Showing 246001 words to 249000 words out of 429394 words

Chapter 83 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

943

yanzu na shigo wanka kawai nayi".

"Bari na zuba maka abinci toh" ta fada tana qoqarin kaiwa qasa se yayi saurin dakatar da ita da cewa
"Aa, I'm full naci gurin Hajiya kafin na shigo".
Yanda tayi da fuska ya nuna rashin jin dadinta amma ta daure ta tsiyaya Zobon a cup ta miqa masa tana cewa
"Ga zobo toh nasan dai shi ba zaka ce ba zaka sha ba".

Karba yayi ba tareda yasha dinba, haka kawai yau yakejin shakkar cin abinda ya fito daga hannun Umaiman, badan yana zarginta da yi masa wani abun ba sedai kawai chanjin fuskar tata a abinda be wuci awa biyu ba ya bashi mamaki, dole tana da wani shiri daya sakata aikata hakan.
Ganin ya riqe kofin be sha ba ya saka ta tsiyayawa a wani kofin itama ta sha, Khalil dake kallonta yayi murmushi a ransa yace
"Ta wanke kanta" kafin ya kafa cup din shima ya kwalkwale dan sosai zobon yayi masa dadi harda qara wani ya sake sha.

Umaimah ta saki murmushin jin dadi ganin haqanta yana dab da cimma ruwa seta dauki Bowl din fruit Salad din ta bude ta saka masa cokali ciki ta miqa masa babu musu kuwa ya karba ya hau sha ita kuma tana masa hira babu laifi kuma ya biyeta yana amsawa dukda rabin hankalinsa nakan labaran da yake kallo.

Agogon falon na buga qarfe goma ta miqe, Khalil ya daga kai ya kalleta, wani yumm yakeji a jikinsa daya rasa kona menene gaba daya neman rasa nutsuwarsa yakeyi. Da kanta ta ringa kwashe kwanukan tana kai su bakin qofar shigowa falon kafin ta kwalawa Ruqayya kira akan tazo ta kwashe su, tana tsaye a gurin har ta gama kwashewa tas tayi mata seda safe kafin ta waiwaya ta kalli Khalil da shima ita yake ta bida kallo tayi masa murmushi sannan ta shige dakinta.

Ajiyar zuciya Khalil ya sauke yana gyara kwanciyarsa dan zaman ya gagareshi. Zuwa sannan ya gama fahimtar abinda yake faruwa dashi, wato Umaimah magani ta saka masa a Zobon nan kenan? Juye juye ya shigayi shi kadai kamar me naquda saboda wani azababben feelings da yaji ya taso masa. Daman can haquri yake yana dauke kai shine saboda mugunta yanzu zata janyo masa wahala. Yafi minti talatin yana malelekuwa tsakanin kan kujerar da qasan a zuciyarsa ya qudurce ze daure bazeje gareta ba dan har yanzu be tabbatar da ta ladabtu akan abinda ta aimata masa ba sannan ga wani ta qara, akan me zata cutar dashi ta saka masa magani a abinci?

Ganin abin yana neman ya zamar masa babba yasa ya miqe dakyar ya nufi dakinta, dakyar yake iya daga qafarsa saboda wani mugun qullewa da ciwo da mararsa take masa daga ji maganin ba kadan ta saka masa ba ko kuma ba a iya zobon bane ta yuwu har fruit salad din ta zuba a ciki. A hankali ya tura qofar dakinta dake a bude, cak ya tsaya saboda jiyo muryarta da yayi da alamar waya takeyi tana cewa wadda suke maganar
"Kin tabbata kuwa maganin nan zeyi aiki? Kusan awa daya fa har yanzu shiru ni banga yayi wani abu ba".

Be san me waccen tace mata ba yaji ta sake yin tsaki tana cewa
"Wallahi nima nasha gani nayi kamarbe yadda da zobon ba yanata juyashi a hannu shine nasha kadan gashi ni duk ya dameni ma wallahi", shiru ta sakeyi kafin tace
"Bana son iskanci kedai ki tayani Addu'a na samu kansa dan nikam da gaji da wannan zama hala ta ko ina komai ya qulle mun ina zan saka raina naji dadi" daga nan sukayi sallama taci gaba da shafa man da takeyi da alama daga wanka ta fito.

Fita yayi daga dakin ya dafe bango yana maida numfashi dan bayajin zeiya zuwa gareta kuma, Wato saboda biyan wata buqata tata yasa ta saka masa magani kenan bawai dan tana da buqatarsa ba to wacce buqatace haka? Ya tambayi kansa. Dakinsa ya koma dakyar ya kwanta kwanciyar taqi masa dadi, dole ya miqe ya dakko ruwa me sanyin gaske yasha ko zeji sauqin abinda ke damunsa ammaa banza ji yayi ma kamar qara masa akeyi. Miqewa yayi da niyyaryaje ya watsa ruwa ko ze samu Sa'ida Umaimah ta turo qofar dakin da sallama. Cura mata ido yayi zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri qamshin turarukan data saka suna sake rikita masa hankali a sannu ta tako zuwa inda yake duk yanda yaso ya yaqi zuciyarsa ta shareta amma ya kasa kafin ma ta qaraso ya janyota jikinsa ya shiga shinshinata kamar wani mayen kare be jira wani abu ba ya sunkuceta ko nauyin ta dana cikin jikinta beji ba ya direta akan gado kafin ya bita suka kwanta.

Sosai suka gurji Junansu cikin tsantsar soyayya da kewar da kowanne yayiwa dan uwan nasa ga tasirin maganin data zuba masan yasa suka dade cikin shauqi har seda ta gaji ta fara masa kukan shagwaba kafin ya iya kyaleta. Tsam ya rungumeta a Jikinsa yana sauke numfashi. Yana son Umaimah tana kuma da matsayi na musamman a zuciyarsa saboda yanda take bashi nutsuwar daya tabbatar baze samu kamarta a gurin kowa ba se itan amma halin ta na kishi da rashin jin magana yake hada shi da ita.

Tare suka kwana a gadonsa bayan lokaci me tsawo da suka dauka basu hada shimfidar ba, a daren kuma ma'auratan suka sasanta. Sosai Umaiman ta kwantar da kai ta ringa sake nanata ban haquri tareda tarin alqawarurrukan ta shiga hankalinta ba zata sake ba. Za kuma ta dage da Addu'a Allah ya maida masa da mafiyin Alkhairin abinda tayi masa sanadiyyar rasawa. Toh Khalil da Umaimansa dai se Allah haka ya karbi tuban mutuniyar ya kuma rungumi abarsa suka shiga shimfida sabuwar rayuwa me ciki da qauna da zaman lafiya.

Sati daya a tsakanin ranar wata Juma'a da safe Mansur ya sake kiransa akan Abokin nasa ya iso yana Kano kuma a yau din ze wuce zuwa Kebbi garinsu dan haka yayi qoqari su hadu ya karbi saqon. Yana Office lokacin daya kirashin yana shirin fita duba wani Site, dan haka ya kira AbdulMajid babban yaronsa da yake aike ya bashi muqullin motarsa tareda number mutumin ya tafi ya karbo saqon shi kuma suka fita a motar company tareda sauran Engineers dinda zasuje Site din. Ranar cur a Site dinya wuni dan can AbdulMajid ya bishi da motar saboda baze koma Office ba.

Guraren qarfe Shida ya kama hanyar gida yana tafe yana sakin qananan tsaki saboda muguwar Gajiyar da yayi ga Umaimah bata nan sun tafi gidansu wuni tace kuma se dare ma zasu dawo bashi da tabbacin tayi girki kafinta fita abinda ya qara bata masa rai kenan dan Yunwa yakeji. Yana tsaye a Traffic ta cikin center Mirror ya hango Baqar leda wadda yake zaton itace saqon Maman su Mansur. Tsaki yayi dan shaf ya manta da batun saqon ma kuma ko a dazunda sukayi waya seda ya sake jaddada masa akan dan Allah ya kai mata gaba daya wanda take sha sun qare,Hawan Jini ne da Sugar suke damun Maman dan haka ya juya akalar motarsa ya dauki hanyar gidan Maman. idonsa.

Seda ya tsaya a hanya ya siyi gasashshiyar Kaza da Yoghurt manyan roba masu sanyi ya qara da Gwangwanin Madara da Milo, Sugar se buredi kafin ya kama hanyar gidan su Mansur. Sanda ya isa be tarar da kowa a qofar gidan ba majalisar da Habibu qanin Mansur yake hadawa da Abokansa duk basa nan jin ana kwada kiran sallar Magriba ya saka ya dauki ledojin ya kira wani Almajiri daya zo wucewa ya taya shi dauka suka shiga gidan dan qofar a bude take. A bakin qaramar qofar da za'a shiga tsakar gidan ya tsaya tareda yin Sallama.

Gidan tsit kamar babu kowa a ciki ga duhun Magriba daya fara kawo kai dan babu wutar lantarki, daga bakin famfo ya hango kamar mutum tsugunne yana alwala dan haka ya sake daga murya yayi sallama suna shiga cikin gidan.

Saurin jan Hijabi Humaira dake Alwala tayi ta rufe kanta kafin ta juyo tana wanke qafarta ta amsa sallamar tasa. Cikin hasken daya ragena rana Khalil din ya ga fuskarta, dukda be gane wacece ba haka suka qarasa shiga cikin gidan, ta qarasa Alwalar ta nufosu daidai nan aka kawo wutar Nefa haskenta ya gauraye tsakar gidan gaba daya. Daga dan nesa Humairan ta tsaya ttanayi masa sannu da zuwa.
Khalil daya bita da kallo yana so ya tantance wacece ita dan dai qannen Mansur Mata biyu ne kuma duk sunyi aure, babu ma me qananun shekaru kamarta. Dauke idonsa yayi daga kanta yace
"Mama tana ciki?" kafin ta bashi amsa Maman ta daga labulen palour ta tana cewa
"Aa, Khalilullahi ne yau a gidan bismillah shigo ciki mana ka tsaya kamar baqo, ina ciki Alwala nakeyi nima".

Sake kallon Humaira yayi wadda itama shidin take kallo kafin ya shiga falon Maman Yaron na biye dashi a baya da Ledoji, karba yayi ya sgiga dasu kafinya zaro dari biyu a Aljihunsa ya bashi ya karba yana godiya ya fita. Seya koma bakin famfon data baro ya shiga daura Alwala jin an shiga Masallaci yana gamawa ya fice daga gidan da sauri ya tafi masallacin. Se bayan da aka idar ya dawo gidan, a falo ya tarar da Maman inda ta idar da sallah tana lazumi yana zama aka dauke wuta.

"Oh kaga mutanen nan se da duhu ya kawo kai da sun kawo wutar kamar gaske kuma sun dauke abarsu" Maman ta fada tana kunna fitilar data ajiye daga gefe sanin daman wutar babu tabbas. Khalil ya kunna Flash ligh din wayarsa shima kafin ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarsa Hajiya dasu Umaimah yace duk suna lafiya.

"Bari a tada Gen din toh Mama, ya kamata ma dai a hada miki solar ki huta kawai" Khalil ya fada yana miqewa tsaye Mama ta ce
"Aiko Allah sa fetur din ma be qare ba, daman Habibu ne duk yake wannan hidimar tunda ya koma makaranta kuma shikenan sedai in sun kawo wutar muga haske idan basu kawo ba zauna a duhun dan waccen salo salon ba iya tada injin tayi ba niko bazan iya yawon kiran yaran maqota ba kullum".

Fita yayi ya wuce gurin injin, Seda ya bude ciki yaga babu mai ko kadan ya qare. Jarkan da Ake zuba man ya duba na cikin ma bashi da wani yawa ko an zuba baze wuce daren yau ba ze qare dan haka ya juye ya kunna Injin kafin ya fito da Jarkar a hannunsa. Humairah na tsaye a bakin qofar dakin Injin, cikin muryarta me sanyi tace
"Daman Mama ce tace nakawo maka fitila ka haska kuma naga kama gama" be amsa taba ya wuceta ya ajiye jarkar a baqin qofa kafin ya leqa yana cewa Maman zeje ya dawo.
Gidan Mai yaje aka ciko masa jarkar taf kafin ya sake komawa gidan. Seda yayi musu magana akan ze kashe injin ya qara Mai kafin ya kashe, full tank yayi musu ya ajiye ragowar kafin ya fito ya tsaya bakin famfo yana duba inda zega omo. Humaira ta fito daga kitchen dauke da Try data shiryo kayan abinci, fahimtar abinda yake nema yasa ta ajiye akan barander ta dawo bakin famfon ta dakko ledar klin ta miqa masa. Hannu ta miqo mata alamar ta zuba masa, cikin sanyin da kana gani kasan dabi'arta ce ta shiga zazzaga masa klin din. Khalil dayaji tamkar ya fizge ledar saboda yanda take laqai laqai ya dago da niyyar ce mata tayi sauri ta zuba daidai nan itama ta dago suka hada ido. Wata faduwar gaba ce ta ziyarce shi, abinda ya gaza fahimtar ko menene ya soki zuciyarsa se kawai yaja tsaki ya fizge ledar Klin din daga hannunta tana ganin haka itama cikin sanyi ta wuceta barshi a gurin. A falon Mama ta aje masa Abincin data saka ta hado masa ta wuce can kan dining taja kujera ta zauna tana jin qirjinta yana bugawa da sauri da sauri.

Khalil ya gama wanke hannunsa ya koma falon, Mama ta gabatar masa da abincin be musa ba yaja Try din gabansa ya bude. Lafiyayyen Tuwon shinkafa ne fari qal yanda aka lailayeshi a leda kadai ya isa ya sa kayi sha'awar ci. Leda biyu ya ware ya saka a plate dan malmalar bata da girma kafin ya janyo flask din Miyar ya bude qamshin Miyar hade dana man shanun da aka bita dashi ya bugi hancinsa har seda ya lumshe ido ya bude. Shidai yana son abinci, both Local and continental dishes girki kuma yana daya daga cikin makaman da Umaimah take yaqarsa dasu dan bata barinsa da yunwa koda yaushe cikin yi masa girkuna masu dade da kashe kwadayi take.

Sosai ya kwashi tuwon dan bayan wanda ya saka seda ya qara Malmala daya. Dukda yana fara ci ya fuskanci ba girkin Maman bane, yanda yake son abinci haka yake iya gane banbancin dandano musamman na abincin wadanda yake so yake kuma ci dan Maman ta iya abinci, zamanin quruciyarsu haka suka rabawa yau idan anci na Hajiya to gobe abincin Mama za'aci, be damu da son jin wa yayi abincin ba tunda ya masa dadi daga yanayinsa kuma ya tabbatar da tsafta da ingancinsa dan haka ya ware ciki ya kwashi abinci dan yasan ba samu zeyi ba idan ya koma gida ba dan Umaimah bata nan Hajiya kuwa yanzu idan ya shiga cin abinci ta ringa fada kenan tana ganin kamar har yanzu basa zaman lafiya da Umaiman ne shiyasa yake zuwa can neman abinci.

A nan yayi sallar Isha, be bar gidan Maman Mansur ba se gurin Tara saboda hira da suka zauna tana ta tuna masa da lokacin quruciyarsu, ya kira Mansur ya hadasu ya sake yi mata bayanin magungunan seda Umaimah ta kirashi akan sun dawo taga baya gida kafin yayiwa Mama sallama ya tashi tafiya tana ta saka masa Albarka da godiyar siyayyar daya yiwo musu.

A waje daya fita ya lura da an dawo da wuta, har ya bude motarsa ya kashe ya koma. Mama na tsakar gida ta fito shanya Hijabinta da ruwa ya zuba akai tace
"Aa, Khalil ashe baka tafi ba mantuwa kayi halan"
"Aa Mama naga an dawo da wuta ne shine nace bari na dawo na kashe muku injin, ina yarinyar take na nuna mata yanda ake kunnawa koda ace sun qara daukewa" Khalil din ya bata amsa. Seta daga murya ta kwalawa Humaira kira ta fito da sauri tana amsawa, Khalil ya bita da kallo ganin yanda ta fito itama ganin sa tsaye yasa ta juya da saurin gaske har tana shirin faduwa Mama nace mata tabi a sannu ta shige dakin.

Hijabi ta zumbulo kan Doguwar riga me hannun vest dake jikinta dan ko dan kwali bata dauko ba ta fito amsa kiran Maman san sam batayi zaton wani ya shigo gidan ba. Kanta a qasa kamar tana gaban suruki ta qarasa tana cewa Maman gata.
"Yayanki ne yace yace kizo ya nuna miki yanda ake kunna Inji da kashewa saboda wata rana, banda ma sakarcinki abinda sukace muqulli ake murdawa ina wahala a ciki" Maman ta fada tana nuna mata Khalil daya shige inda Injin yake se tabi bayansa tana tafiya a hankali. Itafa tsoron taba Injin take, tunda wani dan Unguwar yaje kunna inji yayi bindiga wuta ta kama har jikinsa ya qone sosai har yanzu be gama warkewa ba kusan fin shekara shiyasa take baya baya da sabgar Injin ko Yaya Habib yace taje ta haska masa daga baya take tsayawa.

"Ki dago qafa Malama sauri nakeyi fa" taji muryar Khalil akanta se ta daga qafar ta qarasa. Daga bakin gurin ta maqale tana leqensa, Khalil kalleta ganin yanda ta tsaya kamar wadda take tsoron wani abu ya kamata be san lokacin da ya ja tsaki ba yace
"Da Allah ki matso ko wani abun ne ze kamaki a nan din?"

Cikin sanyin murya kamar me shirin kuka har tana jan qafafunta baya tace
"Ni tsoro nakeji bana son zuwa kusa sa Gen" se kawai ya saki baki galala yana kallonta tsabar mamaki wai tsoro takeji Kura ne ko Zaki da zataji tsoronsa?
Hadiye bacin ransa yayi yace mata
"Ki matso babu abinda zeyi miki" ya fada yana kallonta. Seda ta zuba masa idanunta da suke masa wani iri idantana kallonsa kafin ta matsa kusa dashi din kadan a haka ya nuna mata inda ake Kunnawa da kashewa da inda zata danna wuta ta kawo kafin ya matsa yace tazo ta kashe Injin. Yana kallon hannunta har rawa yake ta murda muqullin ta kashe, Change over bashi da tsaho dan haka yace ta daga ta mayar dashi Nepa bata musa ba jikinta na rawa tayi abinda yace dan ya tsare fuska ganin hasken Nepa ya gauraye gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya Khalil ya kalleta yace
"Ba gashi nan ba yanzun meya cijeki da zakice kina jin tsoro?"

Bata amsa shi ba se kanta data sunkuyar tana wasa da zoben hannunta ya wuce ya barta a gurin bata ma lura ba seda ta jiyo shi yanayi Mama sallama kafin taja qafafunta ta wuce itama.
"Seda safe" ta fada daidai ze gota ta ya fita, ya waiga ya kalleta kawai ba tareda ya amsa na ya fice daga gidan se tabi bayansa ta kulle qofar ta dawo tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi wani abun ta cire Hijabinta ta aje kan kujera tana kallon Mama tace
"Mama shine baban Mu'ayyad ko?"
"Oh ni Humaira gani daya kin riqe sunan yaron nan ni wallahi mantawa nakw shiyasa kawai nake ce masa ina su Alhaji amma ke caraf kin riqe, me yasa to baki tambaye shi yana ina ba?"

"Tab ni tsoronsa ma nakeji wallahi Mama ina kallonsa se naji gabana ya fadi tun lokacin da yake zuwa gidan nan gun Yah Mansur" Humairan ta fada se Mama ta girgiza kai tace
"Ai kowama tsoronsa kikeyi ke daman ki wuce ki debo abinci kici toh".
Miqewa tayi ta zubo tuwon ta dawo taba ci tana yiwa Maman zancen Mu'ayyad wai tana so taga yaron yanzu tasan ya girma sosai. Tun lokacin da Umaimah tajewa Mama yawon arba'in Yaron ya shiga ranta sosai, tayita nacin suje gidansu da Mama amma taqi sedai suje gidan Hajiya.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login