Showing 225001 words to 228000 words out of 429394 words

Chapter 76 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

966

da jiri suka ziyarci kwakwalwarta lokaci daya ta koma ta kwanta tana kwala ihu dan ji tayi kamar ganinya ya dauke saboda jiri ga wani ciwon Mara daya sake taso mata.

Nurse ce ta shigo dakin, take ta rufe Khalil da fada ta fita da gudu ta kira likita haka suka rufu kanta aka sake maida mata qarin ruwan tareda yi mata allurar bacci data rage radadi saboda yanda take ta faman juye juyen ciwo tana wayyo. Fada likita ya shiga yiwa Khalil, abin ya bashi haushi ya fice daga dakin ya barsu idan dai Umaimah ce gasu gata nan ai su da kansi zasu bada labarin halinta.

Gida ya wuce yana zuwa ya tarar da Hajiya cikin shirin sake komawa Asibiti, jiyan bata baro ba seda komai ya daidaita aka bawa Umaiman gado gurin daya na dare kafin Khalifa ya kaita gida ta bar Khalil ya kwana dan yace baza'a kira yan gidansu a cikin daren a tayar musu da hankali ba a musamman Mama bata da lafiya malaria ta kwantar da ita dan haka yace a bari seda safe tukunna a kirasu.

"Khalil, ya jikin nata ta farka kuwa?" Hajiya ta tsare shi da tambayoyi. A taqaice ya bata amsa ya wuce ciki dan gaba daya ji yake kamar kansa ze fashe tsabar bacci da ciwon da yake masa. Jin ana binsa a baya ya sakashi dakatawa ya juya, Hajiya ce se ya qarasa shiga parlour ta biyo ciki suka zauna akan kujera tana kallonsa tace
"Khalil meya hadaka da Yarinyar nan a wannan yanayin da take ciki zaka bigeta? Yaushe ma ka fara dukan Mace ban sani ba karfa giyar kudi tasa ka sauka daga layin da nasan ka aki Khalil?"

Dafe kansa yayi daya sara masa, shikam ya rasa wace irin makauniyar soyayya Hajiya takewa Umaimah da duk abinda ya hado da ita kawai bayanta take bi. Dakyar ya iya bude baki yace
"Haba Hajiya ko banida hankali dai ai kinsan bazan daki Umaimah ba, abune ya hadamu kuma taqi ta tsaya nayi mata bayani ta shiga haukanta da ta saba"

"Au mahaukaciya ma kake kiranta? Idan ma haukan ne ai a gidanka ta same shi kuma akanka takeyinsa" Hajiya ta fada tana harararsa seya bude baki kawai yana kallonta ya kasa cewa komai, gaskiya kuma son zuciyar Hajiya ya wuce misali, to ko Umaimah ta haifa bashi ba ai iyakarta kenan. Ganin idanma ya mata bayani ba fuskantar sa zatayi ba yasa ya miqe yana cewa
"Kishinta ne na banza ya tashi, kuma yarinyar da take haukan akanta ma data kwantar da hankalinta ba auranta zanyi ba" ya haye sama ya bar Hajiyar a zaune tana kallonsa.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda miqewa, tunda take da Khalil baya iya ko kallon cikin idonta ya gaya mata magana sedai ya sadda kai amma yau shine ya tashi ya barta a zaune lallai dole akwai wani abu sata kasa fahimta anan. Miqewa tayi a sanyaye ta wuce inda Khalifa yake jiranta. Sun tarar da Anty, Nuratu se Anty Laure tareda ita wanda Khalil ya kira ya sanar dasu. Umaiman na barci har sannan tambayar Hajiya suke abinda ya sameta a taqaice tace musu itama bata sani ba, ta shigo gurinta a gigice shikenan kuma jini ya balle mata kuma shima Mijin yace haka yazo ya tarar da ita a qoqarin yayi calming nata ne ta fita da gudu zuwa gurin Hajiyar.

"Ko gamo tayi? Amma haka kawai ace yarinya ta fito da gudu ai abin dubawa ne" Anty Laure ta fada tana hararar Hajiya qasa qasa dan tunda sukazo ta tarar da Umaiman ita kadai ranta ya baci. Ya za'ayi su kawo yarinya Asibiti subarta ita kadai tun jiyan ai se suyi waya gidansu a zo idan su bazasu iya zama da ita ba.
"Uhm" kawai Nuratu tace dan Maman Asad ta gaya mata yanda sukayi da Umaiman ta kuma tabbatar baze wuce akan zancen bane take tashin hankali, ai shikenan, idan ta kashe kanta a banza kowa ya huta.
Se bayan Azahar ta sake farkawa, kuka ta ringayi saboda radadin da hannayenta data yanke da kwalabe suke mata saboda Allurar da akayi mata ta saketa ta kuma ida dawowa hayyacinta gaba daya. Seda ta kwana biyu a Asibiti Anty Laure ce tareda ita take jinyarta kafin aka sallameta ta koma gida da gargadin karta kuskura ta ringa abinda ze jigata jikinta.

Da farko ma gida Anty Laurentace ko zasu wuce da ita Mama tace Aa ta barta ta koma dakinta idan yaso ta bita ta qara mata kwana biyu kafin a samo mata me aiki tunda iya hidimar aikin gida ce yara dabdalarsu duk a gurin Hajiya sukeyi bata da matsala dasu. haka kuwa akayi suka wuce gidan da Anty Laure washe gari se ga me aiki Nuratu ta kai mata yar uwar me aikintace tana jin dadin zama da ita sosai shiyasa tayi mata magana idan da wata tace akwai yar uwarta babbace a qalla zatayi shekara Arba'in Mininta ne ya rasu amma bata taba haihuwa ba daman tun tana Asibiti sukayi maganar ba'a yi shawara da ita ba dan sun san ma ba zata yarda ba se ganinta kawai tayi.

A cikin Bedrooms din qasa Umaiman ta koma daya ita da Anty Lauren saboda hawa da saukan baze yuwu ba saboda yanayin jikinta ga dakinta data rigada ta sauyawa Kamanni Khalil yasa an fitar da Furnitures din dukka dan ta lalata su, rabi Glass ne kuma ta rusa shi dole sedai a chanza wasu. Sanda Anty laure ta shiga dakin debo mata kayayyakinta riqe baki kawai tayi cikin mamaki ganin se Gado kawai ba komai a dakin kayan sawarwa ma an juye su akan gadon haka ta tsinto abinda zata iya ta sauka qasa tana wassafa abinda ya faru a gidan. Daman tun tana Asibiti ta lura sam da wata a qasa tsakaninta da Mijin nata.

Idan yazo baya wani dadewa yake tafiya kuma ko magana bata hadasu sedai su ya musu yame jiki ya qara gaba haka tunda suka dawo yau kwana hudu safe da yamma ze shiga ya gaidata ya duba Umaiman amma ko kallon arziqi taga baya hadasu. Ta qyaleta ne batayi mata magana ba taga iya gudun ruwansu amma har sukayi sati babu abinda ya canza Khalil dinma baya nan ya tafi Zamfara daze tafi ma ita yayiwa sallama ya bata kudi ya kuma gaya mata idan buqatar komawa Asibiti ta tashi Khalifa yana nan.
Hajiya ma kullum safe da yamma aeta shiga ta dubata su dan taba hira da Anty Lauren.

Kwana uku tafiyar da yayi ta dauke shi ya dawo cike da farin ciki saboda samun kiran da yayi daga Dr Sabitu akan gobe yaje da sauran takaddun kwangila ya saka masa hannu za'a tura masa da kudi ya fara aiki. Dawowar safe yayi, cikinfara'a ya shiga gidan, suka gaisa da sabuwar me aikin me suna Ruqayya ya tambayeta Anty Laure tace taje gida wai surukarta ce bata lafiya Maman Mijinta marigayi kuma jikin yayi tsanani shine taje dubata a Asibiti amma bazata jima ba.

Dakin da Umaimah ta koma ya tura a hankali ya shiga da sallama. Tana zaune ta jingina bayanta da Gado da waya a kunnenta tana magana ta dago tayi masa kallo daya ta mayar dakai taci gana da maganarta. Fuskarsa har sannan dauke da murmushi ya zauna a gefenta saboda tsokana harda kai hannu ya shafi gefen fuskarta. Yayi missing dinta sosai amma nisantar ta da yayi shine maslaha hat zuwa sanda ze kammala abinda yake gabansa gashi kiwa komai yazo qarshe.

Yafi minti goma a zaune yana jiranta amma taqi kashe wayar, yi tayi tamkar ma bata san da wanzuwarsa a dakin ba seda ya gaji ya saka hannu ya zare wayar daga kunnenta ta juyo a fusace tace
"Malam meye haka? Kana da matsala dani ne da zaka shiga rayuwata ko yaya?"

"Yi haquri maida wuqar naga kamar baki san da zamana bane shiyasa ki bari mu gaisa se kici gaba da wayar taki ko" ya fada yana murmushi se kuwa ta galla masa harara ta miqe tana jan qwafa, miqewar yayi shima yana kama kafadunta ta baya ya rungumeta yana cewa
"Wai fushin ne har yanzu baki dena ba?"
"Wallahi Khalil ka fita a sabgata kafin nayi maka rashin mutunchi, badai aure kace zakayi ba? To mu zuba nidakai a gidan nan shege ka fasa" Umaimah ta fada a fusace tana fuzge jikinta se yayi saurin sakinta yana cewa
"Easy Ma, duk da kin kwantar da hankalinki zancen auran nan fa wasa ne. Da kin haqura dakaina zanyi miki bayanin komai amma kima shiga tashin hankali yanzu kalli abinda kika jawa kanki"

Kallonsa tayi da son jin qarin bayanin wasan da yace maganar auran. Khalil ya daga mata gira kafin yace
"Yes, wasa ne, idan kina so kiji komai kizo muje dakina nayi wanka na huta zan warware miki yanda abun yake". Numfashi ta sauke har sannan tana kallonsa, idan kuma wasa yake so ya qarayi da hankalinta fa? Zuciyarta ta raya mata.

"Muje" ya katse mata tunanin, se kuwa ta bishi kamar wata sokuwa seda sukaje gaban matakalar ta tsaya tana kallonsa tace
"Likita yace karna hau bene"
"Ohk" ya sakw fada kafin ya shiga nade hannun rigar jikinsa. Cak ya dagata cikin takatsantsan ya fara hawa saman da ita be direta ko ina ba se kan gadon dakinsa ya ajiyeta tareda saka mata pillow a bayanta yana mata murmushi ya wuce bandaki.

Tana jiyo qarar saukar ruwa alamar wanka yake ta dannawa Safina kira.
"Ki tsaya kiji abinda zw fada amma dukda haka bazamu fasa wannan plan dinba dan kin ganni ma na kusa layin nasu amma bari na shiga gidan Hadiza Sani na jira muji abinda zece miki" Safinan ta fada bayan data gaya mata yanda sukayi da Khalil. Sun gama tsarawa daman Safina zataje gidansu Zahran tayi tijara ta yanda da kansu zasu fasa bashi auran yar tasu tunda ita jikinta baze bari ta fita ba amma zata dakata taji rainin wayom da ze mata yanzu kafin su aiwatar da nufinsu.

Da kansa ya sauka qasa ya soyo kwai ya hada shayi kafin ya dawo dakin Umaimah data qagu da jira se tsaki takeyi. Dole ta sakata zama inuwa daya dashi dan bala'in haushinsa take ji. Da yayi mata tayin shayin ma harara ta maka masa yayi dariya ya shanye abinsa seda ya gama tas kafin ya dauko Laptop dinsa ya hawo kan gadon da take yana murmushi ya bude.

Wasu hotuna ya shiga bude mata, Taswirar gini ce kamar Kasuwa kamar kuma gidaje ita dai bata wani gane ba saboda yanayin ginin anyi shi rututu gasu nan in ma gidajene sunfi dari seta dago tana cewa
"Nifa ba wannan tasa na zauna jiranka ba tam" ta qarasa tana zumbura baki. Dariya yayi ya koma ta bayanta ya raba qafarsa ya zamana tana tsakiyarsa. Kwantar da fuskarsa yayi a gadon bayanta yace
"My troublesome lover" kafin ya kama hannunta biyu cikin nashi ya shiga labarta mata yanda ya hadu da Zahra har zuwa yarjejeniyar da sukayi da Mahaifinta zuwa kiran da yayi masa na yau ya qarashe da cewa
"Kinga daya saka mun hannu kudi sun shigo shikenan babu ni babu yarsa, daman na yarda ne saboda na samu Kwangilar tunda bayayin abu dan Allah kinga ai idanna yaudare shi nima banyi laifi ba dan Yarsa ba ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?type dina bace kuma ko aure zanyi babu abinda zanyi da sangartacviyar yarinya irinta. Sam bata da Class taya ya ma Mace daga ganin Namiji kawai kice kina sonsa sanna kinga irin rawar jiki da nacin da take mun kuwa? Nooo na raina ajinta bazan iya auranta ba".

Gaba daya surutun da yakewa Umaimah tamkar suna shiga ta kunnen dama ne suna bullewa ta hagu, banda ma ya raina mata wayo wato saboda yana neman abu a gurin Mahaifinta yasa ya yarda ze aureta yanzu so yake ta yarda cewar daya samu biyan buqata ze gujeta kenan shi Mahaifin nata sakaran inane da ze yarda haka ta faru? Ko kuwa ita yake so ya mayar sakarya ta yarda da qaryarsa sedai kawai taji ana matsa zata shigo da Amarya ko? To zatayi maganinsu daga shi har Uban Zahran, Kwangila ce ta hada kuna zata raba kowa ya kama gabansa yaje can ya nemawa yarsa data qi auruwa yake neman kai da ita wani Mijin badai Khalil ba.

Janye jikinta tayi daga ruqon da yayi mata Khalil ya kallonta yace
"Are you now happy? Kin yarda ba cin Amanarki nayi ba ko?"
Murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa tayi kafin tace
"Hajiya tace zatayi mun Danwake yu wa nakeji ko zaka duba idan an gama"
"Sure, kinsan kuwa ban shiga gurinta ba gaba daya hankalina yana kan nazo na wanke kaina a gurin Babbar Hajiyata, bari nayi maza na karbo miki kici nima kizo ki bani nawa danwaken kar ma kice mun Dr ya hana" ya qarasa yana miqewa tareda kashe mata ido daya ya fice daga dakin. Ta balcony dake saman taga fitarsa daga part dinsu kafin ta koma dakinsa tana tafiya a hankali dan idan tayi motsi da yawa har sannan Marar ta na mata ciwo.

Wayarsa daya manta akan Mirror ta dauka. Bata bata lokaci ba gurin nemo number Dr Sabitu ba tareda tunanin komai ba ta danna masa kira ta wayar Khalil din.
"Aa, My son badai har ka iso ba? Kasan itama mutuniyar ina gaya mata zaka zo gata can se fushi take ashe baka sanar mata yau zaka dawo ba" Dr Sabitu ya fada cikin maganarsa me sauri, Umaimah taja iska ta jiqa hunhunta kafintace

"Saboda uwarsa ce ita ko yaya da ze gaya mata ze dawo? Kai kuma tsohon banza me neman kai da yarsa wato ta gama yawon ta zubar dinta ta kasa auruwa shine kake so ka laqabawa Mijina ko to baka isa ba wallahi Mijina nawane kuma yafi qarfin wannan kucakar yar taka. Ka duba a gaba ka nemo mata me rangwamen hankali irin ta ka hadasu badai Khalil ba, kwangilar da kayi masa talala da ita ka riqe abarka ka cinye ka nemo mata Miji cikin abokanan ka masu budurwar zuciya sune zasuyi daidai da ita su rufa mata asiri kuma wallahi kaja mata kunne idan ta sake kiran Mijina a waya sena ci uwar ubanta, har cikin gidanka zanzo na zaneta wallahi" Taja dogon tsaki kafin ta kashe wayar ta juya zata fita kenan idonta ya sauka akan Laptop dinsa dake ajiye.

Komawa tayi ta dauka, computer ta karanta dan haka bata da matsala da ita shiga tayi ta goge hotunan daya nunamata dazuna aikin da duk wasu Documents da suka shafeshi folder gaba dayanta ta goge, takaddun dake cikin jakar laptop din ta ciro ta duba, paper work nr na aikin ba bata lokaci ta rabasu biyu dukda ta fahimci sune ainihin Original takaddun, yagawar bata mata ba ta shige toilet ta watsasu a Sink ta saki ruwa seda ta tabbatar da sun jiqe jagab kafin ta ja qofar ta rufe tayi ficewarta. A hankali ta ringa sauka daga saman harta isa qasa kai tsaye ta shige daki bayan ta kwalawa Rukayya kira tace mata zatayi bacci kar a dameta yan zuwa dubiya ta shige dakin ta murza muqulli seda ta kwanta akan gadon kafin gabanta ya fadi, dana sanin taba masa Laptop yazo mata data tuna wannan din data goge itace kamar backup dinsa na komai. Yanada wata da yake fita office da ita banda Desktop da yake aiki da ita acan wanann yana aje duk wasu muhimman abubuwa da yake gudun rasawa shi yasa da wuya yayi amfani da ita se buqatar haka ta taso kuma daya gama ze maida ita ma'ajiya yana bala'in kaffa kaffa da ita yanzu ya zatayi
"Aikin gama ya gama se ki jira hukunci kawai" zuciyarta ta ayyana mata dan haka taja bargo ta yi luf duk jikinta yayi sanyi dan ita da kanta ta tabbatar da yau ta tsallake limit.

KHALIL
A kitchen ya tarar da Hajiya tana jefawa Umaimah dan waken suka gaisa tana tambayarsa hanya seda suka dantaba hira kafin ya gaya mata abinda ya zo karba.
"Daman wanda ya shiga fadanka da Umaimah shine da jin kunya, gashinan na kusa qarasawa kaje idan an gama za'a kawo mata" Hajiya ta fada tana kama baki seya sosa kai yana murmushi yace
"Bari dai na jira Hajiya kinsan lallabata nake karna koma babu shi sabon balli ya tashi" sukayi dariya gaba daya. Seda Hajiya ta tsame dan wake ta zuba mata a kwano tareda sauran kayan hadin da aka yayyanka. A try ta dora masa da dan kwanon mai dana yaji ya dauka ya fita.

A palour ya ajiye ya shiga dakin nasa yana kiran sunanta. Ganin bata ciki ya sakashi tunanin ko bandaki ta shiga dan haka ya qarasa jin qofa yana cewa
"Ga danwaken an kawo Babe" ya juya gurin wayarsa dake qara alamar kira ya shigo. Anwar ne ya daga yana cewa
"Kana shiga rayuwata Anwar kiran me kuma kake mun yanzu bayan na gaya masa bazan zo office ba?"

"Khalil what have you done? Kana right senses dinka kuwa yanzu ka janyo mana Asara haba Khalil" Anwar ya fada cikin tashin hankali. Cikin rashin fahimtarsa Khalil yace
"Heye hey yi a hankali mana, me kake magana akai sam bangane ba me nayi wace Asara na janyo mana?"

"Dr Sabitu be kiraka ba? For Goodness sake taya ma zaka bari wayarka ta shiga hannunta? Yanzu ba iya wannan contract din mukayi loosing ba i don't think we are going to be able to get any government contract again dan wallahi Dr Sabitu ya wuce yanda kake tunani ko da yake you can tell, we are doomed Khalil Matarka ta gama damu" Anwar ya sake fada tamkar ze fashe masa da kuka. Qirjin Khalil ya buga dum jin ya ambaci matarsa me Umaimah kuma tayi?

Saurin zare wayar yayi daga kunnensa jin Anwar ya kashe se sannan yaga tarin missed calls daga Zahra sena Baban nata guda daya. Qofar bandakin ya shiga bugawa yana kiran sunan Umaimah jin shiru bata amsa ba ya saka ya bude, wayam babu kowa a ciki, takaddu ya hango cikin sink cikin sauri ya debosu tuni sun narke yana dagawa suna qarasa ratattakewa kamar wanda ya warke daga makanta haka ya shiga gwala ido yana kallonsu dan ya tabbatar da abinda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login