Showing 186001 words to 189000 words out of 429394 words

Chapter 63 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1034

da lafiyar abinda yake cikinta wanda a shegiyar qaryarta tace ya dena motsi, anan suka barta da Anty Abba da Baba Abdullahi se Maman Asad da itama ta bisu suka koma gida daman Mama bata jeba ragowar Drama se in ta koma gida za'a qarqareta.

A gidan Hajiyar su Khalil kuwa zaman kurame aka shigayi bayan ya ajiye su ya tafi, dakyar Hajiya ta iya bude baki tace
"Amma ban tana tsammamin ko a mafarki Umaimah zata aikata irin wannan abunba, ina mata kallon me hankali da tunani, wallahi idan ne ya gayamun wannan abun take yanke zan qaryata dukda a yanzun ma na tabbatar da bayin kanta bane, zugar wannan shaidaniyar yarinyar ce kuma Allah kadai yasan abubuwan data gaya mata harta yarda tayi hakan".

"Yanzu fisabilillahi hajiya koma me ta gaya mata ita Umaiman bata da hankali da A'ace tayi abu tayi? Me ya hana ita waccen din tayi da kanta ai saboda tasan illar abun se ita data fi kowa wauta babu tunani babu komai ta aikata. Kafin ta watsa a social media din ai mu ta fara aikowa har a wayarki ta turo mu muka saka Khalifa ya goge dan karki gani hankalinki ya tashi, a wauta da rashin tunaninta wannan abin ne ze saka Khalil ya fasa auranta kinga ai yanzu ko bashi da niyya ta saka shi dole ya aureta dan babu yanda za'ayi a tozartata saboda kuma ya qita dan wallahi dukda wannan abun da aka saka sukayi wasu se sun kalleta da abun, wasu ma cewa zasuyi qaryane anyi kawai dan a wanke ta" Anty Amina babbar yayarsu Khalil din ta fada a fusace se Jalilah tace

"Ai wlh Anty bakiga abin tausayi ba seda mukaje Asibiti dubata, sun dauki haqqin yarinyar nan kuma Allah ne kadai ze rama mata wallahi"

"Allah ya rufa asiri" Hajiya ta fada kafin ta tashi ta shige dakinta, har a sannan mamaki takeyi amma ita tayiwa Umaimah uzuri ta kuma dora laifi kacokan akan Khausar dan ita ta shirya komai.

HALIN KISHI

47


*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 47

KHALIL
Tun daga Nesa ya hango Hadizan tsaye da wani da be tabbatar da waye ba dan ya bashi baya. Ya samu guri ya ajiye motarsa daga dan nesa dasu kafin ya tako a qafa seda ya isa kusa dasu ya gane Musa Kallah ne. A mutunce suka sake gaisawa yana kallonsa yace
"Wato Khalil ka godewa Hadiza, badan tace ta yafe ba ina me tabbatar maka se mun daure matarka daurin da ze saka tayi hankali" se Khalil ya gimtse fuska yace

"Ban fahimta ba, da aka ce muku bata da hankaline ko yaya?"
"Idan ma tana dashi toh be kai yawan wanda ya kamata matured mutum irinta ya mallaka ba, any way Allah ya taimaketa dan da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba" Musa Kallah ya sake fada kafin ya juya kan Hadiza yace

"Kin daiji abinda na gaya miki, ki samu ki huta sosai ki kuma cire duk wata damuwa daga zuciyarki, if you need someone to talk to I'm always available for you and karki manta think about what we discussed ki kuma bani amsa da wurwuri dan bana son jira".

Kanta na qasa ta amsa masa da cewa
"In sha Allah Sir, na kuma gode kwarai Allah ya saka da alkhairi akan qoqarin da kayi mun na gode banida abinda zan saka maka dashi sedai naci gaba dayi maka addu'a Allah ya tsare gabanka da bayanka"

"Amin, amma kece kike da abida zaki biyani dashi kuwa Hadiza sedai idan kuma kai tsaye kina so kice nayi miki tsufa ne se na tattara na koma gurin tsohuwar Matata mu qarasa, bari naje, i have somethings to attended in the office se munyi magana kinji" Musa Kallah ya sake fada yana yar dariya kafin ya juya ya kalli Khalil daya cika yayi tam ya masa wani dan murmushi ya juya inda Driver sa yake jiransa.

Shiru yayi yana kallonta bayan da Musa Kallah ya bar gurin, har wani sama da qasa yaji numfashinsa yana yi masa saboda bacin rai kamar yabi shi ya shaqo wuyansa ya lallasa shi nan shi gani yakeyi ya zama wani Hero a gurinta ko? Kawai saboda yayi shishshigi daya barshi ai shi zeyi handling komai amma ya kwaso wasu qafafunsa kowa ya gayyatoshi ma oho.

"Na gaji da yawa Khalil, ko zaka bari idan ka shirya seka dawo dan naga yanzu kamar baka zo don muyi maganaba" Hadiza ta fada ba tareda ta kalleshi ba se ya sassauta fuskarsa yana qoqarin danne bacin ransa yace
"Amm nasan ba yanzu ne lokacin da ya kamata nazo ba amma na kasa samun nutsuwa ne Hadiza har yanzu ina kallon kaina a matsayin me laifi a gurinki. Nine silar duk abinda ya faru dake nina jawo miki dan Alllah...."

"Na gaya maka ka dena zargin kanka, kuma ko ba wannan ba su kansu wanda suka aikata mun laifin na yafe musu nace me yasa zaka ci gaba da damun kanka idan kuma wannan ne ya kawoka shima babh wata damuwa, zan iya shiga ciki?" Ta fada tana kallon cikin idonsa. Seya kasa ce mata komai, dukda bada fushi ko hayaniya tayi maganarta ba amma shi ya fahimci jin zafinsa a kalamanta.

Ganin bashi da niyyar sake cewa komai yasa ta fara tafiya yayi saurin dakatar da ita da cewa.
"Hadiza, ina roqon da ki bani dama ta biyu. Kuma a wannan karon da gaske nake yi idan kin Amince daganna zuwa qarshen satin nan a daura mana aure mu koma SA tare nasan a yanzu kina da buqatar kiyi nesa na dan wani lokaci kodan saboda nutsuwarki ta dawo".
Tsayawa tayi cak na kusan minti biyu kafin ta waiwayo fuskarta dauke da wani murmushi tace

" Thank you Khalil, idan da rabo wata rana ko a hanya zamu hadu mu gaisa amma daga yanzu bana buqatar ka sake takowa inda nake, ka dauka qaddara ce haduwarmu wadda ta rigada ta afku, ina kuma so kayi qoqarin manta wanzuwata a duniyarka gaba daya kamar yanda na dade da gogeka a tawa duniyar, ina yi maka fatan Alkhairi ina kuma yi maka fatan idan kana da Rabo Allah ya baka macen da zata kula da kai saboda kai mutumin kirki ne.
Tsakanin da akayi mana a Station bada matarka ne kadai ba harda kai, idan kuma kaci gaba da bibiyata" ta saki wani murmushi ta juya tana cewa
"Na barka lafiya".

Yanda kasan hoto haka ta barshi a gurin seda ya dena hangota gaba daya kafin ya iya jan qafafunsa yabar qofar gidan daman yasan da wahala, ba ita ba baya tunanin akwai macen da zata yarda ta rabe shi idan har tasan labarin ta'asar matar sa.

Kwana uku ya qara ya koma SA a lokacin an sallamo Umaimah daga Asibiti kuma har sannan magana bata shiga tsakaninsu ba. Sau daya yaje ya dubata a Asibitin se randa ze tafi daya koma shima bisa takurawar Hajiyarsa. Haushinta yakeji matuqa, dukda yanda ta koma kalar tausayi seka rantse daga sannan Ta shiryu amma shi ya tabbatar da na dan lokaci ne, idan har Umaiman daya sani ce ana nan saboda hali aka ce zanen dutse. Haka ya tattara ya koma yaci gaba da abinda yake a gabansa gaba daya ya watsar da wata Umaimah koda yake ai ita ya kamata ace ta nemeshi ta bashi haquri akan abinda ya faru kafin ya duba ya gani idan da yuwuwar katbar tuban nata.

Yanzu kammaluwar ginin gidansa daya dauko ne a gabansa, an kammala bangaren Hajiya har suna shirye shirye komawa ciki sannan a rushe daya bangaren dayake nasa danhar an shigo da qarin filin daya siya ciki. Da yaso ya dakatar da aikin zuwa wani lokaci amma a yanzu yana jin kawai ze ci gaba, idan har ya samu yanda yake so baze rufe shekarar nan ba tareda ya qara aure ba danya gaji da bala'in Umaimah, nema takeyi ta dora masa ciwon da bashi dasu.

UMAIMAH
Takunkumi Mama da Abba suka saka mata dan daman wayarta tunda Yaya Aminu ya karba ba'a maida mata ba a cewar Abba ma ta gama riqe waya tunda da ita take jaye jayen bala'i fada kuwa ta shashi da nasiha har seda taji ta tsani kanta ta tsani halinta. Babban abinda ya qara damunta yanda ta kasa samun fuska a gurin Khalil. Sau saya ya dubata a Asibiti se ranar da ze koma SA da safe Ya sake komawa shima bisa tursaswar Hajiya, da zuwansa kuma da tafiyarsa beyi minti goma ba. Magana daya ta shiga tsakaninsu ya sake maimaita mata duk abinda take da buqata ta nemi Khalifa Already daman ya biya kudin Antinatal dana haihuwa lokaci kawai ake jira sannan ya saka mata wasu kudi matsayin na siyayyar haihuwa.

Cikin kukan daya zo mata ta tsaya gabansa tana cewa "Dangirman Allah Khalil kayi haquri, wallahi....." Gani tayi ya juya ya fice daga dakin abinda ya hanata qarasa magiyar data debo kenan. Tana jiyo yanda su Anty suke masa fatan sauka lafiya da nasara akan abinda ya tafiyi yayi musu sallama ya fice daga gidan nan ta zube taci gaba da rusa kuka baji ba gani. A zatonta ai komai ya wuce tunda me afkuwa ta afku akan me ze dauki fushi da ita bayan duk ma abinda ta aikata sanadiyyar son da take masa ne da kishinsa ya janyo. Haka taci gaba da zama a gidan cikin takura da qunci, ga rashin waya ballantana ta samu ta kira Khalil din ta rarrashe shi, sau saya ta saci ta Anty ta kirashitunda yaji muryarta daga ranar kota kira baya dagawa, qarshema dena shiga tayi qilan ya tosheta ne.

A cikin haka wata rana Maman Asad tazo gidan, Umaimah na daki ta shiga ta sameta. Cikin tausayawa ta kalleta dan cikinta da ya ke wata tara yanzu harta haura EDD na daya dana biyu gaba daya ta fita hayyacinta baqiqqirin ga uwar rama saboda damuwar data saka a ra ta ta rashin magana da Khalil. Zama tayi a gefe ta kalleta tace
"Sannu Umaimah, se kizo daki ke kadai ko zauna kina faman tunani bakya ko tsoron wani ciwon ya kamaki ga tsohon ciki? Yanzu daman Anty take gaya mun abinci ma ba ci kikeyi ba, wani sa ilin yanda aka ajiye haka ake zuwa a dauka baki taba shi ba anya hakan da kika daukarwa kanki mafita ce?"

Kamar daman tana jira ta fashe mata da kuka tana cewa
"Toh daman waya damu ko jiyo ya kamani na mutu nayi rai duk damuqata ce ba taku ba ina ku kuna rayuwarku cikin walwala da farin ciki? Daga Abban har Mama babu wanda yake hade muku fuska koya hantare ku se nice ba'a tausayi ko duba halin da nake ciki ba'ayi ake mun abinda aka ga dama"

"Ai Umaimah duk abinda ya sameki ke kika jawa kanki, kuma ke ya kamata ki fara tausaya kanki. Ai baki duba halin da kice cikin ba ki ka dauko magana da yanzu badan Allah ya taqaita ba ai qila kina can kurkuku a kulle wayasan ranar fitowarki? Kuma har yanzun babu alamar kinyi nadama dan babu wanda kika nuna wa hakan ballan tana ki nemi afuwarsu su denadaure miki fuskar, ko kuwa zaman da kike a daki da qin cin abincin ne kike zaton ze saka su dakko su shiga harkarki? To idan ma dan haka ne gara tun wuri ki chanza tunani dan a banza zaki kashe kanki qarqari mu miki Addu'a idan mun tunaki" Maman Asad ta sake fada se kuwa Umaimah ta qara ware baki tana cewa

"Daman na sani duk ba qaunata kukeyi ba, fata ma kukeyi na mutu sabida na tsare muku wani abun sannan me qaunar tawa ma an shiga an fita an raba tsakanina dashi wallahi duk abinda mutum yayi shida Allah"
Dariya wauta da rashin hankalin Umaimah ya bawa Hajiyayye tana kallonta tace
"Halinki ne ba'a qauna bake ba, kuma shi me son naki da kike magana ke kika raba tsakaninku ai. Ke yanzu bakiji ko dar ba bakiyi tunanin mutunchinsa ba yanzu ace matarsa ce tayi abinda kikayi? Yanzu haka video ku yana nan yana zaga gari kowa yasan ta'asar da kika aikata dayawa kallon Mahaukaciya ma suke miki saboda kishi kin zubarwa kanki da Mijinki mutunchi ta ina kike tsammanin ze sake bi ta kanki? Ai wallahi kin wa kanki wauta Umaimag kuma kin barar da kanki a gurin Khalil na tabbatar yanzu a kaso dari babu ko Ashirin na So da girman da yake baki dan kin nuna masa baki san darajar kanki ba.

Nidai shawarar da zan baki ki maida hankalinki jikinki ki, ki ringa fita kina motsa jiki ki samu ku rabu da cikin jikinki lafiya kafin ki fara yaqin maido da kanki a gurin Khalil dan dai a yanzu nida ke munsan bakya gabansa" tana kaiwa nan ta fice ta bar Umaimah cikin tunani da neman mafita.

Kwana hudu da zuwan Maman Asad gidan ta tashi da naquda, guraren qarfe goma sukaje Asibiti cikin ikon Allah kafin sha biyun rana ta haifo kyakykyawar yarta itama me kama da Khalil. Seda ta uku a Asibiti saboda jini daya balle mata bayan haihuwar basu dukda komai ya daidaita suka qi sallamarta a cewarsu se sun tabbatar da lafiyarta saboda gudun kar wani abu ya sake tasowa bayan sun koma gida haka yan barka da dubiya suka ringa zarya a Asibitin daga bagaren ta zuwa na Khalil da har yanzu suke cike da jin zafin Umaiman Hajiya ce kadai take rawar jiki da ita dan kullum setaje Asibitin har aka sallame ta da ita suka koma gida ga tarin kayan barka data kawo dukda Khalil dinya gaya mata wannan karon ya bawa Umaiman Kudi ta siyi abubuwan da take buqata amma seda ta hado nata.

Fitowarta kenan daga wanka ta daura Zani sannan ta lullubo jikinta qaton towel, ta zaune a bakin Gado tana jin yanda jikinta daya daddaure yake saki, tunda ta haihu bata samu wanka me kyau ba se yau da safen saboda zaman Asibiti, jiya kuma da suka dawo dare yayi dan haka suka bari se yanzu da safe Anty Laure tayi mata wanka gangariya ta zane mata jiki da darbejiya kuma taji dadinhakan. Nuratu ta shiga dakin sabe da jaririyarta Aidah me kimanin watanni biyu ta miqawa Umaiman wayar hannunta tana cewa
"Gashi za'ayi magana dake" seta karba tana kallon wayar ganin ba akan kira take ba ta ajiye a gefe ta shiga shiryawa.

Tana qoqarin zuge zip din doguwar rigar data saka wayar ta shiga qara, se sannan ma ta ankare da cewar wayar tace aka bata, ta zumburi baki ganin me kiran wallahi badaban muguwar kewarsa da tayi ba da bazata dauka ba. Ai ko babu komai taci darajar haifar masa ya da tayi ya kirata yaji lafiyarta amma ace har se yau kwana hudu sannan ze kirata taja kwafa tana hararar wayar daidai nan kiran ya katse wani ya sake shigowa.

A daqile tayi masa sallama ya amsa murya ba yabo ba fallasa ta shiga gaishe shi ya amsa tareda tambayarta qarfin jiki, seda taja tsaki qasa qasa kafin tace da sauqi sukayi shiru gaba dayansu na kusan minti daya. Jira takeyi taji ya bata uzuri na rashin kiranta sannan ya rarrasheta ya gaya mata kalamai masu dadi irin yanda ya ringa mata sanda ta haifi Mu'ayyad dan har ta fara tattare fuska tana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login