Showing 42001 words to 45000 words out of 429394 words

Chapter 15 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

962

RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
PAGE 13

Dole suka tattaro suka koma gida dan ita mara lafiyar ma Adaidaita ta tare zata hau seda Yaya Hajiyayye ta zageta tas kafin ta kama kanta ta rage zumudin murnar da takeyi. A hanya kuwa bakinta yaqi rufuwa, tambayarsu take dagaske ne gobe za'a kawo lefen? Kenan Khalil be fasa ba amma me yasa ya dena kiranta harta kwanta Asibiti beje babu wanda ya tankata se Anty ce me biye mata dan gaba daya haushi take bawa sauran.

A gidan ma haka suka hadu suka cashe mata, sakarya, mara aji sunkirata dashi yafi sau a qirga amma ko a jikinta ita kam hankalinta naga kiran wayar Khalil da tun dawowarsu take gwadawa amma ana gaya mata a kashe take amma taqi haqura.

"Wallahi tun wuri idan zakiyi hankali kiyi dan Maza ba'a yi musu wannan rawar jikin, kinja ajin ma ya Allah ya cika ballantana kin nuna masa duk duniya babu ya shi muna nan wata rana se kinji yace ze dakko wata idan kin nemi ba'asi yace saboda biyayyarki tayi yawa" Naziyya ta fada.

"In banda sharri Naziyya a ina aka taba cewa biyayyar mace tayi yawa? Yaya Hafsa ta fada tana dariya, Naziyya ta Harari Umaimah dake jifanta da wani kallo saboda ambaton auro mata wata da tayi tace

" Wallahi fa Yaya baki taba ji bane? Nan ga maqociyata nan da aka mata kishiya matar nan babu ta inda ta ragi bawan Allahn nan amma da yake Namiji Namiji ne se gashi wai zeyi aure saboda ita komai yace mata bata musawa zatayi wani lokacin ma bece tayi abuba zatayi shi kuma baya son haka, yafi so wani lokacin dai itama ta dan nuna nata ra'ayin bawai komai ya fada tace daidai bane, ai kuwa yanzu ya samo me ido a tsakiyar kai, tace tana jinsu wani lokacin zata cancareshi amma mutumin nan ko a jikinsa tunda shi abinda yasa ya aurota kenan toh balle Umaimah me suma akan Saurayi idan akayi auran kuma ai se mutuwa".

Qunquni ta shigayi qasa qasa tana cewa "idan gaba da mutuwa ce zanyi ina ruwan mutum, haka kawai baza'a fadi alkhairi akan abu ba ai se ayi shiru nidai babu ruwana baqin bakin mutum ya qare akansa" ta harare su kafin ta fice ta bar musu falon.

Tattauna abinda ya kamata ayi goben sukayi, abin yazo da sauqin musamman da akace mazane zasu kawo dan haka nan take Yaya hafsa ta kira mutuniyarta *Zuhree snacks bar* suka saka orders Meatpie, samosa da springrolls ta kuma tabbatar musu babu matsala zasu karbi order su goben akan lokaci.

Sosai Yaya Hafsa take jin dadin hulda da ita saboda cika alqawari, bayan dan karan dadi da snacks dinta suke dashi ga sauqin farashi duk wanda yaci se ya qara musamman tunda taje taga yanda takeyin aikinta komai a tsaftace shi yasa duk wata hidima data tashi da ake buqatar snacks bata sanya gurin nemo Zuhrii Snacks.
(Domin order snacks dinku na kowanne irin taro, koma haka kawai ki siya ki ajiye a fridge ki ringa soya abinki kina ci ku tuntubeta takan lambar waya 08146426724)

Se dab da magriba suka gama komai dan hatta da kajin da zasuyi pepper chicken an siya an gyara sukayi marinating nasu kafin aka saka a fridge akan Nuratu zata soyasu da safe kafin suzo a qarasa hadawa. Sun kira Aminu sun gaya masa shi kuma ya sanar da kawun nan su daya kamata su halarci karbar lefen yaceze kawo ruwa da lemo iya adadin da sukace za'a bayar Baba Abdullahi kuma yace ze bada tukuici danshima sun yanke abinda zasu bayar idan an kawo kayan.

Har Kowacce ta dauki jakarta zata wuce kenan Naziyya tace "Af an gama lissafin snacks banji an saka da cake ba, ko iya su Samosan za'a basu?"

"Ai kuwa dai nima shaf na manta, Hafsa ki sake kiranta ki gaya mata dashi kar lokaci ya qure" Hajiyayye ta fada, se Hafsan ta zaro wayarta tana cewa "Ina sane dashi, kunsan ko wanne abu yana da gwani, to wata sabuwar gwana na samo a fannin cake. Sunanta *Mcubes bakery, ranar da Baban Mimi ya shigo da wani loaf cake yace a gurinta akayo musu order tsabar dadi har takaddar na hada na cinye, yanzu kuwa cupcakes din yara na makaranta gurinta muke siyowa kar kuso kuji dadin sa koda yake zaku dandana kuji gobe idan an kawo, kai wannan mata ta iya cake, dadinsa baya faduwa se kawai idan kaci bakinka ya gaya maka"

"Gaskiya Yaya Hafsa ki fara sana'ar tallah irin wannan koda cake haka ni har kinsa na qagu naci naji yanda yake, bani numberta ma na ajiye a wayata saboda tsaro" Naziyyan ta sake fada tana zaro wayarta, se Hafsa ta shiga karanto mata tana cewa (08134606093 Mcubes bakery, cake dinda ba'a bawa yaro me qyuya)
"Bazaki gane bane Naziyya sekinci kinji tukunna keda bakya raina abin dadi ai inaga se sunusi ya saka miki waigi" suka kwasheda dariya gaba daya kafin sukayiwa Mama sallama kowa ta hau motarta tayi hanyar gida.

Hajiya Umaimah? kuwa can quryar daki ta shige ta haye gado, kamarbata jin abinda computer take fada nacewar wayar A Kashe take haka taci gaba da kira har seda aka kira sallar Magriba kafin nan ta haqura ta dauro Alwala tayi sallar,bayan ta idad addu'arta gaba daya akan Allah ya mallaka mata Khalil ce ya kuma saka ta ita kadai a zuciyarsa karya taba kallon wata mace da sunan so ko sha'awa bayan ita, bata tashi a gurin ba sedatayi sallar Isha'i hade da shafa'i da wutri kuma har sannan wayar Khalil dintana kashe abinda yasa jiki ta yayi mugun sanyi kenan.

Ta tuno da sanda za'a kawo lefen Nuratu Ango taDr Sagir dakansa ya kirata ya gaya mata cewar za'a kawo tun kafin ma ayo waya daga gidan su a fada za'a kawo din a lokacin har tana mata iskanci saboda gaba daya wayar da sukayi batafi ta minti daya ba yana gama fada mata saqonya kashe Umaiman ta samu nayi wai kamar Wanda za'ayiwa auran dole babu wani zumudi babu komai kawai wani 'Gobe za'a kawo kaya' ya kashe waya" ta fada tana kwaikwayon yanda Sagir din yayi magana, se gashi ita yau bata samu arziqin ma nata Mijin ya kira ya gaya mata ba. Koma dai yaya ne a yanzu babban abinda yake a gabanta shine tabbatuwar auranta da Khalil, dukda wani abu da ze faru ya faru daga baya kuma kawo lefen nan shine babban mataki na gaba da yake tabbatar da cewar maganar auransu tana nan daram.

KHALIL
Tun bayan da suka rabu da Hajiyarsa da kuma matsayar da ya barta akai ya koma gida gaba daya ya kasa sukuni, duk wata hanya da yake tunani zebi dan ya karkato da hankalin Hajiyar ta fahimci abinda yake nufi ya auna yaga bazata bulle ba musamman da ya zamana da zancen Badawiyya a ranta duk wani qoqari da zeyi na fasa auran Umaimah a gurinta zataga yayi hakane danya komawa Badawiyyan wadda sam shi idan badan Hajiyar ma ta tayar da zancen ba ya manta da ita.

Ganin tunani baze fishshe shi ba ga qarin faduwar gaba a duk sanda ya tuna kalaman Umaimah se ya zubar da komai ya kama Allah, Addu' aya dukufa yi babu dare babu rana akan neman zabin Allah.
Kwanaki hudu a tsakani bayan waccen maganar da sukayi sega kiran Hajiyar da rana yana office take sanar masa da cewar ya kawo kayan da suke gurinsa dan gobe za'a kai lefe. kasa ce mata komai yayi in banda "Toh" ya saka hannu biyu ya dafe kansa bayan daya kashe wayar, a duk kwanakin nan da ya tsananta addu'a tamkar ana sake saka masa Umaimah ne a cikin zuciyarsa.

Wani irin sonta da kewarta ce ta addabe shi, ba qaranar dauriya yayi ba da har ya kwashe kwanaki biyar din nan ba tareda ya nemeta ba amma idan ya tuna itama bata sake? kiranshi ba se jikinsa yayi sanyi dan besan ma'anar wannan shirun da tayi masa ba, ta haquran ne ko kuwa wani abun take shiryowa. Koma dai menene yanzu dai magana ta qare tunda yanzu lissafin sati uku akeyi ta zama matarsa.
A daren bayan ya tashi aiki ya hada dukka kayan da suke a gurinsa ya kai gidan babbar Yayarsu Maryam da suke kira da Ummi, yawanci dogayen rigunane da takalma se su agogo da sauran kayan kyalekyalen mata wanda yawancin? abuwan da idan ya gani yayi sha'awane yake siya ko ita Umaiman ta turo masa tace tana so,besan sun taru da yawa ba seda ya ringa zaqulosu shi kansa ya ri ga mamaki kayan. Sanin Halin Ummi da surutu ya saka ya rage wasu daga ciki musamman qananan kaya ya ajiye idan tazo gidan sa se ya bata kawai.

Washe garin da za'a kai lefen da sassafe ya tafi dutse duba wani site da suke aiki, tun yana hanya wayar sa take kukan rashi chaji dan haka yana isa ya kasheta gaba daya ya jona a chajin kafin shiga aiki dukda yaso ya kira Umaimah suyi magana tunda ita taqi kiransa amma ya bari zuwa dare idan nutsu sayi magana kafinya koma Kano.

Ya rigada ya yanke amfani da shawarar Mansur ta cewar? ya sameta suyi magana ta nutsuwa da ze shigar mata da hankali jikinta dan babu yanda za'ayi suyi aure ta tafi gidan sa da wannan tunanin nata na yin fito na fito da duk macen data shiga rayuwarsa, shi be shiryawa tashin hankali ba dan haka idan har taga zata zubar da makaman yaqin su yi qoqarin gina goben su fine, idan kuma hanyar data zaba ita take ganin me billewa a gareta toh tabbas sedai Hajiya tayi haquri, dan yana da inda ze kai maganar da ita kanta Hajiyan bazata tsalkake umarnin sa ba dole ta haqura ta barshi ya nemo wata da zasuyi aure su zauna cikin lumana ba tareda kullum ya fita yana dardar da faduwar gaba ba.

*********
An kawo lefe da yake sabgar maza ce bata mata ba qarfe sha daya har sun gama komai sun juya da tarin kayan tukuicin da akayi musu. Kaya kam se sambarka duk wanda ya gani se ya yaba abu ne sukayi shi cikin tsari. Basuyi qarya ba haka babu qaranta daidai rufin asirin yanda babu inda za'akai kayan a raina su dan gaba daya kayanta manyan suturune kuma kaloli masu kyau da tsari se tsokanarta sukeyi wai tayi goshi amma ita sam ba wannan ne damuwarta ba, rashin ji daga Khalil har zuwa wannan lokaci yafi komai daga mata hankali.

Da safen har ta quduri niyyar zuwa office dinsa taji ba'asin kashe wayar da yayi sedai wayar da sukayi da Rumasa'u ta hana ta zuwan, dukda haka bata haqura ba, idan har wunin yau ya qare Khalil be kirata duk inda yake seta nemo shi taji matsayar ta a gurinsa, shiyasa ma ta hada kayanta idan Yaya Hajiyayye ta tashi tafiya binta zatayi taje ta kasa ta tsare qofar gidan su ayi wacce za'ayi kawai.

Tana kwance a daki saboda gajiya da tsokanar da masu shigowa kallon lefe suke mata wayarta dake gefe ta dauki qara, tasan wanene saboda shi kadai ta sakawa wannan kidan, cike da doki da shauqi tareda kewar sa da duk suka taso mata lokaci daya ta daga wayar da sallama kamar wata ta Allah.

Daga dayan bangaren Khalil ya saki ajiyar zuciya saboda yanda muryarta ta ratsashi amma saboda karya bada kansa se yayi gyaran murya a dake ya amsa mata sallamar tareda dorawa da tambayarta ya take

"Ba lafiya ba Khalil, na kusa mutuwa da yanzu sedai kaji wani ya dauki wayar nan ba ni ba" ta qarasa tareda fashewa da kukan da tasan yana karya masa zuciya ai kuwa tayi nasara dan nan da nan ya rikice ya shiga lallashinta, batayi shiru ba seda tayi me isarta taji sanyi a ranta sannan ta fara magana cikin sheshsheqa

"Nifa ba dagaske nake ba duk abinda na fada maka wallahi bacin raine ya saka amma kayi fushi ka dena kirana idan na kiraka ma baka dauka ko naji wayar a kashe har kwanciya nayi a asibiti kwana uku ban mayi zaton zan rayu ba"

"To yanzu dai ai baki mutu ba koh gaki da sauranki" ya bata amsa, seta bata fuska kamar tana gabansa dan sam yanda yake magana ba irin yanda suka saba a baya bane da alama har yanzu da wani abun a ransa, be haqura gaba daya ba kenan.

"Haka ma zakace, da na mutun ai se kafi kowa shiga damuwa tunda kaine kayi silar mutuwata" ta fada tana tura baki, murmushin da beyi niyya ba yayi yace

"Ko a mafarki kikaga me kama dani ya cutar dake ki tabbata shedan ne yake so ya shiga tsakanin mu dan in har ina numfashi bazan taba bari wani abu mara kyau ya same ki ba".

Wani sanyi taji har ranta dan Khalil dinta ya fara dawowa, seta gyara kwanciya tace
"Nayi kewarka sosai, you have no idea yanda kwanakin nan suka kasance mun ba tareda kai ba, dagaske Khalil idan na rasa ka zan iya rasa raina...."

"Umaimah, rayuwa da mutuwa duk na Allah ne dan haka kik dena cewa idan babu ni bazaki rayu ba, kafin nan Umaimah ina son magana dake, ina so mu zauna akwai maganganun da nake so mu tattauna masu muhimmanci" Khalil ya katseta, daga yanda yayi maganar ta fahimci da gaske yake dan haka itama ta tattara nutsuwarta tace

"Daman yau zan biyo Maman Asad idan zata taho gida, da baka kirani da sedai kawai Hajiya taga baquwar da babu sanarwa kaga shikenan idan nazo se mu hadu a gidanta hakan yayi?"

"Yayi, yanzu zan taso daga Dutse, zuwa bayan sallar Isha idan Allah ya kaimu zan ganki" ya fada daga daya bangaren, jin yana qoqarin kashe wayar yasa Umaimah saurin tare shi da cewa

"Kashewa zakayi, bazaka bari muyi magana ba?"

"Umaimah na gaya miki zan hau hanya ne i see you in the evening alright?" Ya fada sounding pissed off

"Shikenan, Allah ya tsare hanya ya kawo ka lafiya" ta fada a sanyaye saboda yanayin da yayi maganar qarshen yasa taji babu dadi. Haka ta ajiye wayar amma ko babu komai kiran da yayi mata ta ji sanyi a ranta ta kuma tabbatar da sanin sa ake ci gaba da shirin auransu.

Tashi tayi ta bude wardrobe dinta ta shiga neman kayan da zata saka anjiman dan gaba daya dogayen rigunan material ta diba da hijabai tunda tayi shirin zuwa wasan kwaikwayo ne, yanzu kuwa da aka samu change of plan dole ta dibi kayan kwalliya.

Kala biyu masu kyau ta diba da mahadin su tana murmushi ta zuba a cikin jaka, koma wace magana ce tasan dai bazata wuce ta shirin biki da abinda zasuyi ba, ita kuwa bata da ra'ayin yin komai daze halarta ballantana yammata su gane mata shi.

Ganin Yaya Hajiyayye ta shantake ta azalzaleta akan ta tashi su tafi, qarshe da taga zata bata mata lokaci ma gaba tayi ta hau adaidaita dan tana so taje ta dan samar masa wani abin tabawa? ta kuma shirya a nutse kafin lokacin da zasu hadu.

Ana idar da sallar Magriba ta hau shiri dan tana zuwa me delivery ya kawo saqon cup cakes da Yaya Hajiyayyen tayo order daga *MCubes bakery* (08134606093) bayan data ci na dazu da safe ta gigice da dadi nan da nan ta saka order wa Baban Asad da yayi tafiya ze dawo washe gari da safe.

Umaimah na karba ta bude ta samu bowl me kyau ta zubawa Khalil, ga Pepper chicken da ta bata tayo musu gaba dashi ta dumama a microwave shima ta ajiye samman ta hada da ruwa da lemo masu sanyi komai yayi mata daidai ta shiga shirya kanta.
Doguwar rigar Atamfa ta saka A line data yi matuqar yi mata kyau ta kafa dauri a gaban goshi ita da kanta tayiwa kanta kyau, turarukan Yaya Hajiyayye sun ci qaniyarsu dan feshin banza ta fadi tayi musu bayanta gama ta shiga daukar hotuna tana canhar bata san an idar da sallah ba saboda tana fashin ta ne ita.

Sallamar me gadi ce ta katse mata daukar hoton, ta leqa suka gaisa yace tana da baqo a waje, seta dafe qirji shaf ta manta ta zare Sim din daga babbar waya ta saka a qarama dazu kafin ta fito daga gida ta maye shi da data Sim, fuskarta ta sake gyarawa ta fito, tana hangoshi ta narke fuska ta sake ragewa tafiyarta sauri kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta qarasa inda ya tsaya ya harde hannu biyu a qirji yana qare mata kallo.

Khalil
Tun fitowarta ya zuba mata ido yana jin yanda sonta yake qara huda zuciyarsa yana shiga, tayi masa kyau, yanda take qara narke fuska kamar wata qaramar yarinya ba qaramin tafiya yayi da shu ba har besan sandata qaraso ba seda ta tafa hannayenta a fuskarsa, a shagwabe tace

"Wannan kallon fa? Qiris ya rage ka saka na fadi".

Murmushinsa me kyau ya sakar mata kafin yace
"Kinyi kyau", fari tayi da ido itama tace
"Kaima kayi kyau" ta bashi amsa suka saki murmushi gaba daya kafin tayi gaba ya take mata baya zuwa inda kujeru suje ajiye a tsakar gidan.

"Bari na kawo maka ruwa" ta fada tana juyawa ya rakata da ido harta bacewa ganinsa a ransa yana hasaso irin asarar da zeyi idanya rasata, amma idanya tuno wannan dayan side dinnata gaba daya se yaji komai yana juya masa. Yana can tunani yaji qarar ajiye try akan table dake gabansu, ta bude ruwan ta tsiyaya a glass cup ta miqa masa ya karba da murmushu yace
"Thank you".

Seda ya shanye ruwan ya miqa mata ta qara masa ya shanye ya ajiye cup din yana kallonta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login