Showing 174001 words to 177000 words out of 429394 words

Chapter 59 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1045

kuma da yawa idan ka gansu seka rantse bazasu aikata hakan ba shi yasa yake kasa musawa idan Aka ce Hadizan ta aikata abu tunda yaga wadanda suka fita fuskar Salahai ma suna aikatawa.

"Kayi shiru ko ba haka bane?" Barr ya katse masa tunani seya daga kai alamar haka ne ba tareda yayi magana ba.
"Toh ka gani ba, dukda bani da wata doguwar Mu'amala da ita banyi mata sani na sosai ba amma kai tsaye ina ganin abin nace qarya ne. Akwai wanda idan an fadi abu akansa koda ba gaskiya bane kai tsaye za'a gasgata shi amma akwai kuma wanda se kayi dagaske zaka yarda yayi abu koda kuwa a gabanka ya aikata se kaji shakkun anya kuwa shidinne.
Kuma irin wannan abin ba wai yanzu aka fara shi ba haka kawai mutane zasu samu hoto suyi ta yadawa da sharri kala kala qarshe idan zaka kamasu basu san ma mutumin dake jikin hoton ba ba kuma a san daga inda labarin ya faro ba dalilin da ya saka muke so mu daqile irin abubuwan nan kenan kuma zamu zurfafa bincike, duk wani wanda yake da saka hannu a ciki zamu gano shi sannan mu miqasu gaban shari'a tayi musu hukuncin daya dace dasu dan haka nanemeka, ina so kayi tunani ko akwai wani da kuke zargi da ze iya aikata mata hakan dukda na fada maka mun samu bayanan wadda ta wallafa abin a Facebook, amma bazamu dogara da ita kadai ba dan zata yuwu itama ta samo ne tayi karambanin dorawa a nan din".

"Toh nidai a iya hasashena bazan iya cewa ga wani abokin fada da Hadiza take dashi ba da har ze iya yi mata wannan abin, hasalima ita ko qawaye bata dasu qawarta kwaya daya ce Khausar kuma itace wadda take fada mana daman duk irin rashin jin da takeyi a boye tunda ita koda yaushe suna tare a gida ko a gurin aiki kuma ko yanzun kafin na yarda da maganar seda na titsiyeta ta gaya mun gaskiya kuma ta tabbatar mun da haka din ne abinda Hadizan take aikatawa kenan" Isma'il ya fada a sanyaye dan gaba daya maganganun Barr sun sake dulmiya masa tunani sun kuma fara maido dashi kan hanyar daya kaucewa. Allah ya sani ba wai ya yarda da cewar tanayin bane sedan bashida hujjar qaryata hakan.

Maganar Barr tace ta sakashi dagowa da sauri ya kalleshi jin yana cewa
"Wannan ce Khausar din da kake magana ko" ya fada yana miqa masa screen din wayarsa daya kunna Video seya karba bakinsa yaqi rufuwa saboda tsabar mamakin abinda yake gani Khausar ce zaune a tsakiyar qartin maza sun kai biyar ta kwanta jikin daya daga ciki hannunta riqe da dogon pipe na shisha tana zuqa. Shigar dake jikinta tayi muninda kai tsaye ze iya cewa ba ita bace amma hasken gurin daya haska fuskarta tarwai ga sunanta da wanda yakeyin video ya ambata akan ta dago fuskarta yayi mata video ta kuwa dago tana wani shegen fari da ido besan lokacin daya fara maimaita Innalillahi a fili ba.

Barr ya zare wayar daga hannunsa yana cewa
"Se kayiwa kanka Alqalanci ka kuma dora maganganun da take gaya muku akan sikeli, abu na qarshe da zan gaya maka kaje ka taushi yar uwarka Ubangiji kadai yasan halin da take ciki kuma yanzu ne take da buqatar kulawarku da qarfafa guiwa, koda ace abinda akw yawo dashi akanta gaskiya ne a halin yanzu tana cike da nadamar abinda ta aikata kuma tana buqatar wanda ze tallafa mata yajata a jiki ya taimaketa ta bar abinda takeyi ballantana ita da akayiwa Sharri".

Isma'il yayi shiru ya kasa cewa komai gaba daya kunyar kansa ce ta dabaibayeshu, ya akayi ya kasayiwa Tilon yar uwarsa uzuri koda na minti daya yaji ta bakinta? Tunda ake kawo musu magana akanta daga shi har Mama babu wanda ya taba bata damar da zata kare kanta sun kasa yarda da ita duk da daga shi har Maman idanza'a tsire su basu da shaidar da zata tabbatar da gaskiyar abinda suke zarginta dashi ko ake fada akanta suna yarda kawai zallar Son zuciyarsu ne yasa suke gasgata maganar wasu can daban sun kasa yarda da tarbiyyar dasuka bata, Allah sarki Alhajinsu ya tabbatar yau da yana raye baze taba juyawa Hadiza baya ba komai girman abinda ta aikata kuwa dan kamar yanda yake gaya musu a koda yaushe ba'a gyara laifi da laifi. Idan mutum ya aikata kuskure ana gyara masa ne ta hanyar janyo shi jiki a kyautata masa har shi dakansa ya fahimci kuskurensa kuma ya gyara amma sam su basu taba kwatanta hakan ba.

"Karka ji haushin kanka saboda ko wanne dan Adam a rayuwa da yanda yake iya tunkarar damuwa. Wani yakan saka nutsuwa da tunani gurin warware damuwarsa wani kuma yanayi mata gaggawa, dan haka yanzu ka tashi kaje gida ka huta zuwa gobe in Allah ya kaimu, duk wani ci gaba da muka samu akan binciken zan sanar maka. Sannan ka lallabi yar uwarka ina sake jaddada maka ka bata qwarin guiwa akan duk abinda ze fuskantota a gaba, ta qaddara cewar wannan abin da ya faru jarabawa ce daga ubangiki idan tayi haquri ta cinyeta se ta zame mata sikar takawani matakine na Nasara da batayi tsammani ba" Barr ya sake fada kafin suka miqe gaba daya. Har bakin Get ya rakashi yana sake jaddada masa daya je ya taushi hadiza ya kuma bata haquri da kwarin guiwa.

A hanya tunani Isma'il ya ringayi har seda kwallar tausayin Hadizan ta shiga zubo masa. Sam wani abu me kama da tausayinta be zo masa ba se a yanzu, a sanda abin ya faru wani mugun baqin ciki da tsanarta yaji sunyi masa dirar mikiya saboda yasan ta rusa masa shirin daya kwashe tsahon shekaru yanayinsa seda Mafarkinsa yazo dabda cika ya samu Tikitin tsayawa takarar Dan Majalisar Jaha wanda dakyar da roqon Allah damar ta samu se gashi wannan abun ya bullo wanda take Yan Adawa suka samu nayi suka fara sukar sa tun kafin bayyanuwar takarar tasa kowa yasanda ita. Zafin wannan ne ya sake ingiza shi yayi mata dukan da beqi ace ta mutu ba ko ya ji sauqin wani kaso na baqin cikin data qunsa musu.

Gidan Mama ya wuce, ya tarar da Bilkisu ta tafi saboda dare ta baro yara su kadai se Hajiya Zuwaira da Wata Asabe itama maqociyarsu ce Hajiya Zuwairan ta kirata akan tazo ta taya Maman kwana kafin gobe su Mama Innani su iso tuni ma har tasha magungunanta ma bacci ya dauketa se su biyun suna zaune suna ta mayar da yanda akayi.

Be zauna ba yayi musu sallama dan yana buqatar yaje gida ya harhada tunanin da suka tarar masa akai ko ze samu amsar abinda yake gabansa. Harya fita ya dawo, daga bakin qofa ya tsaya kamar baya son magana yana kallon Hajiya Zuwaira yace
"Momy wane Asibiti aka kwantar da Hadizan ne?"

Karkata kai Hajiya Zuwaira tayi tana kallonsa tace "Se yanzu zaka tambayi halin da yar uwarka take ciki Sama'ila? Ai wallahi banyi tsammanin haka daga gareka ba ko kusa ko alama kuwa. Idan hankali ya gushe ai nutsuwa ce take nemoshi fisabilillahi idan baka zama bango majinginarta ba wa kake so ta dafa tayi kuka a rayuwarta? Ka dagawa Mahaifiyarku hankali a maimakon ka kwantar mata sannan ka kama baiwar Allah da duka idan da abin yazo da Ajali ai yanzu ai wani zancen ake ba wannan ba shikenan saboda kaji abu da Allah kadai yasan Al'amari seka nemi Ran baiwar Allah nan duk da mukaje ceto babu wanda be fita da tabon ka ba akan meye eye? To wallahi kayiwa kanka fada kuma ka nemi yafiyarta, mugun bakin da ka saka uwarku ta ringayi mata idan baka saka ta gogesu qaiqayine ze koma kan masheqiya danbata da haqqinku daga kai Har Karimatun".

Shiru yayi mata har ta kai qarshe kansa na qasa kafin ya sake maimaita mata tambayar da yayi ta harareshi tace
"Se kaje ka tambayi matarka yarinyar arziqi ace har tafi ka qaunar Jininka ai wallahi wannan yarinya ta isa yar halak babu kuma abinda zamuce maya sedai muyi mata fatan Alkhairi kaje ka tambayeta zata gaya maka inda take" yana gama jinta ya saka kai yayi waje yana jinta tana cewa
"Dan banza me shegiyar baqar zuciya".

Washe gari gurin qarfe tara Barr ya kirashi yace yazo office dinsa, a can ya gaya masa an gano me Facebook account din Sunanta Rufaida Usman Hamza an kumayi tracing nata har gidan da take zaune sun gano yanzu haka qungiya ta rigada ta shigar da qara magana tana State CID dan basu yarda ma aje wani qaramin Division ba sunfi so ayi me gaba daya dan haka yanzu antura da Jami'ai zasuje su taho da matar. Yanzu zasu tafi can CID dinne dashi su jirayi zuwansu.



*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 45



Guraren goma da rabi Jami'an da aka tura suka dira a qofar gidan Rufaida suka kwankwasa qofa. Da yake Asabar ce Baban Anam yana gida yana zaune a palour yana kallon labarai A shirye yake dan fita zeyi Rufaidan ta tsayar dashi tana so ya sauketa gidansu Umaimah kamar yanda tayi mata alqawarin zata zo.

Jin ana buga qofa ya saka shi fita ya bude yaga mutane biyu maza se Mace guda daya dukkansu sanye da baqaqen Suit. Daya daga ciki ne ya zaro ID card dinsa ya nuna masa kafin yace
"Sunana Detective Ahalan Rano, kuma muna da takaddar izini ta tafiya da matarka me suna Rufaida Usman. Zamuje da ita can Office dinmu dan ta amsa wasu tambayoyi".

Jikin Baban Anam ne ya dauki rawa dan shi irin mutanen nan ne masu tsananin tsoron hukuma shiyasa yake matuqar takatsantsan da duk abinda ze hada shi dasu. Jin cewar Rufaida suka zo tafiya da ita se ya danji dama dama dukda haka tunani ya shigayi na laifin me ta aikata har haka da akw nemanta a CID koda yake shige shigen Rufaida ai se Allah kullum fadan da yake mata kenan yanzu ga irinta nan Allah kadai yasan abinda ta jefa kanta a ciki.

Kallon Detective yayi yace
"Ranka ya dade ko zan iya sanin abinda ta aikata kuwa"
"Gaskiya ba'a bamu wannan damar ba, amma kana iya biyo mu muje can dan kaji cikakken bayanin abinda ake zarginta dashi, please muna sauri ne ka shiga idan tana ciki kayi mata magana ko kuma mu tura da Jami'ar mu ta fito da ita" Detective ya fada fuskarsa babu alamar wasa. Jikin Ma'aruf ya sake daukar rawa ya shiga cewa

"Toh toh bari na shiga yanzu zata fito" ya juya ciki Detective yayiwa Macen da suke tare alamar ta bishi suk shiga a kusan tare daidai nan Rufaida ta fito tana kullo qofar palour ta cakare da wani Dandasheshen Leshi ta kawo dauri gaban goshi daman yaran suna gidan su Ma'aruf din ta kalleshi tana cewa
"Ina ka tafi ne na fito ban ganka ba bayan ka azalzaleni da nayi sauri" matar data gani a bayansa yasa ta gimtse maganarta se ya waiwaya shima dan bema lura da ta biyo shi ba ya hadiye yawu yana kallon Rufaidan yace

"Gurinki sukazo, daga State CID suke zasu tafi dake ki amsa wasu tambayoyi"
"Ban gane ba wa aka ce na kashe ko fashi da makami nayi da za'a kaini CID" Rufaida data saki jakar hannunta ta fada tana dafe qirji, matar ta nuna mata hanya tana cewa
"Muje ba wani abun damuwa bane yan tambayoyi ne zaki amsa su da kin gama zamu sallameki"

"Toh ki tambayeni anan mana baiwar Allah idan da gaske ne base munje can ba, na shiga ukuna dan Allah me aka ce nayi wallahi a rayuwata ko Office din yan Vigilante ban taba zuwa ba bare CID ki gaya mun waye ya kai qarata" Rufaida ta fada hannu aka tana tsalle kamar wata biri saboda tashin hankali, ganin tana neman bata musu lokaci ya saka matar kama hannunta ta fizge zata fada daki matar ta kalli Ma'aruf tace
"Idan tayi gardama zan gaya musu su shigo su saka mata ankwa, kuma zamuyi waya a zo da Hilox da Yan sanda masu uniform su tasata a gaba kaga yan unguwa gaba daya se su san abinda yake faruwa. Na gaya mata ba wani babban abu bane bincike ne ya fado ta kanta idan har mukaje ta fada mana gaskiya zamu sallameta tayi tafiyarta.

Jin da tayi za'a saka mata ankwa a sakata a bayan mota ya sakata tafiya tana matse hannaye idonta har ya fara hawaye ta kalli Ma'aruf tace
"Amma tare zamuje ko?"
"Ina? Kuje kawai ai sunce ba dadew zakiyi ba in kun gama se kimun waya nazo na daukeki" yayi saurin bata amsa. Dariya ya bawa matar dan gani tayi har yafi Rufaidan rikicewa tace masa
"Dagaske ba wani abu ne me zafi ba, ka bimu zata fi samun nutsuwa tayi abinda ake so". Dakyar da sidin goshi Ma'aruf ya bisu a baya da motarsa.

Sun isa aka shigar da Rufaida wani daki, wani Jami'i da fuskarsa sam babu Rahama ya ajiye mata hoton Facebook profile dinta da sukayi printing da kuma na posting din hotunan Hadiza data saka yana kallonta da jajayen idonsa ya tura mata profile din yace
"Wacece wannan?"
"Nice, Facebook dina ne" ta bashi amsa a tsorace tana matse fitsarin dake neman zubo mata tunda tayi arba da fuskarsa. Na post dinya tura mata kafin ma yayi magana tace

"Maqociyata ce Umaimah, tace wannan din budurwar Mijinta ce kuma wata ce ta tura mata hotunan tace mata yar Lesbian ce. Ita kuma saboda ya fasa auranta yasa ta watsa su a social media, na rantse da Allah iya gaskiyar abinda na sani kenan idan kuma baku yarda ba ga wayata nan ku duba zaku ga sanda ma ta turamun harda groups dinmu na WhatsApp data tura a ciki zaku gani".

Isma'il da suke zaune a wani daki tareda su Barr da sauran wakilan qungiya suna ji da kallon duk abinda Rufaidan take fada ya miqe yana cewa
"Tabbas zata aikata mayar Saurayinta ce Khalil".
Barr ya kalleshi yace
"Ka santa ne daman?"
"Kwanaki taje har gida taciwa Mamanmu mutunci ta kuma jaddada mata akan Hadiza ta rabu da mijinta kuma zatayi komai dan ganin ta rabasu. A lokacin na tarar da ita har seda ma fasa mata baki ta tafi da Alwashin seta lalata rayuwar Hadizan shine tayi mata wannan abin kenan" ya fada yana hade hannayensa biyu idonsa suka kada sukayi jajir.

Barr Unaizatu daya daga cikin wakilan qungiyar tasu tace
"Naji tace wata ceta turawa da ita matar saurayin hotuna ta kuma gaya mata hakan to wacece ita?"

"Idan aka kama ta zata fadi duk ma wanda yake da saka hannu a ciki dan haka yanzu mu saurara mu gani komai yazo qarshw tunda har an samu inda Asalin labarin ya fito" Barr Musa Kallah ya fada se suka mayar da hankali kan Rufaida dake tambayar mutumin zata iya tafiya tunda ta amsa tambayar tasu ya galla mata harara se gashi ta kife kai a Table tana kuka kamar qaramar yarinya abin haushi abin dariya.

Bayan gama tattara bayanai kai tsaye Jami'ai suka kama hanyar gidan su Umaimah. Suna zaune a tsakar gida sun baza babbar Tabarma a qasan Bishiya suna cin gujjiyar da Anty sukaje qauye shekaran jiya ta taho da ita se

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login