Showing 201001 words to 204000 words out of 429394 words

Chapter 68 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

992

kintsu irin kintsin daya bawa kowa Mamaki ta kowanne banni yanzu ta dauki gyara. Tuni ta koma Islamiyya kamar yanda Maman Asad ta gaya mata, bayan dogon nazari da karatun ta nutsu da tayiwa kanta ta fuskanci gaskiya ta gaya mata dan haka ta sanarma da Khalil son komawa Islamiyya da bokon ya kumayi na'am da Islamiyyar, bokon ne yace tayi haquri. Da akwai shirin da yake dashi idan Allah ya tabbatar zatayi dan haka ta rungumi Islamiyyarta, sau uku sukeyi a sati litinin zuwa Laraba Goma na safe zuwa qarfe daya dan haka da ta gama ayyukan ta na safe zata fita makaranta idan ta dawo ta huta kafinta shiga aikin girki da tarbar Khalil bata da matsalar yara dan Bibi sam bata da rigima Mu'ayhad ko ya zama dan gidan Hajiya sedai yazo musu ya tafi.

Sosai ta qaru da komawar tata Islamiyya ta farfado da karatunta ga kuma sabon karatun darasin rayuwa da take samu a gurin sababbin gogaggun qawayen da tayi matan da suka san me sukeyi ba tarikican qawayen banza data sabayi ba wadannan matane da duk maganar da zasu fada ta qaruwa ce me amfani haka ta sake shiga whatsapp group a karo na biyu bayan Rufaida tasa an cireta daga duk wanda suke ciki a baya sedai wannan karon groups ne na qaruwa da har seda ta gayyato su Nuratu dasu Mamab Asad duk suka shiga harda Anty ba'a barta a baya ba ta shige suna kwasar darasussukan rayuwa daga Matan da sukaga jiya suka ga yau.

A dai taqin shekara da wani abu Abubuwa da dama sun faru na dadi dana akasin haka. Babban abin dadi daya faru shine budin da Khalil ya samu da har ta kai ga ya bude construction company nasa na kansa wanda ya kafu bisa jajircewarsa da kuma aiki me nagarta da yakeyi wanda shine ya janyo masa samun manya manyan kwangiloli da beyi tsammani ba qarqashin Jaririn Companyn sa dake tasowa a yanzu.

Bayan nan se tafiyar Sa Umaimah da Hajiyarsa aikin Hajji wanda suka sauke faralli cikin wannan shekarar. Base na baku labarin Hajiya Umaimah a saudiyya ba, anyi ibadah dai matuqa addu'a kam Khalil ya shata ta Allah ya hana idonsa ganin wata mace bayan ita, Rikici kuwa babu abinda ta fada dan sedai idan basu fita siyayya tare ba. Haka kawai idan abinta ya motsa zatace wata na kallonsa, idan anyi sa'a yar uwarta ce Bahaushiya ta zageta su kwashi fada kowa ya kama gabansa, idan kuwa ba yarenta bane zagi take musu na tsamar nama sedai su kalleta su dauke kai toh basu ma san abinda rake fada ba kuma duk abin nan bata tabayi a gaban idon Hajiya ba, dan yawanci yawon Kasuwar su Hajiya bata binsu se tayi zamanta a masauki shidai Khalil Sallar sa da dawafi kaf babu a wanda baya roqarwa Umaimah shiriya da kuma zabin Allah akan komai na rayuwarsa, haka dai aka sauke Hajji lafiya aka dawo gida nan kuma Umaimah ta tarar da sabon abu, ginin gidansu da akeyi an canza masa fasali daga yanda aka qirqire shi zuwa zaman Mace biyu a tata fahimtar.

Asalin ginin komai anyi shine a cakude, bangarenta dana Khalil din a hade suke amma suna dawowa yace taje ta duba gida a fara shirin zuba kaya dan damansun siyo wasu abubuwan irinsu Labulaye da Carpet tana zuwa taga wannan tashin hankali, part guda Khalil din ya warewa kansa saboda rainin hankali a cewarta fa harda Kitchen da store, guri dai tsaf kamar mace za'a ajiye.

Babu kalar rantsuwa da bayanin da beyi mata ba ta toshe kunnenta, ta ringa tijara tana rashin mutunchi a gaban ma'aikata, bokitan penti da aka ajiye dan ana pentin gidanne haka ta ringa bi tana zubar masa dasu penti masu tsadar gaske. Ran Khalil ya baci matuqa, babban abin kuma daya qara bata masa rai da sukaje gaban Hajiya ta goyi bayanta.

"Akan me zaka canza tsarin gidan kuma ba tareda kayi shawara da ita ba?" Hajiya ta fada cikin fushi tana kallonsa. Khalil ya kalli Hajiya ya kalli Umaimah dake faman share hawaye bayan tazo ta gama zayyanawa Hajiyar qarya da gaskiya ya hadiye wani abu me daci daya tsaya masa. Badan be taba kama Umaimah da wani abu dayayi kama da Bin Malamai ba da tabbas zece Asirce Hajiya tayi, wannan makauniyar soyayar da Hajiua take mata ba kuma ta ganin laifinta abin yayi yawa. Gyara zamansa yayi yana cewa

"Hajiya ni sam ba abinda take tunani bane yasa nayi hakan. Kinga dai tsarin ginin a farko komai a cakud akayi shi, babu wani kebantaccen guri ko ina kowa yana iya shiga akoda yaushe babu sirri ni kaina se daga baya naga rashin dacewar hakan a matsayi na na me gida ya kamata ace ina da turakata data qunshi komai da komai a ciki bana buqatar fita idan ina buqatar wani abun.
Sannan iyali muke tarawa dole yaranmu wata rana zasu girma, be kamata ace muna cakude dasu a koda yaushe ba dole akwai buqatar sirri tsakaninmu ni wannan ne kawai dalili na ba wani shirmenta mara tushe ba"

"Kuma ahine harda Kitchen da store duk a bangaren naka? Three bedrooms ga qaton palour da dining duk me zakayi dasu?" Umaimah tayi tsugul ta fada kafin ma Hajiyar tayi magana, Harara ya galla mata kamar idonsa ze fado ba tareda yayi magana ba jin Hajiya nacewa
"To ai kamata yayi tun kafin ayi seka gaya mata, base kawai tazo taga abu ba ai koma wacece tunanin daze zo mata kenan a zuciya"

"Idan qara auren tana da hujjar Hanani ne ko kuma akwai Haramci a cikin Hakan?" Yayi wa Hajiya tambayar amma idonsa akan Umaimah data gwalo nata idanun saboda jin wannan gingimemen tashin hankali,

"Bana son neman rigima Khalil, bana so. Ke kuma kinji abinda ya fada dan haka karna sake jin wata magana bayan wadda akayi a nan" Hajiya ta fada musu gaba daya Khalil be jira yaji koda sauran maganar tata ba ya tashi ya fice daga gidan cikin bacin rai. Iya Asarar pentindata masa da yawa kuma wallahi zata sani a cikin kudin da yayi niyyar bata na gyaran gidan idan yaso in basu isa ba ta tare da tsofaffin kayanta. Ya gaji da iskancin Umaimah ba kuma ze sake biye mata ta mayar dashi kamar wani takalmin sawarta ba.
Ya dauka nutsuwar da tayi tun bayan wancan Al'amarin ta gaske ce tunda gashi kusan shekara daya da wani abun bata sake masa shirme ba suna zaune lafiya se yanzun kuma baze dauka ba.

Da daddare be koma gida ba se gurin sha daya sabodaya zauna meeting da wasu campany da zasuyi hadin guiwar wani aiki. A palour ya tarar da ita daman kuma ya tsammaci hakan maganar ba zata mutu ba kamar yanda hajiyar ta yanke hukuncin son rai dan haka yana ganinta ya qara hade fuska ya wuce ze shiga dakinsa tasha gabansa tana cewa

"Kai nake jira tun dazu dan gara ma ka sani bazan koma gidan nan ba idan baka rushe wannan gurin ka maida shi yanda yake ba" ta fada tana karkada qugu kamar Mazari, kallon sama da qasa yayi mata takaici ya rasa abinda ze fada mata seya zagaye ta ya wuce cikin dakin ta bishi cikin daga murya bata ko tunanin yara na bacci karta tasahe su tace
"Khalil dakai fa nake ka wuce ni wato ga mahaukaciya tana magana ko?"

"Ai sunan daya dace dake kenan Umaimah, na yarda baki da hankali kuma idan baki fita kin bani guri ba se ranki ya baci wallahi. Gida kuma karki koma, ke kika rasa gobe idan naga dama zan samo ukun ki na zuba a gidan kin kuma san yana da girman da ze dauke su dan haka ki fita ki bani guri ki koma ko karki koma keta shafa bani ba" Khalil ya fada yana kallon tsakiyar idonta kamar yanda itama ta zuba masa ido kafin ta juya da gudu tabar dakin nasa.

"Mtsw" yaja wani matsiyacin tsaki ya zauna a gefen gado yana dafe kansa da yake masa ciwo ciwo,Umaimah bazata canza hali ba, shekara dubu tana abin kirki idan tsiyarta ta juyo cikin minti daya zata wargaza komai. To wannan karon kam sedai abinta ya qare mata dan bashi da lokacin da ze tsaya yana batawa akanta abubuwan gabansa ma su Ishe shi.HALIN KISHI

49


*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TU???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?RA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 49

KHALIL
Kiransa Hajiya tayi ta rufeshi da fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba taqi bashi ko damar ya gaisheta har seda ta kao aya kafin ta kashe wayarta, yasan baze wuce Umaimah taje ta gaya mata qarya da gaskiyar data saba bane shine zata hau kansa ba tareda shi taji ta bakinsa ba haka ya tashi shirin tahowa dan ce masa tayi ko ya dawo ko Umaiman ta bishi shi kuwa daman ba zaman wani abu yake ba aikin ma da suke gaba daya an kusa kammalashi kuma ya gama bangarensa tuntuni kawai wasu harkokin kasuwanci ya sake samu a can da taimakon wani Co-Architect da sukayi aiki tare shi ya nuna masa hanya ta irin abubuwan da suke tafiya a can wanda basu dashi se an shigar musu daga wasu qasashenda kuma namu na nan da suke da sauqi acan nan da nanya fantsama harkar shigowa da fitar da kayayyaki kuma da Allah ya saka albarka a abin yana ganin haske, ga harkar Gold da yake da sauqi sosai a can, sunq ulla Bashir, danye yake siya su kai Dubai a canza shi zuwa abubuwa da dama wannan hidimomin ne suka dauke masa hankali gaba daya har mamakin kansa yake ta yanda ya iya share tsahon lokacin ba tareda Mace ba kuma baya jin wata damuwa kodanbaya kawo abin a ransa ne yana fushi dame abun sabanin da da ko muryarta yaji yanzu jikinsa ze amsa?

Shidakansa yasan zazzafar soyayar da yakewa Umaimah ta dishashe ba kuma ya zaton zata sake samun matsayi irin wanda take dashi a da cikin zuciyarsa ta rigada ta barar da damarta.

Ranar Lahadi kamar yanda ya fada qarfe sha biyun Rana tayi masa a gidan Hajiya. Dakyar ta barshi yayi sallar Azahar banda ruwa ba abinda yasha ta korashi wanda be so haka ba, so yayi ko ze koma gidan se cikin dare amma haka ya tafi yana ta doka tsaki Mu'ayyad nata kukan ze bishi aka lallabashi da kyar akan se an kwana biyu za'a maida musu shi. A Mota Khalifa dai sedai ya juya ya kalle shi ya dauke kai, tunawa yakeyi lokuta baya idan yayi tafiya ya dawo yanda yake doki da zumudin komawa gidan ya ringa Azalzalarsa da yayi sauri kenan amma yau har fada yake masa wai yana gudu da motar. Har cikin gidan ya shigar masa da mota ya fita yayi masa sallama ba tareda ya tsaya sun gaisa da Umaimah ba.

Numfashi yaja ya fitar kansa na kallon qofar palour da aka liqa wata sticker me qyalqyali an rubuta
'WELCOME HOME HABIBI" A jiki. Waiwayawa yayi ya kalli qaramin compound din da yayi qal Interlocks se daukar ido suke alamar sunsha shara da wanki ga wani daddadan qamshi turaren wuta da yake tashi kamar anyi barinsa a gurin. Da sallama ya tura qofar palour ya shiga, wani qamshi, sanyi, nutsuwa da ya rasa ta mecece suka bige shi lokaci daya, cikin seconds goma ya qarewa palour da babu kowa a ciki kallo. Gyaranda akayi masa is morethan perfect, yanda kasan babu wanda yake rayuwa a ciki saboda yanda komai ya zauna daidai a muhallindaya dace dashi haka ya fara jefa qafafunsa yana tafiya duk taku daya yana jin wata kewar gidanna kama shi, gaskiya masu magana sunyi gaskiya da suka ce no place like home.




Qofar dakinsa ya tura kai tsaye ya shiga da sallama a bakinsa, wani sabon qamshi na daban yayi masa maraba tareda fuskar kyakykyawar Diyarsa dake kwance akan gadon daya sha shimfida ta alfarma itama cikin irin shigar da yake so ya gani jikin yara kamar ta sanshi suna hada ido ta bangale masa bakinta da babu haqori ta qara qarfin gwalantoyin da takeyi daga kwancen. Be san sanda ya dire jakar hannunsa ya isa kan gadon ya dagata ba ya hadeta da qirjinsa yana kissing fuskarta ita kuwa se dariya take abinta.

Umaimah ta bude qofar bandakin da ta shiga tana hada masa ruwan wanka saboda Habiba ta kira ta gaya masa gashi nan a hanya ya baro gidan Hajiya. Daskarewa tayi daga bakin qofar, So, shauqi tareda kewarsa suka shiga shawagi da ita a sararin samaniyar qauna bata san yanda akayi ba se ganin kanta tayi a bayansa ba kuwa ta tsaya tunanin komai ba ta saka hannuwa biyu ta zagaye cikinsa dasu kafin ta dora kanta a bayansa se ji tayi hawaye suna bin kuncinta da ita kanta bata san na menene ba.

A bazata abun yazo masa dan sam beji fitowarta daga bandakin ba gaba daya hankalinsa nakan Yar Babyn tasa da yake jin qaunarta har qololuwa, da yanzu Umaimah ta salwantar masa da ita tab da kuwa ta cuce shi. Saukar hannun mutum kawai yaji a cikinsa se saukar abi me dumi da yatabbatar hawayene ya shiga ratsa jini da jijiyarsa har zuwa cikin bargonsa, sosai yayi ta maza ya dake ya kuma hana kansa juyowa dan yasan tarko ne, idan har ya bari tayi tasiri akansa shikenan duk wani shiri daya dawo dashi ya wargatse.

Hannu daya ya saka dayan na rungume da Bibi ya janye hannayen Umaimah data zagaye shi dasu ya fara takawa zuwa gana kujerar dake cikin dakin ya ajiye yarinyar ya shiga zame rigar coat din daya dora, hannunta ya sake ji a kafadarsa tana taya shi, kafin muryarta da tayi wani irin laushi da sanyi ta ratsa dodon kunnensa tana cewa
"Barka da zuwa Habibin Umaimah, banji shigowarka ba ina ciki ina hada maka ruwan wanka, u are highly welcome" ta qarasa cikin wani sauti daya sakashi saurin sakar mata rigar ta qarasa cireta kafin ta juyo ta shiga balle masa maballin farar yar cikin jikinsa suka shiga kallon juna ido cikin ido kowanne yana karantar tsantsar kewar sa cikin idon Dan uwansa, tana gama balle masa rigar be zata ba yajita cikin jikinsa gaba daya suka yi baya ya samu ya dafe kujerar gabansu tareda qanqameta yana qarewa fuskarta kallo data sha simple kwalliyar nan tata wato pawder da man lebe ta gyara kyawawan idanunta da kwalli da Mascara gashin idon sun qara tsaho da baqi.

Lumshe idonta tayi ta sake bude su akan sa kafin ta raba labbanta data pente da jan lipstick ta sake shafe su Lipbalm me maiqo se daukar ido sukeyi tayi kamar zatayi magana amma ba tace komai ba, Idan yace yace beji wani abu na yayi qary, wani sanyi yaji ya taso masa tun daga tafin qafa ya dire a kwakwalwarsa, wani irin kallo take masa na cikin ido dashi kadai yasan ma'anarsa kuma ji yakeyi tamkar ta saka muqulli tana bude duk wasu qofofin jikinsa da suka jima a rufe, numfashinta da yaji cikin nasa kafin ta kai ga aikata abinda ta niyyata zumbur ya tashi tareda ita a jikinsa, sauketa yayi a qasa kan qafafunta kafin ya juya ya shige bandaki yanajin yanda jikinsa yake harbawa ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login