Showing 48001 words to 51000 words out of 429394 words

Chapter 17 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

975

suke gwangwajeni da dinkuna duk inda na shiga se an tambayeni wayake mun dinki"

"Ga shaida na gani muma ai zamu warwasa da bikin nan dan har na hango yanda dinkunana zasu bada Ma'ana, bani number CEO din ma kiga na sake kiranta ina so naje su dauki measurement dina dakyau, sannan ga maganar Console da Dining Table da nake so na sake danna Nuratu sun tafi da Imani na" Maman Asad ta sake fada, se Naziyyan tace

"Zakiyi mamaki idan nace miki ban taba zuwa an gwada ni ba, Tailor ta daya kawai ta aiko da za'a karbi dinkin da aka kawo su na gwada cif yanda kika san an gwada ni kuwa ai tun daga nan suka sake tashin kaina, shiyasa dinki ko babu awo zan basu nasan bazan ji kunya ba gashi sun san darajar kaya, ko wanne abu sunsan irin dinkin da zasuyi miki a jiki da ze qara fito da kyansa da qimarsa, Dining kuwa ki jira kiga na Yar gaban goshi, ai ni har cewa nayi ma Hajia Bilkisu tayi Son kai dan kayan Umaimah na neman sufi na Nuratu kyau tace ba haka bane, su haka aikinsu yake duk sanda aka maka sabo se kaga yafi na baya haduwa kuma na yarda dan duk sanda aka mun dinki qara sonsu nake saboda kullum sabuwar fasaha suke fito da ita"
*(Ku tuntubi Hajia Bilkisu CEO BIISHAQ LINKS home of funitures and fashion design akan lambar waya 08033950747, suna nan a Tudun-yola get 2 dake birnin kanon dabo)*

Hira suka ci gaba dayi suna daga kayan, Zee Mama ta sakw daga wata fitted gown data shawu shape din nan ya fita ta ko ina tace
"Har na hango rigar nan a jikin Nuratu yanda zata fito amma se tayi ciko sosai a saman nan dan cup din yayi mata yawa"

"Kamar kin shiga raina, tun dazu abinda nake tunani kenan cup din kamar zasuyi mata yawa koda yake daman haka take saka kaya a saka Bra me soso ko ina ya ciko cif ba'a san coge bane, da dai su iya rasa kunya ne ko ina ya cika da kaya sun fito da kyau" Yaya Hafsa ta fada.

Umaimah dake kwance daga can gefe duk a zatonsu bacci take dan tunda suka fara bata saka musu baki ba ta tuntsure da dariya tace
"Ba ciko bane Allah ne ya bamu, wasu ko sedai a hada da soso"

"Shegiya ashe idonki biyu dake an tabo sabgar tsokana zaki fara rashin mutunci ba toh Allah yasa ta jiki yanU ta nada miki na jaki" Zee Mama ta fada, Umaimah ta harareta ta mayar da kai taci gaba da chatting dinda sukeyi da Khalil.

"Wai dagaske kuke ko wasa? Daman duk abin nan cukone Nuratu takeyi ba nata bane" Anty Mamy ta fada tana kallonsu, se Maman Asad tayi caraf tace
"Ki bari kedai ai duk abin tsiyar a kanta ya qare a gidannan, kowa an raba an bashi ita se aka bata iya qasan babu saman ni har tunanin yabda zasu kwashe da Angon nake idan ya gano gaskiya wallahi, bari ma in kirata dai" ta shiga kwalawa Nuratu kira se gata daga ita se Daurin qirji da alama daga wanka ta fito babu cikon qirjin nan a shafe, Umaimah dake jiran qiris ta kwashe da dariya kuwa harda hantsilawa qasa Nuratun tayi kanta a fusace dan tasan dariyar me takeyi tunda ba yau ta saba yi mata ba, wani lokacin ma setaga ta fito daga wanka zata tashi itama ta tube ta daura zani tayi ta yawo a dakin tana waqe waqen neman tsokana.

"Rabu da ita karki kulata Nuratu daman neman nayi takeyi, Wannan ba matsala bane dukda dama ace na sani da wuri da tuni na baki magani kan biki duk se masuyi miki dariyar sunsha mamakin yanda abubuwa zasu cicciko har sufi nasu" Anty Mamin ta fada tana zaro wayarta daga jaka ta dannawa *MAMAN ILHAM ME TULA-TULA* kira.

*Fadila UJ kid's dresses* indai Winkin yara ne, we got you covered =د?.Ana kawo mana mu Winka sannan muna siyar da ready made muna kuma aikawa ko ina in sha Allahu.Kina fama da ?yallaye ?anana da bazasu isa ayi ma princess riga ba?No worries *Fadila UJ kid's dresses* zasu saffara maki su izuwa mini skirts,ba zakuyi dana sani da Winkin *Fadila UJ kid's dresses in sha Allahu*
07037977211
Location:Katsina state muna aikawa ko ina cikin Aminci =?L?

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 15


A speaker ta saka wayar tana dagawa suka gaisa tace
"Maman Ilham qanwata ce zatayi aure ashe dai saman in gaya miki se a slow babu komai duk ciko ne, shine fa hankalinmu ya tashi biki saura sati uku ban sani ba ko akwai abinda za'a iyayi mata"

Daga dayan bangaren Maman Ilham ta amsa da cewa
"Hajiya Mami ai ba abun tashin hankali bane irin hadin nan dai naki za'a bata in sha Allahu kafin satin biki se kinyi mamaki yanda abubuwa zasuyi TULA-TULA"

Anty Mami ta kwashe da dariya tace "kai sunan abun nan na bani dariya Maman Ilham, to ya za'ayi, naga yanzu yamma tayi za'a samu motar da zata taho Kano daga Kadunan kuwa?"

"Kiji ki fa kamar waddaza'a kai saqo Niger ai da yardar Allah kafin Isha ma saqo yazo hannunki yanzun nan zanyi packaging na baya a saka miki a tasha, ki gayawa Amarya ta kwantar da hankalinta wannan matsakar an maganceta, idan da TULA-TULA, babu jin kunya" suka kwashe da dariya daga nan sukayi sallama.

"Allah ya kamaki matar nan, yanzu gashi a bagas munji sirrin yanda akayi abubuqa suke tsaye qyam kamar baki shayar ba" Yaya Hafsa ta fada, se da Anty Mamin tayi fari da ido kafin tace

"Toh ya ranki, yaya hudu na shayar yanzu waze kalleni yace sati na uku da yin Yaye?"

"Au wai kin Yaya Ni'ima amma kalli Nonon a cike koda yake tunda kike yaye ma ai ban taba ganin Nononki ya zube ba, tunda dai yau Allah ya matsi bakinki kin tona sirrin se ki gaya mana da kin gantalar damu da shan wata sabaya, sedai jiki yayi kyau amma abinda ake so ya tsaya din se a hankali, taimakamun kinji Surukata, nima na saka ranar Yaye wallahi har fargaba nake gaba daya nono ya zube ya koma kamar wanda qullin zobo ya fashe" Anty Ruqayya ta fada yanda tayi maganar dole ta baka dariya.

Seda suka dara kafin Anty Mamin tace "wani maganine na samo shi gurin Maman Ilham Sunansa *TULA TULA* Magani ne sadidan na gyaran nono kuma kowa yana iya sha Yan Mata da zawarawa masu Shirin yin aure, me shayarwa dukka kowa nasha Daga mambila Ake kawoshi kunsandai yanda Matan fulanin nan nasu suke qirji a tsaye kamar na babyn roba to TULA-TULA ne sirrin kuma yanayi sosai Bada wasaba koda yake ku zaku bada shedar haka.

Kinga kamar ke yanzu da zakiyi Yaye zaki fara Sha sati daya kafin yayen to In sha Allahu bazakiyi ciwon nono ba ko zubar ruwan nono lafiya lau zekiyi? yayenki Kuma nono baze kakkabeba".

"Amma matar nan anyi me baqin abun, yanzu da shine kika barmu muna ta bulayi kullum kyaji muna jimamnin neman maganin gyaran nan amma kinyi bulumbuqui idan anyi magana kice ku Natural ne toh kin wa kanki" Maman Asad ta fada tana kama baki, Se Anty Mamin tayi dariya tace

"Toh ai ku dangin miji ne ba'a iya muku haka kawai in bankada muku sirrina, Aa gara dai na adana abuna"

"Allah ya yafe miki matar nan, kinga sake kiranta yanzu a hado dashi ina son qulli goma nawane?" Anty Ruqayya ta fada,

"Sannu duk me zakiyi da har guda goma?" Mamin ta fada tana zare ido, Anty Ruqayya ta murguda baki cikin wasa tace "Ina ruwanki, kedai kirata kawai" sauran ma suka dauka gaba daya kowa tace a hado mata dashi tana so nan da nan kuwa ta Kira Maman Ilham ta gaya mata adadin da suke so, basu bar gidan ba se bayan Isha'i lokacin har saqon ya iso daga Kaduna sun aika an karbo musu a tasha kowa ta adana nata a jaka

(Indai matsalar ki Zubewar ko kwanciyar Nono ce tazo qarshe, ki nemi Maman Ilham akan 08135613021 ki siyi naki akan farashi me sauqi, tana Kaduna tana aikawa ko ina a fadin qasar nan da yardar Allah).

Kwanci tashi aka ce asarar me rai se gashi ana lissafin biki ya rage kwanaki biyar a fara, tuni Amare suka dauki harami jiki yayi mulmul fata tayi subul saboda ingantaccen gyara da suke samu daga gurin Anty, sal take sillesu da kurkum da dilka su shige cikin Hayaqin Dukan (wanda ba qaramin gyara mace yake ba, idan so samu ne kowannce mace ya zama tana da itacena gidan ta lokaci lokaci ki ringa turara jikinki yana maganin sanyi da sauran matsalolin mata ga matsi ciki da waje) idan suka gama wannan sukayi wanka kuma su sake mulke jiki da hadaddiyar kolakca sannan a shiga sabon turaren jiki shi yasa qamshi ya kama su duk inda suka gifta se sun bar mutane da bude hanci.

Idan kaga yanda Nuratu ta cicciko abin kamar almara dan Tula Tula ya karbeta, Umaimah me mata iskanci se gashi itama tana bin dare tana diba dan itafa duk ta inda za'a ce wani ya fita se tabi ta toshe qofar, Khalil yayi Namijin qoqari dan dubu dari biyar cis ya bata kudin hidimar biki, sanda ta gayawa Mama abinda ya turo din fada ta ringa yi mata akan me yasa zata takurashi ta karbi kudi masu yawa haka bayan babu abinda ba'a yi musu ba, har Khalil din ta kira, ya tabbatar mata da ba ita ta roqeshi ba. Kawai dai ya samu kudade ne shima dan sosai yake samun gudummawa tunda katin daurin auran ya fita Manyan mutane da ya tabayiwa aikin zanen gida kawai sedai yaga Alert ko yaji an kirashi a waya ance yaje ya karbi cash.

Allah kenan, a lokutan baya idan yana tunanin aure se ya ringa ganin kamar ba ze iya ba dan bashida abinda zeyi hidimomin se gashi yanzu ya yarda da abinda Hajiya take fada masa na cewar shi aure ba'a shirya masa shi yake shirya kansa, duk sanda mutum ya niyyata yinsa se kaga Allah ya buda masa gashi kuwa ya gani dan rufin asiri samun sa yake ta ko ina babu abinda ze ce sedai ya qara godewa Allah ya kuma tabbata Umaimah Alkhairi ce a rayuwarsa dan tunda ya hadu da ita yake samun budi ta hanyoyi daban daban, shi yasa bazeji qyashin kashe mata ko nawa bane a cikin dukiyarsa.

Ranar Alhamis ana gobe Kamu sukaje qunshi da gyaran gashi. Wani Hadadden Salon sukaje na mataasu Aji dan tundaga harabarsa zaka gane hakan saboda irin manyan motocin dake zube na matan da sukazo qunshi, gyaran gashi ko gyaran jiki.

Da yake sun rigada anyi musu booking basu bata lokaci ba nan da nan aka farayiwa Umaimah Jan Lalle wata kuma ta shiga wanke mata kai akayi steaming dan kitso zatayi Nuratu kuma aka saka mata Relaxer.

Cikin abinda be wuce awa uku ba se gata ta fito a Amaryarta fes, tayi kyau na gaske lallen da aka mata Jan yayi maroon sosai ya kwanta a fatarta da bata da haske sosai amma gyaran data samu ya taimaka gurin sake fito da ainihin kyan lallen ga qananan kitso an yarfa mata dole ka kalleta seta burgeka.

Tana zaune daga kan kujera ana zanawa Nuratu Baqin lalle bayan an gama mata jan dan ita Umaimah cewa tayi bata so duk yanda masu lallaen suka kada suka raya kuwa taqi dole suka haqura. Khalil ne ya kirata Video call, santin kitson da jan lallen ya ringayi dan ba qaramin kyau suka masa ba.

"Babe har an gama ne na taho na dauke ku? Dan bazan iya bari wani ya fara gane mun wannan gayun naki ba" ya fada bayan daya gama kodata, Murmushu tayi masa tace
"Aa Yaya Nuratu ake qarasa baqin lalle amma ana qarasawa zan kiraka kafin kazo yasha iska se mu tafi ta wanke a gida".

"Yauwa ke ba'ayi? miki wannan flower black ba da naga anayi yanayi mun kyau sosai, kice su rubuta miki sunana a nan" ya fada yana nuna mata gefen wuyanta, fuska ta dan bata tace

"Ni bana sonsa amma tunda kana so bari ayi mun"
"No ki barshi in bakya so wannan ma ya isa amma yanayin kyau sosai idan na ganshi a hannun mutane yana burgeni kuma musamman ma nasan idan akayi miki se yafi na kowa yin kyau" Khalil din ya fada, jin haka kuwa ba shiri ta bata fuska tace

"Wato kallon yammata kake yi har lallensu yana burge ka koh?"

"Ba haka nake nufi ba, idan su Habiba sunyi nefa nake gani. Ni ina naga lokacin kallon wasu yammata kullum ina site ina fama da sumunti da yashi" ya bata Amsa yana qunshe dariyarsa, ta maka masa harara kafin tace

"Se anjima idan mun gama i will call you"
"Ok ayi miki ke kyau kinji Babe, love you" ya fada tareda huro mata kiss, baki ta tura masa yayi dariya ya kashe wayar, seta kalli wadda ke zanawa Nuratun lallen sun gama saura qarashen hannu daya, murya a cukule tace

"Idan kin gama mata zakiyi mun, kuma yafi nata kyau"
"An gama Amarya" matar ta fada tana dan murmushi dan tun tana wayar suke kallonta daman kuma Nuratun ta fada tace su jira su gani zayi gashi kuwa.

Lalle me kyau matar ta zana mata na Amare dukda Umaimah nata noqewa a barshi yayi yawa amma ta shareta seda tayi mata yanda ya kamata ita da kanta kuma ta dawo tana Admiring lallen ganin yanda ya qawata hannunta sosai.

"Hajia Ango fa yace a rubuta miki sunansa a wuya" Me lallen ta fada bayan sun gama dataga Umaiman na shirin kishingida a kujerar da take, wani kallo ta watsa kafinta fara magana cikin fushin da bata gama saukowa ba na zancen lallen da Khalil yayi tace

"Daman samun ido kikayi har kina jin abinda mijina yake fada? Irin kune daman masuyiwa mutane labe kuna sauraran conversation dinsu ko? Toh bari kiji Mijina yafi qarfinki sedai ki qare a nan kina zana baqin lalle da baqar fuskar ki a gurin" sosai ta ringa spark tana bala'i ma'aikatan gurin na bata haquri dan a policy dinsu customers are always right, koda kuwa sune da rashin gaskiya.

Nuratu da ta shiga toilet wanko lallenta ta jiyo hayaniyar babu shiri ta fito
"Umaimah meye haka? Me yasa ke baki da mutunci daga abin arziqi shine zaki fara zaginta" Nuratu ta tareta se kuwa ta juya kanta tace

"Babu ruwanki saboda ba naki mijin tayiwa labe ba shi yasa zaki tare mata, akan me zata saka kunne harta ji muryar sa?"

"Da kika san bakya so aji muryar me yasa zakiyi waya a gaban mutane ko kin manta da video call kikayi kuma a speaker baki saka earpiece ba? Wallahi Umaimah ki shiga hankalin ki tun wuri kafin ki jawowa kanki baki" Nuratunta fada a fusace itama, Umaimah ta bude baki zata bata amsa wayarta tayi qara, Khalil ne.

A fusace ta miqe bata damu da lallen ta da be gama shan iska ba ta yayibi mayafi da jakarta tayi waje Nuratu taja tsaki ta koma ta ci gaba da wanke lallenta a ranta tana takaicin halin qanwar tata da duk inda akaje seta siyar da Hali, tana guje mata taje cikin dangin miji tayi musu wannan haukan tabbas babu inda auranta zeje dan babu Namijin da ze yarda ta ringa wulaqanta masa yan uwa haka.

A waje kuwa a fusace Umaimah ta qarasa inda ta Hango motar Khalil, bawan Allah daya sha gayunsa ya fito da murmushi amma ganin fuskarta a dinke kamar Hadirin August yasa ya tsaya daga inda yake harta qaraso

"Mu tafi" ta fada tana qoqarin kama murfin motar yayi saurin bude mata yana cewa
"Easy Babe, wa kuma ya bata miki rai haka"

"Duk ba kai kaja ba, akan me zaka kirani bayan kasan ina cikin mutane su kuma mayu daga jin muryarka har wata ta riqe abinda ka fada" tayi maganar cikin fada kamar meyi da dan cikinta. Sakato Khalil yayi yana binta da ido, ikon Allah yanzu kuma kiran da yayi mata ne ya zama laifi gaskiya yarinyar nan ya yarda saitin kanta na gocewa.

Ganin ta dage tana surfa masa masifa dan har masu wucewa sun fara kallo su yasa ya dakatar da ita, cikin tsawa ya kira sunanta Yace
"Kirawo Nuratu mu wuce"
Yanda ya hada fuska babu wasa sam yasa dole ta juya ba taredata musa ba amma da taso suyi tafiyarsu ne su barta idan yaso ta hau Napep ko ta kira nata Mijin yazo ya daukota tunda tafison me lalle akanta.

Kafin ta qarasa shiga gurin Nuratun ta fito da wata ma'aikaciya a bayanta ta ruqo mata Paper Bags masu tambarin salon din guda biyu seta juyo tana ci gaba da kumbure kumbure ta tsaya a kusada Khalil daya harde hannu biyu a qirji kawai yana binta da kallo, ran Nuratu babu dadi ta bude baya ta shiga yarinyar ta miqa mata Jakunkunan ta karba tareda godiya kafin ta juya har tayi gaba ta waiwayo ta kalli Umaimah da Khalil, ita Umaimah daman idonta akan yarinyar yake shi kuma Khalil yana nazarin Umaiman yarinyar na juyawa kuwa tayi missing step ta tafi taga taga zata fadi Allah ya taimaketa dafe bango

"Mayya dama kin fadi kin karya haqori gobe kya sake kallon Mijin wata" Umaimah ta fada, cikin jin haushi yarinyar ta mayar mata tace

"Ni ba mayya bace kuma na kalle shi din tunda ai Namiji ne badan ke kadai akayi ba"

"Kan babbar bala'i, me kika ce?" Umaimah ta zabura tayi kan yarinyar, Tsawa Khalil ya buga mata, ba ita ba hatta da Nuratu dake cikin mota tana kallon ikon Allah seda ta razana,

"Get in side" ya fada yana nuna mata qofar motar, dole ta shige dan a yanda taga bacin rai a idonsa tabbas yana iya kai mata mangari. Seda ya kulle mata qofar kafin ya zagaya bangaren sa ya tada motar, da gudu ya figeta suka fice daga gurin zuciyarsa na tafasa wannan wane irin zubar da qima ne? Yanzu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login