Showing 411001 words to 414000 words out of 429394 words

Chapter 138 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

967

ace Khalil Matan banza yabi da qila idan ta gano take zuciyarta zatayi bindiga ta mutu dan ba zata iya hasaso irin tashin hankalin da zata shiga ba. Tayi Adawa da matar sunnah wadda suke da matsayi daya da ita har a gurin Allah ita kam wai ina hankali da tunaninta suka tafi sanda tana gidan Khalil? Soyayya da Kishin karya hadata da kowa ya rufe mata ido yasa bata tunanin komai se son zuciyarta.

KHALIL
A kullum cikin godewa ubangiji yake bisa ni'imar da yayi masa. Tabbas ya yarda da cewar sakamakon haquri Alkhairi ne mara iyaka. Soyayyar Umaimah, Auranta da rayuwarsu ya dauke su a matsayin jarabawa daga ubangiji haka haqurin da yayi da ita ba sakalci bane kamar yanda da yawa suke dauka dan a yanzu gashi yana dandanar romon dutsen daya dafa. A baya ya kanyi tunanin yanda rayuwarsa zata kasance ba tareda matar da yake tsananin qauna ba se gashi yanzu ya rayu babu ita na tsayin shekaru kuma babu abinda ya canza a rayuwarsa sema tarin alkhairai da suka dabaibaye shi.

Dukda dai lamarin zuciya da abinda take so amma bashida zabi illah yaci gaba da bata Matsayin uwar yayansa bawai Masoyiya ba. Samun Humaira da yanda Al'amura suka daidaita tsakaninsu ya sakeyin tasiri matuqa gurin mantar dashi kewarta da tunaninta dukda a wasu lokutan su kan motsa masa. Kewar Umaiman tana damunsa idan ya tuna wasu abubuwan dadi da suka wanzu tsakaninsu se ya ringajin tamkar yaje gareta musamman idan yaji suna hira da yaransa yanda tayi sanyi qalau da mu'amalarta na matuwar dukan zuciyarsa tana kuma bashi tausayi, idan yaje gidan ya ganta sanyi qalau se yaji wani iri kamar ya tsokaneta tayi buyaginta tafi kyau a haka amma yanzu ta zama wata Umaimah ta daban da ko yatsa aka saka mata ya tabbatar ba zata gatsa ba. Duk sanda yaso shagala a irin shauqin nan daya ya tuno da wasu al'amura da suka gabata tilas yake danne komai yaci gaba da shafa mata fentin da ganinsa tareda ita ne kadai ze hana zuciyarsa karaya ta koma mata a karo na biyu. Allah ya sani yana qaunar Umaimah Al'amarin da yakeji a kanta baze misaltu ha ba kuma ya tsammanin ze jishi tareda wata mace amma ya haqura da ita tunda ya haifu dan Halal ne shi ba shege ba yanda tayi iqirari.

Qofar bandaki aka bude Humaira ta fito daure da Towel babba ta yafa wani qarami akanta, Khalil dake kwance daidai ya lula duniyar tunani qarar qofar ta farkar dashi ya kalleta, a tare suka saki murmushi kowanne da ma'anar nasa a ransa ya miqa mata hannu ta noqe kafada seya fashe da dariya sosai ita kuma ta shagwabe fuska kamar zata fasa kuka tana cewa
"Dole kayi mun dariya mana tunda ka kusa jawomun aiki, ni wlh bazan yarda bama se munje an duba ance babu komai sannan zan yarda mutum babu tausayi daga yin Arba'in dina baka ko duba ni yar yarinya ce kayita cin zalina ai Mala'ikun Allah suna kallonka"

Dariyar ya qarayi har yana shirin kwarewa ya tashi zaune yana cewa
"Ji wata magana fa yarinyar nan, Fushi zumbura baki da qunquni babu irin wanda ban gani ba a gidan nan ke kin rainani sannan yanzu tun ba'aje ko ina ba kin karaya dama ai na gaya miki yatinya lafiyata ta miki yawa baki yarda ba amma yanzu gashi kin fara gani a shekara biyu kinyi yan uku, to ki shirya wasu biyun suna tafe nan da wata tara dan aikin dana sha jiya ba a banza ba nasan nayi babbar Ajiya".

Pillows da suka watso qasa ta shiga diba tana jefa masa tana kukan shagwaba, tunda ta dawo daga wankan Abid abubuwa suka qarasa warwarewa Khalil din ya dawo garau kamar wanda aka canzawa inji, tun tan jin dadin abin seda ta fara kuka tana neman mafaka dan kamar me biyan bashi haka ya ri ga gurzarta kullum babu daga qafa kamar abinci seda ta fara rama kafin ya tattara hankalinsa guri guda ya fara saurara mata, shikansa ya ringa mamakin inda ya samo wannan qarfin da Lafiyar amma ya danganta hakan harda tsoron rasata daya fara tunda har ta nuna qiri qiri ta gajiya da halin da yake ciki tofa shikenan rayuwa ta qara armashi, Humairan riritashi take kamar Gwal shi kuma yana kasheta da kalolin soyayyarsa masu tsayawa a rai. Sunyi kyau dasu da yayansu gidansu na cike da walwala a kullum cikin godewa Allah yake bisa ni'imar da yayi masa. Watan Abid din goma sha takwas ta haife yan biyu Mace da Namiji wanda basu san da cikinsu bama seda yayi wata kusan uku sannan, yasha daru da ita, dukda bata ce bata so ba amma kullum cikin kukan danta jariri ne ko yayeshi batayi ba ace ciki haka ya ringa lallabata da aka ce musu biyu ne nan ta sake rigimewa qarshe se Mama ce ta dauke mata Abid dinda cikin yayi wata bakwai saboda ta samu sauqin abubuwa haka kuwa akayo ta turawa har Allah ya rabasu lafiya aka cire mata Hauwa (Jiddah) da Takwaran da yayiwa kansa suna ce masa Adil.

Yau din kwananta shida da dawowa daga wanka dan wannan karon ma gidan Mama ta koma bisa umarnin Hajiya Khalil kuwa ya ringa bala'i kamar ze ari baki saboda masifa akan me za'ace haihuwa ta uku ta tafi gida Hajiya tayi masa banza a cewarta lafiyar Humairan tafi komai ga aiki ga rainon yan biyu idan ta zauna a gidan fitinarsa kadai ba zata barta ta warke ba gara taje gida haka kuwa ya haqura qarshe ma ya qirqiri tafiyar dole ya bar qasar seda ya rage saura kwana uku ta dawo sannan shima ya dawo, tunda ta dawo din kuwa yake murzarta son ransa da sunan hukuncin yarda ta tafi gida da tayi, ita kuwa tadawo da shirin tarairayar mijinta dakyau, zata jurewa yanayinsa a kowanne hali ba zata gajiya ba.

Seda yayi dogon rarrashi kafin ya barta ya shiga wanka saboda buga qofa da akayi yan biyu na kuka. Ta shirya shi kuma ya shiga wanka, seda ya fito ya lura da lokacin daya bata qarfe goma yake so ya fita gashi har goman tayi da kusan minti ashirin. A gurguje ya shirya ko karyawa be tsaya ba ya fita saboda akwai baqin da zeyi kuma sha daya zasuzo shiyasa yaso fita tun goma ya sake duba takaddun da zeyi amfani dasu. Qarfe sha dayan daidai baqin suka iso, kai tsaye Conference room dinsu Anwar ya kaisu. Seda ya hada duk abinda zeyi amfani dashi kafin ya shiga, fuskarsa a washe ya shiga yi musu maraba yana kuma basu haqurin jiran da sukayi ya zauna akan kujerarsa idonsa ya sauka akan Umaimah data sunkuyar da kai da alama wani abu takeyi a wayarta take zuciyarsa ta buga har seda wayarsa ta subuce Anwar yayi saurin taro masa ita yana duba abinda Khalil din yake kallo da har yasa ya saki wayar be sani ba.

Seda yayi qoqarin tattara nutsuwarsa kafin ya zauna yana qoqarin kore abinda ya taso masa. Umaimah data gama turawa da sabon Bazawarin da tayi me suna Abdulwahab saqo danya kirata ne ta katse ta sanar masa sun fita wani uzuri idanta gama zata kira ta ajiye wayar bayan ta sakata a Silent kafin ta dago ganin dakin ya danyi duhu an kunna projecter karaf suka hada ido da Khalil da duk yanda yaso ya hana kansa kallonta ya kasa.

Jikinta ya dauki rawa zuciyarta ta ringa bugawa da sauri da sauri seta hade hannayenta biyu ta runtse idonta ji takeyi kamar ta tashi ta fice daga gurin, mamakin yanda ganinsa ya rudata haka ma ya kamata dan ba yau ne karon farko data ganshi ba bayan sun rabu, sun sha haduwa a gida a kusa kusa ma ba kamar yanzu da suke da tazarar gurin zama ba dukta ringaji mema yasa ta rako Hajiya Hudan. Aikin sabunta ginin Ma'aikatarsu za'ayi sun rubuta gwamnati ta sahale musu Hajiya Huda ce ta nemo musu Falcon Bridge construction company din a matsayin wadanda zasuyi musu aikin dan haka yau din tace tazo suje tareda wanda suke kula da bangaren kudi dan au qarasa qulla yarjejeniyar.

Har akaci aka cinye ba zatace ta gane abu daya da sukayi a gurin ba, muryar Anwar dake ta zuba bayani kawai takeji dan Khalil din shiya bawa takaddun ganin kamar Khalil din baya cikin nutsuwarsa yakashi karba kawai ba tareda yace wani abu ba ya jagoranci yarjejeniyar har aka gama suka saka hannu a takaddu Umaimah na ganin Hajiya Huda ta miqe itama ta miqe dan jinta takeyi kamar akan qaya, karo sukaci da Khalil da shima yake shirin fita tayi baya zata fadi ya tarota kafin ya saketa da sauri ya fice kamar wanda ya tuna wani abu.

A mota da Hajiya Huda ta tambayeta meya sameta ta birkice haka take ta fashe mata da kukan da take ta riqewa. Idan za'a saka mata wuqa ba zatace ga dalilin kukan ba, duk ta rikitasu, Aminu Sani daya daga cikin ma'aikatan da suka tafi tare, irin mutanen nan ne masu dan banzan surutu da saka ido, seya kalli Hajiyar yana gyara zama ya ce
"Hajiya kamar da sanayya tsakaninta da Shugaban kamfanin nan dan naga suna hada ido gaba dayansu suka rikice, shima bakiga a yanda ya fita ba? Hajiya Umaimah ko tsohon masoyi ne kun fitar da ran sake haduwa yau kuka gamu?"

Daga Umaiman har Hajiya Huda babu Wanda ya kulashi, ita tana cigaba da kuka qasa qasa ita kuma Hajiyar tunanin maganganunsa takeyi a zuciyarta tana tunanin to ko shine tsohon Mijin nata? Tabbas ta lura da yanda ya rasa nutsuwarsa ba kamar yanda ya shigo da farko ba kafin ya lura da Umaiman, irin kallon da ya ringayi mata duk tana ankare har ta ringa ayyana Allah sa tsuntsun soyayya ne ya dirar musu da kuwa Umaiman tayi Miji to amma yanzu ta gasgata maganar Aminu duk yanda akayi shine Mijinta da suka rabu inko hakane dole tayi kuka domin ya kai Mijin da wani ma ze maka takaicin rabuwa dashi balle ita da ta zauna tare dashi dan tasan shi sosai, Abokin qaninta ne tana jin labarin kirkinsa a gurinsa dan har akwai wata qanwarsu da qanin nata ya ringa cusa masa lokacin Khalil din yaqi yace shi yana son matarsa baze mata kishiya ba.

Da suka koma office din jiki a sabule ta dauki kayanta data bari bayan ta dauraye fuskarta ta gyara dukda haka idan ka kalleta seka san tayi kuka. Abdulwahab daya isheta da waya ya iso ze dauketa, Kyakykyawan Farin bafulatani Matashi ne da zasuyi sa'anni da Khalil ko ya dan girme shi da kadan. Ma'aikaci ne a hukumar yaqi da cin hanci da rashawa (EFCC) kusan Hadiza ce ta hadasu dan a office dinta suka fara haduwa yaje gurin itama Umaiman ranar taje suka gaisa har sukayi yar hira a gurin kafin suka rabu kwana biyu a tsakani Hadizan ta kirata tana sanar mata da cewar ya nemi number ta kuma ta bashi.

"Mutumin kirki ne Umaimah, na sanshi tunda dadewa munyi aiki tare yana da mata daya Khadija da yara hudu kuma ya tabbatar mun dagaske yakeyi idan kun daidaita kafin Azumi ma yake so ayi aure nan da wata hudu kenan. Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki bashi dama, nasan harda rashin bude zuciyarki da bakiyi ba yasa duk cikin wadanda suke zuwa kika rasa wanda yayi miki amma nasan in kika bawa Abdul dama zaki ce na gaya miku, halayensa suna kamanceceniya dana Khalil zaki so shi a hankali kuma ki tsananta addu'a" Hadizan ta gaya mata. Badan taso ba kuna dan karta ga tayi rashin kyautawa dan ita bama tason farin Namini amma a haka ta fara kula Abdulwahab.

Se gashi cikin qasa da sati daya sabo ya fara shiga tsakaninsu kamar yanda Hadizan ta fada halayensa suna kamanceceniya dana Khalil, yana da matuqar kirki da sanyin hali ga shi ya iya kula da tarirayar mace. A sati dayan kullum se sunyi waya ya kuma sanar mata da duk wani abu daya kamat ace ta sani akansa hatta da hoton matarsa da yaransa ya tura mata, ya gaya mata Hadiza ta gaya masa komai akanta kuma ya gamsu dan haka shi da gaske yakeyi auranta yake so yayi kuma daya dawo Kano dan a Abuja yake aiki zezo kuma da yayi zuwa daya yana so na biyu ya zama iyayensa ne zasuje nema masa auranta.

Gaban Umaimah ya ringa dukan dari dari da cewa da yayi Hadiza ta gaya masa komai akanta. Tana so ta tambayeshi yasan komai harda mugun HALIN KISHInta amma ta gagara, tsoro takeyi karta tono abinda zesa shima ya gudu dan zuciyarta ta fara amincewa dashi amma ba zataso ace su qulla magana akan qarya ko kuskuren tunani ba. Zata so ace yasan komai akanta kamar yanda tasani akanshi sannan ya yarda ze zauna da ita a hakan tana tsoron kar yaji wani abu daga baya yasaka shi canza ra'ayi dan haka ta qudure duk in suka hadu ita da bakinta zata fayyace masa komai. Kafin yaji a bakin yan unguwar da suke kore mata maneman gara yaji gaskiya daga bakinta akan wannan shawarar ta tsaya.

Da kanta ta gayawa Maman Asad haduwarta da Abdulwahab din, ta ringa murna ita ta gayawa sauran da Mama gaba daya suka tsaya akan shawarar kar Umaiman ta kaishi gida kai tsaye. Ta kaishi gidan Baba Abdullahi, shawarar Maman Asad din take Nuratu tace babu wannan maganar dan ta tabbata kawunda kansa ze fara watsa gayyar dan yayi rantsuwa duk wanda yazo neman auranta seya gaya masa komai dan baza'a hada baki dashi a cuci mutum ba haka kawai taje ta illatashi. Nuratu tace mata ta kaishi gidan Maman Asad din, suyi zancen su a can idan sun daidaita sun gama shirya komai sannan se yaje ya gaida Abba da yan uwansa base an gansu tare ba bare aje a lalata maganar tun kafin taje ko ina. Da wannan maganar sukayi Na'am, zuwansa na farko ta kaishi gidan a can sukayi zancensu tayi matuqar qoqari gurin sake bayyana masa wacece ita da Mugun HALIN KISHInta da yayi sanadiyyar mutuwar auranta amma seta gagara fada masa aika aikar da tayiwa Khalil da irin diban Albarka da tayiwa surukarta, ai Allah ma bayason wanda yake aikata laifi sannan ya ringa fada cikin Alfahari.

Abdulwahab yace yaji ya gani ya kuma yarda tunda har ta iya fada da kanta to dagaske take da cewar ta canza,ya sake jadda mata da cewar yana tsananin sonta kuma yasan bazata samu matsala da matarsa ba dan tana da haquri da kawaici ya tabbatar daga bangaren ta dai ba za'a taba samun wata matsala ba sannan kuma ba gida daya ma ze ajiye su ba, ita Umaiman ze tafi Abuja da ita saboda ita Hauwa tace tafi son zaman Kano yana daga babban dalilin daya saka yake son qara aure dan ya gaji da zama haka a can kuma zaman nasa yafi yawa a Abujan akan Kano ba kuma yaso ya shiga haqqinta yayi mata dolen komawa can shiyasa ze auri wadda zata yarda ta bishi a karan kanta.

Daga nan soyayya ta falle a tsakaninsu, dukda bawai tana Jinsa har cikin zuciyarta bane amma ta karbeshi kuma zata aureshi a rashin wanda zuciyartata take da muradi. Zuwan da yayi yau din kamar yanda suka tsara zeje ya gaida su Abba sannan qarshen sati iyayensa zasuje nema masa auranta, duk wasu shirye shirye sunyi nisa hatta da matarsa ya hadasu a waya sun gaisa haka Mamans?????"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"#a da qanwarsa guda daya ita kam tuni suka qulla zumunchi tana yawan kiran Umaiman itace dai bata shige mata.

Suna tafe yana janta da hirarsa ta barkwanci kamar yanda ya saba amma gaba daya yaga yanayinta ba kamar kullum ba dan haka yayi shiru ya qara musu sautin kidan dake tashi a radion motar, dama tunda ta fito yaga idonta ya tambayeta meya sameta tace masa zazzabi takeyi shiyasa fuskarta da idonta suka kumbura, yace su je Asibiti taqi, a cewarta taje an bata magunguna suna gida. Haka suka qarasa gidan, ta rigada ta sanar dasu zuwansa dan haka sun shirya. A falon Abba aka saukeshi, suka gaisa a mutunce Anty ta gabatar masa da abinda aka tanadar masa, tambaya daya biyu Abba ya gano Mahaifinsa Alhaji Sale sun zauna a kasuwa tare Rumfuna uku ne tsakaninsu, baban nasa ya gamu da paralysis kusan shekara goma yanzu abinda yasa suka bayar da hayar rumfar kenan dan babu me kula da gurin yaron shagunan nasa suka ringa Almundahana su kuma duka yayansa aikin gwamnati sukeyi babu wanda ya maida hankali a kasuwa dan haka ya bada hayarta kawai sukayi gwanjon kayan ciki.

Hira sosai suka sha da Abban, shiya kwatanta masa wani Alhaji Zakari da yake nan qasan layinsu shima dai tate suke a Kasuwar kuma Aminin Alhaji Salen ne sosai Abdulwahab din yace tabbas ai ko jiya ma Alhaji Zakarin yaje duba Alhajin nasu, komai yazo da sauqi ma tunda abin na gida ne. Be bar gidan ba seda sukayi sallar Magriba, ya cikasu da Alkhairi Umaimah na kwance ya kirata a waya akan ze tafi. Seda ta rakashi har bakin motarsa ya tafi kafin ta koma ciki tana kallon Samarin da suka maida musu da qofar gida Majalisa duk saboda suka giftawarta ko wani yazo gurinta suyi rige rigen bata ta. Komeye ribarsu a soke aure oho.

Zuwan Abdulwahab da kwana biyu waliyyansa sukayi waya akan zasu tambaya tunda har Abba sunyi waya da Alhajin nasu an qara tantanto juna. A daren ya kira Umaimah yake ce mata ta kira Abdulwahab suje suyi duk wasu gwaje gwaje daya kamata ace anyi tun kafin magana tayi qarfi base abu yazo ba kuka ba fata ba a samu wata matsala da zata iya hana auran saboda ita AS ce. Tana barin gurinsa ta kira Abdul din, abin dariya abin haushi wai shi a shekarunsa bema san Genotype dinsa ba, koda za'a daukeshi aiki kawai zuwa yayi aka masa medical report din ba tareda an gwadashi ba ta ringa masa masifa kamar wani danta, sune suke yaqi da cin hanci

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login