Showing 288001 words to 291000 words out of 429394 words

Chapter 97 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

968

daga mana hankali to karta fasa, aurene kamar anyian gama da izinin Allah sedai baqin ciki ya kasheta Khalil kuwa nan gani nan bari wlh tana kallo ze dauko santaleliyar Matarsa su more soyayya ita yana can Kishi ya haukatata an kaita Dawanau"

"Idan baki bar gidan nan ba se na bata miki Jalilah" Hajiyan ta sake fada, se Jalilah ta koma ciki tana qunquni, jakarta da gyalenta ta dauko ta fito tana Kallon Khalil dake nan kamar gunki tace
"Har daki ta tarar da uwarka ta zaga tace kuma idanka haifu kayi mata kishiya ta gani, to ina jira na gani nima ka haifu cikin Bayero ko kuwa a Asibiti aka qarawa Hajiya kai bayan ta haifeni" dukan da Hajiya ta kai mata yasa ta matsa da sauri ta fice daga gidan Hajiya ta kalli Khalil tace
"Babana ya isa haka tun ba'aje ko ina ba kaga abinda ka kira mana to ka janye maganar nan kawai ka haqura kayita addu'a Allah ya daidai ta maka zamanka da matarka kawai dan ni bazan iya tashin hankali ba" ta juya ta koma cikin gida.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daga qafarsa da kyar ya fice daga gidan, seda yayi sallar isha kafin ya dawo, a compound din tsakiyar ya zauna ganin Khalifa a gurin shima is muzurai yakeyi Khalil din na zama yace
"Gaskiya Yaya ya kamata kayiwa gidanka garambawul, ace har rashin mutunchin Anty Umaimah ya kai taje har gaban Hajiya ta kirata da munafuka? Wallahi tun wuri kayiwa tufkar hanci dan idan ba haka na gaba bamu san abinda zatayi ba kuma muma ba zamu zauna mu zuba ido tanayiwa mahaifiyar mu duk cin kashin dataga dama ba"

"Munafuka?" Ya maimaita kalmar cikin mamaki, Umaimah ta kira Hajiya da Munafukan akan me?
"Kuma itama Hajiya da laifinta fa Yaya, saboda Anty Jalilah ta mareta bakaga yanda Hajiyar ta taso mata ba kamar zata rama mata marin kuma wai ta shiga lallashinta tana bata haquri ai wlh naji dadi dan antyn ta gaggaya mata magana ta kuma jaddada mata aurenka babu fashi sedai ta mutu da yake mahaukaciyace se cewa tayi se tayi Ajalinka ni kuwa nayi recording wlh kuma ko kwarzane ya sameka se mun hadu da ita a Kotu akanta zan fara practicing profession dina" Khalifa yaci gaba da magana Khalil dai kallonsa kawai yakeyi shi maganar zata kashe ma bata bashi mamaki ba dan ba yau ya faraji ba tun kafin ya aureta take jaddada masa wannan kuma ta gwada ya gani Munafuka data kira Hajiya dashi ne ya daure masa kai sosai ya bashi mamaki dan be dauka rashin darajarta harya kai haka ba, ya zata dai shi da yake marainin wayonta take zaginsa sanda taso abun akansa ya tsaya ashe ya tsallake ya isa har kan uwar data haifeshi.

Can qasan ransa sosai yake jin fushi da bacin ran abinda tayin yana kuma ayyana abubuwan da zeyi mata na daukar fansa amma kuma cikin zuciyarsa ko kusa ya kasa hasaso laifin da tayi balle ya samu kwarin guiwar hukuntata, dafe kansa yayi yana karanta hasbunallahu wani'imal wakeel a fili seda ya samu yar nutsuwa daga abinda yakeji kafin ya miqe a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ya wuce cikin gidan Khalifa ya bishi da kallo.

UMAIMAH
Dan kanta ta gaji da zage zagen ganin ya haye sama ya barta nan se kuma ta juya kan kayan dake cikin falon ta shiga jifa dasu tana kuka kamar wadda kanta ya tabu, kan kujera ta zube taci gaba da kukan, kamar wadda aka tsikara ta miqe tunawa da maganar Mama Hauwa da tace sunyi magana da Hajiya dazu kuma ta gaya mata a satin nan za'ajewa Khalil neman aure wato ma Hajiya ce ta shirya komai, qila ma ita ta turashi yaga Humairan ita take so ta hada auran me yasa tun farko batayi tunanin bama. Fita tayi ta wuce bangaren Hajiyar, tun daga kan barander ta jiyo muryar Jalilah na cewa
"Nifa bazan tafi ba Hajiya se Hussaini yazo mun qarasa lissafin nan, da za'a bi tatawa ma a hada komai har lefen su tafi dashi kawai a huta da jeka ka dawo kinga gari da nisa ga yanayin hanya an huta tunda daman Mazan ne dai zasu koma su kai"

"Toh uwar Azarbabi duk saurinki dai ai se kin jira sunje sun tambaya ance an basu kafin kice akai lefe ko?" Hajiya ta mayar mata cikin raha kafin Jalilan ta sake cewa wani abu Umaimah ta banka qofar falon ta shiga duk suka kalleta a tsorace saboda bazatan da tayi musu.
"Lafiya Umaimah ko jikin ne?" Hajiya ta fada seta watsawa Hajiyar wani kallo tace
"Dole ki tambayeni ko lafiya Qasurgumar munafuka. Ni daman na sani babu yanda za'ayi wata uwar Miji ta qaunaceka tsakani da Allah har ta fifitaka sama da yayan data haifa ashe jira kike na saki jiki dake kafin ki nuna mun Halinku na rashin Amana to wallahi bari kiji ni kadai kika haifawa Khalil ba kuma ki isa ki sake soko wata mace cikin rayuwarsa ba bayan ni duk wani munafunchi da kutunguilar ku ya qare akanku amma Khalil nan gani nan bari idan bakiyi wasa bama kedashi sedai gani daga nesa dan se nayi...." Marin da Jalilah ta dauketa dashi ne ya sakata yin shirun dole ba tareda ta shirya ha ta dafe idonta da taji kamar an watsa mata barkono a ciki.

Nunata Jalilan tayi tana cewa
"Ke qaramar mahaukaciya ki iya bakinki ki kuma san a inda kike, tsakaninki da Khalil canku gane dan da saninsa ya kwasowa kansa Annoba dan haka duk wani haukanki da dabbanci ya tsaya akansa na rantse da girman Allah koda wasa kika sake takowa nan kika ce zaki harari uwarmu balle har ta kai ga ki zageta sena zubar miki da haqora na karyaki na watsar da abin banza ko yanzu darajar abinda yake jikinki kikaci bazan dakeki na yi dakon rai na amma dana banbance miki tsakanin aya da tsakuwa yanzun mara kunyar qarya"

"Ya isa haka Jalilah, wani irin sakarci ne wanann bakiga a halin da take ciki bane zaki mareta?" Hajiya ta daka mata tsawa se Jalilan ta kalli Hajiya fuska dauke da mamaki tace

"Hajiya naga halin da take ciki Halin hauka ba ta samu zaucewar tunani dan shine ze saka ta aikata abinda tayi yanzu to ko Dawanau ce a kanta qarewarta ita ya shafa nidai na fada" seta juya kan Umaimah dake dafe da ido tace
"Sannan kuma maganar hadin aure da kikeyi ta isa ne shiyasa ta hada, wace uwace ma har zata dauke ido danta ya zauna da shaidaniya irin tsahon shekarun nan bata saka ya kadaki inda ya kwasoki ba? Yazu kuwa aure take so tayi masa da yarinyar kirki data san mutunchin mutane ba irinki ba kuma ko zaki mutu se anyi auran nan in Allah ya yarda".

Cikin qunar rai Umaiman ta kalleta tace
"Haka kikace? To na rantse da Allah se nayi sanadin Khalil sedai kowa ya rasa nida ku duk se dai muyi Asara" tana fadar haka ta juya fuu Hajiya ta bita tana kiran Sunanta Jalilah ma bin bayansu tana cewa
"Ai idan Khalil ya mutu Umaimah se kinfi kowa shiga uku wlh mu sedai muyi jimami na rashin dan uwa ke kuwa Allah dai ya taqaita amma inaga idan baki bishi ba se kin haukace".

Sanda ta koma bangarenta zama tayi a qasa cikin kayan data farfasa ta sake fashewa da kukan dayafi ma dazu, Ruqayya ta tsaya tsuru daga gefe tsoron kulata takeyi karta huce akanta amma haka ta ja numfashi ta matsa kadan tana ce mata
"Hajiya kiyi haquri ki dena kukan nan kodan halin da kike ciki, kishiya ai ba ciwon Ajali bace ba kuma kanki aka fara ba dan Allah ki tattara hankalinki guri daya ki nutsu, addu'a ya kamata ki tashi tsaye kiyi akan duk ma wadda zata shigo Allah ya tsare ki daga sharrinta ya hadaki da Alkhairinta".

"Ruqayya idan kika sake yimun magana se naci abu ta kaza kazan ubanki" Umaiman ta fada tana kallonta da jajayen kumburarrun idanunta da suke tsiyayar sa hawaye kafin ta juya taci gaba da kukan kamar yarinya se kuma ta ta miqe ta shige dakinta, wayarta ta dauka ta shiga kiraj Safinah tana dagawa tace
"Safina duk inda kike duk abinda kikeyi ki bari ki maido mun da kudina da kuka damfareni keda dan abu ta kaza kazan Malaminki, kuma daga yau ko hanya karki bari mu hadu idan ba haka ba sena huce haushin bata mun lokaci da kika kaini akayi kuka yaudareni na dauka aikinsa yayi ashe zagon qasa yayi mun ya daka rusa komai" ta qarasa tana rushewa da kuka.

Safina dake zaune a falo tayi baqi qannen Mijinta ta miqe ta shige daki tana ce musu tana zuwa. Seda ta shiga bandaki ta kullo qofar dan kar wani ya shigo yaji abinda take fada kafin tace
"Haba Umaimah kiyi shiru kiyimun bayani me ya faru kuma? Ina dazu da safe kike ce mun har aiki ya fara ci me kuma ya faru yanzu har ya kawo wannan maganar?"
"Babu ruwanki sa abinda ya faru kwai kiyi abinda nace idan ba haka ba kin san halina wallahi se nazo na farke miki laya, yanda banyi nasara ba kema se Alqadarinki ya karye wlh" Umaiman ta sake fada a fusace se Safina tayi saurin mayar mata itama cikin fushi tace

"Kinga bafa tsoronki nake ji ba da zaki ringa gaya mun magana ina wani lallashinki, aiki na rakaki akayi miki da yardar kuma ba daukarki nayi akai na ballantana kice ke uwar garaje da jaraba an ce miki kibi komai a sannu amma ba haka ba na tabbata yanzun ma wani haukan kika tafka ya warware komai zakizo kina dora laifi akaina. Daman ai na gaya miki ko kinyi Asiri dole ki hada da kissa idan kina so kiga daidai amma ke kamar wadda ake girki a zuciyarta dan qaramin abu kin dau zafi bazaki ringa tankwara zuciyarki kina dauke kai ba ai ita rayuwa bata yuwuwa haka idan kana so kaci riba ai seka yi haquri kayi juriya".

Shiru Umaimah tayi tana rusa mata kuka, Safina ta sake jan tsaki dan harga Allah ita kanta Umaiman ta isheta inaga Khalil kuma ai wallahi yana bala'in qoqari, sake ce mata tayi
"Kinga kuka baya maganin komai gara ki bude baki ki gayamun abinda ya faru najin idan da akwai ta inda zan taimaka miki in kuma Malam zan kira na gaya masa toh se musan abinyi"

"Ni karki sake sakomun wani malam a magana kuma ba haqura nayi ba se kin biyani kudina, bayan yace mun maganar aure zata watse kuma se yanda nayi dasu gashi nan ba inda aka je ni banga komai ba. A gaban Hajiyar yar uwarta take jaddadamun aure babu fashi kuma bata hana ba bayan har naman kan na dafa kuma taci sannan shi kansa na bashi umarnin ya kira yarinyar ya gaya mata ta fita a sabgarsa yaqi qarshe ma se munafukar uwar ruqon nata ce ta daga wayar har takr yaba mun magana tana gayamin wani satin za'aje tambaya, wallahi Safina ji nake kamar na dau wuqa na cakawa kaina kawai na mutu na huta da baqin ciki" ta sake rushewa da Kuka wiwi.

"Yanzu akan dan wannan abun kike kuka kamar wadda akazo daukar ranta wallahi Umaimah Jidalinki na banza da wofi ne. In banda ke banma san me zan kiraki ba shi aikin ce miki akayi ana yi take yanke yake ci daman se kace wani tsafi? To ai ko tsafi Malama se Aljanun sun samu zama a Jikin mutum kafin su fara aikinsu kuma wannan dinma ai kya jira duk abinda kikayi yabi jikinsu kafin kice zaki fara gwada iko nidai nayi mamaki da a dare daya kika ce aiki har yaci koda yake hayaqin da ya baki na Jinnil Ashiq ne da kwarjini to su babu Mamaki idan kince sun miki aiki amma rufin baki dai se a hankali ai bawai nan take ne zasu kasa musa miki ba. Kawai yanzu ki share hawaye ki dena wannan kukan idan kin samu dama gobe ki fito mu koma gun Malam in kuma ba zaki iya ba zan kirashi ko aikene se yayiwo miki a samu a daidaita a shashantar da maganar auran".
Haka ta ringa lallabata tana sake tabbatar mata da ta kwantar da hankalinta tasan aikin Malam zeci kawai haquri zata koya da danne zuciya nadan lokaci kafin Ludayinta ya hau kan Dawo seda taga ta dan nutsu kafin sukayi sallama akan gobe ita Safinan zataje gurin Malam taji koda abinda ze qara bata tunda ita Umaimah ta kafe bazata koma ba kuma se an biyata kudinta. A nan inda suka gama waya da Safina baccin wahala yayi gaba da ita, bata farka ba se uku da motsi na dare shima wata Azababbiyar Yunwa ce ta tada ta se a sannan tayi sallar Magriba da Ishar da batayi ba.

KHALIL
Tunda ya samu ya haye Sama ba tareda sun sake haduwa da Umaimah ba be sakko ba, yana so yaje gurin Hajiya amma besan me zece mata ba. Matarsa ta zageta ta kirata munafuka amma ya kasa yin komai to da wanne ido ze kalli Hajiyar?
Haka ya kwana saqa da warwara akan abinda ya kamata yayi, wani sashe na zuciyarsa yana ganin beyiwa Humaira Adalci ba da yake shirin janyota cikin wannan rayuwar da yake a ciki inda wani bangare yake tabbatar masa da ita ce warakarsa, za kuma ta fiddashi daga duk wani qunci da damuwa da yake ciki ta maye masa da tarin farinciki da ya dade yana mafarkin samu idan Umaimah ta barsu kenan.

Tunanin raba musu gida ya fado masa yana ganin hakan shine ze kawo masa sauqin da kuma kwanciyar hankali idan ya zamana kowacce tana muhallinta na daban ba kamar yanda Su Jalilah suke fadin ya ajiye Humaira a nan separate part dinsa na Sama da Umaimah ta hanashi amfani dashi hasashenta ya tabbata kenan daman da tace dan wata ya gina gaskiya baya zaton haka zata yuwuwu gara ya gyara tsohon gidansu da suka taso ya ajiye Humairan a can yafi musu kwanciyar hankali daga shi har ita. Yana gama tunanin ya miqe ya dakko Laptop dinsa, seda ya duba lokaci sha biyu ta gota kafin ya bude ya shiga binciko proposal design din dayayi ze maida ginin dan da yayi niyyar ya gyara shi ne ya siyar amma yanzu zeyi masa amfani. Zanen ya duba ya dakko takadda da biro ya shiga lissafin abinda yake ganin ze kashe da tsahon lokacin da ze dauka kafin ya kammalu, a nasa lissafin idan yayi sauri yana ganin ze gama a wata uku in kuma yaja lokaci wata biyar zuwa shida, akan wata shidan ya bari ze gayawa su Baba Abu idan sunje neman auran su saka rana wata shidan zuwa sannan yasan hatta ita Umaiman tayi duk abinda zatayi ta saduda shikenan.

Washe gari bakwai bata qarasa ba ya bar gidan, a waya ya kira Hajiya yayi mata qaryar ya tafi Rano, yanda batayi masa maganar jiya ha shima beyi ba illah ce masa da tayi Jalilah ta kawo kaya jiya idan ya dawo ya shiga ya gani yace mata toh gaba daya beji dadi ba saboda yanda yaji muryarta yasan abinda Umaiman tayi mata ya doketa sosai kawai dai ta shanye ne bata nuna ba. Seda ya kira Habiba ta tabbatar masa Hajiyar na lafiya kawai dai magana ce bata cikayi ba tun jiyan se ta zauna tayi shiru yace mata ta zauna da ita karta ringa bari tana tunanin saboda jininta idan ya dawo ze shigo, haka ya tafi office ya zauna aikin ma ya gagara yi kansa ciwo ya ke masa, shafa ya manta ma jiyan beci abinci ba seda Anwar yazo yake ce masa ko karyawa beyi ba ya fito saboda ya ce masa yana office sannan suka fita tare sukaje cin abinci.

Suna dabda komawa Kiran Baba Abu ya shiga wayarsa, seda gabansa ya fadi ya daga da sallama kamar yanda yayi tunani kuwa ko amsa masa beyi ba ya dira fada ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba fadi yake
"Ibrahim wace irin shaidaniya kake zaune da ita a matsayin Matane yanzu ace rashin tarbiyyar yarinyar nan har ya kai ta kalli idon uwarka ta kirata munafuka saboda ta shahara a rashin mutunchi? Wallahi badan dattijantaka irin ta uban ta ba da nace ka sakar musu ita kowa ya huta amma iyayenta mutanen kirki ne, Jarabawa ce da kowanne bawa baya rabo da kalar tasa Allah ya basu wannan yarinya amma dukda haka ba zamu zuba mata ido ta tinga iskanci yanda taga dama a rasa me taka mata burki ba, ina dai akan kiahiya take wannan diban Albarkar ko to kuwa aure babu fashi, da na cewa Hajiyar se qarshen wata zamuje toh na fasa, yanzu zan kira Alhaji Garba da Sabi'u da Imrana tunda dasu zamuje na gaya musu duk su shirya Juma'ar nan mu tafi mu kwana a can Asabar mu juyo, seka shirya dan tare zamuje dakai gu ganka ko ka gaida surukan naka amma wannan mata taka dole ka tashi tsaye ka dauki mataki a kanta, idan ta kama kasa ayita sauke mata qur'ani in makarai ne a kanta masu son tada husuma duk ayi maganinta".

Shidai har Baba Abu ya gama banbaminsa bece komai ba seda yayi shiru kafin yace masa toh, Allah ya kaimu Juma'ar kwanaki uku harda ranar masu zuwa kenan dan suna Talata. Yana gama wayar Anwar da yaji kusan rabin maganar ya kalleshi fuska a sake yace
"Ango kace uwargida tayi bore ta sakw ballowa kanta ruwa to Allah ya fitar da ita"
"Hmm" kawai Khalil yace masa ya wuce Office dinsa zuciyarsa duk babu dadi. Ana cikin wannan halin wane Jalingo zasu tafi kuma itama Jalilah tana da matsala wani lojacin akan me zataje ta gayawa Baba Abu yanzu daya gayawa Hajiya Mansura Matarsa ya tabbata yanzu dangi duk se sunji labari su qara sakata a gaba.

Bayan sun fito sallar Azahar ya duba wayarsa yaga Humaira ta tura masa da saqon ban haquri, murmushi yayi ya kirata tana dagawa ta fasa masa kuka, Khalil ya dafe kansa da daman a cike yake da damuwar Umaimah yace
"Me kuma ya faru?"
"Ba kaine kake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login