Showing 66001 words to 69000 words out of 429394 words

Chapter 23 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

964

aka dauki jininta suka bata robar da zatayo fitsari a ciki tayi ta mayar musu kafin suka koma can inda ake zama ayi jira.
Suna zama aka kira Sallar Magriba Khalil ya wuce masallacin Asibitin ya barta yana tashi ta zaro wayarta dake cikin Aljihub doguwar rigarta ta shiga WhatsApp.

Da saqon Rufaida ta fara cin karo
"Wannan mata ko mayya ce se haka ta haihun ma bazata zauna ta huta ba seta addabi rayuwata da takura haba" Umaimah ta fada a fili kafin ta bude saqon tambayarta take me yasa ta fita daga group tace mata babu komai groups din ne sun mata yawa. Daga nan take gaya mata qarfe goma na dare zata gabatar da ita a Qasaitacciyar Mace group din dan haka sukeyi, idan sabon Member ya shigo ze gabatar da kansa saboda kowa ya sanshi daga nan ya zama dan gida dan haka ta zauna online kafin lokacin.

Cigaba da duba saqonnin mutane tayi seda ta hango Khalil tayi sauri ta kashe Data ta jefa wayar a Aljihu, yana qarasowa aka miqo musu Test result din kai tsaye suka koma office din likita ya karba ya duba fuskar sa dauke da murmushi ya miqawa Khalil hannu yana cewa
"Ina tayaka murna madam nada shigar ciki".

Daga ita har shi bude baki sukayi suna kallonsa da mamaki, cikin tabbatarwa yace
"Kuna mamaki ne? Gashi nan abinda sakamako ya nuna kenan, yanzu zaku dawo nan da Two weeks zaku dawo ayi scanning musan cikin sati nawane" ya hau rubutu a takadda ya basu yace su karbi maganin a pharmacy kafin ya qara musu da shawarwarin yanda zata kula da kanta da abinda yake cikinta.

Khalil da Umaimah dai se yar kallo kallo ake bakin nan kamar ya tsage dan tsakanin su bazakace ga wanda yafi wani farin ciki ba, 'ikon Allah daga qaryar cuta ashe silar jin abin arziqine' Umaimah ta raya a ranta haka suka dauki hanyar gida bayandaya tsaya yayi musu take awayn abinci da kayan kwalama, duk abinda ya gani a hanya seya tambayeta zata ci abin nasa ma tun yana bata dariya har ta fara jin haushi.

Da suka isa gidan ma hanata fita yayi daga motar, kamar wata yar baby haka ya dauketa ya kaita kan kujera ya ajiye yana cewa
"Kina ji dai likita yace a kula dake dakyau banda aikin wahala, dan haka duk wani aiki me yawa a gidan nan na sauke miki shi, kiyi wanda zaki iya ki bar sauran idan na dawo zan ringayi.

A daren nan taga tarairaya da ririta ta kuma shaida yanda Khalil yake son haihuwa dan harya fara lissafin abubuwan da zasu siya da sunan da za'a sakawa Babyn idan Macece ko Namiji.
"Nidai nafison Namiji" Umaimah ta fada tayi daidai akan cinyarsa yana bata Ayaba a baki bayan da suka gama cin abinci.

"Ni kuwa koma menene indai Mutum ne kika haifa ina so" Khalil ya bata amsa yana jan hancinta kafin ya qara cewa

"Wai, yanzu fa hancin nan nan da kwana kadan ze bude ya zama qato naga haka hancin su Jalila yakeyi idan suna da ciki duk su fita a kamanninsu, bari ma na kirata na gaya mata su shirya samun sabon baby a family" ya qarasa yana janyo wayarsa dake gefensu, hade rai tayi tace

"Kawai kuma seka wani fara kiran mutane kana gaya musu ai ka bari dai muji ma kwanakin cikin kafin a fara yayatawa".

Daga yanda tayi maganar yasan halin tsiyar ne ze motsa dan haka ya bata rai shima yace
"Eh na yayata din yan uwana zan gayawa kema ban hana ki kira naki ki gaya musu ba" ya fada yana danna kiran layin Jalila babu dadewa ta daga tana cewa

"Dan qanina kamar kasan yanzu nake so na kiraka kwana biyu dai Amarya ta kwace mana kai baka neman mu muma bama samun ka"

"Ba haka bane wallahi kin san na koma aiki idan na fita bana samun zama dana dawo kuma kashe wayar nakeyi saboda masu damuna, amma zan ware layi daban dai inaga" ya fada cikin jin kunya dan dagaske ya yada su, kai hatta Hajiyarsa seda tayi qorafin rashin zuwansa gidan kamar farkon auransa da kullum idanbeje da safe ba zeje da yamma yanzu kuwa seya jera kwana biyu uku be leqa su ba sedai ya kirata a waya shima tace Umaimah tafi kiransa akanta dan kullum ta Allah ne seta kirata sun gaisa da safe.

"Toh ai shikenan daman lafiya ce ai take buya, yanzu ya akayi ta samu ne naga kira da tsohon daren nan" Jalilan ta sakw fada,
"Albishir na kira nayi miki kin kusa yin sabon baby, Amarya nada ciki" ya fada yana shafa kai dan wata yar kunya kunya yaji na neman kamashi.

Cikin muryar farin ciki Jalilan tace "Ah kace dan qanina ya girma no wonder ka buya ashe kai kasan aikin da kakeyi irin wannan sharp sharp haka? Ta bari na shiga group yanzu na shelanta musu a saka sabon adashi matar Usaini tayi ciki, ka gayawa Hajiya ko na gaya mata?" ta qarasa cikin dariyar shaqiyanci.

"Kefa baki da kirki wallahi daga gaya miki abin arziqi zaki farayiwa mutum tsiya kuma karki sake cemun Usaini wallahi" Khalil din ya fada yana dariya.

"Aa zancen gaskiya mana toh bari zan gayawa Hajiyar tunda naga kunya kake ji, ina qanwar tawa mu gaisa?"

Kallon Umaimah data tunzura baki gaba yayi dan a speaker ya saka wayar tana jin duk abinda suke fada se yace
"Ta kwanta Kinsan likita yace ta ringa hutawa"

"To shikenan zuwa da safe zan kirata in Allah ya yarda amma fa ba wai kuma ance ta huta ka saka ta tayita kwanciya kamar ruwa bata motsa jikinta ba, Aa ana so a ringa motsawa aikin da ze jigata ta ne dai ba'a so kaima seka rage zalama ka bar yar mutane ta nutsu tunda kayi abinda kake so, Allah ya inganta ya bada lafiya" Jalilan ta fada daga nan sukayi sallama tana sake jaddada masa daya kula da Umaiman.

Umaimah kuwa hankalinta na kan Agogo, qarfe goma na bugawa ta tashi ta dakko wayarta dake jikin chaji ta koma kan kujera ta harde, shima bebi ta kanta ba ya chanza tasha zuwa Channels ya fara kallon labaran qarfe goma.

Tana hawa ta bude group din kuwa ita ake jira dan har an rufe group anyi mata Admin, shugabar gidan me suna Anty Haris kamar yanda ta gani a rubuce ce ta fara gabatar da ita a matsayin sabuwar member daga nan ta bata dama akan ta gabatar da kanta.
"Sunana Umaimah Sabo Mukhtar, ni yar Kano ce, ina da aure. Shekaruna 22" ta tura musu a taqaice.

"Masha Allah Malama Umaimah muna mik barka da zuwa wannan gida, amma baki fadi Unguwar da kike ba saboda idan da wanda kuke kusa kinga se ku qulla zumunchi haka mukeyi a nan" daya daga cikin Admins din ta bata amsa,

"Ina unguwar Tudun-yola Gate 4" ta sake turawa tana yatsina fuska, sun fiya iyayin tsiya Allah sa dai ana abin arziqi a group din.

"Aa kice yar unguwarsu uwar daba ce, Ke Rufy kina ina fito ga yar Area kin samu" Admin Anty Haris ta turo da Emojin rawa kafin ta sake ce da Umaiman
"Saura ki turo da Hotonki ki kuma yi voice note saboda mu tabbatar da Macece yar uwar mu ba masu shigewa cikin mata ba"

"Kan bala'i lallai ma mutanen nan da rainin wayo suke" Umaimah ta fada a fili tana gyara zama, Khalil ya juya ya kalleta beyi magana ba ya maida kai yaci gaba da kallon News dinsa se yaga ta miqe ta shige cikin daki kuma.

Tana shiga kan gado ta haye, hotunanta ta shiga dubawa ta samo wani da sukayi weekend din daya wuce sunje Zazu cin Abinci da yamma Khalil ya dauketa tayi kyau sosai dukda Hijabi ta saka tana turawa ta sake aika Voice note tace
"Inayiwa kowa fatan Alkhairi" daga nan aka bude group aka shiga yi mata barka da zuwa yan group dai masu kirki anata faran faran da ita nan da nan itama ta sake aka fara hira sam bata ankare da lokaci ba seda taji an turo qofar dakin tayi saurin tura wayar qasan pillow tayi lamo kamar me bacci dan daman ta kashe fitila.

"Umaimah" Khalil ya kira sunanta daga bakin qofa tayi shiru bata amsa ba, seya qarasa ya tsaya daidai kanta murya a cukule yace

"Tashi muje mu kwanta" nan ma tayi masa shiru bata motsa ba.

"Nasan kina jina dan haka ki tashi karki bata mun rai" ya sake fada, yabda yayi maganar sam babu wasa a ciki ya sakata yin miqa tana tura baki ta kalle shi tace

"Nifa bacci nakeyi ka tasheni"
"Wuce muje" ya fada yana matsa mata hanya, se data harareshi ta qasan ido kafin tace

"Kaje zan taho bari na shirya".
Kwafa yayi ya fita dan tunda dazu da ta tashin ya rage volume din Tv yana jiyo ta tana playing voice notes din mutane har kuma yazo jikin qofar yaji dariyarta seda ya taba qofar tayi qara kafin yasan ta ajiye wayar shine zatace masa bacci takeyi to dole ya taka mata burki dan baze dauki wannan salon chatting din daren ba, yana zaune ta mayar dashi hoto tana hira da wasu can a waje da mazansu basu damu dasu ba da har suke barinsu su raba dare suna chatting

Kusan minti goma da shigarsa dakinsa yaji ta shiru a fusace ya sake komawa dakin nata, bata ciki, jikin socket din da take saka chaji ya duba bega wayarta ba dan haka kai tsaye ya wuce bandaki.

Umaimah kuwa Khalil na fita ta dauki wayarta ta shige Bandaki, akan Masai ta zauna taci gaba da duba Messages din group dan wata ce take neman shawara akan mijinta nada kule kulen yammata shine ake ta bata shawarwarin abinda ya kamata tayi ta sakankance se jin bude qofa tayi, a sittin ta jefa wayar cikin kwandon kayan wanki ta durqushe a qasa ta fara kakarin Amai daidai sanda Khalil ya tura qofar ya shiga.

"Subhanallahi Amai kuma?" Ya fada yana qarasawa inda take duk fushin daya shiga dashi lokaci daya ya washe ya ruqota jikinsa yana shafa bayanta ganin yanda take kakarin Aman kuma babu abinda yake fita.

Sunfi minti biyar tana ta yunqurin iska kafin ta miqe tana riqe ciki a qaryarta wai juya mata yake Allah sarki haka ya ringa mata sannu yana lallabata ya tara mata ruwa me dumi ya wanketa tas ya dauketa suka wuce dakinsa, madara tace masa zata sha kuma se an tafasa, ba yanda ya iya haka ya kwantar da ita ya wuce kitchen din dukda sha biyu ta gota a sannan Umaimah ko tanajin ya sakaya qofa ta fito daga dakin sadaf sadaf taje ta dakko wayarta daga bandaki, bata tsaya bata lokaci ba ta kashe ta gaba daya kafin ta jona a chaji ta koma dakinsa ta kwanta. Daya kai madarar ma kurba biyu tayi tace ta qoshi ya karba ya ajiye yana ta mata sannu ita kuwa tayi kwanciyarta dan har yanzun fa ba wai ta yarda dagaske tana da wani ciki bane ma tunda babu abinda take ji ko wata alama da ake fada ta masu ciki.
Ita haushin ta katse mata hirar da yayi tana shirin bada tata shawarar, amma babu komai sa hadu da safe.

Washe gari da ta kama juma'a tunda Asuba yace ta shirya idan ze fita seya sauketa a gida ta wuni, sosai ta ringa murna, tare suka hada abin karyawa dan cewa yayi tabar shara kwanukanda suka bata kuwa suna gamawa yace ta shiga wanka shi kuma ya daurayesu kafin shima ya shirya. Qarfe tara suka fita seda zasu gota gidan Rufaida tace masa

"Au na manta wallahi matar gidan nan ta haihu idanna dawo yau ko gobe zan shiga nayi mata barka"

"Allah ya kaimu, idanda abinda zaki kawo mata se ki gaya mun" ya bata amsa kafin suka ci gaba da hirar su har suka qarasa, a gurguje ya gaisa da Anty dan basu tarar da Mama ba tun sassafe sun fita tareda Abban taje asibiti ganin likita idonta ya matsa mata da ciwo dan haka be zauna ba ya wuce Office dan ya makara, Umaimah kuwa guri ta samu ta fara zuba iskancinta yanda ranta yake so.

Da farko Doya da kwai Anty ta kai mata da kunun gyada, saboda tsabar shahara a iskanci irin nata da son ta nuna musu tayi ciki Antyn na ajiye flask din doyar ta toshe hanci da hannu biyu tana ja baya, kallonta Antyn tayi da mamaki tace

"Lafiya Umaimah?"
"Bana son qamshin doyar ki fita da ita" ta fada kamar zatayi kuka se Anty ta saki murmushi tace
"Toh ai da tun kafin kuzo ya kamata ki kira ki fadi abinda kike so a dafa miki, yanzu me zaki ci toh?"

Yatsina fuska Umaiman tayi tace "ba komai"
"To ko a baki kunun zallah shi zaki iya sha ai dan yanzu ma aka tafi kaiwa Nuratu tace tana so" Antyn ta sake fada.

Kamar wadda aka wa dole haka ta ringa wata yatsina tana shan kunun, can cikin ranta ko hadiyar yawu take dan doyar ta shiga ranta gashi ta rigada tace bata ci. Tana kallo Yaya Aminu yazo ya zubo doyar da kunun ya zauna kusa da ita yana ci Anty na ce masa daya koma gefe Umaiman bata son qamshin. Yace
"Ikon Allah su kuma daga ita har Nuratun daga zuwa ko wata biyu baku rufa ba se ciki tab Allah ya raba lafiya toh"

"Kaji mun mutun se kace shi ba wata tara tasa matar ta haihu ba ze sakawa Mutane ido" Umaimah ta fada a zuciyarta tana hararar sa qasa qasa dan duk rashin mutunchinta bata shiga sabgarsa dan ubanta yake ci, Anty ce ta tare musu ya gama cin doyarsa ya tashi daidai sanda Anty take tambayar Umaiman me zata ci

"Wai yau Juma'a ba wake da shinkafa akeyi a gidan nan gaba daya dana sadaka ba shine zaki tsaya kina tambayar me zataci se ta dafo abinda take so daga gidanta ai ta taho dashi ko" ya fada yana ficewa daga dakin

Haka ta wunitana nade a daki tana aikin dannan waya, sanda Mama ta dawo taga iskancin nata bana qare bane bata bi takanta ba, abincin ranar ma da aka saka mata man gyada har tayi loma biyu ta ture wai da Manja take so aka sake janzawa ana ajiyewa tace a fita dashi bata so Anty ce take ta jigila akan ta me take so me za'a mata se wana baiwar Allah take can qasan ranta tana tuntsura dariya tana kuma hasaso yanda zata saka Khalil a gaba da laulayin qarya ba ita ta samu salama ba se da Khalil ya dawo ya dauketa suka tafi bayan da Mama ta ja mata kunne sosai akan shegen Chat din da take tayi tunda taje gidan.

Daga nan gidan Hajiyarsa suka biya, beyi zaton Jalila zata gaya mata zancen cikin ba seda sukaje kunya tsakanin shida Umaimah aka rasa wanda ze boye wani ita kuwa Hajiya ko a jikinta jan Umaiman take tana gwada mata hanyoyin da zata kula da kanta da abubuwan da zata ringayi. A gidan sukayi sallar Magriba da Isha sukaci Tuwon da Hajiyar tayi da kanta kafin ta zuba musu wani suka tafi dashi ko zasuyi dumame tana sake jaddadawa Umaiman ta kula da kanta ta kuma ringa Addu'a, karta yi wasa da Azkar din safe da yamma dana kwanciya bacci idan an kwana biyu zatazo gidan zata taho mata da saqo da haka sukayi sallama bayan data hada ta da tarin kayan kwalamar da akasan masu ciki dasu, zuciyar Umaimah fal da soyayyar Dattijuwar, yanda take ji da ita take nuna mata qauna ko Mamanta data haifeta bata nuna haka a fili ita kam me zatacewa Allah banda godiya.

Suna tafe a hanya tana duba waya, abin da ta lura da sababbin yan group din nasu basu fiya hira da rana ba seda daddare, koda yake daga jiyan zuwa yau ta fahimci da yawan su manyan mata ne ma'aikata da kuma yan kasuwa shiyasa basu da lokaci da rana se dare lokacin kowa ya gama uzurinsa.

"Nifa wayar nan taki ta fara shiga haqqina gaskiya, shikenan yanzu bazakiyi hira dani ba sedai kiyi ta danna waya kina dariya ke kadai" Khalil ya fada yana tabata ganin yana ta magana shikadai bata ma san yanayi ba.

Dagowa tayi ta kalle shi tayi murmushi tace
"Kasan na dade bani da waya yanzu ina dokinta ne"

"Nidai ban yarda ba daga yanzu indai muna tare karbe ta zan ringayi na yarda idan bana nan kiyita chatting dinki amma indai ina nan dukka lokacinki nawa ne" Ya sake fada daidai sanda suke karya kwanar gidansu, seta kashe data ta zura wayar a jaka tace

"An gama yallabai ka gani ma na kashe ta bazan sake kunna Data ba se Allah ya kaimu gobe"

"Yawwa na tuna gobe Saturday ko may be zamuje Kaduna akwai aikin da zan duba ban dai gama tabbatar da tafiyar ba tukunna amma dai ki kwanta cikin shiru saboda tsaro"

"Allah ya kaimu, yanzu se na hada kaya kwana nawa zamuyi?" Ta tambaye shi dukda qasan ranta bata so dan ita haka Allah yayita bata son tafiye tafiye ba kuma tayi zaton idan sunyi aure da ita ze ringa yawon gari garin da yakeyi duba aiki ba.

"Karki damu kawai kiyi parking abubuwa masu muhimmanci, kayan sawa idan munje zamu siya dan nima ban san kwana nawa zanyi ba kinga daman bamu je honeymoon ba daga can kawai se muyi can muyita zaga gari har se an ganmu kawai" ya fada yana kashe mata ido daidai sanda ya paka mota a qofar gida, seta jefa masa hararar wasa ya fita ya bude Get ya dawo yana cewa

"Kinga da kin iya mota kawai shigo da ita zakiyi amma yanzu se naje na kuma dawowa"
"Uhm" Umaimah tace, ta gaji sosai dan haka suna shiga wanka ta farayi da ruwa me zafi sosai ta gasa jikinta, cikin kayan da Hajiya ta bata ta lalubo tsami gaye ta zauna tana sha saboda jin bakinta da tayi babu dadi, wai yanzu cikine da ita itama zata haifi Da tab lallai akwai bidiri ranar.

Da wuri suka kwanta saboda tafiyar da aka tabbatar masa zeyi a goben, Umaimah dake kwance lamo kamar me bacci ta miqe a hankali bayan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login