyasa na fito nan kar motsina yayita damunka" ta sake marairaicewa,
"Hmm" Khalil yace dan beyarda sam da maganar ta ba amma ya share ya ruqo hannunta yana cewa

"Tashi muje ki kwanta kuma ko ba yau ba karki sake tashi cikin dare ki fito ki zauna ko dan saboda lafiyarki da abinda yake cikinki".
Seda tayi Addu'a ta kwanta kafin ya kashe musu fitila shima ya kwanta a gefenta, ji yayi baccin da yaje idonsa ya tafi dan daman ruwa ya farka ze sha ya duba be ganta ba abinda yasa ya fita nemanta kenan.

Wannan sabuwar Dabi'ar tata ta chatting din dare ta fara damunsa dan shi a rayuwarsa duk inda qarfe goma take ya sauka Online, ko kafin ya aureta haka suke goma nayi sukeyin sallama kenan idan ya kashe Data ita ci gaba takeyi da chatting dinta har tsakar dare kenan?
"Wai ma dawa take chatting din?" Zuciyarsa ta jefo masa tambayar, baya so ta dasa mata zargin wani abu a ransa amma qaryar da takeyi masa da yanda take boye waya duk sanda ya kamata yasa yaji yana son ganin menene a cikin wayar tata.

Kallon Umaimah da bacci yayi awon gaba da ita daga kwanciyarta tana sauke numfashi hankali kwance yayi, a nutse ya miqe dan ma karta ji qarar qofa daya bude se ya tokareta ya barta a bid ya wuce kan kujerar data bar wayar ya dauka.

Da contacts dinta ya fara daga farko har qarshe numbobin tarkaceb qawayentane babu adadi sena yan uwa dan ze iya irgi number dayaga sunan namiji akai. Bangaren kira ya koma nan ma yawanci kiransa ne sena yan gidansu da kuma Hajiyarsa, haka yayi ta shige da fice yana bincike a wayar har WhatsApp da Facebook dinta seda ya duba babu wani abu na rashin gaskiya a ciki, lokacin qarfe biyu harta gota da yake a kunne tabar Datar yana kallon messages nata shigowa daga wasu groups daya tabbatar da abinda yake sakata raba dare tana chat din kenan, to kuwa tabbas ze taka mata burki be hanata hira da kowa ba da rana amma duk inda ya dawo gida lokacinta nasa ne dole ta ajiye kowa da komai ta fuskance shi idan ba haka ba kuma ya kwace wayar kowa ya huta tunda ita batajin magana.

Kashe mata Datar yayi ya jona a chaji kafin ya koma ya kwanta, da Asuba dukkansu suka makara tashi saboda rashin komawa bacci da wurin da basuyi ba, shiya ja su jam'i, suna idarwa Umaimah ta kwanta a gurin dan wani bacci takeji sosai.

"Ki tashi kin san muna da tafiya a gabanmu" Khalil ya fada murya a daure, seta miqe zaune tana tura baki, be kulata ba ya shige bandaki tana jin alamar zubar ruwa tasan wanka yake seta fice daga dakin tana qunquni
"Se kace ni nace ina so naje ni da zakayi tafiyarka ka barni ma da nafi son haka" ta wuce kitchen ta dora ruwan shayi ta soya kwai tunda akwai bread.

Qarfe takwas suka kama hanyar Kaduna, shi yake tuqi tana zaune a gefensa tasha kwalliya da wata farar Abaya fuskarta se walwali takeyi suna tafe suna yar hira jefi jefi har Khalil ya gaji da yanda idan yayi magana daya seta dauki lokaci kafin ta bashi amsa saboda hankalinta gaba daya yana kan wayar ta se yayi mata shiru ya kunna radio kawai a ransa yana ayyana yanda zero magance wannan danne dannen wayar tata.

Qarfe sha biyu saura suka shiga Kaduna, kai tsaye hotel din daya rigada yayi musu booking daki ya nufa da ita, a gurguje ya karbi mukulli ya rakata dakin ya nuna mata wayar tafi da gidanka da zata kira idan tana da buqatar wani abun a kawo mata kafin ya wuce Site din da zeyi aiki dan tun suna hanya suke kiransa a waya.

Khalil na fita ta zare doguwar rigar jikinta ya rage skin tight da vest da ta saka a qasa ta haye kan gadon daya sha shimfida bayan data ware Ac ta duqufa kan wayarta tana sana'ar Chatting.

Rufaida ce tayi mata magana tana mata qorafin bata shiga barka ba kwana biyu bata online ma bata nemeta ba se Umaimahn ta bata haquri da uzurin bata gari amma da sun dawo zata shigo.

"Ai naga kin zama yar gida a Group har cigiyarki ake idan anjiki shiru" Rufaidan ta turo mata, se Umaimah tayi murmushi kafin ta mayar mata da cewa
"Ai group din naku akwai qaruwa kullum ana kawo topics masu ma'ana da dole kaima se ka bayarda taka gudummawar"

"Wai me yasa ma kika fita daga wancan group din bayan abubuwan qaruwa ake turowa? Kinsan fa zamanin nan dole seka tashi tsaye ka zama karuwa a cikin gidanka idan kina so ki kama mijinki a hannu dab dai kinsan yanda yanzu maza suka baci da yawon biye biye, to duk irin abubuwan da matan wajen suke musu kenan mu na gida kace kunya ka kasa sakewa ka bawa miji farinciki. Wani ma ko baya biye biye zakiga yana kallo a waya se ya zama kome zakiyi masa da yar qaramar wayewarki ba zaki burge shi ba" Rufaidah ta turo mata da voice.

Ta voice din ta bata amsa tace
"Hakane amma ni gani nakeyi wannan abin ai ba se an koyawa mutum ba ko kuma se kaje ka kalli haram zaka koya saboda wannan kallon daidai yake da mutum ya aikata zina bayan zunubi ga illar da kallon tsiraici yakeyiwa ido gaskiya bazan iya zama a group din ba ni, iya ilimin da nake kwasa a group Malamina ya isheni kuma da qaramar wayewar tawa haka yake gigicewa idan na masa abu" ta qarasa tana murguda baki kamar tana gaban rufaidan dan gaba daya haushinta taji ya rufeta kuma ta farayi mata kallon yar iska dan ita ko irin sakin bakin nan da mata sukeyi idan ana hira raina mace takeyi ta kuma ringayi mata kallon yar iska, to idan ba dan iska ba waye ze ringa zancen batsa ko ya kunna a waya ya kalla?

"Allah ya baki haquri ni bada wani abu nake nufi ba" Rufaida ta fada saboda jin martanin Umaiman, se itama tace

"Nima ba wani abu nake nufi ba ai ra'ayina kawai na gaya miki iya wannan ma da nake ciki ya isheni, bari nayi sallah an kira" daga haka ta kashe Datar gaba daya ta tashi jin cikinta na qugi dan yanzu tana yawan jin yunwa qila nata kalar laulayin kenan dan dai har yau ita bata ji wani abu da ze saka ta yarda dagaske tana da ciki ba.

Waya ta kira ta fadi abinda za'a kawo mata kafin ta shiga bandaki, "uhm ko nawa ya kama dakin nan se Allah" ta fada tana qarewa bandakin kallo tayi fitsari ta dauro alwala daidai nan aka buga qofar dakin, seda ta zura dogon hijabi a jikinta kafin ta leqa ta yar hudar dake Jukin qofar taga ma'aikaciyar hotel dince da Tryn abinci dan sosai Khalil yaja mata kunne akan idan an buga ta fara duba waye kafib ta bude qofa, bude mata tayi ta shigo ta gaishe ta kafin ta ajiye abincin ta fita.

Seda ta qulle qofar da muqulli kafin ta tayar da sallah dan har biyu ta gota tana can tana surutu bayan ta idar ta dauko wayar data saka a chaji ta zauna tana cin abinci tana danne dannenta, data gama goge hannunta kawai tayi da tissue ta mayar da qafafunta kan dogowar kujerar da takr kwance ta miqe da kyau yanda zata ji dadin kwanciyar ta ci gaba da gashi.

Kiran Maman Asad ne ya katse mata fafatawar da sukeyi a wani group da Halima qawarta ta sakata ana zancen kishiya.
"Ke gani qofar gidanki muna ta bugu shiru halan baccin nan naki na asara kike yi" Maman Asad din ta fada bayan data amsa kiran, se Umaimah ta harari wayar kamar tana gabanta tace

"Toh ni bana nan ai da se ki kirani kafin kizo ko idan baccin ma nake sena tashi".

"Karki ga kinyi aure kice zaki mun rashin kunya ubanki zanci wallahi, zaki bude ne ko kuwa na kama gabana dan ina da gurin zuwa ni" Maman Asad din ta fada a hasale, se Umaimah ta kwashe da dariyar shaqiyanci tace

"Nifa dagaske bana nan muna Kaduna dazu da safe muka tafi"

"Yanzu zakuyi tafiya bazaki fadawa kowa ba ko dan abubuwan gyara a baki ki dan sabunta shine kika tafi ziqau dake ko bayan ko jiya ance a gida kika wuni? ai shikenan zanga randa zakiyi hankali kedai. Me kuka jeyi kuma wadanne irin kaya kika diba?" Cewar Maman Asad.

"Woh Yah Hajiyayye sarakan gyara yanzu tafiyar ma se anyi mata wani gyara gaba daya watana nawa a gidan mijin ma bare a faramun wani garanbawul? Kawa kuma yace karna dauki komai zamu siya a nan ni nigh gowns da undies kadai na debo kuma fa aiki yazo yi ba wai hutu muka zo ba" Umaimah ta fada

"Ai shikenan ki zauna kar kiyi gyara kinji idan baki fara tun yanzu ba ya zamar miki jiki sanda jikin naki yake da buqatar gyaran bayi zakiyi ba dan baki saba ba a shegen halin son jikinki da qazanta ma ai ke kam dole a ringa miki garambawul din akai akai, saura kije ki zauna masa shabar kamar buhun masara kina sana'ar danna waya dan jiya naga last seen dinki har kusan dayan dare toh ki shiga hankalinki, idan zaki ware ki ringa masa salo da kisisi na kala-kala yaji kamar karku dawo gida, inda ba hutun yake so kuyi ba in iya aikine ai shi kadai zeyi tafiyarsa.

Idan yaji dadin tafiya dake kinga shikenan kin samu lasisi duk inda zashi kina gefensa idan ba haka ba kuwa kina kallo zeyita yawace yawacensa kina gida kina masa gadi" Maman Asad ta sake fada kafin sukayi sallama ta kashe wayar tana sake jaddadawa Umaimah da tayi kwalliya ta daukar magana kafin ya dawo, idan ma bata da kaya ta zauna da Towel shima duk cikin salon gayun ne.

Hamshaqiyar kuwa kofi ta cika da lemo tana sha ta koma WhatsApp suka ci gaba da cece kuce tana kumfar bakin babu macen data isa ta kula mata miji,

"Ai ni mijina dan ni kadai aka yi shi babu kuma macen data isa ta rabeshi a duniya idan ta wuce uwar data haifeshi se yan uwansa da suke ciki daya, duk wata mace bayan wannan tace zata tsallaka hurumin Mijina toh kuwa ta taro yaqin da ze qarar da danginta kaf bama ita kadai ba, shima ya sani ba kuma zeyi gangancin saka yar mutane a masifa ba dan na rantse da Allah zan iya halaka yarinya sedai duk abinda ze faru ya faru shi da kansa ya fada ni kadai na ishe shi" Umaimah ta tura da voice note.

Sabon cece kuce ne ya tashi, masu goyon bayanta suna yi masu nuna mata kuskurenta da cewa ta rage zafin kishi sunayi, wata me suna Rabi'atu dake da rabon karbar nata kason rashin mutunchin tabi Umaimah Pc tace mata

"Haba baiwar Allah kamar ba musulma ba ki ringa iqirarin halaka wata akan kishi ko dauki dakon rai, ba a aure ke ya aureki? Kinga ai bazaki fitar da ran wata rana ze sake gano wata yayi sha'awar auranta ba kawai dai kiyi addu'a idan Mijinki nada rabon qara aure Allah ya hada kanku ya bashi ikon yin Adalci amma irin wannan kalaman ai idan kika zamu wata yar tijarar irin ki tsaf zata iya cewa ita kuma zata nemi mijin naki taga yanda zakiyi".

Zabura Umaimah tayi daga kwancen da take ta miqe tsaye tana qara karanta saqon daga baquwar lamba kafin ta shiga mayar mata martani da cewa

"Nice yar tijara? To uwar data haifi Uban Kakarki itace Tijararriya kuma da zaki ce wata ta nemi Mijina kai tsaye ki fito kice ke zaki auri Mijina,? idan baki fasa neman Mijina kin aure shi ba ke tsinanniyace kuma uwarki shegen ki tayi ta kaiwa ubanki, ni kuma ko sunan Mijina naji kin kama a bakinki ballantana ta kaiki ga neman inda yake sena nuna miki ni Umaimah na haifu kuma ina fada da cikawa idan kuma keep na ganin wasa nakeyi ki gwada".

"Allah ya shiryeki idan kina da rabo kuma in sha Allahu se an miki kishiya ko dan kiga iyakarki" Matarta sake tura mata kafinta danna mata block dan bazata iya da dingimemen tashin hankalin Umaimah ba.

Hohoho ina wuta Umaimah ta jefata? Wasu mulmulallun Ashariya masu maiqo ta shiga antaya mata amma ganin da tayi messages din basa tafiya alamar tayi blocking dinta kenan yasa ta koma group tayi tagging sunanta taci gaba da zaginta tana sake nana ta mata idan ta cika mara kunya ta fada mata inda take ita kuma zata zo ta sameta ita dai baiwar Allah yayi tsit dan taga abin yafi qarfinta yan group nata bawa Umaimah haquri masu fushi da fushin wani da basu san kan zance ba suka shiga tayata tagging matar suna zagi, a cewarsu baze wuce ta bita Pc bane zatayi mata wa'azinta na munafunci data saba ai gara haka yau ta jangwalo wadda tafita baki ita dai mata da taga babu sarki se Allah babu bata lokaci ba tayi left daga group bayan data sake cewa Umaiman

"Ko iya wannan jahilin kishin naki ya isa ya saka ayo miki kishiya kuma kina ji kina gani ze samo kamilar mace me aji ba ballagaza me zage zage a social media ba" tana turawa ta arce daga group.

Kiran layin matar Umaimah ta shigayi tana jin zuciyarta kamar zata fito saboda tsabar baqin ciki, ita zatayiwa wannan cin mutunchin? Ai kuwa duk inda matar nan take seta nemota taga ubanda ya tsaya mata se kuma ta nuna mata ita ba kanwar lasa bace.

Wayar taqi shiga ta gwada da dukka layukanta guda uku bayan wanda take chatting dashi dan daman tasan dole zatayi blocking nata amma duk a banza basu shiga ba, kwafa tayi ta jefar da wayar ta zauna tana jijjiqa qafa a zuciyarta tana ayyana ta inda zata binciko matar nan.
Da ace Yaya Aminu mutumin kirki ne shi zata bawa Lambar ya nemo mata ita tunda shi jami'in tsarone amma tasan seya tsareta da tambayoyin jin ba'asin abinda yasa take nemanta qarshe idan magana ta fashe itace a ruwa dan tasan babu me goyon bayanta dan haka dole tasan ta ina zata zaqulo matar nan dan wallahi bata zagi bulus ba.

Tana kallon Halima na kiranta a waya tayi banza da ita dan tasan baze wuce labari ya isar mata na abinda ya faru a group din ba tunda bata Online ita, tana zaune nan zaman saqa da warwara har bata san lokaci ya tafi ba sejin motsin bude qofa tayi ta zabura ta miqe tsaye tana kallon kanta da gurin da take zaune kwanukan ab???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?incin data ci na nan a bude ko murafen bata iya mayarwa kai ba bare aje ga kawar dasu gefe ga lemon da take sha ma ashe ta ture shi ya zube a garin masifa bata sani ba ya bata farin centre carpet din dake dakin seta juya ta kalli Khalil dake takowa zuwa inda take, ganinsa tayi tas sam beyi kama da wanda ya fito daga Site ba inda ake aikin Yashi da sumunti se ji kawai tayi hawaye na ziraro mata

"Umaimah lafiyarki kuwa" Khalil ya fada yana jijjigata ganin yanda ta zura masa ido tana hawaye tunda ya bude qofar ya shiga har ya isa gabanta bata motsa ba yanayinta kuma ya tabbatar masa da bata cikin hayyacinta.

Ajiyar zuciya me qarfi ta saki kafin ta fada jikinsa ta fashe da kuka kamar wadda aka kwadawa Mari, yanda take kukan har jikinta na rawa ya dagawa Khalil hankali babu shiri ya shiga karanto addu'oi yana tofa mata dan abinda zuciyarsa ta bashi gamo tayi dan haka ya dage yana karanto Addu'oin tsari yana tofa mata Umaimah kuwa banda kuka babu abinda takeyi, idan ta kalli fuskar Khalil ta tuna abinda matar can ta gaya mata seta sake rushewa da kukan.

Ganin da yayi bazatayi shiru ba ya kuma tabbatar in har shaidanu ne dagaske irin addu'ar daya tofa mata zasu lafa sedai idan nata shedancin ne ya motsa dan haka ya jata gefen gado ya zaunar da ita yana cewa

"Ya isa kiyi shiru menene?"
Seda ta kwashi kusan wasu mintuna biyar kafin ta fara tsagaita kukan tana jan shashsheqa da Ajiyar zuciya.

"Babe, kiyi magana meya same ki dan Allah wani abu ya faru a nan ko a gida?" Ya sakw fada cikin sanyin murna dan ya fara tsorata da kukan nata kar fa wani mugun abun ne ya faru da ita ko bayan fitarsa.

Dakyar Umaimah ta iya bawa kanta haquri ta fara magana cikin muryar kuka tace
"Ba wata mata ce ba haka kawai tace wai in sha Allahu se kayi mun kishiya kuma..kuma ta kwace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login