Showing 114001 words to 117000 words out of 429394 words

Chapter 39 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

996


Misalin qarfe tara bayan Khalil ya fita aiki tana kishingide akan kujera da waya a hannunta Mu'ayyad data samu ta lallaba dakyar yayi bacci na kwance akan dan gadonsa me lilo yana shillashi, wani series take kallo a YouTube taji ana qwanqwasa Get, tasan baze wuce Aliyun Maman Hauwa ba ko yayi mantuwar wani abun, wake ta aikawa da Ramatu kishiyar Maman Hauwan tayi mata Alalan gwangwani zatayi baqi qannen Hajiyar Khalil ne sukazo daga Gaya zasu zo ganin Mu'ayyad din.

Hijabi ta saka taje ta bude, Rufaida ce da qaton cikinta ta sako wani uban Hijabi se haki take saboda tafiyar da tayi ta bud mata ta shigo tana cewa
"Uwar biyu daga ina haka?"
"Wallahi gajiya nayi da zama ni kadai shine nace bari na shigo na dan rage lokaci kafin rana tayi" Rufaidan ta bata amsa suka wuce ciki Umaimah na cewa
"Kin ganni nima fa wai baqi zanyi amma babu abinda nayi na samu dai na bada Ramatu tayi mun Alala ina da zobo in hada musu dashi gyaran gidan ne na gagara yi wallahi duk na gaji"

"Ai kina ma qoqari ni idan kinga nayi shara yanzu ai Abban Anam yana gari ne, ina zan iya dazu ma na kira Maman Salaha inji yaushe zata dawo idan ba haka ba na nemi wata kawai na gaji da wanne zakaji da aikin gida ko da wahalar kanka, kema da me aikin kika nema kawai kika huta ta rage miki aiki"
Rufaida ta fada, Umaimah ta yatsina fuska tace

"Me aiki ni Allah ya rufamun Asiri zanyi abinda zan iya na bar sauran kawai"

"Iyayen kishi" Rufaida ta fada cikin sigar tsokana kafin taci gaba da cewa
"to ko ba me kwana ba ai seki nemi me zuwa ta tafi, da safe idan megidan ya fita tazo kafin yamma ya dawo ta gama miki ayyukanki ta tafi ba shikenan ba"

"Ke nifa me aikince gaba daya bana so ki barni zanyi aikina" Umaiman ta fada cikin qosawa da zancen me aikin da kullum Rufaida se tayi mata kamar ita take mata ayyukan gidan balle tace ta gaji, a maimakon ta tashi tayi abinda zatayi kafin zuwan baqin nata nan suka shantake suna hira bata ankare ba se jin bugun qofa tayi ta kalli Agogo qarfe sha daya na safe ta miqe tana salati ta je ta bude, Ramatu ce da kanta da kular data bada a zubo mata Alalen, daga bakin Get ta tsaya ta bata tana cewa
"Yaran duk suna makaranta kuma naga lokaci yayi shiyasa nace bari na miqo miki da kaina"

Umaimah ta karba tana cewa
"Wallahi nima ban ankare da lokaci ba se yanzu, nagode sosai Allah saka da Alkhairi" daga haka ta juya ciki da kular Alalen ta ajiye a kitchen tana jiyo kukan Mu'ayyad daya farka daga bacci ta shiga tana yamutsa fuska ta kalli palour tana tunanin ta ina zata fara gyaransa, Mu'ayyad din ta karba ta bashi Nono, Allah ya sota da wuri tayi masa wanka yayi kashi ya bata jikinsa ta hada gaba daya tayi masa wanka kawai, yana gama sha ta ajiyewa Rufaida shi, kayan wankin dake kan kujera ta shiga kwashe tana watsa su a kan gadon dakinta, ta tattare Gadon da sauran tarkacen Mu'ayyad ta kai Store.

Sama sama ta share palour ta kunna turaren wuta ganin sha biyu saura kwata yasa ta kwaso kaya da diaper ta ajiyewa Rufaida tace ta canza masa ita kuma ta shige bandakin dake palour ta daurayeshi ta dauraye jikinta dan tasan zasu buqaci shiga yin Alwala dakinta kuwa baze shigu a yanzu ba dan gyaransa ze dauki lokaci.

Tana gama saka rigarta taji bugun qofa tasan baqin ne suka iso dan qarfe sha biyu daman aka ce zasu zo, ta goge fuskarta da soson powder ta fesa turare ta yafa mayafi, ita da kanta data kalli kanta seda taji wani iri yanda kasan wadda ta tashi daga bacci duk a firgice haka ta fita ta bude musu tana yiwa Rufaida datayi rashe rashe magana kan ta gyara.
Su biyu ne manya da tana ganinsu taga kamanninsu da Hajiya se wata da zasuyi Sa'anni da Khalifa daya kawo su.
Ta tarbe su da fara'a tayi musu iso cikin palour suka zauna, seda ta gabatar musu da Ruwa da Lemo da Cake suka gaisa tana kallon yanda yarinyar ciki ke qarewa palour kallo duk seta tsargu taji wani iri, basu taba zuwa ba be kamata ace sunzo sun? tarar da wani abu ba daidai ba.

Sun jima sosai a gidan har seda Khalil ya dawo sunci Alalen suna ta santinsa da zasu tafi ta juye musu ragowar da tarin tsarabar data hado musu cikin kayayyakin data samu na barkar Mu'ayyad ta hada musu da turaren wuta, Khalil ne ya tafi kaisu suna fita ta goye Mu'ayyad ta shiga gyaran gidan dan ta tabbata mita ce zata sha ta kamar ba gobe idan ya shiga dakin ya tarar dashi yanda ya barshi da safe.

Allah ya taimaketa har ta gama ta sake wanka tayiwa Mu'ayyad sannan ya dawo gidan lokacin har anyi sallar Isha. Wanka ya farayi shima ta kawo masa Taliyar data dafa ta dumama masa stew yace ya qoshi yaci abinci a gidan Hajiya.
"Anty Umma tace ya kamata a samo miki me aiki wai taga kamar aiki yayi miki yawa sannan ga raino" Khalil ya fada yana kallon Umaimah dake shayar da Mu'ayyad, ta yamutsa fuska a ranta tace
"Tsabar munafunci ko ina ruwanta oho" a fili kuwa tace

"Ni na gaya mata ina da buqatar me aiki ko nace na gaji, kaima sonbata bakinka ne kawai amma sau nawa zna gaya maka bana son wata yar aiki indai ba kuma so suke su kawo mun wadda zata kwacemun miji ba"

"Kin yarda wata zata iya kwace miki mijin kenan?" Ya tambayeta yana dage gira ta harareshi tareda tura baki tace
"Sedai uwar yarinya ta haifi wata kuwa"

"Toh nidai na gaya miki ne dan kar kiga me aiki daga sama dan ta rigada tayiwa Hajiya magana ma kuma an kira wata da take kawo su tace a bata kwana biyu, karki damu na wassafa musu irin wadda za'a kawo baqa mummuna da bazan iya kallon fuskarta" Khalil ya fada cikin sigar tsokana, bata kulashi ba se qananan mitocinta ta dura a ranta ko ta ayyana ko uwar wa tazo mata gida seta koreta dan ita bata ce musu tana da buqatar mataimaki ba balle a mata iyayi.

Ashe abinda ya faru tun a hanyar mayar dasu gidan Anty Umma da sam bata gani tayi shiru tayiwa Khalil maganar hargitsewar gidan nasu da rashin kintsin ita kanta Umaimar.
"Ita wannan matar taka daga haihuwa daya ji yanda ta fita hayyacinta se kace me yaya goma gida duk ya qazance kodai daman kazamace se yanzu ne abin ya fito fili? To koma dai yaya ne ka nema mata me aiki ta ringa kama mata wasu ayyukan dan idan ba haka na wannan ta qara tara yara bamu san yanda zata zama ba kuma" Anty Umma ta fada, Khalil yayi shiru a ransa yana juya maganarta, shikansa halin qazantar da Umaimah ta koya yaja damunsa danshi Allah yayi shi sam baya son datti ko kadan ita kuwa yanzu ta daura abota da qazantar da take fakewa da sunan jego.

Gida se yayi kamar anyi yaqi a ciki sannan zata gyara, kwalliyar safe kuwa ya manta yaushe rabon daya fita ya barta tsaf se an auna arziqi ne ze dawo ya tarar tayi wankan tayi kwalliya kayan wanki kuwa na Mu'ayyad se yayi kamar me sannan zata wanke abubuwan dai gasu nan kala kala se shegen chatting din da baze amfana mata komai ba ta tasa a gaba shi yasa koda suka isa gidan Hajiya Anty Umma tayi mata zancen a nemawa Umainah me aikin be musa ba dukda yana hango takurar da zasuyi saboda yanayin gidan amma in har zata ringa kintsa gidan yanda yake so zasuyi manaji na dan lokaci kafin ya samu yanda yake so ya canza musu muhalli wanda shine plan dinsa na gaba.

Kwana biyu a tsakani kuwa sega Habiba tareda wata yarinya da bazata wuci shekaru sha uku zuwa sha hudu ba da qullin kayanta Habiba take gaya mata Hajiya ce tace a kawo mata me aiki aikuwa ko ruwa bata basu sun sha ba tace su juya bata buqata ranta kamar ana hura mata wuta saboda ganin yarinyar fara kyakykyawar bafulatana dukda yarinya ce amma tana da kyau me daukar hankali.

Ta ringa surfa masifa ita kadai a gida koda Hajiya ta kirata akan me yasa tace a maida yarinya kai tsaye tace
"Nifa Hajiya ban buqaci wata me aiki babu abinda ya gagareni yi a gidan nan" ta bawa Hajiyar Amsa kanta tsaye, Hajiyar bata ja ba tace shikenan tunda tace haka sukayi sallama ta kashe. Koda Khalil ya dawo shima seda ta tasa masa wata mitar akan kawo me aikin ya mata banza har ta gaji tayi shiru dan kanta kafin ya kalleta yace

"Tunda kin kori me aiki ki tabbata karna sake ganin wani abu da ba daidai ba a gidannan, daka kan tsaftar jikinki zuwa ta cikin gida har abincina bana son a sake samun wani akasi idan ba haka ba dole ki nemi me aiki dan bazan iya rayuwa cikin qazabta ba"

"Amma dai ina iya qoqarina, kana kallon dai yaron nan idan ya tasa rigimarsa komai hanani yi yakeyi sedai na goyashi ni kuwa ina zan iya sunkuyon aiki dashi a baya, zanyi abinda zan iya kawai wanda be samu ba a ringa haquri kwana nawa ne ze girma komai ya dawo daidai" ta bashi amsa tana daddanna wayarta se ya ja tsaki dan kulata ma qara masa ciwonkai zatayi tunda ita duk maganar da aka fada tana da amsarta.

Hakan da sukayi yasa kwana biyu ta dage ta dena komawa bacci bayan Asuba, da tayi sallah zatayi qoqari tayi shara da mopping ta wanke Bandakuna tsaf ta gyara gida kafin ta hada musu abin kari har tayi wanka Mu'ayyad na tashi tayi masa shima idan Khalil ya fita seta samu ta lallabashi su koma baccin se ya zamana bata da lokacin hawa social media yanzu sosai da rana seda daddare a lokacin kuma suyi ta fada da Khalil da yake cewa tana shiga haqqinsa.

Bangaren tara wanki ne dai ta kasa denawa dan seta hada na kwana uku hudu taga kayan sa na tsakar gidan sun kusa qarewa sannan zata wanke su sedai ba'a kwashe cikakken wata ana haka ba ta sake komawa ruwa a cewarta ayyukan sunyi mata yawa wani lokacin ta zama se a hankali gidan ya fita a hayyacinsa musamman da Mu'ayyad ya fara rarrafe haka ze ta watsar da kaya wani lokacin ta ajiye ruwa ko lemo ya zubar akan carpet din haka gurin duk ze hadu ya ringa warin ruma ko kuma ta barshi babu Diaper duk ya fitsare palour abin na Umaimah dai se Addu'a kawai babu abinda ya dameta idan ta sake shi ya shiga sabgoginsa ita kuma zata harde a kujera ta hau chatting.

Tafiya ta tasowa Khalil zuwa Abuja wani aiki kuma ze dauke shi a qalla sati biyu zuwa sama ya san sarai zasu sha daga da ita akan tafiyar dan haka be sanar da ita ba seda ya rage sauran kwanaki biyu da daddare ya gaya mata, yanda ya daure fuska tamau yayi maganar ya saka ta kasa yi masa musun baza taje ba, a zuciyarta ta ringa juya yanda zata kaucewa tafiyar nan dan ita dagaske ta tsani binsa ko ina, sedai tasan idan tace kaitsaye bazataje ba rigima zasuyi dan haka tayi shiru har washe gari bata shirya komai ba, sanda ya gaji yayi mata maganar bega tana hada kaya ba bata ce masa komai ba ta shiga daki ta hada masa jakarsa tsaf tana cikin hada kayan ya shiga ya sameta, ya kalli akwatin tasa yace

"Ku ina naku kayan naga nawa kadai kike hadawa"
"Zan hada mana so nakeyi na gama da nakan" ta bashi amsa badan zatayin ba, Allah ya sani bata son binsa tafi so ya tafi ya barta a gida ta samu yancin yin yanda take so bayanan bare ya ringa damunta. Be sake kulata ba yayi shirin kwanciya yana sake jaddada mata da qarfe goma zasu tafi kuma karta kwashi kaya da yawa dan jirgi zasu bi yayi kwanciyarsa ya barta tana ganin yayi bacci kuwa ta gyara Mu'ayyad da shima yayi baccin ta kwantar dashi ta bar musu dakin.

Palour ta koma ta dauki wayarta ta hau WhatsApp taci sa'ar samun Rufaida Online nan take gaya mata har yanzu ta kasa samun mafita fa akan tafiyarsu gashi har gobe ne
"Kema dai son wahalar da kai kawai seda nace miki ki fito kawai kice masa ke bazakije ba dan ni haka mukayi da Abban Anam shikenan wai yayi zuciya be Sam cewa ze tafi wani guri dani ba niko ko a Jukina indai z ajiye mun komai ya tafi Allah ya dawo dashi lafiya" Rufaida ta fada, Umaimah taja numfashi kamar tana gabanta tace

"Baki san halinsa bane shi yasa nidai gara ki bani ko wata qaryarce da zanyi masa ya barni amma ba kai tsaye bace bazani ba"

"To ai kuwa se ki tashi ki hada kaya ku tafi tunda bazaki iya ce masa ba zaki ba, nikam bari naje na kwanta dan nima gobe zani Asibiti idan kun tafin to idan kuma kina nan ma hadu in Allah ya kaimu" daga nan sukayi sallama. A palour taci gaba da zama tana chatting da duba Ticktok da IG har bacci ya kwasheta seda Mu'ayyadya farka yana kuka Khalil ya fito ya tasheta yana mitar wannan dabi'ar data samu ta zaman kallo har tayo bacci a tuninsa, ta wuce ta koma dakin daman ko kayan jikinta bata samu canzawa ba taci gaba da bacci.

Da Asuba suka tashi da Alhinin rasuwar Mijin Anty Hafsa sanadiyyar ciwon ciki da yayi a cikin dare kafin Asuba rai yayi halinsa. Sosai suka kidima da jin wannan labari dole suka tafi gidan Jana'izar daga can bayan an gama Khalil yayi mata sallama ya wuce Abuja shi kadai ya barta nan wannan dalili ya rushe tafiyarsu tare sedai sati daya bayan rasuwar ya kirata akan ta shirya ze saka Khalifa ya siya musu Ticket din jirgi zata same shi a Lagos dan daga Abuja can suka wuce anyi canjin Manager bangarensu na kamfani dan haka an bashi ruqon kwarya kafin a gama tantance wanda za'a bawa be san tsahon lokacin da abin zero dauka ba kuma Allah ya sani baze iya ci gaba da zama shi kadai ba ba tareda ita a kusa dashi ba.

Duk da sanin yanayin Khalil din da irin halittarsa ta san baya iya jure dogon lokaci ba tareda ita ba amma tayi biris da maganarsa, daman tana gidan Anty Hafsa tun bayan rasuwar har akayi bakwai da aka watse Mama tace ta koma gidanta tace dan Allah ta barta ta zauna da Anty Hafsan kodan Halin da take ciki dakyar Maman ta barta shima saboda Khalil din baya gari dan haka koda yayi mata maganar bin nasa babu wanda ta gayawa har ana ya gobe ranar da yace zasu tafin tazo a ranar Taje gida dauko musu kaya ita da Mu'ayyad Khalilfa ya kirata akan zeyi booking musu ticket na qarfe nawa take so kai tsaye tace masa sunyi magana da Yayansa yace a barshi.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 32


Hankali kwance taci gaba da sabgoginta musamman da daman ya aiko mata da kudade masu nauyi da sunan ko zatayi wani shiri na tafiyar ta tasa su gaba siyi banza siyi wofi rantawa qawaye da zubin Adashin Maman Hauwa da Rufaida ta sakata shiga dole duk a haka ta rabar da kudin Khalil nacan tun yana zuba idon ganinsu har hankalinsa ya fara tashi musamman daya kira wayarta a kashe se ya maida akalar kiran ga Khalifa wanda nan take ya shaida masa yanda sukayi da Umaiman.

Sosai ran Khalil yayi baci lokacin daya kira Khalifa yake tambayarsa zancen tahowar tasu ya gaya masa ai tace sunyi magana an fasa. Bece masa komai ba ya kashe wayar, ya gwada wayar Umaimah yafi sau a qirga amma a kashe daya gaji ya sake kiran Khalifan yace yaje gidan ya gaya mata ta kunna wayar ko ya bata tasa suyi magana dukda a lokacin dare ya farayi haka ya tafi ya tararda gidan kulle da kwado abinda ya sake harzuqa Khalil din kenan ya qudurce aransa baze sake kiranta ba, duk ranar da ta kirashi da kanta a sannan zeji ba'asin abinda tayi masa.

Kamar wasa kuwa seda ya kwashi kwana uku a Lagos ba tareda sunyi magana da Umaimah ba, duk yanda yaso akan ya shareta karya kira wayarta ya kasa jin kuma har kwana ukun wayar a kashe se ya fara tunanin kodai ba lafiya ba amma idan da wani abu ya faru da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login