Showing 132001 words to 135000 words out of 429394 words

Chapter 45 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

979

Jan Aji irin na Umaimansa. Tunawa da yayi Umaimah zata iya shigowa dakin a ko wanne lokaci ya sakashi watsa ruwa babu shiri ya fito, wayar ta katse dan haka ya sakata a Silent, hakan be masa ba ya jefata a Aljihun rigar daya cire kafin ya koma yaci gaba da wankansa.

Tana zaune a kan kujera ya fito tana ganinsa ta miqe tana ce masa
"Ga abinci nan tuwo nayi naga kwana biyu baka cin abinci sosai"
"Sannunki" ya bata amsa yana nufar Dining din ta bishi a baya, ita ta zuba masa ta tura masa komai gabansa kafin ta nemi kujera ta zauna kamar me gadinsa yau ko danne dannen wayar da takeyi babu shidai cin abincinsa yakeyi lokaci lokaci yana kallonta tareda karantar yanayinta harya qarasa ya dauki bowl din data zuba fruit salad ya koma cikin palour ya chanza channel zuwa tashar labarai.

Sake binsa tayi ta zauna a kujerar kusada wadda yake kai ya zuba masa ido ba tare datace komai ba. Yanda kasan an daure mata harshe, so take ta bashi haqurin amma shedanna nan yana zugata akan kartayi zata bada kanta daga qarshe dai ta yakice shi ganin ya mayar da Hankali kan Tv tamkar ma besan da zamanta ba ta bude baki dakyar tace
"Khalil kayi haquri ka yafe mun laifin da nayi maka wallahi sharrin shaidan ne".

Shiru yayi kamar beji taba, ta sake maimaitawa kafin ya dago fuskarsa da dan murmushi yace
"Wane laifi kikayi mun kuma?"
"Qin binka da nayi Lagos, kayi haquri wallahi...."
"Wannan ai ba laifi kikayi ba, ra'ayinki ne bakya son zuwa ni ya kamata na baki haquri da nake neman tilasta miki ki ringa bina wani waje alhalin bakya son zuwa, kiyi haquri kinji in sha Allahu bazan sake cewa kiyi mun rakiya wani guri ba duk inda zanje zan tafi ni kadai" Khalil ya tareta, yanda yayi maganar babu damuwa sam a fuskarsa amma tasan magana ce kawai ya gaya mata ta yaya ma zece beji haushi ba seta sake marairaicewa tace

"Toh idan bakayi fushi ba me yasa tunda ka dawo kaqi kulani?"
"Ni kuma naqi kulaki yanzu ma ba gashi magana mukeyi dake ba?" Ya fada yana kallonta seta tura baki wato so yake ma ya raina mata wayo be gane me take magana akai ba kenan dan haka tace

"Ba irin wannan ba, nasan baka iya daukan lokaci ba taredani ba amma ka iya zama kusan wata biyu a can kai kadan sannan yanzu ma daka dawo kai kadai kake kwana ko nazo korata kakeyi".
Dariya yayi a ransa yana jinjinawa Umaimah da wautarta wato Maye ta dauke shi ko,ta aza ze jure duk wukaqancinta saboda jikinta to shima ya koyi yanda ze hadiye zalamar tasa seta qarata can da abinta kafin ya samo wata. Kallonta yayi yace

"Toh yazanyi? Daman saboda ina ganinki ne na saka rai da zan samu shiyasa nake damuwa amma tunda babu kinga dole nayi haquri kuma koda na dawo daman ai akansa ne kike mun wukaqanci shine na barki ki huta ko, ban nema bama ballantana raina ya baci idan kin hanani".

Shiru sukayi gaba daya, shi ya maida hankalinsa kan TV ita kuma tana ta jan yatsun hannunta tana auna abinda zata gaya masa, ganin tayi shiru taqi magana ya sakashi miqewa yana cewa
"Karfa ki sakawa ranki damuwar ko ina fushi dake ne Aa, kawai ina baki space ne kamar yanda kika zaba"

"Dan Allah kayi haquri" ta fada kamar zatayi kuka har idonta sun kawo kwalla, qoqarin wuceta ya shigayi yana cewa
"Bakiyi mun komai ba" seta riqr qafarsa ta sakar masa kukan shagwaba hade da kissa tana cewa
"Kayi haquri ka yafe mun wallahi na horu bazan sake yi maka gardama ba ko China kace na bika zanje amma dan Allah ka yafe mun bazan iya ci gaba da jure rashin ka ba"

"Ikon Allah" ya fada a zuciyarsa a fili kuma ya saka hannu biyu ya dagota ganin tana neman kayar dashi tana miqewa kuwa ta fada jikinsa gaba daya ta kanainayeshi tana sake sakar masa wani kukan tana nanata yayi haquri"

"Ya isa Umaimah kinga karki tashi Mu'ayyad na haqura shikenan?" Ya fada yana qoqarin janyeta daga jikinsa, noqe wuya tayi tace
"Ba shikenan ba, baka haqura ba"
"To me kike so nayi da zaki yarda na haqura" ya sake fada yana jan numfashi saboda kusancinsu yayi yawa tana qoqarin tayar masa da abinda yake dannewa. Kanta ta kwantar a wuyansa tana cewa

"Nima ban sani ba amma baka haqura ba na sani"
"Toh sakeni se naji me kike so nayi" ya fada yana dago kanta daga wuyansa saboda yanda dumin numfashinta yake shigarsa, kamar wata kaska haka ta maqale masa yayi yayi ta sake shi amma taqi qoqari takeyi ta hade bakinsu yaqi bata dama dan yasan inhar ta samu dama zancen fushi kuma dole ya qare dan baze iya tsalkakewa tarkonta ba shi kuma be yarda da nadamarta ba yanzu, ko ze sakko se ta sake horuwa tukunna wannan tuban nata beyi kama dana gaskiya ba.

Wayarta da aka kira ce ta cece shi, babu bata lokaci ya shige dakinsa ya barta tsaye tana hawayen baqin ciki a ransa yace
"Kema kiji irin yanda nakeji idan da dadi" dan ya karanci a buqace take sosai.
Da safe yayi zaton tayi fushi se yaga akasin haka dan kafin ya fito harta hada musu breakfast, jikinta a sanyaye sosai fuskarta ta kode kamar wadda take jinya se yaji tausayinta ya tsirga masa amma daya tuna tasa jinyar daya sha se ya danne tausayin nata yaci abincin ya kama hanyar office.

Seda suka sake cin sati a wannan yanayin zuwa sannan ya tabbatar da ko badan Allah ba Umaimah ta biyu, ranar daya shammaceta ya amsa gayyatar ta har kuka seda tayi masa se ya rasa tsakanin shida ita wayafi kewar dan uwansa daga nan komai ya daidaita sukaci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi ko sanda ya fahimci Hauwa keyi mata ayyukan gida bece komai ba tunda daman ya dade yana mata maganar ta nemi me aiki dan baya son qazanta tunda bazata ringayi na ta nemo wadda zata tayata, kawai yaja mata kunne akan karta kuskura ta bata gyaran dakinsa haka girki tayi da kanta se rainon Mu'ayyad da take tafiya dashi ya hana, yace duk abinda zata tayata dashi tayi a nan a gabanta karta qara bayar masa da Yaro a tafi dashi wani gida tadai kiyaye wasu daga sharuddan amma wasu kam ta take kamar maganar Raino kam daya fita idan Hauwan tazo tayi mata aikin da zatayi zata bata shi su tafi, se yamma lis kafin lokacin dawowarsa zata kawo mata shi girkin ma wata rana bata takeyi sedai ta tsaya tana dubawa ko gurin saka maggi da sauran kayan hadi ta saka da kanta ta barta ta qarasa toh ina zata iya ita tunda tasan dadin me aiki ai kuma shikenan.

A bangaren Khalil da Hadiza kuwa tun daidaiton sa da Umaimah ta kasa gane kansa, gaba daya yanzu shareta yakeyi dan harga Allah yana mantawa da ita wani lokacin tunda me guri ta dawo dole yar haya ta kama gabanta. Lokutan da yake samu ya kira daman irin lokacin da suke waya da Umaimah ne idan yana office dan haka yanzu ma sun dinke abinsu sau da yawa idan Hadizan ta kira sedai taji call waiting in taci sa'a ya daga yace mata yana aiki ze kira shi kenan sedai idan ita ta sake kiransa kuma.

Ranar wata Laraba ta kirashi akan tanason magana dashi, magiyar datayi masa ta sakashi yarda su hadu a wani gurin cin abinci. Ya rigata zuwa dan ita tareda Khausar suka fita sun tsaya wani guri qarshe ma tafiya tayi ta bar Khausar din saboda yana jiranta.
"Khalil bansan me yasa kake guduna ba, baka son magana dani a waya ballantana kazo inda nake, idan nayi maka wani abun ne ka sanar dani na baka haquri dan Allah?" Hadiza ta fada kamar zatayi masa kuka.

Shiru yayi dan besan ta inda ze farayi mata bayani ba, dukda cewar be taba yi mata alqawarin aure ba a zuciyarsa kadai yake qudurta hakan sedai yasan itama lissafinta kenan tunda soyayyarsu ba soyayyace ta banzaba, suna mu'amala ne irinta wanda suke shirin gina wata rayuwa a gaba tare.
"Khalil kayi shiru kayi magana" ta sake fada, se ya qaqalo murmushi yace

"Bakiyi mun komai ba Hadiza kawai ayyuka ne suka sha kaina, sannan kinga nan akwai banbanci da snada ina Lagos, a nan idan na tashi aiki gida nake komawa gurin iyalina kinga babu dadi ace na koma gida kuma na ringa waya da wata a waje Matata ba zataji dadi ba".

Shiru tayi kafin tace
"Na sani amma a qalla ko sau daya ne ka ware lokacin da zamuyi magana duk sanda na kiraka fa uzuri kake bani, daga na aiki se kana kan hanya tuqi kakeyi kuma idan ka gama ba zaka kirani ba me yasa?"

"Hadiza, qorafi kike so ki koya kema? Na gaya miki uzurina baki yarda dani bane ko yaya" ya fada yana tsareta da ido, itama kallonsa tayi tace
"Hadiza?"
"Oh sorry Dijahna, shikenan?" Ya fada yana dage mata gira daya seta sun kuyar da kanta qasa, wato tana son Khalil da yawa, she can't wait ace ta zama matarsa".

"Yanzu ya akayi, kin ce kina son muyi magana me muhimmanci" ya katse mata tunaninta seta daga kai ta kalle shi tace
"Daman Yaya ne yayi mun magana akan ya kamata idan da gaske kakeyi ka turo da manya su shiga maganar" ta qarasa a sanyaye, Khalil dake shan ruwa be san sanda ya kware shi ba ya shiga tari duk ta rikice tana masa sannu, seda ya lafa masa kafin ya kalleta da idonsa da sukayi ja yace

"Dijah, amma bakiyiwa su Mama bayani akaina bane ba?"
"Kamar Yaya Khalil wane bayani kake so nayi musu kuma? Na fada musu wanene kai da Komai naka dana sani shine dalilin ma da Yayan yace na gaya maka ka turo dan yayi bincike a kanka kai mutumin kirki ne" Hadiza ta fada tana kallonsa. Seda ya hadiye yawun daya tarar masa a baki a ransa yana cewa
"Abinda nake gudu kenan" a fili kuma yace

"Amma baki fada masa shekarata biyu da aure ba ko?"
"Meye hadin shekarun auranka da maganar namu auran kuma?" Ta mayar masa da tambayar seya tareta da cewa

"Yana da Hadi sosai ma Hadiza, yanzu misali ace kece Matata, haka kawai babu wata matsala tsakaninmu shekara Biyu nace zan qara aure zaki yarda?
Bama Matata kadai ba hatta da iyayena nasan idan naje musu da maganar a yanzu se sun tuhumi dalilin da ya saka nake son qara auren".

"Kenan yaudarata kake yi daman ba aurene ya kawo ka gurina na?" Hadiza ta fada muryarta na rawa se Khalil yayi saurin cewa

"Wallahi Aa, Allah shine shaidata banzo gurinki da niyyar yaudara ba amma nima ki fahimceni dole ina da buqatar saita abubuwa da yawa kafin nace zan taso da maganar aure yanzu, dole ne na fara samun goyon baya daga gurin Magabatana sannan ita kanta Matata sena samu hadin kanta kafin nace zan turo da magana gidanku"

"Kenan ni kuma ina zaune ina zaman jiranka idan baka samu hadin kan nasu ba na tashi a tutar babu koh? Wallahi Khalil ka cuceni ka bata mun lokaci. Da kasan baka shirya auran ba me yasa ka shigo rayuwata har ka saka na kori kowa duk a tunanina na samu Mijin aure? Lokacin da kake cewa idan ka samu yanda kake so kafin qashen shekarar nan zakayi aure daman duk yaudara ce ko kuma akwai wadda kake nema bayan ni ni bata mun lokaci kawai kakeyi? Hadiza ta fada cikin Kuka tana miqewa tsaye se shima ya miqe ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu.

"Kiyi haquri Ki zauna kinga mutane suna kallonmu karsu dauka wani abin nayi miki" ya fada cikin lallashi seta zabura tace
"Su kalle mu mana kuma ai wani abun kayi mun yaudarata kayi ka ha'ince ni" ta fada cikin daga sauti kafin ta figi jakarta tana cewa

"Bazan yafe maka ciwon son daka jefani a ciki ba, in sha Allahu kaima se Allah ya jarabceka da son wata kuma ta wahalar dakai"
miqewa yayi ganin ta fara tafiya ya sha gabanta yana cewa
"Haba Hadiza ya zaki yimun Allah ya isa ki tsaya muyi magana nifa ba cewa nayi bazan aureki ba lokaci nace ki bani na samu na daidaita abubuwa"

"Ka matsa mun na wuce Khalil" Hadizan ta fada yanda tayi maganar se yaga kamar ba'a hayyacinta take ba, dafe qirjinta da yaga tayi ya sakashi tunawa da tana da Ciwon qirji kuma damuwa ce take tayar mata dashi ta gaya masa, qoqarin yi mata magana yakeyi amma taqi tsayawa so kawai take ya bata guri ta wuce, ganin da yayi tana layi kamar zata fadi ya sakashi riqota yana cewa

"Ki nutsu kinga zaki fadi muje mota dan Allah ki nutsu badai maganar na turo bane zan turo ina sonki zan aureki Hadiza". Tallafeta yayi a jikinsa har suka qarasa jikin motar sa ya bude gaba ya sakata seda ta zauna dakyau ya kulle qofar ya zagaya mazauninsa. Da qarfi qirjinsa ya buga ganin wani Saurayi fuskarsa sanye da Facemask dab dasu ya daga wayasa kamar meyin video, sakin murfin motar yayi ya nufeshi sedai saurayin na ganinsa ya juya da sauri ya bar gurin nan take ya bace masa.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 36

Motar ya koma yana tunanin wanene wannan din kuma me yake dauka? Ganin bashi da me bashi amsa ya saka ya mayar da hankalinsa kan tuqin da yakeyi yana yi yana lallashin Hadiza dake kuka, har qofar gidansu ya kaita, be barta ta fita ba seda ya tabbatar ta sakko kuma ta dena kukan da takeyi ya lallabeta ya kuma tabbatar mata da In sha Allahu ze aureta amma tayi haquri ta bashi lokaci kuma ta ringa musu Addu'a.

"Ina son Matata sosai bansan ta yanda zan kalleta nace mata zan qara aure ba" ya fada yana kallon Hadizan ta buga masa wata harara tareda jan tsaki kafin ta kama murfin motar ta fice batareda ta tanka masa ba ya rakata da Murmushi, haega Allah yana son Hadiza kodan sanyin Halinta da kulawar da take bashi kuma tafi sonsa akan wanda yake mata yasan zata riritashi ta kiyaye bacin ransa to amma damuwar ta inda ze tunkari ita Uwargidan da wannan magana dan ta Hajiya da duk wani da ze iya kawo cikas me sauqi ne.

Gaba ya danyi ya bar qofar gidan nasu ya samu guri ya tsaya. Jalila ya kira ringing biyu ta daga tana cewa
"Aa Hussaina yau ka tuna dani kenan"
"Dama na taba cewa na manta dake ne?" Ya bata amsa se tayi yar dariya tace
"Toh ai muj sallamawa Maman Mu'ayyad kai, ta tsare gaba ta tsare baya Hajiya kadai ake bawa damar ganinka da magana dakai sanda taso mu kuwa idan mun gaji da neman ka sedai mu kirata mu bada saqo"

"Kina da Matsala Jalila yanzu duk meya kawo wannan qorafin" ya katseta, seta sake cewa
"Gaskiya ce kawai ba qorafi ba gaba daya ka maqalewa Mace baka da lokacin kowa yanzu se nata duk sunkasa fasa maka ne ni kasan bazanyi shiru ba"

Qaramin tsaki yaja yace
"Mutum na cikin wata damuwar zaki zo ki qara masa, kiranki nayi ki bani shawara amma zaki cikamun kunne da mita haba" yanda yayi maganar cikin alamun abu na damunsa ya sakata sassauta murya tace

"Yi haquri toh dan qanina meya faru, wace damuwa kake ciki kuma shawarar me zamuyi?"
"Aure nake so na qara Jalila" ya bata amsa kaitsaye dan bayaso aja maganar se tayi shiru kusan minti daya kafin ta numfasa tace
"Aure Khalil, ka gayawa Hajiya kuma ta yarda?"
"Ban gayawa kowa ba shawararki nake nema me kike gani akai nayi ko Aa?" Ya mayar mata da wata tambayar se Jalila ta ajiye numfashi tace

"Wannan ai ba maganar da kai tsaye zance maka yi ko karkayi bace. Qarin aure yana zuwa ne akan abu biyu, buqatuwar yin hakan ko kuma yazo maka baqatatan daga Allah dukda dukka biyun nufin Allah ne amma kashin farko da niyya kuma mutum yaso yin hakan kai wannene naka a ciki?"

"Nima ban sani ba" bata amsa kamar me shirin fasa kuka, baya so Hadiza ta zarge shi da laifin yaudara dukda wani mummunan abu be taba shiga tsakaninsu ba ze iya cewa ko hannunta be taba ba sedai bisa kuskure amma dukda haka bazeso haqqin Soyayyar da takeyi mishi ya kamashi ba kuma tsoron sa Allah tsoronsa yanda ze tunkari Umaimah musamman da yanzu suke zaune lafiya babu wata matsala a tsakaninsu. Dariyar Jalila ce ta dawo dashi hayyacinsa yaji tana cewa

"Dan qanina maganar nan bata waya bace, ka samu lokaci kazo mu tattauna in fahimceka kafin nasan abin da zan baka shawara akai"
Yayi Na'am da shawararta dan haka yace mata
"Shikenan zanzo, amma dan Allah kar wanda yasan wannan maganar ko da Hajiya ce na gaya miki ban sanar da kowa ba seke, ba kuma naso suji se na gama yanke shawarar yi ko akasin haka"

"Haba kaima kasan babu meji, ko mun taba kashewa mun rufe kaji wani ya tada maganar?"
"Naga kin koyi tsogumi ne yanzu shiyasa musamman tunda kun sakawa Matata ido qila ku kuke ta mata Addu'a har naji abin ya darsu a zuciyata" se Jalila ta saka dariya tana cewa
"Ai ko ace muna da wata matsala da Matarka bazamu goyi bayan haka kawai kayi mata kishiya ba indai ba da wani babban dalili ba ballantana ma babu, ka samu lokacin ka shigo se mutattauna kaji" daga haka sukayi sallama ya tada motar yaci gaba da tafiya.

Office ya koma amma gaba daya ranar be iya gane abinda yakeyi ba dan hankalinsa ya rabu da yawa.
Kwana biyu a tsakani cikin damuwa yayi su, tunanin yanda ze magance Matsalar Hadiza yakeyi gashi tayi fushi koya kirata a waya se taga dama zata dauka har tana cewa ashe yana da lokaci daman niyyar kiranta ne kawai bashi dashi se yanzu se ya ringaji toh kawai ya rabu da ita mana salin alin su rabu ga mafita ya samu amma yana tsoron haqqinta, yasan zafin soyayya tunda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login