Showing 153001 words to 156000 words out of 429394 words

Chapter 52 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

972

tana juyawa waje. Dakinta ta koma ta zauna akan gado tana jiranta se gata ta shigo kamar munafuka ta samu can gefe ta rabe kai kace mabaraciya ce.

"Ki dawo nan ki zauna magana zamuyi dake" Maman ta fada tana nuna mata gefenta, seda ta daka mata tsawa sannan ta taso bata zauna kan gadon ba ta zauna a qasa, Mama ta hadiye abinda kw taso mata cikin muryar limana tace
"Ki fadamun meye matsalarki Umaimah"

Cikin rashin fahimta ta kalli Maman, Mama ta sake maimaita mata ta qara da cewa
"Ki fada mun idan akwai wata cutarwa da Khalil yakeyi miki a zaman auranku"

"Babu komai Mama, ni babu wani abu da yakeyi mun" ta bata amsa tana kallon qasa.
"Kin tabbatar babu wani abu a idan da akwai ki gaya mun kinsan dai babu abinda zaki boye mun ko?"

"Wallahi Mama babu abinda yakeyi mun, wani ya ce miki anayi mun wani abun ne?" Ta fada cikin sigar tambaya se Maman ta girgiza kai alamar Aa kafin tace

"Idan babu cutarwa a zaman ku me yasa kike gudun haihuwa dashi, ko yana da wani mugun hali da bamu sani ba da yasa baki so ki hada zuri'a dashi?"

Kamar tace tayi kuka sega hawaye sha sun fara zuba, seta daga mata hannu tace
"Ba kuka nace kiyi mun ki bude baki kiyi mun magana kinji koh"

"Ni Mama babu abinda yake dashi kawai haihuwar ce yanzu bana so. Gaba daya fa shekarar Mu'ayyad daya da wata biyu kuma ance inda ciki har wata uku fa Mama Kwanika fa kenan ni gaskiya bana so se kace wata Matar qauye kawai ina goyo se a ganni da ciki ai se mutane suyi mun dariya ma..." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta ya sakata yin shirun dole hawayenta kuma suka qara qarfi kamar an kunna Famfo.

Nunata Mama tayi da yatsa cikin bacin rai tace
"Ai daman idan bakiyi haka ba baki cika tantiriya mara mutunchi ba, yanzu abin naki har ya zarce kan mu mu ababen halitta kin koma kina fito da mahaliccinki ko, ubanki ne yake raba cikin balle kice saboda sanayya ce tasa ya baki?
Mata nawane suke neman Allah ya azurtasu da haihuwar, zasu iya sadaukar da komai nasu dan su samu abinda suma zasu kira Ya ko dan su amma ke ubangiji ya zabeki cikin Miliyoyi yayi miki baiwa shine kike kiran bakyaso bazaki iya haifarsa ba ko? Toh karki fasa, kiyi duk yanda kika ga dama da cikin idan Ajalinki ne kinga seki janyo shi kusa, a garin salwantar dashi seki salwantar da taki rayuwar ki bishi ku tafi tare.

Kuma idan Ubangiji ya qadarta zuwansa doron qasa ke kinyi kadan ki hana faruwar hakan, kina ji kina gani se ki mutu shi ya rayu shasha sha da baki san ciwon kanki ba. Ba'a haihuwa aka haifeki gashi nan tunda kikazo baki bar mutane sun huta ba kullum da kalar sabon jidalin da zaki tattarowa mutane. Ina jiye miki tsoron duniya Umaimah ki taka a sannu karki ga Allah ya ara miki dama kina yanda kika ga dama lokaci daya idan yaso ze iya canza komai ki dawo abin tausayi dan haka kibi a sannu ki kuma yiwa kanki guzurin Arziqi"

Tunda Maman ta fara magana take kuka kamar ranta ze fita, ita sam bata ga aibun abinda tayi ba amma shine har Mama zata ce tana fito na fito da ubangiji ita a wa? Amma a duba mata mana, yanzu da yaro daya ma yaya takeyi kullum cikin yi mata carin tana qazanta bata kula da yaron ake yi ballantana ace ta sake haihuwa nan kusa sun zamar mata jarirai biyu kenan. Kuma da zata ce zata mutu idan Allah yayi Haihuwa ce Ajalinta ai dole ta mutu kuma ko babu komai tayo shahada, duk baqaqen maganganu da bakin da suke mata a wanke mata su ta tafi lahira salin alin abinta.

Tsawar da Maman ta katsa mata akan ta fita ta bata guri ce ta dawo da ita hayyacinta ta miqe jiki na rawa ta bar dakin gaba daya ta tafi dakin Anty. A can ta dasa mata rashin mutunchin da bata samu damar yiwa Maman ba tana birgima tana kuka kamar yarinyar goye tana cewa ita dai a rabata da wannan cikin bazata iya ba.

Anty dai ganin abin tayi kamar ba'a hayyacinta take ba seta miqe ta tafi dakin Mama ta gaya mata, Umaimah na jiyo muryarsu a tsakar gida Antyn na ce mata tazo ta ga abinda takeyi anya lafiya tana jin motsinsu ta miqe da gudu ta afka dakin Anty ta banko qofa.
"Da ki tsaya mana da yau sena sauke miki duk wani iskanci da yake miki yawo akai yar banza me qeqashashshiyar zuciya kamar ta mutanen farko" ta fita ta bar Anty na jimami.

Yanzu Nuratu kuma tace me ita da nata cikin ya kai kusan wata shida yanzu idan ma befi ba gashi tana aiki ga hidimar gidan Amma daga ita har Mijinta farinciki suke da qaruwar da suka samu har ta yaye yarta Maman Mijin ta dauke mata ita kafin ta haihu se ita me zaman banza babu cas babu As ita ce zata ce bata son haihuwa kuma ta tabbatar da shi Khalil din baze ce baya so ba. "Kai wannan Umaimah dai jidalinta se Allah" ta fada a fili kafin ta koma tsakar gida taci gaba da ayyukanta.

Qarshe wunin daki tayi ranar dan abinci ma kamar wata yar birsin ta window ta saka Salma ta miqa mata shima seda taji Yunwa na neman ta halakata Anty ko duk uzurinta na cikin daki se haqura tayi dasu. Bayan an idar da sallar Magriba Ummu-salma tayi kiranta inji Abbansu. Badan tana jin tsoronsa ba da bazatajeba danta tabbayar da Mama ta gama karanta masa komai. Haka ta zura Hijabin Anty ta fito kanta a qasa ta wuce bangaren Abban.

A zaune ta tarar dasu, Abban, Mama, Khalil se Yaya Aminu. Ta samu can gefe daga bakin qofa ta zauna kafin tayi musu kudin goro gaba daya ta gaishe su.
"Yaya jikin naki?" Abba ya tambayeta cikin kulawa yana kallonka kafin ma ta amsa Mama tayi hanzarin cewa
"Alhaji tambayarta ma kakeyi yaya jikinta kamar ban sanar dakai abinda ta gama yi dazu ba?
Nida na zata tana zuwa zaka kwashe mun yar banza da Mari ka tumurmusata idan ka gama Yayanau ya dora nasa"

Seya yi murmushi yace
"Haba Mamansu ayi mata haquri badan ita ba ko dan abinda yake jikin nata" ya sake juyawa kan Umaimah yace
"Umaimah kiyi haquri kinji ko, ita haihuwa ce baiwace da kudi ko wata isa basa bawa mutum Allah ke bayarwa ga wanda yaso a sanda yaso. Karki sake furta bakyason kyautar da Allah yayi miki kije ki raine cikin ki ki haifa kiyi fatan Allah ya baki me Albarka wanda zeji qanki kinji ko?"

Seta daga masa kai hawaye nabin fuskarta. Nasiha ya sakeyi musu gaba daya Mama dai ta cika fam qiris take jira ta fashe, haka ya gama ya saka musu Albarka kafin yace su tashi su tafi dare yayi, Umaimah ce ta fara yin gada da sauri ta shige dakin Mama ta kwaso tarkacenta tana fitowa suka ci karo a bakin qofa. Aminu da Khalil na daga gefe suna magana Maman ta kalleta sama da qasa kafin ta juya kansu tace

"Ku zama shaida, idan har wani abu ya damu cikin jikin yarinyar nan bisa gangancinta ban yafe mata ba".
"Haba Mama haba Mama kalmar tayi tsauri da yawa kiyi haquri ko sauqaqa mata akwai fa qaddara zata iya fadawa akai" Aminu yayi saurin fada yana matsowa gaban Maman, seda ta harari Umaimah da ta daskare a gurin kafin ta sake kallonsa tace

"Na fika saninqaddara kuma nasan kuma san halin Umaimah sarai da kafaffiyar zuciyarta tunda ta furta bata so na san tabbas seta salwantar dashi toh taje na kuma fada idan har tayi sanadin cikin nan da kanta ban yafe mata ba" tana gama fada ta shige daki ta barsu a nan Umaimah ta fashe da kuka tana sakin kayan hannunta tace

"Tsine mun fa tayi Yaya" Aminu ya make bakinta yace
"A ina ta tsine mikin ke da bakinki babu abinda ya sani se janyo masifa, sharadi ta baki idan kuma kika saba kinji abinda ta fada. Ku wuce kuje zan lallabata idan ta huce ke kuma ki kula da abinda ta fada"

Tana Kuka Khalil ya kama hannunta suka fita shi gaba daya kansa ma ya rufe ya rasa bakin Magana, wannan tsakanin da Mama tayi mata ya masa dadi dan yasan tashin hankalin da ze sha akan cikin nan se Allah idan da ba'ayi haka ba amma kuma Maganar tata tayi tsauri da yawa.
Seda suka shiga mota aka fito da Mu'ayyad da yayi bacci Anty da kanta ta kawo shi, tana dakinta duk budurin da akayi dazu taqi fita ta gaji da lamarin Umaimah kullum babu sauqi se qarin ciwon kai.

A cikin gida kuwa bayan Aminu ya bi Mama cikin daki yake ce mata
"Haba Mama ya zaki fadi haka bayan kinsan halin Umaimah sarai duk abinda aka hanata shi tafi bada muhimmaci akai tayi, dan Allah ki janye maganarki, kin saka mata Albarka ma ya Allah ya cika ballantana kin fadi akasin haka akanta?"

"Aminu duk iskancin da Umaimah takeyi saboda tasan babu abinda za'a mata ne illah fada wanda baji takeyi ba, ai ba mahaukaciya bace ita taje tayi duk yanda taga shine daidai a gurinta nidai na gama magana ta" tana gama fada masa haka ta shige daki ta barshi.
Abba ma dai da Aminu yaje ya gaya masa yayi mata magana abi daya ta maimaita masa akan ba zata janye ba, kuma ta qara da in har ta cire cikin babu ita babu ita ta nemi wata uwar daban tunda bata isa ta gaya mata taji ba.

A bangaren Umaimah da Khalil dai ranar kwana tayi tana masa kuka shi kuma yana aikin bata haquri dan abin yazo da sauqin da beyi tsammani ba amma fafur taqi bawa Mu'ayyad Nono a daren seda safe daya dameta da kanta kuma ta jashi ta bashi bayan ta gama kuma ta fasa Kukan yanzu idan wani abu ya same shi fa ance idan yaro yasha ciki lalacewa yakeyi, dole ya kwasheta suka koma Asibiti, Likita ya tabbatar mata da babu komai taci gaba da shayar da shi har zuwa sanda taga zata Yaye shi, sannan ya rubuta mata magunguna da zata sha su qara taimaka mata, haka suka dawo gida a zuciyarta idan taji kamar tayi masa maganar cikin se ta tuna da kalaman Mama ta fasa sedai taci kuka ta godewa Allah yanzu kwanika zatayi? Tana zagin masu ciki da goyo ta ringa cewa sun fiya haihuwa kamar Awaki gashi yanzu itama ta zama Akuyar.

Dole ya dakko mata Habiba ta dawo gidan da zama dan wannan karon cikin nata me zafin laulayine, kusan kullum cikin jinya take ga quncindata sakawa zuciyarta dan har sannan ba wai ta gama aminta da tana son cikin bane shi yasa duk tabi ta lalace ta fita hayyacinta.

Khalil ya samu saqon Khausar da take zarginsa da yi mata zagon qasa ya kwace mata waya, ta sanar masa da cewar yaci nasara akanta wannan lokacin amma ya jirayi abinda ze biyo baya dan bazata saki ba kuma ya aika mata da layukanta.
Murmushi kawai yayi sanda yaga saqon ya saka lambar data turo a blacklist, ba ita ba Hadizar kanta yayi blocking number ta dan bayan faruwar wancan abin ta sake neman dawowa rayuwarsa tana kiransa da magiyar ya duba ya sama mata gurbi a rayuwarsa shi kuwa yanzu baya buqatar wata damuwa, shirye shiryen tafiyar da zasuyi ce a gabansa ga yanayin jikin Umaimah da yau lafiya gobe Asibiti duk hankalinsa akanta yake ga aikin ginin daya tattago dan tuni an Baje gidansu gaba daya Hajiya ta koma dakunan da yake ciki shida Khalifa a da an faro aikin ginin daga bangarenta dan so yakeyi idan Allah ya nufa a cikin shekara daya ya kammala ginin harda nasu bangaren su koma can.

A cikin wata biyu da suka biyo baya shirin tafiyarsu SouthAfrica ya tashi dan da maganar ta kwanta lokaci daya Babban Manager su ya kirashi akan ya fara shiri nan da sati daya zasu tafi, Kwangila ce suka samu daman kuma se ta nemi ta lalace saboda Manyan companies da suka fi nasu sun nemi su karbe da Allah kuma ya nufa ta tabbata tasu. Kwangila ce babba da suke saka ran jan manyan kudade idan ta kammala.

Tafiyarsu da Umaimah bazata yuwu ba saboda yanayin jikinta da yaqi dadi dole ya yanke shawarar ta koma gida kawai dan hakan zefi samun nutsuwa idan yaso zeyi qoqarin yaga yana samun damar zuwa duba su dan a qalla aikin da zasu je ze dauke su kusan wata shida ko sama da haka, duk idan ya gama da bangarensa na zane zane ze iya dawowa, amma dole yana da buqatar tsayawa dan tabbatar da duk abinda ya zana haka aka aiwatar dashi.

Yana ta shirin tafiya gaba daya yana cikin damuwar yanda ze tafi yayi watanni ba tareda iyalinsa ba sedai sam bega wata damuwa a tattare da Unaimah ba dan ita murnar komawa gida ma takeyi dan tuntuni taso Mama ta hana, shiyasa ma ta yaye Mu'ayyad, idan ya tafi Habiba zata wuce dashi gidan Hajiya ita kuma ta koma gidansu.

"Nikam naga murna kikeyi zan tafi na barku me yasa Umaimah" Khalil ya fada yana kallonta, Umaimah ta muskuta daga kwancen da take, cikin ta ya fito dan yana cikin wata na shida ne ta kalle shi tace
"Haba dai wani irin murna kuma"
"Eh mana, jifa ko a jikinki sabgogonki kawai kikeyi ni kuwa duk na damu i can't imaging me living for 3 months without you" ya sake fada yana janyo ta jikinsa seta narke masa tana cewa

"Daurewa kawai nakeyi nima amma nasan zanyi missing naka sosai"
"Toh mu tafi tare kawai, kinga kin Yayae Mu'ayyad zasu tafi gurin Hajiya muyi tafiyarmu kawai hankalina zefi kwanciya" ya fada yana kissing wuyanta ta noqe tana cewa

"Nidai Aa, kana kallon dai kullum bani da lafiya tunda na samu cikin nan"
"Kiyi addu'a Allah ya raba ki dashi lafiya bana son irin maganganun da kikeyi bana jin dadi idan kina cewa bakya son cikina kamar bakya so nane".

Baki ta tunzura gaba tace
"Kaima dan baka san wahal????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
ar da ake sha bane shiyasa"
"Shikenan tunda bakya so daga wannan kin gama ni kuma se na nemo wadda zatayi ta haifamun wasu yaran ba tareda tayi qorafi ba dan ni ina so na tara yara da yawa" Khalil ya fada yana saka kansa a wuyanta da qarfi ta ture shi ta tashi zaune tana harararsa, dariya abin ya bashi har ya kasa riqeta ai kuwa ta fasa masa kuka ta hau dukansa ganin abin nata da gaske ne ya saka ya riqeta yana rada mata magana a kunne daga nan labari ya canza.

Da yamma suka fita sukayi shopping sosai na kayayyakin buqatarta da wanda Mu'ayyad ze tafi dasu gidan hajiya, bayan sun gama suka biya gidan Maman Asad, Dambun Nama, kilishi, soyayyar Miya, yaji ja dana daddawa ga cake da cincin haka ta hada mata anyi packaging nasu tsaf yanda bazeyi masa wahalar dauka ba. Ita tayiwa Umaiman maganar ya kamata tayi masa dan a lissafinta ko gishiri batayi tunanin ya kamata ya tafi dashi ba suka karbo kayan a daren ya kai Habiba da Mu'ayyad gidan Hajiya kuma yayi mata sallama dan washe gari zasu tafi qarfe biyu na rana.

A daren ta tayashi ya hada kayansa tsaf itama ta hada nata. sunyi kwanan farinciki da soyayya me tsayawa a rai washe gari qarfe goma suka kulle gidan. Khalifa ne yazo ya dauke su, seda ya fara sauketa a gida yayiwa su Mama sallama kafin suka fito ta rako shi seda taga tabbacin tafiyar ze yi sannan zuciyarta ta karaya ta saka masa Kuka, Khalil da daman dauriya kawai yakeyi amma shi yasan ze azabtu ba kadan ba a wannan tafiyar ya rungumeta a jikinsa yana rarrashi ji yake kamar shima yayi kukan ko zeji sanyi a ransa.
Seda yayi dagaske tareda yi mata qaryar bayan wata daya ze dawo sannan ya samu ta haqura ya lallabata ya tafi dan Abokanan tafiyarsa suna ta yi masa waya.

"Kamar gaske, wanda be san halinki ba Umaimah kin sha dashi" Yaya Nuratu da suka tarar a gidan ta fada, Umaimah ta balla mata harara bata kulata bata shige cikin daki ta kwanta kewar Mijinta na damunta.

Bayan wata daya

Umaimah na kwance a qasan Dakin Anty duk maganar da taketa faman yi mata akan kwanciyar qasan taqi tashi, tace mata sanyi ze kamata tace ai sanyin take bi daman har ta gaji da magana ta qyaleta. Wayarta ce a hannunta tana dannanwa, basu dade da gama magana da Khalil ba dukda daman kusan kullum cikin waya suke, daya samu sarari z kirata Audio call ko Video call wani yammatanci sukeji haka zasuyi musayar kalaman soyayya masu tsuma zuciya a cewarsa ji yake yi kamar yayi tsuntsuwa ya dawo gida amma babu dama.

Saqo a turo mata ta WhatsApp da wata sabuwar number, bata fiya amsa baqin lamba ba tun abinda ya faru tsakaninta da Maman Nihal wanda se daga baya ta samu cikakken bayani ashe ita din Asalinta yar me aikin gidansu Maman Nihal ta gaskiya ce. Sun tashi sa'anni dan haka suke shiri kuma itama tana matsayin me aikin Maman Nihal din ce a haka tayi aure ta tafi tareda Abun saboda sun shaqu, takai ta kawo ko fita qasar waje zatayi har bayan Abu tayi aure idan tana buqatar me kular mata da yara zata kirata haka kuma batayi mata iyaka da komai nata shine har ya bata damar yin basaja da sunanta a gari tana janyo rigima.

Fita tayi daga WhatsApp din ba tareda ta bude saqon ba ta tashi dakyar saboda fitsarin da taji ya dameta. Bayan tayi ta dawo ta dauki wayarta data tarar da Missed call biyu akai still number babu suna amma ta kira data tuna akwai wanda Rufaida tace zata hada ta dashi me siyar da kayan Jarirai ko shine ya tura mata da hotuna ta gani.

Sallama tayi daga daya bangaren wata mace ta amsa sukayi shiru gaba dayansu kafin cikin jin haushi Umaimah tace
"Naga Missed calls na kira kuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login