Showing 39001 words to 42000 words out of 429394 words

Chapter 14 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

944

irin wadannan abubuwan indai ba lalura ba yanzu ina kai ina hada jiki dasu yanzu ai ko dan gudun bacin ran matarka ka kiyaye ai"

"Yanzu dai Hajiya duk baki fahimci abinda nake nufi ba" Khalil ya fada kamar ze fasa kuka, hujjar da yake ganin ze fake da ita ya fada amma bata da niyyar fahimtar sa sema qara goyon bayan Umaiman takeyi, shi kuma baya so ya fada mata furucin ta na na kisa saboda gudun abinda zeje ya dawo toh yanzu yaya zeyi?
Haka ze zuba ido yana ji yana gani a qulla masa ita.

"Idan ma wani ne ko wata ya zugoka zaka zo ka mayar da mutane qananan mutane tun wuri ka koma ka gaya musu basuyi nasara ba, koda wani ya zabo maka ita ba kai kace kana sonta zaka aureta ba? Daga Ilun har Zahra'un ai na gaya musu babu wannan maganar dan dukda Badawiyya take tawa amma nasan Umaimah ta fita Nagarta nesa ba kusa ba" Hajiya ta fada cikin tsare gida, seya daga kai ya kalleta da mamaki yace

"Hajiya Kawu Ilu kuma? Me yace miki ni bamuyi wata magana dashi ba wallahi rabona ma da gidan sa tun sanda na kaiki kika duba Fauzan da bashi da lafiya, kuma magana tsakanina da Badawiyya da take tsohon zance, ita fa taqini kuma ni ban sake koma mata ba shine yanzu zasu dawo da maganar"

Oho dai duk ma yanda kukayi nidai na qara jaddada musu da babu wannan magana kuma koda ace babu saka ranar wata akanka bazaka aureta ba. Nan yazo yana zancen wani a qarfafa zumunchi tunda daman ka taba nemanta ayi haquri da abinda ya wuce yanzu ta gama karatu kamata yayi ka dawo ayi aure ita wannan tunda yarinyar mutane a basu haquri ace ka fasa gida be qoshi ba ba'a kaiwa dawa ba, nayi masa fata fata be daddara ba ya sake turo uwarta itama na silleta tas

Wato ada tunda baka da abin duniya shi yasa suka qi hadin yanzu ka samu Allah ya buda maka?shine zasu lallabo yarsu taqi auruwa su liqa maka ba yanzu ko nan gaba babu wannan maganar dan hakan idan ma sune suka hure maka kunne, kai ko Asiri suka maka sena warwareshi auren ka da Umaimah babu fashi sedai idan iyayenta ne sukace sun fasa baka".

Sababi Hajiyan ta hauyi tana tariyo masa abinda ya faru a baya lokacin daya taba neman yar qanwar Babansu Badawiyya, ganin abinbana qare bane yayi musu sallama a hanya yana tafe yana mamakin wai Kawu Ilu da Goggo Zara'u ne suka iya duban idon Hajiya suce ya komawa Badawiyya.

Kusan ze iya cewa a rayuwar sa kaf itace mace ta farko daya taba sha'awar yin zaman aure da ita duk da asannan daga shi har ita suna da qananun shekaru basu kai ga isa aure ba. Sunyi soyayya a lokacin Mahaifinsa yana da rai duk abinda ya samu Badawiyya lokacin yana karatu a UK idan z dawo haka ze shaqo mata uban akwati da tsaraba su karbe baki har kunne a sannan babu ya ita a Yayan dangi bare aje ga yan unguwa.

Bayan rasuwar Mahaifinsu lokacin da al'amura suka chanza suka rasa duk abinda suka mallaka se kuma aka bude sabon shafi, da farko bashi da matsala da yarinyar amma idan yaje gidansu ba kamar yanda ya saba ba Goggo Zara'u ta ringa haba haba dashi kenan kamar sabon jariri, abinci kuwa idan aka fara jera masa kwanuka se yace a barshi haka amma da rayuwa ta canza ya zama ko ruwan sha seya roqa,

tafi tafi ma zancan aka koma yi a soro dan se Goggonn taji zuwan sa zata baje kolinta a palour da suka saba zama suyi hirar, gaisuwa kuwa tana shan qamshi da yatsina zata amsa masa daga baya ta hurewa yarinyar kunne itama ta fara lale masa nata katin rashin mutunchin tunba da samari suka yo mata caa ba saboda a sannan ta sake zama cikakkiyar budurwa gata da kyakykyawar sufa.

Wulaqanci na qarshe da akayi masa da ya saka ya janye jikinsa gaba daya shine bayan ta qare secondary school, a yanda aka tsara acan baya data gama za'a daura musu aure dan da ita da iyayenta basu da sha'awar taci gaba da karatu dukda Khalil din yaso haka sukaqi, se gashi wata rana yaje gidan Babanta da kansa ya tareshi akan wai ya dakata da zuwa saboda Badawiyya zata fara zuwa makaranta kuma zuwansa ze ringa dauke mata hankali.

Sosai yaji dadi, ya tattara dan abinda yake hannunsa duk da a lokacin suna cikin matsi sosai yace tayi littattafai se gashi ashe makarantar tara samari ta shiga, qofar gidansu ta zama majalissar Samari da Alhazan birni wannan yazo wannan ya tafi Goggo Zara'u ko murna yarta me farin jini kowa yazo ya ajiye masu abin arziqi.

Tun tana boye wa karya sani har ta fito fili take abu ta ko a gaban idon sa ne zata tsaya da saurayu, Tsabar cin fuska wani lokacin idan zatayi zancen ya zama Baqon na musamman ne ma nan gidan su take kawo shi, da yaso yayi magana Hajiya tace ya barsu, duniya ce ta ishi kowa se gashi tun ba'aje da nisa ba kasuwar samarin ta watse ba tareda an samu na aure ba, shine kuma saboda tsabar rashin kunya suka dawo suna rara gefe harda cewar ya fasa auran wata ya komawa yarsu tunda daman Asali ita ya fara nema dan Adam kenan.

Gaba daya haka ya qarar da ranar daga tunanin mafitar lamarin Umaimah se jinjina qarfin hali irin na iyayen Badawiyya, toshi yanzu ko ya rasa macen aure me zeyi da ita? Yarinyar da ba daya ba biyu ba yasha ganinta a mabanbantan Hotels a lokacin da take ganiyar rashin mutunchinta ta kuma maze tamkar babu wata alaqa ta jini bare soyayya a tsakanin su ita za'a ce ya koma ya aura ai gara ya qarata da Umaimarsa sau dubu dan yana son abarsa, halinta ne kawai yake bashi tsoro.

Harya kwanta bacci be sake ganin kiranta ko saqon waya ba, kenan da gaske ta haqura da auran itama ta daura sabuwar Aniyar addabar rayuwarsa. a ransa ya qudurce baze nemeta ba, idan ta sake kiransa ze haqura ya dauka zabin da Allah ya masa kenan daga nan ya gindaya mata duk sharudan da suka kamata idan taji ta yarda shikenan amma idan bata kirashi ba tabbas sedai Hajiya tayi haquri amma wannan magana ta watse babu ita hakan yana nuni da rabuwar ce mafi Alkairi.

Umaimah

A can Asibiti kuwa se Yamma Lis Umaimah ta farka daga dogon baccin dolen da likita ya sakata, jikinta yayi tibis dan banda idonta babu abinda take iya motsawa se kallon yan uwanta dake ta kaikawo a dakin suna mata sannu takeyi. Anty Saratu da Anty Hafsa babbar yayarsu ne suka kamata suka kaita Bandaki saboda Fitsari datace tana so tayi daga nan Antyn Hafsan ta hada ruwa ta taimaka mata tayi wanka ko zata ji qarfin jikinta hakan kuwa ya taimaka tana gamawa ta dauro Alwala suka fito.

Cikin kayan da Anty ta debo mata dazu ta bata duguwar riga mara nauyi ta saka, shayin data hada mata kafin tayi wanka ta miqa mata ta shiga yatsina fuska alamar bazata sha ba, da rarrashi da komai suka sakata tasha shayin, se gashi ta bige da cin faten dankali da Yaya Hajiyayye ta kawo taci sosai ta dora da wani kofin shayin nan da nan kuzarin jikinta ya fara dawowa dan harda Yunwa a mutuwar jikin nata saboda ko karyawa batayi ba.

Seda tayi sallar Azahar da la'asar kafin ta idar aka kira Magriba dan haka ta hada tayi, ta mimmiqe qafafu akan sallayar ya gawar sababi anata yi mata sannu tana gyada kai tana qare musu Kallo, kowa ya hallara a dakin banda Mama, can kawai se ji sukayi ta fashe da kuka na irin wanda ya tuni wani gagarumin abu da yake ci masa rai.

Gaba dayansu suka gigice saboda yanda dazun wata Nurse me shegen kanbama abu ta rikitasu akan jikin Umaiman, fadi take Zuciyarta ta kumbura qiris ya rage ta fashe dan haka dole a lallabata kar a kuskura wani abu ya sake bata mata rai, zancenta ya gigita Yaya Aminu har seda ya tafi gurin likita babu shiri dan ya tabbatar nan fa likitan ya rufe Nurse din da fada yana tuhumarta akan me zata fadi qarya abinda ba haka ba, ya gaya musu gaskiyar abinda yake damunta, babu abinda ya samu zuciyarta kawai dai idan taci gaba da shiga halin damuwar ne suke ganin zata iya samun matsala.

"A haf duk daya abinda ta fada kenan itama ai kawai dai saboda hankalin mu ya kwanta ne ya saka ya wani sassauta abin, koma menene mudai fatan mu Allah ya bata lafiya" Yaya Hafsa ta fada.

"Umaimah menene? Meya same ki ko jikinne?" Suka hada baki waje fada kowa na qoqarin zuwa inda take, mutuniyar an samu yanda ake so ai nan ta kware baki ta ringa zunduma ihu baji ba gani, idan ta tuna wai fa Khalil yace ya fasa auranta se taja wani Kukan me hade da shashsheqa ta dafe qirji duk tabi ta ruda bayin Allah sunyi cirko cirko akanta, Anty Momy matar Yaya Aminu ce tayi hanzarin tafiya kiran Likita, yazo ya ringa balbaka musu masifa kuwa akan me zasu tada mata da hankali,

me suka fada mata daya saka ta kuka haka kowa dai tayi gum da baki tana kallon ikon Allah to su me suka ce kuma? Qarshe da daya da daya suka silale aka barta ita da Anty bayan da likitan ya mayar mata da ruwan da aka cire mata, se lallashin ta yake tana ajiyar zuciya kamar wata yar baby, bw bar dakin ba seda ya jawa Anty kunne akan a guji abinda ze bata mata rai ko ya sakata kuka, magana idan ba dole ba ayi shiru saboda basu sani ba ko zasu fadi wani abun da ze sosa mata rai.

Haka suka kwana Anty dole tayi gum daga sannu se idan zata tambayeta ko akwai abinda take da buqata ne, nan Umaimah ta samu yanda take so, kwana tayi tana tsara yanda cikin ruwan sanyi zata saka su nemo mata Khalil su sasanta ba tareda hankalinta ya sake tashi ba dan ta rantse ita da Khalil mutu ka raba, badai yace ya fasa auranta ba wallahi.

A haka ta shafe kwana uku a Asibitin kafin aka sallameta, sau daya Mama taje dubata dan ita dai tace kallonsu kawai takeyi amma bata yarda da wannan rashin lafiya ta Umaimah ba, Anty data sha zaman jinya har qaramin ciwo tayi itama bayan an sallamosu saboda fi'ilin datasha gurin Umaimah.

A gidan ma bata haqura ba sabon salo ta fito dashi na zaman daki bata leqowa ko qofar dakin tana ciki duk kuma sanda za'a leqata kuka takeyi seda ta kwashe kwana hudu tana wannan halin abinda ya fara damun Mama kenan dake daukar abin nata da a matsayin wasa gashi har sannan basuji wata magana daga bangaren Khalil ba, a lissafi kuma biki yana ta qaratowa dan saura sati uku ne da kwana biyu.

A kwana na hudun ne Maman ta kasa shiru da safe ta samu Abba yana shirin fita tace masa
"Alhaji yanzu kana gani haka zamu zubawa Umaimah ido tana nema ta illata kanta? Bafa ta fitowa ko tsakar gida tana cikin daki, abinci kansa se Saratu tayi da gaske sannan take ci babu abinda takeyi se aikin kuka gaba daya ta lalace a yan kwanakin nan ta fita hayyacinta".

"To yanzu Malika me kike so ayi? Na kaita Asibiti an bata magunguna likita ya kafa mata dokoki da sharuda ai ita ba qaramar yarinya bace da za'ace se anyi mata tuni akan muhimmancin lafiyarta, tunda abinda ta zabawa kanta kenan taga ya fiye mata se tayi duk wanda zeji mata babu dadi ai ba kamar ita da ciwo yake a jikinta ba" Abban ya bata amsa cikin halin ko in kula.

"Haba Alhaji be kamata kace haka ba mafita dai za'a nema tunda dai ko yaya Umaimah fayar muce muna kuma son farincikinta. Damuwarta dai gaba daya akan yaron nan Khalil take, kaga tun waccen ranar bana tunanin ya sake zuwa kuma basu turo wani babba akan maganar tana nan ko sun fasa din da gaske ba.."

Katseta Abba yayi da cewa
"Toh se ku jira duk daren dadewa ai zasuzo, idan suna ciki za'a sani idan ma fasawar sukayi duk za'aji. Kawai a ci gaba da shirye shiryen ita Nuratu tunda shine magana dahir a yanzu ita kuma zuwa lokacin se muga abinda Hali yayi".

"Baza'ayi haka ba Alhaji kenan haka zamu zuba mata ido a cikin wannan yanayin? Dan fa baka leqawa ka ganta ne Alhaji kai da kanka nasan se tabaka tausayi wallahi" Maman ta fada cikin muryar karaya, se Abba ya kalleta yace

"Ai saboda karma naji tausayin nata ta sakani yin abinda banyi niyya ba ya saka bana leqawar, sannan duk ki dena wani zagaye zagaye nidai bazan kira yaron nan ko iyayensa ba akan maganar auransu a yanzu tunda damab ba tallanta na kai masa ba shi ya gani yace yana so. Akwai iya lokacin dana diba idan basu magantu ba a sannan ni da kaina zan tattara komai da suka kawo a mayar musu shikenan magana ta qare.

Kije kiyiwa yarki fada ki nuna mata muhimmancin tawakkali ba komai da kake so a rayuwa kake samu ba, kuma sau tari abinda kake so be fiya zamar maka Alkhairi ba dan haka ta bawa zuciyarta haquri, ta kuma qudurce koda Khalil ko babu shi zata rayu. Sannan shi aure lokaci ne duk sanda ubangiji ya tsayar mata zatayi" yana gama fada ya dauki jakarsa da waya dake ajiye yayi mata sallama ya fice.

Jiki babu kwari Maman ta biyo bayan sa tana yi masa Adawo lafiya, dakinta ta shige gaskiya a wannan gabar bazata zuba ido yarta ta shiga depression akan Namiji ba. Gara susan abinda ake ciki, idan ya fasa da gaske ya fada da Addu'a da roqon Allah zasu san yanda zasu cire mata sonsa daga zuciyata amma wannan zaman rashin sanin madafar baze kaita ko ina ba.

Gaba daya hankalinta a rabe yake bata ma da nutsuwar da zatayiwa Nuratu nata shirin auran, tana murna Allah ya kusa yanke mata zata aurar da yammatanta gaba daya ashe da wata a gaba toh Allah ya zaba abinda yafi Alkhairi.

Da yammacin ranar Jikin Umaimah yaqi dadi, kuka ta dasa tun rana tun tana na qarya sega abu na neman ya zama na gaske se kokawa take da numfashi kamar me cutar Asthma.
Suna tsaye a tsakar gidan suna jiran Nura dan maqotansu ne Salman ya nemo shi dan akai Umaiman Asibiti a motarsa sega Yaya Hajiyayye.

"Alhamdulillahi gara da Allah ya kawo ki Hajiyayye, Sharifa kamata muje tunda ga mota" Anty dake tsaye kan jiki kan qarfi akan lafiyar Umaimab ta fada. Se Hajiyaye ta bisu da kallo ta shiga tambayar meya faru, ganin halin da take ciki yasa ta bawa Salman key tace ya kaisu kawai su zasu biyo bayansu a Adaidaita aka ciccibi Umaimah aka yi Asibiti da ita.

Tareda Mama da Hajiyayen suka hau Adaidaitan, a hanya take gaya mata dalilin zuwanta Hajiya Maryam Babbar Yayarsu Khalil ce ta kirata akan gobe zasu kawo lefe, tana ta bada haquri na rashin sanar dasu da wuri saboda sun so su bari se cikin weekend Hajiya ta dage akan se an kawo goben,
"Na gayawa Yaya hafsa da Naziyya suna hanyar zuwa gidan yanzu suma nasan saboda mu shirya yanda za'a tarbi baqin ga kuma wata sabuwa ta tashi" Hajiyayyen ta fada.

"Alhamdulillahi, ai da tun a gida kika bada wannan daddadan labarin da ba se munzo Asibiti bama" Mama ta fada cikin tsananin murna, se Hajiyayye ta kalleta da rashin fahimta, a taqaice Maman ta fayyace mata yanda akayi tun zuwansu dubiyar Hajiyar Khalil da dalilin kwanciya ciwon nata.

"Amma Umaimah anyi mara hankalin yarinya, setayi abu kuma tazo ya dameta, tace ta fasa toh duk wannan ciwon na magani da menene takeyi in banda tsabar iskanci. Wallahi Mama har tunani nake kar azo ayi abin nan taje ta zubdawa da mutane mutunci da mugun halinta, dan ma Allah ya rufa asiri ta rabu da wadannan yan iskan qawayen nata da suke qara ingizata tana rashin hankali" Hajiyayyr ta fada cikin jin haushin abinda ya faru,

"Kedai addu'a zamu cigaba da yi mata ina tayi ba dare ba rana Allah ya shiryeta, yasa kuma Auran nan ya zama Alkhairin da kowa se yayi farin ciki dashi, kuma ina ji a jikina in Allah ya yarda auranta da Khalil shi ze kawo qarshen duk wasu fitintunu nata, se kowa yayi mamakin yanda Umaimah zata dawo" Mama ta fada daidai sanda suka sallami me Adaidaita Hajiyayye ta amsa da "Amin".

Sun tarar dasu a Emergency suna zaune babu gado, kusada Umaimah dake?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ta kuka tana Jan numfashi Yaya Hajiyayye ta tsaya tana kallon Anty tace
"Nifa nazo muku da good news gobe za'a kawo lefen Umai, se gashi ashe ita tana qoqarin sheqawa lahira ma. To bari na kirasu na gaya musu ashe tace ta fasa bani da labari dan in suka rigada suka? kawo fa kaya ya shiga sahun gado mu zamu rabe abinmu".

Kafin wani ya bata Amsa Umaimah ta yunqura ta dire a gabanta tana zare ido tace "lefen wa Maman Asad? Kardai kice mun nawa da gaske Khalil be fasa aure na ba?"

Hararar wasa Hajiyayyen tayi mata tana danne dariyar data taso mata saboda irin alkafurar da Umaimah tayo tace
"Toh in ba naki ba wace za'a kawo lefe, kinsan dai an kawo na Nuratu koda yake yanzu? nake samun labari kin fasa gara tun wuri na sanar musu su san abin yi..."

"Wallahi qarya nake ban fasa ba" Umaimah ta katseta kafin ta miqe tsaye kamar wata iska Feee tayi waje bakin ta a washe yanda kasan an mata bushara da Aljanna mutanen dake zaune a gurin suka bita da kallo, ranga ranga aka shigoda ita gashi ta miqe akan qafarta har tana gudu wannan abin Al'ajabi da yawa yake.




PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login