Showing 198001 words to 201000 words out of 429394 words

Chapter 67 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1040

compound din da yayi qal Interlocks se daukar ido suke alamar sunsha shara da wanki ga wani daddadan qamshi turaren wuta da yake tashi kamar anyi barinsa a gurin. Da sallama ya tura qofar palour ya shiga, wani qamshi, sanyi, nutsuwa da ya rasa ta mecece suka bige shi lokaci daya, cikin seconds goma ya qarewa palour da babu kowa a ciki kallo. Gyaranda akayi masa is morethan perfect, yanda kasan babu wanda yake rayuwa a ciki saboda yanda komai ya zauna daidai a muhallindaya dace dashi haka ya fara jefa qafafunsa yana tafiya duk taku daya yana jin wata kewar gidanna kama shi, gaskiya masu magana sunyi gaskiya da suka ce no place like home.




Qofar dakinsa ya tura kai tsaye ya shiga da sallama a bakinsa, wani sabon qamshi na daban yayi masa maraba tareda fuskar kyakykyawar Diyarsa dake kwance akan gadon daya sha shimfida ta alfarma itama cikin irin shigar da yake so ya gani jikin yara kamar ta sanshi suna hada ido ta bangale masa bakinta da babu haqori ta qara qarfin gwalantoyin da takeyi daga kwancen. Be san sanda ya dire jakar hannunsa ya isa kan gadon ya dagata ba ya hadeta da qirjinsa yana kissing fuskarta ita kuwa se dariya take abinta.

Umaimah ta bude qofar bandakin da ta shiga tana hada masa ruwan wanka saboda Habiba ta kira ta gaya masa gashi nan a hanya ya baro gidan Hajiya. Daskarewa tayi daga bakin qofar, So, shauqi tareda kewarsa suka shiga shawagi da ita a sararin samaniyar qauna bata san yanda akayi ba se ganin kanta tayi a bayansa ba kuwa ta tsaya tunanin komai ba ta saka hannuwa biyu ta zagaye cikinsa dasu kafin ta dora kanta a bayansa se ji tayi hawaye suna bin kuncinta da ita kanta bata san na menene ba.

A bazata abun yazo masa dan sam beji fitowarta daga bandakin ba gaba daya hankalinsa nakan Yar Babyn tasa da yake jin qaunarta har qololuwa, da yanzu Umaimah ta salwantar masa da ita tab da kuwa ta cuce shi. Saukar hannun mutum kawai yaji a cikinsa se saukar abi me dumi da yatabbatar hawayene ya shiga ratsa jini da jijiyarsa har zuwa cikin bargonsa, sosai yayi ta maza ya dake ya kuma hana kansa juyowa dan yasan tarko ne, idan har ya bari tayi tasiri akansa shikenan duk wani shiri daya dawo dashi ya wargatse.

Hannu daya ya saka dayan na rungume da Bibi ya janye hannayen Umaimah data zagaye shi dasu ya fara takawa zuwa gana kujerar dake cikin dakin ya ajiye yarinyar ya shiga zame rigar coat din daya dora, hannunta ya sake ji a kafadarsa tana taya shi, kafin muryarta da tayi wani irin laushi da sanyi ta ratsa dodon kunnensa tana cewa
"Barka da zuwa Habibin Umaimah, banji shigowarka ba ina ciki ina hada maka ruwan wanka, u are highly welcome" ta qarasa cikin wani sauti daya sakashi saurin sakar mata rigar ta qarasa cireta kafin ta juyo ta shiga balle masa maballin farar yar cikin jikinsa suka shiga kallon juna ido cikin ido kowanne yana karantar tsantsar kewar sa cikin idon Dan uwansa, tana gama balle masa rigar be zata ba yajita cikin jikinsa gaba daya suka yi baya ya samu ya dafe kujerar gabansu tareda qanqameta yana qarewa fuskarta kallo data sha simple kwalliyar nan tata wato pawder da man lebe ta gyara kyawawan idanunta da kwalli da Mascara gashin idon sun qara tsaho da baqi.

Lumshe idonta tayi ta sake bude su akan sa kafin ta raba labbanta data pente da jan lipstick ta sake shafe su Lipbalm me maiqo se daukar ido sukeyi tayi kamar zatayi magana amma ba tace komai ba, Idan yace yace beji wani abu na yayi qary, wani sanyi yaji ya taso masa tun daga tafin qafa ya dire a kwakwalwarsa, wani irin kallo take masa na cikin ido dashi kadai yasan ma'anarsa kuma ji yakeyi tamkar ta saka muqulli tana bude duk wasu qofofin jikinsa da suka jima a rufe, numfashinta da yaji cikin nasa kafin ta kai ga aikata abinda ta niyyata zumbur ya tashi tareda ita a jikinsa, sauketa yayi a qasa kan qafafunta kafin ya juya ya shige bandaki yanajin yanda jikinsa yake harbawa ba tareda ya qarasa cire kayan jikinsa ba ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana gangarowa daga gashin kansa har zuwa qafafunsa.

Bazece ga iya adadadin mintinan daya kwashe a qasan ruwan ba, gajiya yayi dan a maimakon ya samu sauqin abinda yake ji se ya zamana tamkar ma yana qara iza wutar ne. Cikin ruwan data hada masa a bahon wankaya shiga bayan da ya cire jiqaqqun kayan jikinsa ya kwanta a ciki tareda rufe idonsa so yake ya tunano duk tarin laifukan da tayi masa ko zasu dishashe abinda yake bijiro masa akanta amma abin takaici ko daya yaqi zuwa, idan ma sunzo sam sun gagara bata masa rai ballantana har su gushe kaifin abinda yake ji qarshe dai yayi wanka ya dauro towel din data rataye masa ya fito.

UMAIMAH
Da kallo ta rakashi harya shiga ya kullo qofar kafin ta sauke ajiyar zuciya ta zauna kusada Bibi dake ta wulga idanu tana kallon fitilar dakin. Gaba daya jiki ta yayi mugun sanyin da batajin zata ko iya tafiya, abinda ta hango cikin idonsa ya sake sare mata guiwoyi, dagaske ne Khalil ya tsaneta ya zatayi da ranta?

Tana nan zaune cikin duniyar Lissafi har ya kwashe mintocinsa ya fito daure da towel a qugunsa, Kallo ta bishi dashi kamar wata tsohuwar mayya, ya wuceta ya dauki wayarsa dake kan gado kafin ya koma gaban mudubi yaja kura ya zauna bayan dayayi yan danne danne a wayar ya saka a speaker
"Kaje Ten to Ten ka karbo mun usually meal dina yanzu" ya fada kafin ya latse wayar ya janyo Mansa ya fara shafawa.

Hadiye abinda ya tsaya mata a wuya tayi ta tashi dakyar ta isa kusa dashi, ta cikin mudubin yake qare mata kallo, doguwar fitted gown din data saka ta Dark Orange din Lace tayi bala'in yi mata kyau ta fito da duk wani tudu da komadar jikinta daya qara cika dam kamar zata fashe, saurin dauke kansa yayi sanda ta iso ta karbi Man daya diba ta shiga shafa masa a banyansa, daga shi har itan ba zasu misalta yanda sukeji ba, Ta gaka shafa masa a bayan ya juyo tana fuskantarsa, hannu biyu ta saka taja shafa masa man A fuskarsa da tasa gyara saboda jiya yayi Aski cikin muryarta da tayi rauni kamar zatayi Kuka tace
"Nayi maka abinci, kuma naji kana cewa a kawo maka"

"Oh, thanks" ya fada yana miqewa saboda ya tabbata idan ta sake bude baki tayi magana cutarsa kawia zatayi. Wardrobe ya bude ya dauko Jallabiyya da boxer ya saka ya sake dawoa inda take tsaye ya dauki turare ya fesa kafin ya juya ya dauki Bibi data bingire da bacci ya fice daga dakin.

A kan Dan gadonta da ya gani a gefen kijera ya kwantar da ita tareda pecking goshinta. Kai tsaye kan Dining din ya wuce ya kalli wasu Luxury warmer data zuzuzuba abincin a ciki su kadai kyan su ya isa ya saka ka cin abinda yake ciki ko bakayi niyya ba. Zama yayi ya bude babbar ciki, Tuwon shinkafa ne fari so a ciki, ya waiwaya ya kalli Umaimah data biyo bayansa kamar mara gaskiya, da yar mutunchi suke tashi zeyi ya dagata yayi juyi da ita dan kamar ta shiga zuciyarsa, abinda yake muradi kenan yaci har mafarki yake ya samu tuwo dan tunda ya tafi ko a ido be ganshi ba, zuwan da yayi kwanaki ma zaman hotel ya qare harya tafi be ci ba.

Qaramin murmushi ya sakar mata, Umaimah ta sauke ajiyar zuciya har yana ganin yanda maqogaronta yayi sama da qasa kafin ta taho kamar wahainiya ta shiga bude masa sauran warmers din. Miya kala biyu tayi masa, Miyar Egusi dataji duk wani kalar Wasali da ake sakawa miya ga hadaddiyar Kuka wadda tayi digiri a London tasha zabi da suka dagargaje saboda yanda ta bata lokaci ta dafu.
Dayan kwanon Jellop din shinkafa ce itama dai se wanda ya gani ga wani Musulmin peppe meat tsabar qyallin da yake kamar zaka ga fuskarka a jiki. Se casserole data zuba hadin potatoe Salad dayan kuma ganyan lattece yasha garnishing se wani bowl me kyau data zuba Samosa da spring roll ga kuma Jug din Coconut drink dana Zobo se Jarkokin ruwa me sanyi har diga yakeyi

Duk yanda yaso ya daure seda ya kama hannunta na dama ya sumbata, qarshen abincin sa kenan ta hada masa su, ga Tuwo ga shinkafa ga nama.ga kayan fulawa. Kadan ta zuba masa kowanne a plate yayi bismilla ya shiga ci yana kallon fuskarta data marairaice kamar marainiyar Mage, tuwo ya gutsira ya nufi bakinta dashi, Allah sarki yanda take abu se yaji kamar zata bashi tausayi amma ya kanne haka suka shiga cin abincin yana ci yana bata har suka gama ba tareda wani yace qala ba.

Ita ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo ta goge gurin harda fesa freshner, a ransa yace
"Ikon Allah, su Umaimah course din tsafta aka yo kenan yana kallo ta ta shige daki babu dadewa ta fito ta zauna akan kujerar gefensa.
"Na same ku lafiya?" Ya fada yana chanza channel, da sauri ta amsa masa ya daga kai ya kalleta, yanda take muimui da baki alamar tana son yin magana se juya yatsunta take kamar me jin tsoron yayi bala'in sake kunna shi.

"Kaak...kayi haquri dan Allah" ta fada dakyar hawaye na kawowa idonta, banza ya mata yaci gaba da chanza channel din da yakeyi
"Dan Allah Khalil ka yafe mun, wallahi sharrin shaidan ne bazan sake ba" ta sake fada cikin muryar kuka"
juyowa yayi ya kalleta, a cikin idonta ya karanci laushin da tayi na gaske ne ya kuma tabbatar da wannan ladabin bana qarya bane da gaske takeyi amma dukda haka baze saki da sauri ba, haka nan baze fasa qudurinsa akanta ba.

Hannu ya miqa mata fuskarsa dauke da wani murmushi da kai tsaye bazata iya fassara ma'anarsa ba yace mata
"Zo nan, haka ake bawa Miji haquri a garinku" ya qarasa yana dorata a cinyarsa ya zura kansa cikin wuyanta yana shaqar qamshin turarenta da tun gamuwarsu ta dazu ya hautsina masa kwakwalwa. Baki ta buse da niyyar sake magana yayi saurin rufe mata da nashi, daga nan labari ya canza, da farko cikin nutsuwa da soyayya ya ringa tafiyar da ita, seda tafiya tayi nisa ya birkice mata. Cikin wani irin fushi da sauri yake saraffata, tayi kuka tayi magiya Bibi kanta dake bacci seda ta farka ta shiga taya Mamanta kukan neman ceto amma be saurare su ba, seda dan kanshi yaji ya samu nutsuwar da yake da buqata kafin ta qyaleta, be ko bi takanta ba ya tsallake ta ya shiga dakinsa ya yiwo wanka ya dawo ya dauki yarinyar dake faman tsala kuka.

Ki tashi kiyi wanka ki karbeta" ya fada yana kallonta cikin sigar bada Umarni dole ta tattara jikinta da take ji kamar Buldozer tabi ta kanta, dakyar take iya daga qafarta ta kuma tabbatar da yaji mata ciwo ba kadan ba. Haka ta ringa gas jikinta tana kuka taredajera masa Allah ya isa a zuciya. Da tasan muguntar daya shirya mata kenan da bata shige masa ba. Ta gaya masa da wannan salon muguntar tasa gara ya saka bulala ya zane ta idan tayi masa laifi amma Allah yana kallo kuma seya saka mata.

Tsawar daya bugo mata akan tayi sauri ta fito ta karbeta ce ta sakata qarasa wankanba shiri ta fito, an kira sallar La'asar dan haka tana karbarta ya fice daga gidan yana sakin wani mugun murmushi na jin dadi, riba biyu, ya kwashi dadin da yaji kamar ze manta sannan ya horata yanda zataji a jikinta, Allah ya kaimu dare zata sake gane kurenta, tunda ita bata ji ta haka ze ladabtar da ita har se kunnenta ya ringa jin abinda yake gaya mata.

Da daddare daya kirata dakinsa kuka kawai ta saka masa dan ta tabbata ranta kuma yake nema, tun dazu da yammar zazzabi ya saukar mata, wani irin azaba takeji a qasanta dukda yanda ta shiga ruwan zafi ta gasa kanta dakyau amma kamar batayi ba ta tabbata hakan nada alaqa da uban maganin matsin da tayi amfani dashi bayan dinki da akayi mata na haihuwa. Daman seda Nuratu taja mata kunne sanda tace ta bata dan ita Allah ya taimake ta duk haihuwar da tayi bata samu qari ba shiyasa take yan gyare gyarenta amma Umaimah ga dinki ciki da waje ta nace seta bata,
"Jiki magayi" abinda ta fada kenan gashi kuwa tana gani. A daren nan haka Khalil ya sake moreta seda yayi bidirinsa tsaf ya gama kafin kuma ya fara jin tausayinta, haqoranta har haduwa suke saboda zafin zazzabi ya taimaka mata ya gasata sosai kukan ma ta denayi se ajiyar zuciya kafin ya hada mata tea me kauri tasha da maganin rage zugi daya siyo bayan daya fita sallar Magriba dan yasan zata buqace shi dole sannanta samu bacci ya dauke ta.

Da safe seda ya tsokaneta tana kwance yazo kamar ze shiga jikinta yanda ta zabura idonta ya fito seda ta bashi tausayi da dariya. Yanayin zafin jikin dayaqi sauka yasa dole sukaje Asibiti, dinki dai ya farke tas oho shi bema ji ba haka aka saka Umaimah a Theatre aka sake sabon dinki, bala'i dai ta ganshi muraran dan suna hanyar dawowa daga Asibitin kuka ta ringayi tana roqonsa ya maida ita gidansu. Da wannan Azabar data sha daga jiya zuwa yau ai gara zaman Cell din da tayi Aradun Allah shidai Khalil dariya kawai yakeyi a zuciyarsa dan ba wai iya hukuncinta kenan ba, ta gama wannan jinyar yana nan ze jijjigo mata gagarumar jinya ta gaske.

Seda Umaimah ta kwashe kusan sati hudu tana jinyar jikinta, Ummu-Salma ce ta dawo gidan tana taya ta da ayyuka saboda suna hutu sannan, a bangaren Khalil kuwa wani mugun tsoronsa ne ya darsu a ranta, duk abinda takeyi idan taji muryarsa se gabanta ya fadi ta fara tsuma musamman da ya samu sarar daure mata fuska a yanzu tun bayan daya gama dagargazarta ya dinke fuskarsa tsaf baya mata dariya, idan kaji muryarsa yana wasa to da Salma yake magana ko kuma ya dauki Bibi yana mata wasa ita kuwa tsakaninta dashi gaisuwa ce daman itama bata so din wata doguwar magana ta hadasu ballantana har a sake maimaita abinda ya faru.

Se a yanzu tayi nadama ta gaske ta kuma tsinewa shegiyar Khausar data ja mata, da bata shigo rayuwarta na da duk wadannan abubuwan basu faru ba. A haka aka ci gaba da gungura rayuwa, Umaimah ta canza lokaci daya tayi wani irin sanyi qalau. Gidansu me cike da soyayya da kwanciyar hankali ya dawo kamar wani gidan Makoko, babu wani karsashi a cikinsa idan kaji magana me qarfi Tv aka kunna ko Bibi ce take rigimarta, a bangaren Khalil kuwa be ma cika zaman gidan ba yanzu se dare. Daga office idan ya tashi ze wuce sabgoginsa dan yanzu Yana taba abubuaa da yawa ga kuma sabgar ginin gidansa da bayan dawowarsa seda yasa aka canza abubuwa da yawa saboda ba'ayi su yanda ya tsara ba, idanya koma gidan ma tsakanin su gaisuwa ce idan tayi abinci in yayi niyya yaci idanbega dama ba ya ciyo a gidan Hajiya haka suka kwashi kusan wata biyu a wannan yanayi.

Babu inda take zuwa gashi maqotan da suke gaisawar ma gaba daya Rufaida ta rabata dasu yanzu babu me shigowa gidanta se Kishiyar Maman Hauwa da ita kadai suka ci gaba da zumunchi se wata Amarya da aka kawo ita kuma ba mazauna bane Mijin a kudu yake aiki kuma tare suke tafiya haka zata wuni a gida sedai tayi ayyukanta dan yanzu tsafta kam babu kama qafar yaro, Khalil har gulmarta yake a zuciya daman ita tun Asali idan suna fada ko suka samu sabani tafi nutsuwa ta ringa abinda ya kamata yanzun ma haka ta kasance gidan nan ko yaushe qal ta saka turare wannan karon jego take na masu hankali daga ita har Bibi bazaka gansu da qazanta ba musamman da tayi sa'a yarinyar bata da rigima sam idanta qoshi zatayi wasanta daga nan tayi bacci gashi har sannan ba'a dawo da Mu'ayyad ba, tsabar tunani da zaman Kadaici ya saka depression ya nemi kamata.

Wani mugun ciwon kai tayi ranar Allah ya saka yana gida Weekend ne, tana cikin daki daman tun dare take fama da ciwon kan zuwa safiya ko motsin kirki bata iyayi saboda yanda takeji tamkar ana kwada mata guduma idan akan.

Kukan Bibi daya keta jiyowa ya saka shi shiga dakin nata dan a zatonsa ko ta shiga bamdaki ta barta ne sedai yanayindaya tarar da ita dole ya kwasheta suka tafi Asibi babu shiri hankali a matuqar tashe, seda tayi jinyar sati kafin aka sallameta yan gidansu dasu Hajiya gaba daya sun dauka ciki ne da ita musamman saboda muguwar ramar da tayi ta dashe kowanne bangare da suna mitar tunda Mijinta ya dawo ta yada kowa ba inda take zuwa se suka bata uzurin qila bata so a san daga komawa tayi ciki shiyasa ta guji kowa.

Randa aka sallameta suna komawa ta dasa masa kukan gida zata tafi, ba zata zauna ta mutu a banza ba tunda ya dena sonta ya sallameta kawai ai haquri babu irin wanda bata bashi ba idan baze yafe mata ba gara ya sauwaqe mata kawai ta kama gabanta akan baqin cikinsa ya kasheta. Isaraa tayi da surutan banza, dukda jikinta har sannan da saura haka ya jata sula shilla sama lulaye amma wannan karon ya banbanta da wancan, tafiya ce akayita ta nutsuwa suka goge duk wani Virus daya shiga memoryn su ya dawo sabo fil daga nan aka bude sabon babin soyayya da zaman lafiya tsakanin Sabuwar Umaimah da Khalil din nata.

BAYAN WANI LOKACI
Zama yayi dadi tsakanin Habibi Khalil da Habibtynsa Umaimah. Zama ne sukeyi irin wanda Khalil ya dade yana mafarki cikin zallar soyayya, zaman lagiya da tattalin Juna dan Umaiman tasa ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login