Showing 300001 words to 303000 words out of 429394 words

Chapter 101 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1024

yana nuna mata ledar magungunan dake kusa da ita. Miqewa tayi ta Kashe Ac da aka kunna a Falon ta sama data qasa ta sake zama tana cewa
"Ko wannan uban sanyin da kuke babalawa kanku ya isa ya sakar maka da ciwon qafa ai, ina Matar gidan da zata samu ruwan Zafi ta dan gargasa maka qafar ka shafa maganin in Allah ya yarda zatayi sauqi kafin goben tayi ayi hoton ko?"

"Ciwon ma ya lafa Hajiya yanzu zan tashi naje nayi wanka sena gasa da kaina" ya bata amsa yana yunqurawa cike da qarfin Hali dan ji yake kamar an qara dora masa duwatsu an danne qafar. Hajiya ta miqe tana cewa
"Zaka iya hawa bene kuwa Ka shiga can dakin ba nan Umaiman itama take yanzu ba?"
"Babu komai Hajiya zan iya kuma likita yace karna zauna na ringa motsa qafar sosai, bari nayi wankan kafin a kira Sallah zan shigo idan na dawo daga Masallaci"

"Shikenan Allah ya qara afuwa je kayi wankan" cewar Hajiya, Khalil ya fara takawa cikin qarfin hali amma kana kallonsa kasan yana jinjiki, ya fara hawa stairs din kenan aka bude qofar falo shida Hajiya dake tsaye har sannan tana jiran ya haye saman suka kalli me shigowar, Umaimah ce ta shigo da qaramar sallama ganin Hajiya tsaye yasa ta danyi turus se kuma ta kalli Khalo daya tsaya shima yana kallonta.
"Ashe bakya nan, to wannan jikin naki ma keda shi din ai duk masu neman taimako ne da se nace kije ki kamashi ya hau saman amma bari na turo masa Khalifa" tana gama fadar haka ta rabe Umaimah dake tsaye tana kallon Khalil ta fita.

Ajiyar zuciya Umaiman ta sauke a sanyaye tana ci gaba da kallonsa ganinya juta yaci gaba da qoqarin daga qafar yana hawa saman Khalifa ya shigo ya qarasa da sauri ya kamashi da yake shima jikin nasa irin na Khalil ne kusan daga shi ya ringayi se gashi ya haye dashi saman seda ya rakashi har bakin qofar bandakinsa ya shiga ze fita Khalil din yace ya jirashi ya nemi kan kujerar dake dakin ya zauna zuciyarsa fal cike da tausayin yayan nasa.

Umaimah kuwa gaba daya jikinta ne yayi sanyi yanda taga Khalil din na tafiya ya bala'in taba zuciyarta yanzu fa ita ce sila me yasa ba tayi tunani ba ta aikata yanzu idan ya rasa qafarsa gaba daya fa ya zatayi?
Dakinta ta wuce ta kullo qofa da muqulli, watsar da jakarta tayi dake cike da tarkacen abubuwandata karbo a gidan wani sabon Malami da Safinan ta sake kaita yau, a cewarta gara ayiwa aikin rubdugu dan a samu biyan buqata da gaggawa. Wayarta ta dauka ta shiga kiran Safinan, tana dagawa tace
"Safina na shiga uku karfa Malamin na ya gurgunta mun Miji kinga yanda Khalil ya koma kuwa a dare daya sefa an kama shi yake iya tafiya"

Tsaki Safina tayi tace
"Ban taba ganin mutum me garaje a duniya ba irinki Umaimah tukunna ma bake kika ce ayi masa abinda ze saka ya fasa tafiyar da yayi niyya ba? Da kinsan ma da zeyi tafiyar ne ba Malam din ne ya gano miki ba kuma dazu kike tabbatar mun da bayan kin koma jiya ya gaya miki da bakinsa zeyi tafiyar meye to abin tayar da hankali a ciki? Malam ya gaya miki aikin ko ba'a karya baqar qarinsa kwana uku ze karye da kansa amma in so kike ya dakatar bari na turo Miki lambarsa kawai ki kirashi da kanko kawai ki gaya masa dukka ayyukan ma da yayi miki ya karya kowa ya huta na gaji da shegun qorafinki da basa qarewa".

"Ba haka bane Safina wlh dan baki ganshi bane daman tunda aka fara ayyukan nan wlh ya fita a hayyacinsa sam bashi da nutsuwa kamar ba Khalil dina ba nifa gaskiya indai haka za'a ci gaba to gara a bari dan ba so nake Mijina ya zauce ba ana zaune lafiya ni aure nace a hanashi yi amma gaba daya ya samu se damalmala masa rayuwa yakeyi" Umaiman ta sake fada se Safina taja tsakin da yafi na farko tace
"Kanki ake ji, in kinga dama ki aikata saqonnin da muka karbo yanzu in kuma baki gani ba ki bari, sannan wannan na Gasashshen naman na gaya miki kiyi dan nayi jiya kuma naga Aikinsa amma in kinga har yanzu zuciyarki na kokonto to ki saki ki dauki qaddara kawai ki zauna da kishiya"

"Allah ya isa tsakanina dake kuma kishiya sedai ki ganta a gidanki banza muguwa kawai" Umaiman ta fada kafinta kashe wayarta ranta ya harzuqa da maganar Safinan ta qarshe. Idan zuciyarta ta karaya taga rashin kyautawa akan abinda takeyi seta tuna da cewar Khalil din shi ya jawa kansa koma menene daya ce zeyi mata kishiya.
Wanka ta shiga har sannan jikinta a sanyaye da yanayin Khalil din tana fitowa tayi sallah, kitchen ta wuce ta cire Kaza da tun da safe ta saka Ruqayya tayi mata Marinating dinta kafin ta tafi gida wai Mamanta aka kira akan bata da lafiya.

Hadata tayi irin hadin da Khalil din yafi so ta saka a Oven sannan ta dora masa ruwan shayi, seda ta juye ruwan a flask ta koma falo tayi Sallar Isha. Har kazar ta gasu ta fito da ita ta jera masa komai akan Dining. Ragowar tuwo ta dumama abinta taci ta sake neman guri a falon ta zauna tana jiran Khalil dinya dawo daga Masallaci amma har kusan qarfe goma be shigo ba zuciyarta ta kumbura iya wuya, tasan yana can gurin Hajiya suna qulla qulle amma duk suyi su gama ta tabbatar da ita ke da Nasara akan su. Ciccibawa tayi ta miqe tana shirin shigewa daki Khalil din ya shigo yana takawa a hankali kamar Wanda ya warke daga Paralysis.

KHALIL
Wanka yayi ya gasa qafar sosai da ruwan zafi ya sake Alwala kafin ya fito yana dafe bango Khalifa na ganinsa ya tashi da sauri ya taimaka masa ya zauna a gefen gado, Khalifan ya nunawa duk abinda yake da buqata ya dakko masa yanayi a zuciyarsa yana zagin Umaimah, yanzu a ace tana cikin gidan Mijinta na a halin buqatar taimako amma ko a jikinta, a ringa cewa bata da lafiya amma ai hakan be hanata tsinannen yawo ba tunda kullum seta fita kuma ita takr jan mota da kanta.

Tare suka sake sauka qasan, motsin da yaji a Kitchen ya tabbatar masa itace haka suka fita zuciyarsa babu dadi, yanda tayi data shigo kamar bataga Hajiya ba balle ta gaidata dukda Hajiyar tayi mata magana abin ya qona masa rai daman shi yasan ba zata kulashi ba. A masallacinma a zaune yayi sallah, Hankalin Baba Musa yayi bala'in tashi dayaga Khalil din fadi yakeyi
"Ibrahimu anya al'amarinka da lafiya kuwa ya za'ayi daga ciwon kai kuma se qafa ta riqe gaskiya ya kamata ka tashi a tsaye ka nemi magani wannan daga gani maqiya sun shammaceka sun maka bugun kwaf daya bari goben nan in Allah ya kaimu zan kira qanina a can qauye in gaya masa komai ya hado maka magani ya bayar a kawo dan aikinsa kenan karya sammu wannan maganin ciwon kan ma shi yake bani shi, yanzu baka ga wannan Yaron ba da da kuke zaune kai da kanka kana mun qorafin yanda yake tafiyar da Al'amuransa amna da muka dage da roqon Allah ba gashi komai ya daidaita ba? Mutanene babu Allah a ransu yanzu kyashi da hassada yayi yawa a zuciyar jama'a".

Shidai Khalil murmushi kawai yayi dan baze taba yarda da cewar wai Asiri wani yayi masa ba to meya hadashi da wanin da har zeyi masa Asiri ana zaune lafiya?. Daga masallacin bangaren Hajiya ya wuce, a can yaci abinci yasha maganin dan ya shafa na shafaqar tunda yayi wanka. Bayan ya gama Hajiya ta kalle shi tace
"Yanzu tafiya ba zata yuwu ba kenan Babana ga ciwo ya sako kai kuma bana zaton ka kira kawun naku ka sanar masa ko ka barsu suna ta shiri sun katse abubuwan da suke a gabansu" tana rufe baki wayar Khalil dake ajiye ta dauki qara ya dauka yana cewa

"Kinga Baba Abun ne yake kira" se ya daga ya saka a kunnensa da sallama. Fada Baba Abu ya shigayi masa bayan daya amsa sallamar ya shiga cewa
"Yanzu Ibrahim zamu yi doguwar tafiya gobe kasan kuma Asubanci zamuyi amma baka zo mun tattauna yanda za'a tsara tafiyar ba ko kuwa mu kake so mu biyoka tunda mu zaka je tambayowa auran"

"Aa ba haka bane Baba kayi haquri, yau din na fita da wuri ne na qarasa wasu ayyuka saboda jiya ban samu fita ba sannan kuma na dawo bana jin dadi daman yanzu muke maganar da Hajiya nace zan kiraka muji yanda za'ayi".

Sassauta fadan Baba Abu yayi saboda ko daga muryar Khalil din ya fahimci dagaske bashida lafiya yace
"Toh me kuma ya same ka?"
"Ciwon qafa ne Baba dakyar nake taka qafar wlh" ya bashi amsa se Baba Abu yace
"Subhanallahi badai ciwon nan namu na gado bane ya sarqafeka tundaga yanzu? Toh Allah ya taqaita ya rangwanta maka kaga kenan tafiya bazata yuwu dakai ba kenan"

"Toh da tunani nakeyi ma Baba ko zamu daga tafiyar zuwa idanna dan samu sauqi koda wani satin ne kona sama se muje" Khalil dinya fada se Baba Abu yayi saurin katse shi da cewa
"Toh kuwa sedai ka tafi ka nemowa kanka auran da kanka, seda duk muka dakatar da abubuwan da suke a gabanmu saboda kai baka daukar komai da muhimmanci zaka ce a daga wani satin Aa wata shekarar za'a daga ba sati ba, Malam ka turo mana da kudin Mai kawai tunda Alhaji Garba yace a motarsa za'ayi tafiyar dan cin banzar baze yi maka yawa ba mu biya maka sadaki sannan muyiwa kanmu kudin motar zuwa nema maka aure"

"Allah ya qara girma Baba zan tura yanzu harda wanda zaku sha ruwa a hanya ma duka" Khalil din ya fada yana murmushin rikicin Baba Abu, Hajiya dake sauraronsu dan a Speaker yasa wayar ta karba tana cewa
"Rabu dashi Abubakar banda ma kace zaku tafi taren ai daman ku kadai za kuje, badan abun yazo a qurarren lokaci ba daman ai kamata yayi ya fara zuwa ya gaida su kafin yace ze tura iyaye, amma tunda sun yarda da hakan ma babu laifi Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya ya kuma saka a qulla Alkhairi. Ga kayan Lefe nan uwar Azarbabi Jalilah ta gama hadawa idan zaku hada dashi ku tafi toh suna can gidanta yanzu se ta kai gidan Alhaji Garban a zuba a Mota kawai gobe ku dauki hanya"

"Aa wannan ta gaya mun ai har munyi magana da waliyyan yarinyar suka ce su basa karban wani lefe ya ajiye idan taje gidansa se ya bata to na gayawa Jalilan ai se ku barshi in dangin uwarta sunzo Biki a kai musu nan gidan Hajiua Hauwan ko tunda abune da akeyi ba ace a barshi ba, shi kuma ya samu man Tafarnuwa ya ringa shafawa qafar yana maganin sanyi se kuma ya rage zama cikin Ac nan tasu ta fama"

"In sha Allahu, Allah ya qara girma, Allah kuma ya tsare hanya ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" Hajiya ta sake fada kafin Khalil ya karbi wayar suka sakeyin magana, so yakeyi ya gaya masa zancen wata shida da yake so a saka amma yasan Baban yanzu ze sake birkicewa amma haka ya daure yace masa
"Baba nace idan sun tambayi lokaci asaka kamar wata shida haka"
"Idan kuma basu tambaya ba fa? Kaga ka fita a idona in bamu fasa zuwa ba kace ba Abubakar nake ba" Baba Abun ya fada ze Khalil ya fashe da dariya yace
"Allah ya huci zuciyar Babana"
"Yauwa naji Alert yanzun nan inba haka babu inda zamuje sedai kayi ta zama da matarka me motsi akai" Baba Abu ya sake fada daga nan sukayi sallama.

Dubu dari biyu ya turawa da Baba Abun daman yayi niyyar badawa kudin auran to sun biya masa dan haka ya maida musu sa sha Man dashi duk da yasan rigimar Baba Abu ce kuma daga qarshe dai in one way or the other se kudinsa sun sake dawowa. Hira sukaci gaba dayida Hajiya har qarfe goma kafin yayi mata sallama kamar karya tafi ya wuce bangarensu yana tafiya a hankali danya danji dadin Qafar bayandaya sha ya shafa maganin.

Seda gabansa ya fadi daya tararda ita a falon shi yanzu baya son abinda ze saka su zauna guri daya da Umaimah balle har magana ta hadosu, tunda ya kalleta sau daya ya yi qasa da kansa yaci gaba da tafiya a hankali, muryarta yaji abazata tana ce masa
"Yaya qafar?" Seya dakata a inda yake ya kalleta itama shi take kallo fuskarta babu yabo babu fallasa. Qasa qasa yace mata
"Da sauqi" yaci gaba da tafiyarsa se ya sake ji tace
"Ga abinci nan, Ruqayya bata nan Mamanta bata da lafiya taje gida Kaza na gasa mana se Tea".

Kallon Mamaki ya sake yi mata a zuciyarsa yana qoqarin gano shin wannan shiri ne takeyi na wani abun ko kuwa har zuciyarta da gaske take be gama Mamakin ba yaji tana cewa
"Nasan abubuwan da suka faru ban kyauta ba kayi haquri kuma da Safe zanje na bawa Hajiya Haquri itama sharrin shaidan ne".

Ikon Allah wai na kwance ya fadi to meya samu Umaimah haka amma daya tuna jiya taje gidansu seya ta'allaqa hakan da cewar Tirsasata Mama tayi data basu haqurin. Ajiyar zuciya ya sauke kafinya juya akalar tafiyar sa zuwa kan Dining din ya zauna dukda baya jin yunwa amma ze cine saboda samun daidaito a tsakaninsu, tunda har aka ci Sa'a aka tan kwarata kuma ta biyu ta bashi haquri harda yi masa girki yana saka ran komai zezo da sauqi in Allah ya yarda koda ace maganar aurance ta taso zebi ta hannun Maman ne kawai ita ta sanar mata yasan zata fi shi sanin ta hanyar da zata lallashi Umaimah.

Kwanon Kazar ya bude yaga ta yanki kusan rabi ragowar ta bar masa seya miqe ya wanke hannunsa a Sink ya zauna da bismillah ya fara cin Kazar bayan daya Hada Tea. Umaimah dake zaune tana kallonsa daga cikin Falon a fili tayi magana yanda baze jita ba tace
"Zaka gane kurenka Khalil tunda har ka shiga gonata".
Yana cin Naman wayarsa tayi qara ya daga ganin Anwar ke kiransa, speaker ya saka yana ci gaba da cin abincin dan ya saba yawanci a speaker yake amsa qaya shi bayan sun gaisa Anwar ya tambayeshi ya qafa kafin yace
"Na manta har muka rabu bamuyi maganar zuwa Jalingo gobe ba koda yake ga qafa kuma anya zata yuwu?"

Seda ya kalli bangaren da Umaimah take yaga hankalinta nakan Tv besan kunnuwanta na nan ta bazasu tana jiran taji dawa yake waya ba kafin yace
"Tafiyar nan an fasa babu ita Anwar se wani lokacin idan Allah ya kaimu"
"Toh, amma dai shikenan, Allah ya nuna mana lokacin yasa hakan shine mafi Alkhairi" Anwar da yayi niyyar yin magana ya fasa saboda tunawa da yayi da dabi'ar Khalil din kuma yaji maganar na dawo masa kar yaje ya kunno wutar da ba zata kasu ba. Sallama sukayi akan se gobe sa hadu a office idan yaji dadin qafarsa yaci gaba da cin Naman yana satar Kallonta be wani ci da yawa ba ya rufe ya wanke hannunsa ya koma cikin falon.

"Har ka cinye" ta fada tana kallonsa seya zauna yana cewa
"Aa kadan naci na rigada naci abinci gurin Hajiya, ko ajiye mun ragowar da safe se na qarasa".
Shiru sukayi na dan lokaci ya canza tashar labarai yana kallo yaji ta sake cewa
"Ka fasa tafiya goben kenan"
"Eh wlh saboda ciwon qafar nan bazan iya dogon zama a mota ba, daman wani aiki muka samu zamuje dubawa amma na basu uzuri idan naji sauqi se muje ko kuma Anwar da su Patrick suje kawai" ya bata amsa yana duba wayarsa da yaji saqo ya shigo, Humaira ce ta aiko masa da wani zazzafan Text na soyayya ya karanta ya sake karantawa ya tabbatar wannan aikin Unaizatu ne seya maida mata da martanin
"I love you, karkiyi bacci zan kiraki seki fadamun kalaman nan da bakinki bana son su a rubuce"
"Ni kashe wayat zanyi ma yanzu, i love you more Gud nyt" ta maida masa itama yana karantawa kuwa ya shiga kiranta amma a kashe kamar yanda yace din ya daga kai yana murmushi ze dauki remote karaf suka hada ido da Umaimah da tun fara dannan wayar tasa take kallonsa.

Duburburcewa yayi dan gaba daya ya manta da tana zaune a gun, ya saba zama a falonsa shi kadai shiyasa yanzu ma yaji kamar a can yake se ya shiga borin kunya dason kare kansa daga balahirar ta yace
"Wani abu na gani a Twitter ya bani dariya"
"Uhm" tace masa tana maida kanta kan tata wayar da suke chat da Safina tana gaya mata yaci naman, daman Yajin Maganin barbade kazar tayi dashi dan karma a samu akasi yace baze dan gwala da yaji ba dan haka yake wani lokacin.

Khalil kuwa satar kallonta ya ringayi ganin bata kulashi ba yasa ya shiga WhatsApp, saqon Anwar ya gani yana tambayarsa da gaske an fasa zuwa nan yayi masa bayanin Su Baba Abu zasuje
"I thought that bana so nayi subutar baki ko Sarautar tana kusa na tada Bomb shiyasa nayi shiru" Anwar ya tsokanesa, seya kalli Umaimah data dukufa tana danna waya kafin ya maida masa da cewa
"Aiko da sedai na taho gidanka na kwana dan tana kusa kuma yai kaga abin Allah har girki tayi mun alamun ta fara sakkowa kenan kafin azo ayi fadan qarshe"

Emojin dariya Anwar ya turo masa da cewar
"Ai ko fadan qarshe a kashe Boss, Ni'ima na nan tunda na gaya mata zaka qara aure wai jira kawai take ranar tazo ta qagu taji ana bada labarin Abinda Umaimah tayi ta ringa cewa ai ta santa matar Abokin Mijinta ce"
"Ni'imar nan taka is Sick Anwar, ka gaya mata babu abinda ze faru se Alkhairi jikina yana bani hakan"
"I pray so Bro, ka ci gaba da Addu'a Allah ya kawo komai cikin sauqi, bari naje na lallaba Baby na tayi bacci Bye" Anwar ya maido masa da Amsa. Murmushi Khalil yayi ya kashe

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login