Showing 45001 words to 48000 words out of 429394 words

Chapter 16 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

945

yace

"Umaimah, kin shirya aure na dagaske?"



PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
PAGE 14

Kallon rashin fahimta ta bishi dashi kafin tace
"Kamar yaya na shirya auranka da gaske, daman ana auran wasa ne?"

Gajeran murmushi Khalil yayi tareda gyara zamansa ya tattara hankalinsa gaba daya a kanta ya zuba mata ido, dole tayi qasa da nata idanun saboda yanda yayi mata kwarjini ta shiga juya zoben Azurfar dake hannunta a ranta tana so ta gano ma'anar tambayar da yayi mata wai ta shirya auransa, to me Khalil yake shiryawa ne?

"Tambayarki nayi kuma amsa nake da buqata taqaitacciya Eh ko Aa, Umaimah kin shirya aure na?" ya fada still idonsa akanta, seta dago tayi masa kallo daya kafin ta juyar da fuskarta dayan gefen tace
"Eh"
"Good, kinsan me Aure yake nufi?" Ya sake jefa mata wata tambayar har sannan yana kallonta, seta juyo itama ta kalleshi, harara taso maka masa amma yanda ya tsare gida dole yasa ta saita idonta ta bige da qiftasu kamar an jijjiga bera a jarka kafin ta bude baki tace

"Wai me yasa kake mun irin wannan tambayoyin ni ban...."
"Umaimah! Ba wasa ya kawo ni ba, magana nake so muyi kuma dole ki amsa mun duk tambayoyin da nayi miki kai tsaye ba na son wata magana ko nuqu nuqu" yayi saurin katseta, seda ta watsa masa harar qasan ido kafin tace

"Aure ibadah ce da Mace da Namiji suke zama a qarqashin inuwa daya matsayin mata da miji dan su bautawa Allah kuma su zama ababen debe kewa ga junansu".

"Menene matsayin Namiji a cikin aure?" Ya sake jefa mata wata tambayar,
"Guy din nan fa ya raina mun hankali ji wasu tambaya kamar dan jarida" Umaimah ta fada a ranta, a fili kuwa tace

"Namiji shine shugaba wanda haqqin ci, sha, sutura, muhalli, neman lafiya da biyan buqatar matarsa ya rataya a wuyansa"

"Ita kuma mace fa" Khalil ya sake fada yana bin bakinta da kallo, yanda take bayanin tana murguda bakin ba qaramin birgeshi yake ba. A'uziyya yake taja lodi lodi a zuciyarsa saboda yanda shedan yake sake qawata masa bakin nata.

"Ita mace Allah ya wajabta mata yiwa mijinta biyayya akan duk wani abu da be sabawa Mahalicci ba saboda Aljannarta ta koma qasan qafarsa daga sanda tabar gaban iyayenta. Sannan dole ta girmamashi, babu musu ko jayayya a tsakaninsu, ta kuma mutunta Iyayensa da yan uwansa sannan zata kula dashi tayi tattalin dukiyarsa data qunshi Arziqi na Yaya da kudi" Muryar Umaimah ta dawo dashi daga tunanin daya tafi.

Kai ya jinjina ya dan tabe baki kafin yace "se kuma me?"

"Se kuma dukkan su suji tsoron Allah su zauna da junansu Amana kar wani ya cutar da dan uwansa" ta fada murya a cunkushe dan ta gaji da wadannan tambayoyin na titsiye.

"Idan har kinsan duk wadannan abubuwan da kika fada me yasa ke bakya girmamani" Khalil ya fada yana kallonta, se ta dago kanta data duqar qasa ta kalle shi itama, yar banzar zuciyar ta tana ce mata "kice saboda shi ba mijinki bane" ta kirkin kuma tana kwabarta,

"Magana nakeyi kinyi shiru, Umaimah me yasa bakya ganin qimata, kin raina ni bakinki yana iya furta mun duk kalmar data zo miki a duk sanda kika ga dama, a gabanido na kike zagina ki zagi yan uwana hakan yayi miki kama da suffar mace ta gari wadda take neman Aljannar ta a gurin Mijinta? Ko kuwa kina ganin tunda bamu rigada munyi aure ba dan haka kina da damar da zaki yi mun duk abinda kika ga dama?

Toh bari kiji, halin da kika nuna a waje shine ze bani haske akan halinki acikin gidana bayan munyi aure, tun daga waje bakya shayin ki kalli idonaki zageni Umaimah ki jefeni da kalmomi marasa dadi a haka kike tunanin zan aure ki? Ban samu kwanciyar hankali dake a waje ba sanda baki zama doke na ba taya ya zanyi tunanin samun sa bayan na kawo ki gidana?

Gaskiya Umaimah ina tsoron abinda ze faru idan har haka kike, ba kuma zan daukarwa kaina damuwa na kai cikin gidana ina sane ba, macen da bata girmamani ba a waje bana tunanin zata girmamani acikin gida bayan data gama sanin koni wanene" Khalil yayi maganar cikin daga murya da dakiya gaba daya ya chanza daga Khalil din nan me sanyi ya dawo wani daban dan.

Kallon sa ta kumayi saboda yanda taji muryarsa har tsakiyar kanta kafin ta kalli can gefe tana qoqarin hadiye maganganun dake son fitowa daga bakinta dan a yanayinfuskar sa ta tabbatar yau baze dauki raini ko kadan daga gurinta ba, abinda yafi mata sauqi ta kama kanta ta kuma gyara bakinta dan haka ta maye gurbin kalamn tsiwar tata da cewa

"Kayi haquri nasan nayi kuskure, raina ne ya baci amma in sha Allahu bazan sake ba. Zan koyi yanda zan ringa sarrafa zuciyata akan kishinka" ta qarasa maganar cikin rawar murya tana janhanci kamar me son fashewa da kuka.

"Kar kiyi mun kuka" ya fada, kamar me jira kuwa sega hawaye shaaa sun fara zubowa, ta rigada tasan weak point dinsa, baya son kukanta ko kadan shiyasa take amfani dashi gurin karya lagonsa.

"Kinga ni ba kuka nace kiyi ba magana kawai mukeyi kuma dole na nuna miki kuskurenki saboda aure zaman aure zamuyi, babu yanda za'ayi mu tafiyar da rayuwa a haka babu girmamawa a tsakaninmu, bacin rai ai ba gushewar hankali bane da zesa ki manta matsayina a gurin ki ki gaya mun duk maganar da kika ga dama" Khalilya fada cikin kwantar da murya, se ta sake fashewa da wani kukan harda sheshsheqa tace

"Toh ya kake so nayi? Duk abinda nayi kishinka ne ya saka ni ba dan bana ganin girmanka ko na raina ka ba. Ina sonka da yawa Khalil ni kaina ban san irin son da nake maka ba, idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na shaqe kaina shi yasa bana sanin sanda nake fada maka magana mara dadi amma ka yarda dani na fika jin daci da haushin duk wata kalma mara dadi dana gaya maka, kuma nayi maka alqawarin bazan sake ba, tun waccen ranar nayi nadamar abinda ya faru na kuma chanza.

Alqawari ne nayi maka Khalil bazaka taba nadamar aure na ba, Zaka sameni me matuqar biyayya tareda gujewa bacin ranka, zanzamar maka baiwa banida wani aiki se aiwatar da unarninka muddin be sabawa Allah ba kuma inada yaqinin bazaka taba sakani nayi abinda ya kaucewa shari'a ba, amma nima ina roqonka daka tausaya mun, kar kayi amfani da raunina akan Soyayar ka ka cutar dani.

Ina matuqar kishinka ka tayani rufe duk wata qofa da zata kawo matsala a tsakanin mu dalilin kishi ni kuma nayi maka alqawarin zame maka duk irin matar da kake so. Bazan bawa idon ka damar ganin wani abu a waje kayi sha'awa ba ni kadai na isheka Khalil zan kuma tabbatar maka da haka dan seka bigi qirji wata rana ka gayawa duniya kafi kowa yin sa'ar mata saboda ina sonka Khalil, kuma farincikin ka shine nawa" ta qarasa maganar tana saka kwayar idonta dake jiqe da hawaye cikin tasa suka yiwa juna kallon tsakiyar ido n dan lokaci kafin ta janye nata tana ci gaba da jan shashsheqar kuka.

Wani irin yarrr yaji tundaga kansa har tafinqafarsa, yanda kasan wanda aka tsoma a baho dake cike da ruwan qanqara a lokacin sanyi haka haka jikinsa ya dauki rawa seda ya hada hannayensa biyu ya rungume kansa tare da rufe idonsa yana furta "Hasbunallahu wani'imal wakeel" a zuciyarsa a hankali sanyin da yake ji ya ragu nutsuwarsa ta fara dawowa, be dena ambaton Allah ba seda yaji komai ya daidaitar masa ya bude idanunsa da suka kada sukayi jaa lokaci daya kamar wanda aka watsawa yaji ya kalli Umaimah da kanta ke sunkuye har sannan tana kuka qasa qasa.

"Umaimah!" Ya kira sunanta cikin wani irin sauti, bata amsa ba illah sagowa da tayi ta kalle shi ta sake mayar da kanta qasan.
"Look at me Umaimah, look directly in to my eyes" ya sake fada cikin shaqaqqiyar murya yanda kasan shine yayi kukan ba ita ba.

Jiki a sanyaye ta dago ta kalle shi idanunsu suka sarqe. Ji takeyi tamkar yana cake mata ido da wani abu amma ta kasa janye idonta kamar yanda shima ya saka mata ido yana kallonta, sun kwashe kusan minti biyar a haka kafin Khalil ya bude baki yace

"Ina sonki, and i will prove it to you ranar da kika zama mallakina, zan riritaki zan baki gatan daya dace dake a matsayin ki na mace da Allah yayi muku daraja ta daban, and I am giving you this assurance, ni KHALIL ke kadai kin isheni a rayuwata Umaimah. Idan har kika ga wata mace bayan ke a duniyata to ki tabbata qaddara ce wadda babu wanda ya isa ya kauce mata kuma idan haka ta faru ina fatan dani dake zamu rungumeta da hannu biyu, amma ki sani baki da ta biyu a zuciyata duk kuma wani abu da ze zo toh bayan UMAIMATAH NE".

Yanda kasan ta taka rawar murna haka taji sanda yace ita kadaice a duniyarsa amma qarashen kalaman nasa suka datse murnar tata, wato yana fata kenanwata rana wata ta shigo rayuwarsu? Ita kuwa zata dawwa ma tana roqon Allah da karya nuna mata wannnan rana da ranta, dan kuwa bata san yaya zatayi ba. Tabbas idan bata kashe ko wacece ta shiga rayuwar Khalil dinta ba toh ita zata kashe kanta ta huta da baqin ciki.

Hannunsa daya kai fuskarta ya dawo da ita daga tunanin data tafi,
"Tunanin me kikeyi Amaryata?" Ya fada yana mata murmushi, seta mayar masa da martanin murmushin, a ranta tana jin dadin halin Khalil na rashin ruqo, yanzu sun gama wannan maganar kenan har abada sedai idan ita ta sake tayar da ita.

"Ke kikayi wannan cake din, yayi dadi sosai" ya fada bayan daya gutsiri cupcake din, seta girgiza kai tace

"Aa, amma zan tambayi Maman Asad inda ta siyo naje a koyamun tunda kana so"

"Thats my babe" ya fada yana kashe mata ido, kafin yaci gaba da cewa
"An kawo kaya dazu ko? I'm sorry i was supposed to tell you ban samu dama ba, koda yake laifin kine da kika shareni kwana da yawa bayand kika gama yimun barazana. Ni ai ban san yar sara suka bace ke se ranar" ya qarasa yana mata dariya, seta shagwabe fuska tace

"In dai akan ka ne ka kirani yar Daba ma, kuma ni ba qin kiranka nayi ba tun ranar bani da lafiya seda na kwanta a Asibiti kwana hudu".

Ayya sorry my princess shiyasa she nayita jina se a hankali, kinsan sati dayan nan was the longest week in my whole life saboda rashin ganinki da banayi, kawai na ringa rayuwa ne amma ni kaina nasan nayi loosing focus, God i can't imagine life without this my little troublesome lover" ya fada yana jan kumatunta irin yanda akeyiwa yara wasa.

Dariya suka saka gaba daya, daidai nan Yaya Hajiyayye ta shigo gidan. Seda ta gama daidaita parking ta fito daga motar dan yaran tuni sukayi gurin Khalil da gudu me aikinta kuma ta shige da Baby Ummu-salma.
A mutunce suka gaisa tana tsokanarsa Ango Ango se sunkuyar da kai yakeyi, ta faki idonsa ta gallawa Umaimah data qunshe fuska Harara dan taga aika aikar da tayi mata, daman tasan za'a runa ai kuwa seta biya kudinsa dan Mijinta ta siyowa shine zata kwashe ta bawa nata Mijin.

Yaya Hajiyayyen na wuce wa basu dade ba sukayi sallama bayan daya ce tayi lissafin abinda take da buqata na hidimar biki ta tura masa, shidai a bangarensa reception kawai zeyi bayan an daura aure tace masa ita ba abinda zatayi tasan dai Mama zatayi Kamu da Mothers eve, yace dai taje tayi tunani daga nan suka rabu akan idan sun shawarta abinda zasuyin zata gaya masa, ta raka shi har bakin Gate ya wuce gida.

A cikin gidan tana shiga kuwa Maman Asad ta tsareta seda tayi mata transfer kudin cake dinta cif sannan ta kyaketa bayan ta kwashe ragowar wai zasuci ita da yaranta gobe a kawowa Dadyn wani, ko a jikin Umaimah dan ita zuwan Khalil da daidaitawar su yau ya wanke mata komai. Haka tayi baccin farin ciki bayan da suka sha waya suka kuma kashe junansu da kalaman qauna masu tsuma zuciya.

Washe gari Asubanci tayi ta bar gidan tunda ta gama abinda ya kawota tao zaman me zatayi dan haka bata bari ma Maman Asad din ta tashi daga bacci ba ta fece dan karta tsayar da ita tace ta tayata girkin tarbar Mijinta.
Bayan ta isa gida ta kwanta ramuwar baccin safen kenan seda Imran autan Anty ya tadata wai taje Antyn tana kiranta.

Kamar ta kwada masa mari amma ta kanne dan ko babu komai Antyn nan duk wulaqancin da take mata ta shanye kuma a yanzu kaf gidannan babu me yin ta tata kamarta, haka ta tashi tana hada hanya ta tafi dakinnata.

Can uwar daki ta same ta ta baje wasu jarkoki da robobi da aka zuba garin magunguna ta kalleta tace
"Zauna Umaimah bamu da lokaci, ta miqa mata jarka tsumi tace
"Maza shanye ki bani robar, gasu nan zan saka miki a fridge, safe da yamma kullum kizo ki dauki daya ki sha kinga Nuratu inaga yanzu ta gama shanye wadanda na bata".

Kallon ta Umaimah tayi ta kalli jarkar, kullum se taga Nuratu na shan abun amma da yake tun wancan incidence din ba magana suke ba shi yasa bata tambayeta menene ba, tana kallo kullum zata hada yan abubuwanta tasha, ga Fruits da tun Asali daman cimarsu ne amma na kwanannan yafi yawa dan wani hadi na musamman taga Nuratun na shiga daki dashi na Kankana, kwakwa, dabino da madarar gari suna da yar qaramar blander a dakin a ciki zata hade su ta markade abinta Umaimah na kallo ta shanye ta barta da hadiyar yawu, sedai idan ta faki idonta idan ta ajiye ta kurba ita dai bazata ce mata komai ba.

Bayanin sauran abubuwan Antyn tayi mata, ingantattun magungunane da Antyn da kanta take hada saiwoyi da itatuwan ta daka wanda kuna yammata kamar su zasu iya sha, tun bayan tsayar da ranar auran daman suka fara shan maganin sanyi wanda yake mataki na farko na gyaran mace dan duk maganin matan da zaki sha indai da sanyi a jikinki kamar kina shuka dusa ne. Bayan kawo lefen Nuratun Anty ta fara bata tsumi da magungunan wanda daman duk yarinyar da za'a aurar a yaran Maman ita take daukar Alhakin yi musu gyaran na ciki da waje, Umaimah dai saboda rashin sanin inda aka dosa da maganar auran yasa se yanzu da aka samu tabbaci sannan za'a fara nata.

Sosai taja mata kunne akan kullum tazo tasha magungunan dan tasan idab ta bata a hannunta qarshe zuwa zatayi ta ajiye su ayi a sara. Wani hadin sabulu ta dakko cikin bokiti da bata, daga yanayin qamshin da yakeyi Umaimah ta tabbatar da zeyi kyau, koda yake ita shaidace dan ga Antyn nan tas da ita dan kullum cikin gyara take da kwalliya , ba ita kadai ba hatta Mama dake neman tsufar da kanta Antyn bata bar haka ta faru ba, ita take hada muau duk wani abu da ze taimake su ayi gyaransu tare shiyasa gasu nan tas dasu abinsu.

Godiya tayi mata ta wuce da bokitin a ranta tana yaba kirkinta, tasan Anty na sonsu tana kuma zaune da Mamanau lafiya amma ita laifin Anty daya a gurinta data hada Miji da Mamanta. Data sani a matar wa ko qanin Abba tazo da tabbas setafi shiri da ita sama da kowa saboda halin son gayun su yazo daya amma yanzun ma dole???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? zata danne zuciyarta kodan saboda Khalil dinta tunda duk abinda Anty zatayi mata na gyara yanU shi akayiwa.

Kwana biyu a tsakani Su Yaya Hafsa, Naziyya, Maman Asad da Anty Mamy matar Yaya Aminu, Anty Ruqayya Autarsu Mamansu se Zee Mama cousin dinsuce da itama ta tashi a gidan tareda su Naziyya, taruwa sukayi saboda su tattauna yanda za'a gabatar da shagulgulan biki, Dr Sagir ya rigada ya sallami Nuratu ya bata dubu dari biyu kudin hidimar biki da duk abinda zata buqata, sannan a bangarensa yace zasuyi Dinner abokansa sun shirya masa amma se bayan an kai amarya.

Suna zaune a falon Anty, Dinkunan Nuratun da Tailor ya kawo sannan ya karbi Na Umaimah suka baje suna dubawa Maman Asad ta daga wata peplum blouse da dinkin ya zaunu breastcup din ya fita kamar an saka shi ma a jiki tace

"Wai ni a ina kuka samo wannan multitalented Matar ne Naziyya? *BIISHAQ LINKS*, sanda naga kayan furnitures din Nuratu seda na rantse na waje ne muka ringa musu da Yaya Aminu yace shi yaje kamfanin suka debo kayan bana waje bane a nan akayi sannan ga dinkuna kuma wai duk na mace ce kamfanin ashe, gaskiya sun iya dinki dan Allah kiga rigar nan a tsaye kamar an saka ta a jiki ni nayi mamakin kudin danaji kin fada duk kyan dinkin nan amma farashin yayi sauqi".

Naziyya da ita ta hadasu da Shagon dinkin na *lBIISHAQ LINKS Dake Tudun-Yola gate 2 Kano* tace "ai ki jira sema an kawo dinkunan da zasu saka na Kamu da Yini zaki sake shan mamakin yanda suka iya occasional dinki a farashi me sauqi, ni ai tuni na dawo daga rakiyar yan qaryar designer dinnan a qare da bata maka kaya ga gangariyar kamfanin dinki na samu kina kallon yanda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login