Showing 6001 words to 9000 words out of 429394 words

Chapter 3 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

920

faru yasa ta manta da batun zuwa yinin Halima gashi babu waya bare su kirata, washe gari da take Lahadi ma a gida ta wuni cur ba um babi um um fuska duk ta kode saboda kuka. Mutanen gidan kuwa babu wanda ya shiga sabgarta gara ma Anty ita ce me leqata har ta kai mata abinci wanda a gurin Umaimah ba gwaninta take mata ba dan data fita zata rakata da harara.

Ranar Monday tana da Test dan haka dole ta shirya fita makaranta dukda babu abinda ta karanta saboda wancan satin duk sun qarar dashi a yawon shirin biki, Lahadi da tayi niyyar zama a gida tayi karatun kuma ga yanda abubuwa suka kasance.

A tsakar gida ta tarar da Abbansu yana sallamar Anty dake da girki ranar, kallo daya ya mata ya ci gaba da magana da Antyn ko gaisuwar da tayi masa be amsa ba dan tun wacceb ranar ya dena Amsa gaisuwarta haka babu sakin fuska ko yaushe suka hadu harara ce take rabasu.

Gaba tayi da niyyar fita ya daka mata tsawa yana tambayarta ina zataje, se ta lumshe Idanunta da suka kawo hawaye ta juyo murya na rawa tace

"Makaranta zanje ina da Test yau".
Be tanka mata ba haka itama bata motsa daga inda take ba harya yi sallama da Anty kafin kamar baya so yace mata " muje" yayi gaba ta bishi a baya.

A motarsa ya kaita har cikin makarantar, tafiyar kurame sukayi dan babu me cewa wani qala se sheshsheqar Kukanta dake tashia hankali duk a sonta na tausayinta yayi tasiri azuciyar Abban saboda sam baya so yagansu a damuwa amma kamar dutse ko ajikinsa.

"Qarfe nawa zaku tashi" ya tambayeta yana miqa mata naira dubu, ta karba tace
"Qarfe sha biyu ne test din, se kuma ina da practical 2-4pm"
"Karki kuskura na rigaki komawa gida, idan kuma ba haka ba zamu gauraya" ya fada a kausashe kafin yaja motar ya fita.

Kujera ta samu a gurin ta zauna kawai ta fasa kuka, ita ya zatayi? Ko tausayin abinda ya sameta bazasuji ba kuma se abi a ringa tsangwamarta ana daure mata fuska.

A gurin Su Fauziyya da Nabila suka sameta dan daman nan suka saba zama su jira junansu

"Umaimah lafiya zaki zauna kina rusa kuka kamar wadda akawa mutuwa jifa har kin fara tarawa kanki mutane ana kallonki" Nabila ta fada tana kama hannunta

"Toh ina ruwan wani dani kowa yaji da damuwar sa mana an san abinda yake damuna ne da zaa zo ana kallo na" ta fada cikin kukan.

"Kinga tashi mu bar nan, ga Malam Tsalha guntsi fesa can ta taho tun kafin ta debi wani sharrin taje tana yayaki a gari" Fauziyya ta fada ganin wata course mate dinsu Jamila ta nufo gurin, irin masu dan banzan gulma da sa idon nan ce, zance kuwa na kowa a makarantar nan kaji shi a bakinta shi yasa suke ce mata Malam Tsalha.

A hanya suka hadu da Rumasa'u da shigowarta kenan suka rankaya cafteria suka samu guri can baya suka zauna anan take basu labarin fasa auranta da Qasim yayi.

"Amma gayen nan dan yarfi ne,yanzu akan dan abin nan shine zece ya fasa auranki? koda yake kansa yayiwa dan dai nasan baze taba samun hadaddiyar baby kamar ki ba wallahi dan wahala shi yayi Asara. Seki share hawayenki da kyanki da quruciyarki bazaki rasa mijin aure ba. Kuma duk mutumin ma daya kasa haquri da halinka tun kafin ya aure ka ta yaya zaku zauna dashi bayan aure ki manta dashi kawai" Nabila ta fada.

"Amma fa Umaimah kema da laifinki ko nace laifinki ma yafi yawa, kishi ai ba hauka bane amma ke idan naki ya tashi rufe miki ido yake kiyi tayin abu kamar wata me tabin hankali. Jifa yarfin da kika masa ranar a gaban mutane dan Allah, be yi fushi ba ya dauke ki har mukaje gida kina zaginsa shi da iyayensa kika sauka kika kuma qara masa, ina ke kika ce idan ya haifu cikin uwar sa ya je ya auri Siyaman ke ya qyale ki? Gashi kuwa ya nuna miki ya haifu saura ki jira ganin IV auran sa da ita nan gaba kadan" Ruma ta fada iya bakin gaskiyar ta.

"Ai ke daman kina baqin ciki da duk wani farin cikin Umaimah a rayuwa ni na dade da sanin kina baqin cikin tarayyarta da Qasim waya sani ma ko da sa hannunki a ciki? Toh Umaimah dai nan gani nan bari duk mugun abin mutum sedai ya koma kansa saboda ke kin rasa mashinshini shiyasa kike farin ciki dan ta rasa nata" Fauziyya ta hayayyaqo mata, seta miqe tsaye itama tana kallo ta tace

"Dani dake babu meyiwa wani gorin ya rasa mashinshini dan gara ni ana gani ana yabawa ke fa? Cusa kai kike amma mazan yi suke kamar basu san da wanzuwarki ba. Ita gaskiya daya ce daga qinta kuma se fada, the earlier da kika gane laifinki kika gyara the better. Amma idan kinga zaki ci gaba da zama da maqaryata suna dora ki a keken bera shikenan, nidai har a gurin Allah na fita dan na fada miki gaskiya ruwanki ki gyara ruwanki kiqi amma Umaimah babu Namijin da ze aure ki da wannan mugun HALIN KISHIN naki" Rumasa'u ta qara fada idon ta akan Umaimah da tayi shiru.

"Kut baki kike mata na karta auru? Toh wallahi tun wuri Umaimah kisan abinyi dan bamu san irin bakin ta ba, Mune shaida" Nabila ta fada cikin son qara kambama abun.

"Ke kika hadu da ita rana tsaka dab haka ke zamu bincika muji ko kina da mugun baki amma ni ki tambayeta ta sanni ta san asalina, kuma duk wanda ze so Umaimah a cikin ku baya nane dan ni son tsakani da Allah nake mata ina kuma so ta gyaru ta rabauta ba irin naku na son zuciya da sake ingizata zuwa ga Halaka ba" Ruman ta fada a fusace kafin ta juya ta bar gurin, a ranta ta qudurce ko Su ne kadai suka rage da zatayi qawance dasu a rayuwa ta haqura, ita Nabila zata kira Mayya?

Umaimah kuwa zama sukayi a gurin Fauziyya da Nabila na sake yi mata famfo da gaya mata kalam da suke fasa mata kai take ganin takai inda bata kai ba. Basu bar gurin ba seda lokacin shigar su test yayi suka tabbatar da sunyi brain washing nata ta hanyar nuna mata daidai abinda take aikatawa da kuma cewar duk wanda ya rabu da ita shi yayi Asara ba ita ba.

Haka suka shiga test din babu wadda ta karanta komai a cikinsu, daman ita ce me qoqarin da take goyasu to yau itama batayi karatun ba gashi anyi fada da Ruma bare ta basu Amsa. Da suka fito daga practical ma sun so su jata wai suje gidan Halima dan tun safen ta ke musu waya suje ita bata zo yin test din ba se taqi saboda tuna gargadin Abba na dazu, haka suka rabu a get ta kama hanyar gida ita kadai dan Ruma da gaske ta dauki fushi ko sashin da suke bata sake kallo ba.

*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 3


Sosai take jin ta a takure saboda rashin waya, idan taje makaranta ta dawo sedai ta zauna shiru in ta gaji ta dauki littattafanta ta duba dan har yanzu babu me shiga sabgarta a gidan se Anty ita kuma ba kulata take ba.

Ita bata ga abin da zesa gaba daya su wani dauke mata ba bayan ita abun jaje ya sama kamata yayi ataru a tayata amma duk an tsangwameta hatta da Yayyanta da suke gidan Aure kowa tazo harara da zagi ne yake raba su a cikin wannan yana yi taci sati biyu, sauqin ta ma bata zaman gidan sosai saboda gabatowar jarabawa da zasu fara ta qarshe kusan idan ta fita makaranta takwas se biyar take dawowa.

Tana da buqatar waya saboda harkar karatu wani abun softcopy ne zaa bayar dole seda wayar ko system hakan yasa ta niyyaci tunkarar Abban su da zancen siya mata waya.

Bayan sallar Isha ta same shi a palour sa, sam ta manta da Mama ce da girki seda tayi sallama ta shiga ta tarar da ita tana hadawa Abban shayi, kamar ta juya amma ba hali tunda sun tigada sun ganta haka? ta nemi guri ta zauna ta shiga gaishe su kai a qasa.

"Ya akayi Hajia Umai" Abba ya fada cikin sakin fuska ba kamar yanda yake mata tsahon kwanakin ba hakan ya bata kwarin guiwa ta gyara zama tana cewa

"Daman Abba saura sati uku mu fara jarabawa ne, kuma handouts da yawa softcopy ake bamu, bayan nan wani lokacin ina so na danyi browsing babu dama tunda bani da waya"

"Yanzu me kike buqata" Abban ya tambayeta, seda ta kalli Mama da tayi kamar babu ita a gurin kafin tace

"Waya nake so dan Allah Abba ko taka ce ka ringa bani aro in zan duba abu"

"Tawa kuma Aa salon kiyimun jagwalgwalo, bari dai zanyiwa Yayan ku magana se a samo miki ko qarama ce" Abban ya sake fada. Da alama yau yana cikin yanayi me dadi, kamar tace Aa karya saka Yaya Aminu dan tasan da wuya idanze bari a bata sedaita kanne tayi masa godiya kafin ta miqe ta fita. Daga bakin qofa ta labe tareda kasa kunne ilai kuwa ta jiyo Mama tana cewa

"Haba Alhaji, yanzu kai har ka yarda da wannan lambon da tayi kamar ka manta wacece Umaimah shine zaka dauki waya ka bata"

Murmushi Abban yayi yana kallo ta yace
"Malika kenan, takura da tsanani fa baya gyara sedai su qara kangarar da yaro, iya lokacin da aka dauka ai taji a jikinta idan muka ce zamu ci gaba da takureta kuma tun tana biyuwa har zaa iya kaiwa matakin da zata fito da wata sabuqar hanyar da bamu sani ba.

Zan gayawa Babangida ya kawo mata? wayar, daman ko batayi magana ba ina da niyyar sawa ya kawo dan jiya ina jinta tana yiwa Nuratu magiyar ta bata aro ta hana ta, amma hakanbaze chanza komai ba, sannan ina me sake tabbatar miki ki kuma jaddada mata idan wata biyun nan ta cika bata tsaida miji ba sadakarta zan bayar"

"Sadaka kuma Alhaji se kace wata wadda ba'a so" Mamanta fada tana zare ido, se ya miqe tsaye yana cewa

"Kun dauka wasa ne kenan? Daman Lawan megadin gidan Alhaji Manniru ya taba nuna sha'awar auranta toh inaga shi zanyiwa magana kawai, Allah ya nuna mana lokaci zaku gani" ya shige dakin sa ya bar Mama tana cewa

"In sha Allahu Allah ze fito mata da miji amma wane irin sadaka da ita abu babu dadin ji haka".

Qirji Umaimah dake labe a bakin qofa ta dafe, a fili ta furta "na shiga uku daman Abba da gaske yake ni ze bayar sadaka?" Saurin barin gurin tayi gudun kar su ganta a ranta tana ayyana irin diban Albarkar da zatayiwa Lawan duk randa suka hadu, saboda ya raina mata hankali ita ze kalla yace yana so harma ya samu Abban su? Ai kuwa seya gane kurensa, ze san ita ba sa'ar wasan sa bace.

Tana barin gurin Abbaya fito daga daki yana murmushi yace "Ja'ira, Allah dai ya shirya Umaimah yasa ta dena abinda takeyi"
Mama dake jimami ta amsa da "Amin dai, amma Alhaji zancen nanda watan nan daka qara daga qafa. Aurefa ba abin gaggawa bane, dole seta samu wanda suka daidaita ya ga ze iya da ita tukunna dan kasan bazaayi abu a gurguje ba ba tareda an fahimci juna ba ba fata ba daga baya ta falle halinta mutum yazo yana cewa an rufe shi".

Seda ya zauna yaja shayin data saisaita masa kafin yace " Nasani nima na fada ne kawai saboda na qara tsoratar da ita dan tana tsaye ta labe ba tafiya tayi ba, dukda haka da gaske nake ta mayar da hankali ta tsayar da Miji dan naga sako sakonda taga ana mata ya saka take duk iyashegen da takeyi, dan haka karma ki kuskura ta gane ba haka bane".

Umaimah kuwa Haka ta kwana tana juya maganar fito da miji a wata daya, toh ta ina zata fara ma bayan tunda Qasim ya fasa kamar wanda ya tafi da duk farin jininta ko a hanya wani be sake tare ta da sunan soyayya ba.
Idan ta tuna wai Lawan yace yana sonta kuwa wani takaici ne yake taso mata, ta quduri niyyar qare masa tanadi tsaf duk randa sukayi ido hudu kuwa.

Washe gari guraren 10 sega Yaya Aminu da sabuwar waya Infinix me kyau ya kawo mata. Ta karba tayi godiya kafin ta kunnata ta jona a chaji ta wuce makaranta dan daman shiri take.
Fix lecture ce ta wani malami da be samu ya gama musu darasin sa ba ga lokacin Exam yayi. Tana shiga Ajin ta hango Rumasa'u da yanzu ko kallon arziqi ba tayiwa inda suke se ta zarce gurin nata dukda su Halima dake mata magana suna nuna mata gurin da suka tanadar mata amma bata kula ba.

Sallama tayi musu ka gaisa da wadanda ke kusa da Ruman kafin ta zauna akan desk din gabanta tace
"Hajiya Ruma fushin ne har yanzu baa sakko ba" dauke kai gefe Ruma tayi tace
"Fushi? Aini ba fushi nake ba Umaimah, buqatata ne bakyayi a cikin rayuwar ki shi yasa na fita na barki da masu hali da ra'ayi irin naki tunda bakya son gaskiya".

"Uhm to yanzu dai ai komai ya wuce, bayan haka fa keda Nabila kukayi cacar baki ba dani ba amma da kika tashi kikayi mana kudin goro gaba daya"

"Ai sanda take zagina ta kirani mayya kurmancewa kikayi da kika kasa magana ko kuwa? Kinga dan Allah matsamun a nan ga malam nan ya shigo" ta qarasa tana janyo littafi daga cikin jakarta.
A kusa da ita Umaimah ta zauna har aka qare lecture din dukda Ruman ba kulata take ba, malamin na fita ta sake kafa mata surutu har seda Rumah ta sakko daga fushin tace mata

"Na haqura amma dai bazan sake jerawa dake ba in dai kina tare da wadancan da basu san ciwon kansu ba" ta fada tana hararar Nabila da tun zaman Umaimah a gun hankalin na kansu.

"Baki haqura ba kenan, itama Nabilan zan mata magana zata baki haquri akan abinda tayi shikenan?"

"Ba shikenan ba, kinsan ni a rayuwa bana jurar wulaqanci bazan tsaya wata banza ta gaya mun magana ko da da nake musu shiru kin sani ba tsoron su nake ba kawaici ne amma yanzu daidai nake da kowacce yarinya a cikin su"

"Ohni Rumah kin zama masifaffiya toh dai dan Allah kiyi haquri" Umaimah ta sake fada
"Shikenan, na haqura"

Da haka suka miqe gaba daya suka nufi qofa. A kusa da su Fauziyya Umaimah ta tsaya tana cewa
"Ku tashi muje mu karbo exam card"

"Yar wulaqanci se yanzu kika san damu bayan kina shigowa muka baki seat amma kika share kikayi tafiyarki abin ki" Fauziyyan ta fada, Nabila kuwa tabe baki tayi suna yar harara da Rumasa'u dake gaisawa da Halima Amarya.

A waje suka zauna saboda Me bayar da Exam card dinbe riga ya qaraso ba,

"Waini meya farune Ruma da Nabila naga se wani fizge fizge kukeyi lafiyar ku kuwa?" Halima ta fada tana kallo su. Fauziyya ce ta labarta mata abinda ya faru tsaf se ta kalle su gaba daya tace

"Ai gaskiya ta fada muku, wallahi Umaimah idan baki canza wannan halin ba babu namijin da ze iya zama dake. Kai gidan aure fa ya wuce duk yanda kuke hasashensa, kunga dai zazzafar soyyar nan da mukayi da Hayati to wallahi ko sati bamu rufa ba muka fara bala'i kawai dan ya bar wayarsa na dauka ina bincike.
Da na zata shwarwarin banzar da muke a nan zasu kawo mun mafita na hau na zauna akai ashe qara tabarbara abubuwa kawai zanyi badan Allah yaso ni Anty Zully tamun orientation ta gayamun gaskiyar abinda yake akwai ba ai inaga da yanzu wani zancen ake ba wannan ba.

Toh wallahi tun wuri in zakuyi hankali kuyi in ba haka ba, jikin yarinya ne ze fada mata"

"Gashi can an bude office din, ku tashi muje" Umaimah ta fada da rashin bama maganar Halima Muhimmanci, suka miqe gaba daya Halima nacewa

"Ina nan da daya da daya zaku same ni, dadina da gobe ai saurin zuwa" suka rankaya office din. Kwankwasawa sukayi aka basu izinin shiga suka tura kai gaba dayan su ciki, mutumin na zaune akan kujerar sa se wani akan kujerun da suke a gefe suna Hira suka shiga Umaimah ce akan gaba tayi sallama karaf idanunsu suka hadu da wanda yake zaune akan Kujerar gefen, kallo daya ta masa ta dauke kai dan vata taba ganin fuskarsa a office dinba is dai idan sabon ma'aikaci ne aka dauka suka qarasa gaban teburin suka gaishe shi ragowan suka waiwaya suka gaida baqon banda Umaimah data kafa kai tana binciko musu Exam cards dinsu a jikinta tana jin ido na yawo akan ta abinda yasa ta ringa sakin gajerun tsaki kenan tana mita a ranta.

Ita ta ringa miqa wa kowa nata suna signing a takaddar dake gefe har suka gama, dake ita ce qarshen fita seda takai bakin qofa kafin ta kalli baqon dake binta da kallo tunda suka shiga ya kasa dauke idonsa akan ta ta maka masa harara qasa qasa tace
"Ayita kallon mutum kamar an bashi ajiya saboda sa ido" tayi waje abinta.

Tsaf ya ji abinda ta fada se kawai yayi murmushi ya kalli abokinsa dake cewa
"Umaimah kenan, sarqa uwar rikici. In kana neman danger wutar baya ka samu yarinyar nan ka gama kawai abokina"

"Allah ko? Ni kuma ta burgeni. Da ace na shirya aure dana gwada sa'a ta dan a kallo daya ta shiga raina kuma tayi dai dai da matar da nake so na aura".

Hannu ya bashi suka tafa yana cewa " Bayero Bayero namu, to ka afka mana, amma fa karka ce ban gaya maka ba zaka sha rikici da ciwon kai a gurin nan kai kuma gaka ba gwanin daukar hayaniya ba"

Murmushi Khalil yayi yace "toh ai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login