Showing 306001 words to 309000 words out of 429394 words

Chapter 103 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

936

zata karbi Al'amari, kuma bisa mamaki se yaji sam hankalinsa be tashi ba farin cikin da yake ciki ya saka yake jin komai ma da zezo me sauqi ne, Allahn da ya qaddara faruwar auran shi ze wanzar da zaman lafiya ya kuma sanya mata dangana, yana fata yana kuma addu'ar Umaimah ta karbi abun da kyakykyawan tauhidi ta yarda cewar Allah ne meyi babu kuma wanda ya isa ya qetara masa iyaka. Ajiyar zuciya yayi ya kalli Hajiyar yace
"Duk ma wani abu yanzu Hajiya ai daga baya ne aure dai an rigada an daura nasan zatayi tashin zatayi rigima zatayi duk abinda zuciyarta ta ingizata tayi amma na lokaci ne dole da kanta zatayi ta gaji ta kuma haqura tunda babu yanda zamuyi da abinda Allah ya qaddaro".

"Hakane to Allah ya shiga cikin al'amarin ya kawo faruwar komai cikin sauqi, Abubakar dai yace kar a gayawa kowa to ita waccen uwar karambanin gata can ta gama gayawa yan uwanta dukda dai na tsawatar mata akanta gaya musu maganar ta tsaya iya mu cikin gidan nan, se kaje kayi tunanin ta hanyar da zaka fada mata wannan maganar amma ka bari ba yanzu ba mu jira har zuwa Allah ya rabata da cikin jikinta lafiya tukunna se ayi wacce za'ayi" Hajiyar ta sake fada. Shiru sukayi kowa da tunanin da yakeyi a zuciyarsa. Jalilah ta fito cikin shirin tafiya ta kalle shi tace
"Ango kasha qamshi irin wannan murmushi tunanin me kakeyi?"
Kallonsa Hajiya tayi yayi sauri gyara zamansa dakyau yana daure fuska tareda hararar Jalilan shi kansa besan murmushin da yakeyi a zuciyarsa ya fito fili ba ita kuma da bata gani tayi shiru shine se tayi magana
"Da dai kin wuce kin tafi gida kina gani har goma saura" Hajiya ta fada swta yafa Mayafinta tace
"Ai tafiyar zanyi Hajiya ni wlh tsabar murna ma ji nakeyi kamar nayi kwanciyata a nan nasan ko naje gidan ma ba iya bacci zanyi ba wlh Allah Allah nake gobe tayi in dawo"
"Daman karki kuskura naga qafarki a gidan gobe bama gobe ba sati biyu nan gaba bama gayyarki kuma kin daiji abinda nace nasan Jamila da Amina basuda dan banzan surutu da neman magana irin naki, Habiba da Khalifa basu sani ba dan haka in har naji maganar nan a wani guri kece kuma se ranki ya baci" Hajiya ta fada seta zumbura baki ciki ciki tayi musu sallama ta fita, Jalilah na fita Hajiya ta kalli Khalil tace
"Bi bayanta, Jalilah ba gudun magana take ba yanzu se kaji wani abun"

Ilai kuwa yana fita a qofar shiga bangarensu ya tarar da ita tana kwankwasawa dan dazu daya fita ya saki Jamlock din
"Me zakiyi a nan kuma?" Ya fada yana qarasawa seta kalleshi tana murmushi tace
"Sallama zanyiwa Uwar gida yau duk bamu hadu ba tunda nazo" ya bude baki da niyyar bata amsa aka bude qofar Umaimah ta leqo ta saka dogon Hijabi qamshin turarebta ya bigi hancinsu. Qara washe baki Jalilah tayi tana kallonta tace
"Uwargida sarautar mata ina wuni, ya jiki jiki? toh Allah raba lafiya".

Tsaki Umaiman taja ganin itace ta juya ba tareda ta amsa mata ba Khalil ya ballawa Jalilah harara yace
"Toh neman maganar taki be samu guri ba ki tafi dan Allah seda safe"
"Korata kakeyi daga gidanka ko Khalil ai shikenan nida na sake taka qofar nan se randa na kawo Amarya daga nan se naga uban daya isa yamun iyaka da shiga gidan dan uwana
"Allah ya bamu Alkhairi" ya sake fada yana jan hannunta kamar yar yarinya, seda ta shiga motarta Sammani ya bude mata Get ta leqo cikin shaqiyanci tace masa
"Amma dai zakaje kadan ji dumin yar shilarka ko tunda Allah ya ceceka kaima dai yau ka canza ka rungumi sabon jini"
"Allah ya shiga lamarinki Jalilah" ya fada yana dariyar dabe shirya ba, Jalilah shaqiyya ce ta gaske neman rigimarta kuwa besan a inda ta samo shi ba dan Babansu har yafi Hajiya sanyin Hali nesa ba kusa ba. Be koma bangaren Hajiya ba kai tsaye ya wuce nasu bangaren, be tarar da Umaimah a falo ba se Tv da take aiki ya shiga kitchen ya dakko ruwa ya fito kenan itama ta fito daga daki ta cire Hijabin, wata Bubu gown ce a jikinta pure cotton ta kwanta a cikinta sosai ya kalleta se yaga kamar cikin a karkace yake indai ba idonsa ne be gani da kyau ba.

Fuska ta sake hadewa ta zauna a qasa sgi kuma ya hau kujera duk wata nutsuwa da yake da ita ya tattaro ya aza wa kansa dan baya so yayi abinda ze tunzurota balle har ta fahimci wani abu saboda Umaimah shu'umace, kamar me aiki da Aljannu yanzun nan tana iya karanto masa abinda yake cikin zuciyarsa.
"Ka ja mata kunne wlh idan ta sake shiga sabgata ba zatayi mana da kyau ba daman bawai na haqura da abinda tayi mun bane danbata mari banza ba lokaci kawai nake jira da zan rama" Umaimah tayi magana seda ya gama sauraronta kafin cikin sanyin Murya yace
"Allah ya baki haquri ba kuma zata sake ba Mari kuma da kaina zan rama miki karki damu"
"Qaryar banza kawai, kumada take cewa zata rako Amarya duk yar abu takzan uban da tsautsayi yasa ta shigo gidan nan da ita da masu rakotan sedai a fita da gawayinsu danma mutum ya sani qonasu zanyi qurmus babu abinda ya shafeni" ta sake fada shidai shan ruwa yake kamar an sakashi dole ya sake ce mata
"Ai kinci gida naki ne kiyi yanda kike si babu wadda zata shigo miki".

Banza tayi masa ganin ta maida hankali kan Tv yasa ya miqe yana ce mata
"Babu dan wano snack a gidan ne?"
"Babu" ta bashi amsa kai tsaye ba tareda ta kalleshi ba, se yayi hanyar Bene yana cewa
"Bari na duba Sama kwadayi nakeji nasan bazan rasa ragowar Biscuit din Bibi ba oh that's reminds me yaushe zasu dawo gobe fa akwai Tahfiz"
"Na taba tambayar sanda zasu dawo idan sukaje gidan yan uwanka? Kasan dai ba cinye su za'ayi ba se ka jira goben tayi kaga ba'a dawo maka dasu ba kafin kayi magana uban yan son yaya" Umaimah ta fada a hasale tana kallonsa.

Jiya da safe Maman Asad ta mata text a WhatsApp akan jiyan Birthday din UmmulKhairi Salman yazo ya dauke su da yake ana hutun makaranta shine kwana daya ze wani fara cigiyarsu se kace taga shi nasa yan uwan wata ranaana makarantar boko ma Jalilah daukarsu takeyi sedai su ringa zuwa daga can. Khalil kuwa sama ya wuce ba tareda ya tanka mata ba, seda ya kulle qofa da muqulli kafinya wuce Bedroom dinsa ya cire jallabiyyar jikinsa ya kwanta akan gado ya shiga sake kiran Humaira, daman babu wani biscuit da ze dauko yanda yaga yau har yar kwalliya tayi masa yasan yan mutunchin na kusa shi kuwa Muryar Amaryarsa kadai yake so yaji shi yasa ya nemi hanyar da ze samu space. A kashe yaji wayar tata, ya cije yatsa danba haka yaso ba, wata tsumammiyar soyayya yakeji yau din kuma so yake ya fara dora mata hadda da wuri dan baya so ta shigo gidansa da sauran ruwan yarinta a kwakwalqarta, so yake ta goge tas ta yanda zasu tsinki furen soyayya da allura, rayuwar auransa is just a fantasy which he wants to brought into reality yanzu yake so ya san yayi aure duk nutsuwar daya rasa a baya so yakeyi ya sameta shiyasa baze taba hada Humaira da Umaimah gida daya ba dan yanda bata kwantar da hankalinta ba babu yanda za'ayi ta bar nasu ya kwanta.

Kwanaki biyu da suka biyo bayan daurin auren sosai alaqarsu da Umaimah ta sake gyaruwa, ta sakko sosai ta fara dawowa Umaimanta dan jiya Lahadi har Hajiya ta shiga ta gaida dukda bata jima ba Ita bata sake ba Hajiya kuwa jinin jikinta ne ya daskare har seda Umaiman ta fita kafin ta iya aje numfashi me kyau. Amarya Humaira kuwa wasan yar buya sukeyi dashi, washe gari Asabar daya gaji da kiranta bata dagawa ya tafi gidan Unaiza amma qememe taqi fitowa suyi magana har dakin da take ya shiga amma ta shige Toilet ta kulle kanta a bakin Unaizatun yaji kalar drama da sukasha jiya kuka da birgima ta ringayi wai an daura Mata aure da abinya ishi Unaizatu ta kira Mamaa speaker ta saka mata ita Mama cikin fushi tace mata
"Toh tunda bakya sonsa bari yanzu na kira Baban naki ai daman yan uwannasa basu juyo ba kawai a warware auran shikenansu duba cikin yaransu a sake daurawa da wata kowa ya huta tunda ke bakya sonsa" se kuma rigima ta dawo sabuwa akan me Mama zatace Khalil ya saketa a aura masa wata a Jalingo, da dai sukaga lamarinnata yarinta neda shirme suka qyaleta tasha kukanta ta gode Allah ta haqura amma fa taqi amsa wayarsa saqon ma daya turo tana karantawa tana murguda baki kamar Khalil din ne da kansa tana gamawa kuma ta kashe wayar har washe garin yana zuwa gidan tana kwance da taji muryarsa da alamun ze shiga dakin ta runtuma Toilet ta kullo qofa taqi fitowa.

Rarrashi babu wanda beyi mata ba amma taqi budewa daya gaji yace mata
"Shikenan tunda ba zaki bude ba bari na tafi na koma gurin matata da take sona, nima fa auran ba wai ina wani sonsa bane da ace ma sun nemi shawarata kafin a daura zance musu Aa ba yanzu ba amma kin kasa fahimta se wani fushi kikeyi kina qin daga wayata na tafi kuma bazan sake dawowa ba".
Taku yayi ya bude qofar ya rufe yayi saurin labewa a bayan Wardrobe a ransa yana addu'ar Allah sa plan din nasa yayi aiki aikuwa se gata babu shiri ta banko qofar bandakin ta fito tana waige waige, fita tayi daga dakin da sauri yaron Unaizatu ta gani a corridor ta tambayeshi Khalil shi da besan ma Khalil din ya shiga dakinta ba yace mata ai ya tafi ta kusa fashe da kuka harda shashsheqa ta juya dakin Khalil ya fito daga maboyarsa ya tsaya a bakin qofar tana shiga ya saka mata qafa gaba dayanta ta tafi zata fadi amma ya tareta ya fada jikinsa ya rungumeta irin rungumar da akeyiwa jariri sabon haibuwa. A kunnenta ya rada mata
"Zan iya jure komai amma banda ki hanani jin muryarki da ganin fuskarki, I so much love you my little wife".

Lamo tayi a jikinsa banda rawa babu abinda nata jikin yakeyi haka zuciyarta se bugawa takeyi da qarfi saboda tsintar kanta a sabon yanayin da bata taba shiga ba, hannunsa daya daya zagayeta dashi ya cire ya tallafo fuskarta amma taqi bari su hada ido sema ta kulle idanun nata ganin ya dage dole seta kalleshi, idonta a rufe ba tayi tsammani ba se jin saukar Cold lips dinsa tayi akan nata babu shiri ta bude idonta tareda zaresu Khalil dake kallonta da nasa ldon da sukayi laushi ya saki murmushi har sanna Lips dinsu na hade seya lumshe nasa idon ya shiga aika mata da wani passionate kiss me tafiya bisa umarnin zuciya be barta ba seda yaji numfashinta na barazanar barin jikinta, rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta yana sakin ajiyar zuciya a jere a jere dan dan wannan abun da yayi ba qaramin tayar masa da kwadayi yayi ba kuma dole ya hadiye abinsa kafin ya qarasa tsorata Amaryar tasa dan yanzunma se jan numfashi take tana qoqarin ture shi amma ta kasa.

"Relax mana Aisha" ya fada a hankali kamar me magagin bacci seta dena tureshin da takeyi, zuciyarta fal cike da tsoron abinda Khalil din yayi mata ga wata kunyarsa da tayi mata rubdugu bata zaton daga wannan abun zata qara bari su hada ido dashi ita fa badan Anty Mariya matar da take zuwa gurinta gyaran jiki ta gaya mata ana wadannan abubuwan ba daman da cewa zatayi kawai Dan iska ne Khalil.

"Idonki yana kyau idan kika tsorata" ya fada yana kissing saman idonta,Humaira dai taga abinda yafi qarfin qaramar Kwakwalwarta bata iya cewa komai se ido take wulgawa tana neman hanyar da zata tsere daga wannan tashin hankali daya sameta. Tafiya ya farayi da ita still a jikinsa ya zauna gefen gadon dakin tareda zaunar da ita akan cinyarsa, ta zabura saboda jinta akan wani abu da bata san menene ba
"Me yasa kike fushi dani?" Ya fada yana sake zaunar da ita a jikinsa mutsu mutsu taci gaba dayi tana qifta ido tana so ta fashe masa da kuka seya jata jikinsa ya rungumeta yana cewa
"Cry cry baby kinga abinda Allah yayi ko? Ba kuka zakiyi ba addu'a ya kamata kiyi mana Allah yasa hakan ya zamo mana Alkhairi sannan Allah ya bani ikon kulawa dake nayi miki Adalci. In sha Allahu ba zaki dana sanin aurena ba".

Lamo tayi a jikinsa saboda duk maganar da yayi a cikin kunnenta ne kuma cikin wani sauti da ya saka gaba daya tsigar jikinta ta miqe, peck ya sakar mata a gefen kunnenta ta zille da sauri ta sauka daga jikinsa ta durqushe akan gadon seya miqe shima yana kallon yanda take rawar jiki kamar wadda zazzabi ya rufe a zuciyarsa yace
"Akwai aiki". Bandakin data fito ya shiga, Humaira ta bishi da kallo kamar munafuka be jima a ciki ba ya fito yana goge fuskarsa suna hada ido tayi saurin juya masa baya ya qarasa inda take yana cewa
"Zan tafi ki kunna wayarki". Shiru tayi bata amsa ba yayi taku biyu da niyyar riqeta ta duqe qasa tana yarfe hannu seya fasa ya juya yana murmushi dan idan ya biye mata za'ayi abin kunya.

Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah ana maganar kwanaki biyar kenan da auran Khalil da Humaira wanda har zuwa yanzu Uwargida Umaimah bata san da wannan Al'amari ba. Sharafinta kawai takeyi saboda ta samu duniya yanda take da buqata Khalil ya dawo tafin hannunta juya shi takeyi son ranta haka zancen auran daya taso dashi ya mutu murus, koda wasa bata sake jin wani ya tayar da maganar ba haka nan shima tana biye da sawunsa kuma bata ga wata alama da take numa cewar yana tare da wata Mace ba. Abinda bata sani ba shine tsabar iya taku ne ya saka Khalil din ya koma mata yanda yake dukda ta wanni bangare tayi nasarar Samunsa amma fa ba kamar yanda take gani a zahiri ba irin biyayyar da yake mata da riritata da yakeyi damkar Jaririya duk yana yin hakan ne domin gujewa abinda ze kawo fasuwar sirrin da yake ta ririta yanda ze bayyana shi.

Sabuwar waya ya siya da sabon layi kuma da ita yake amfani gurin kira ko chat da Amaryarsa wadda tun tana bore tana noqewa a yan kwanakin nan ya bude mata ido da soyayyarsa wanda tun kafin ta kai ga sanin inihin Khalil din bala'in kishinsa takeyi, idan suna tare dan kullu yaumin ne se yaje ya ganta idan yace mata ze tafi ta ringa fushi kenan tana tura baki tunaninta gaba daya tafiya yakeyi yanzu haka zeje yayi ta Hugging Anty Umaimah yana gaya mata kalamai masu dadi irin wanda yake mata haka zatayi ta baqin rai tana fushi Unaizatu dai sedai ta kalleta tayi murmushi a ranta tace
"Yarinya dan ma baki san ainihin abinda ake yiwa Kishin ba kenan" ita dai ta dage tana gyara Humairan tareda koya mata duk wasu dabarun zaman aure da idanhar ta riqe su zata zauna lafiya da kowa".

Tun zuwan da Khalil yayi ya kai mata madarar waken suya da akace tana qara qiba Unaizatun ta fahimci yana so Humairan ta murmure tafi yanda take batayi qasa a guiwa ba gurin Siyo mata ZUMAR QIBA A GURIN KHADYS EMPIRE ( 08147832793). Zuma ce gangariya da take ciko da jiki ya murmure ba qiba me yawa wadda zata saka muni ba tayi amfani da ita taji dadinta shiyasa saboda ta tabbatar da ingancinta sannan babu kwaya a cikin hadin zumarta kuma ta karbi Humairan nan da nan jikinta ya fara murjewa ta ciko ta qara haske saboda Hadaddun Mayuka da Sabulan da take amfani dasu ga qamshi duk inda ta gifta seta barshi tuni ta lura da Khali ya dena bari su kebe su biyu idan yazo a falo suke zama suyi hira a ranta tayi ta dariya tana cewa
"Su Yah Khalil ana gudun abun kunya".

Ranar da aka cika sati guda da daurin auran ta kama Juma'a, kamar yanda ya saba yana ya tashi daga Masallaci ko office be koma ba ya wuce gurin Humaira. Yunwa yake ji sunyi waya ya gaya mata dan haka tace zata hada masa Lunch, a cikin satin nan har wata yar qiba yayi ta kwanciyar hankali har tunani yakeyi shib baze yuwu ba aci gaba da tafiya a haka ba tareda Umaimah tasan da batun auransa ba? Shi a nasa bangaren bashi da Matsala tsaf ze iya dauke Humairan ya ajiyeta inda koda wasa Umaimah ba zata tana sanin da zamanta ba haka kuma ze iya takunsa kamar yanda yakeyi a yanzu ba tareda ta gano ko ta zargi wani abu ba amma matsalar yasan babu me bashi goyon baya akan hakan.

Jiya seda Hajiya tayi masa magana akan ya kamata zuwa yanzu yasan matsaya akan maganar auran saboda sunyi waya da Mama Hauwa kuma a cikin hira ta kawo mata zancen son sanin inda ze ajiye Humairan saboda su san shirin da zasuyi nayi mata kayan daki. Rasa abinda ze cewa Hajiyar yayi a zuciyarsa so yakeyi yace mata ita da kanta ta sanarwa da Umaimah maganar auran idan wannan qurar ta lafa daga baya se azo ayi ta zancen inda ze ajiye amarya amma ya kasa.
Jalilah tayi masifar tayi bala'in lusari ko ta kirashi yafi sau cikin kwando akan ya tsaya tsoron mace ya kasa tabuka komai, badan iyakar da Haiya tayi mata shiga sabgar gidansa ba da tuni ta fasan kwan kowa yaji amma ko yanzun lokaci ta basu idan taga sun gaza zatayi musu aikin dan babu yanda za'ayi a bar yarinyar mutane da aure yana zagayawa yana lalubeta ya kasa yin jarumtar da ze kawota cikin gidansa a cewarta kenan.

A falo tayi masa masauki kamar koda yaushe, irin kwalliyar da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login