Showing 57001 words to 60000 words out of 429394 words

Chapter 20 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1033

ta fice har tana yarda Asoken hannunta da cloche.

Mansur da kansa ya dauki ledojin Kazarta da yoghurt ya nemi daya daga cikin yammatanda ya gani suna fira a qofar gidan ya bata da kayan ta data zubar kafin ya koma mota lokacin har Khalil ya dawo gaban ya cire hular sa yana shafa kansa.

"Khalil be kamata ka ringa mata ihu haka ba, kasab matsalar yarinyar nan nasiha da lallami ne ze tafiyar da ita bawai hargagi ko fada ba" Mansur din ya fada bayan daya tayar da motar suka fara tafiya, Khalil yayi shiru kamar baze yi magana ba can ya sauke ajiyar zuciya yace

"Mansur ina son Umaimah amma bazan boye maka ba ina tsoron irin zaman da zamuyi da wannan halin nata. Ace ita bata san ya kamata ba? Ka kalla fa Mansur idan badan Anty Hafsa tayi mata horo ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba na tabbata yarinyar se tayi abinda har a freedom radio se anji labarin mu sannan kana kallo ina mata magana a maimakon ta bani haquri ma se wasu hawaye takeyi saboda tasan bana son kukanta to ta dena yaudarata da su wallahi".

Shidai Mansur yayi bakan yana jinsa har suka qarasa gidansu, suna shiga Mukhtar daya daga cikin Abokansu ya kira wayar Mansur yana musu masifar gasu a Hotel tun dazu su ina suka tsaya dan sun hada Barbeque zasuyi, haquri ya bashi kafin ya shiga lallaba Khalil din da gaba daya Umaimah ta gama bata masa mood ya tashi ya shirya suka fita bayan daya bawa qannensa Kajin da suka siyo dan shaf ya manta da batun barbeque din.

Umaimah kuwa tana shiga cikin gida a sittin tayi kwana saboda hango Anty Hafsa data kasa ta tsare bakin hanya tana jiran shigowar Umaiman daman sedai ta makara dan tara tara suka mata Anty Laure na daga bayanta dan haka tana juyawa ta riqeta.

Yanda kasan sun samu Damin gero haka suka hau jibgarta ihun ta ya fito da yan biki ana tambayar lafiya Anty ta kwaceta da kyar daga hannunsu tana masifa tace

"Wannan wane irin wulaqanci ne Hafsa? Kema Laure zaki biye mata ku kama yarinyar da duka salon ku ja mata tsautsayi ta tafi gidan miji da jinya"

"Idan bata tafi da jinya ba ai mu data zubar mana da mutunchi ta barwa kanta abin magana har yaya da jikoki, banda tsabar iskanci dan ubanta ta rasa ranar da haukarta zata tashi se yau a cikin taron jama'ata bata mun tari?
Ai ba a nan ya kamata ku dake ta ba, so nayi seta tube ta shiga wanka zan kama yar banza ga Darbejiya can na saka Salmanu ya tsinko mun na farfasa wa yar banza jiki idan yaso tayi jinyar da kyau" Mama data qaraso gurin ta fada.

Ita dai Umaimah tunda ta samu Anty ta ceceta sukayi ciki shikenan, can uwar dakinta ta wuce da ita ta hada mata ruwan wanka tana yi tana mata fadan abinda tayin

"Yanzu Umaimah idan bakiyi hankali ba se yaushe zakiyi? Kina kallo Allah ya taimakeki ya hada ki da dangin miji masu sonki ki kalli yanda suke rawar jiki dake a gurin nan shine kikaje zaki bada kanki. Dan Allah ko koyi haquri ki kuma ringa sakawa zuciyarki salama dan wallahi yanda Khalil yake binki yana lallabaki a waje ina tabbatar miki daga gobe labari se chanza, halinki na gari ne ze zaunar dake a gidan miji, duk wannan buyagin da hayagaga babu abinda zasu ja miji se wahala" Antyn ta fada tana shafa mata dilka a jikinta.

Umaimah dake jin kamar ta sauke fushinta akanta ta dai daure ta ringa cewa toh dukda qasab ranta tasan gaskiya suke fada mata dan gashi nan tun ba'aje ko ina ba ta fara ganin chanji a gurin Khalil din, gashi jiya dakyar suka sasa ta yanzu ma ta sake kunno wata rigimar kai ita dai Allah ya shiga lamarinta.

A dakin Antyn ta kwana dan da Abba ya aiko kiransu shida yan uwansa zasuyi musu Nasihar bankwana ma Antyn ce ta rakata ta kuma kasa ta tsare har aka gama suka dawo ta bata Kazar data dafa musu da tafasashshiyar madarar shanu taci tayi nak kafin tayi bacci.

A safiyar washe gari dakyar ta yarda akayi mata light Make up ta shirya cikin fari da Golden din Lace iri daya dana Nuratu dake walwalarta kamar kowacce Amarya, ita kuwa ta samu guri ta zauna zugudi duk yanda qawayenta suke tsokanarta da amma ta kasa tanka musu dan rashin ji daga Khalil da batayi ba tun daren jiya ya bala'in daga mata hankali.

Furucinsa take tunawa da yace mata idan ta sake yin wani shirme ba ana gobe daurin auransu ba ko a ranar ne seya fasa yanzu ita ta rasa ma a wanne matsayi take dashi dan tun jiyan be kirata ba ita kuma tsoron abinda zeje ya dawo ya hanata kiransa a waya haka ta zauna ana ta hidimar daurin aure kowa ka gani cikin farinciki banda yana walwala banda ita.



Alqawarin Allahya cika, qarfe 11 na safiyar Asabar din Aka daura Auran Dr Nuratu Sabo da Angonta Dr Sagir Nafi'u Tareda na Umaimah Sabo da Angonta Architect Khalil Umar Bayero akan sadaki naira Dubu 100 kowaccensu.

Dafe qirji tayi lokacin data ji sanarwar daurin auran ta cikin lasifiqar masallacin layin nasu inda ake daurin auran, Khalil be fasa ba kenan?.

A zahiri babu wata murna ko farincikin data nuna amma badininta ko fadar yanayin da take ciki ma bata bakine, wai dagaske yau ta zama matar Khalil ta halal daga yau sun zama daya ita dashi ina zata saka kanta dan murna amma sam halin da take ciki ita da angon nata ya danne murnar se ya zamana kawai gatanan ne tana zaune.

Lokacin da Angon Nuratu da Abokan sa suka shiga gidan Dakin Anty ta shige ta zauna dukkiran ta da ake akan ta fito suyi hoto taqi to ta fita tayi musu me? Baqin ciki ya kasheta tunda ita nata angon ba zuwa zeyi ba?

Tana nan zaune ta jiyo wata maroqiya ta ware murya tana zabga kirari, idanba kunnenta ne ya jiyo mata qarya ba sunan Khalil tajiyo tana ambata sannanga wata sabuwar hayaniyar maza na shigowa seta miqe da sauri ta daga labulen window ta leqa idonta ya sauka kan Khalil daya sha Light blue din shadda yayi kyau har bata san yanda zata misalta ba, kumallon ya motso mata saboda yanda ake ta daukar Angwayen hotuna da wayoyi amma taringa qoqarin dannewa se numfarfashi take kamar wadda kunama ta harba daidai nan Maman Asad ta turo qofar dakin tana cewa

"Allah ya yaye miki baqin hali Umaimah, nan kika zo kika boye ga angonki can yana nemanki dalla wuce muje mutuniyar banza kawai da bata san Annabi ya faku ba" Maman Asad din ta qarasa tana kamo hannunta suka fice daga dakin.

Kasa riqe hawayenta tayi lokacin da Maman Asad ta qarasa da ita gaban Khalil dake tsaye fuskarsa babu yabo babu fallasa, girgiza mata kai yayi alamar kartayi kukan amma ina kamar yace tayi sega hawaye sha se kawai ya bude mata hannu ta fada jikinsa ta qarasa sake masa kukan harda sheshsheqa.

Ihu aka dauka masu daukar su hoto da Video kuwa daman sun samu nayi qawayenta se ihu suke suna daukar su a hoto
"Awwn love in Tokyo, Umaimah bazaku kashe muda salonku ba wanda bashi da masoyi ai se takaici ya qume shi" Yaya Naziyya ta fada cikin salon wasa aka sake fasa dariya Umaimah dai tunda tayi luf A jikin Khalil, a kunnenta ya rada mata

"I get you wife" .
Haka aka ringa daukar su hotuna, ran Umaimah kamar an saka Hypo an wanke matashi tas dukda fuskar Khalil din babu fara'ar nan data sanshi da ita amma kukawar daya bata a gaban mutane ta gama mata komai, ta kuma tabbatar da zuwa dare zasu sasanta dan bazata bari ta shiga gidan sa suna takun saqa ba.

Haka aka gama photo session Angwaye suka wuce gurin reception Amare kuma aka shiga hidimar yinin biki da shirin miqasu gidajensu saboda da wuri za'a kaisu dan Dangin Mijin Nuratu zasuyi Dinner.

Qarfe hudu aka dauki Amare, Nuratu aka fara kaiwa Umaimah tayi mata rakiya har cikin dakinta, shaquwa ba qarya ba, duk irij tarangahumar tashin hankalin da suke sha a gida kamar masu ganin hanjin juna se ga Umaimah ta fashe da kuka da batayi ba a gida har aka taho dasu ta fada jikin Nuratu suka rungume juna.

Yanda suke kukan dole suka karyawa sauran yayyensu zuciya suka hade gaba daya suka ruguntsune, jarumtar da sukayi a gida se gashi Umaimah ta karya musu dakyar aka yakiceta suka wuce nata gidan aka bar Nuratu da wasu daga cikin Masu halartar Dinner kafin sukaita itaka su koma gida su shirya.

A dan madaidaicin gidan na Khalil aka sauke Amarya Umaimah. Gidan two bedrooms ne a cikin madaidaicin palour asalin ginin daki daya da bandake ne daya babu daya tashi gyara ya tashi wani daki falle daya dake tsakar gida ya shigar da bandaki a dayan dakin ragowar ya qara mata a kitchen da yake atsakar gidan shima aka fitar fa store se qaramin bandaki na tsakar gida.

Gaba gidan bashi da girma dan filin tsakar gidan mota daya ze dauka amma yanda Khalil din ya saka kudi ya gyara gidan abinka da Architecture dole duk wanda ya shiga seda ya tafi da santin gidan ga hadaddun Furniture da suka qara qawata gidan sun saka komai yanda ya kamata.

A dakin da yake matsayin nata suka ajiyeta, Nasiha sosai Anties dinta sukayi mata irin me ratsa jiki da tasa Umaiman tayi tubus kamar wadda ruwan sama yayi wa duka kafin sukayi mata sallama aka barta da qawayenta uku, Rumasa'u, Farida Cousin dinta se Fatima.

Su suka gyara mata gidan tsaf suka wanke bandakuna. Seda sukayi sallar Magriba kafin Umaiman ta sake wanka, kafin ta fito sun bi gidan lungu da saqo sun saka hadaddun Turaren wutar da Akayi musu a gurin *Meerah_Perfumes_More* wanda Gudummawa ce takanas Aminiyar Mamansu Hajiya Findiga ta aiko musu shiga daga Adamawa inda take.

Seda sukayi sallat Isha kafin su Ruman suka fara haramar tafiya dan shiru babu Angwaye, tana cikin yi musu magiyar kar su tafi su barta ita kadai su qara jira yanzu zasu zo Farida na masifar me yasa ita bazata kira Khalil din ta gaya masa zasu tafi ba se wani su zauna take cewa suka jiyo qarar bude Get.

A dakin suka barta suka koma palour Khalil suna zama su Khalil din suka shigo su hudu, Mansur, Mukhtar se Cousin dinsa Awwab. Rumasa'u ce ta fito musu da Umaiman data sha uban lullubi da laffayar data nade jikinta har fuska ko gani batayi se Ruman ce take mata jagora ta zaunar da ita akan two sittet inda Khalil ke zaune.

Basu wani bata lokaci ba bayan barkwanci da aka san kowanne abokan Ango da qawayen Amarya nayi daga nan Mansur ya bude musu taro da addu'a, sosai sukayi musu Nasiha da shaqarwari ta daidai matsayi irin nasu na Abokai Awwab ya rufe musu bayan da suka ajiyewa Amarya kedojin kayan siyan baki suka bawa qawayenta kudin kati kafin sukayiwa Amarya da Ango sallama kowa ya miqe aka fara haramar tafiya.

Umaimah bata taba zaton zataji irin abinda taji lokacin da suka fara barin palor suna mata sallama da fatan Alkhairi ba, shi kenan yanzu fa ita tazo ita da gidansu ko wani guri sedai yawo duk inda zataje ta dawo nan din dai nan zatazo ta shigo sabuwar rayuwa da bata da tabbacin a yanda zata zo mata.

Tana zaune tana tunanin taji motsin rufe qofar Khalil da yayi musu rakiyaz kamar munafuka ta dago ido ta saci kallonsa karaf suka hada ido gabanta ya yanke ya fadi, fuskar sa a dinke ga wanu kallon da taga yana jifanta dashi data kasa fassara kona menene gashi kamar wadda ya sakawa glue ta kasa janye idonta daga nashi.

"Zo" ya fada yana kallonta, seta miqe jiki babu laka ta nufeshi, hannu ya bude mata bata bata lokaci ba ta fada jikinsa ya mayar da hannun ya rufe. Wata irin runguma yayi mata da seda taji kamar ze hade mata qasusuwan jikinta tayi yar qara saboda taji zafi dagaske, rabata yayi da jikinsa fuskarsa dauke da murmushin da yau ta kira dana mugunta yace

"Na dena bata yawun bakina yanzu ian da hanyoyi da yawa da zan hukuntaki yarinya karki fasa rashin ji" kafin ta samu damar cewa wani abu ya sake sakata a jikinsa tareda hade bakinsu ya shiga mata wani kalar kiss daya sa taji kamar hankalinta ze bar jikinta.

Abu biyu ne suka dirar mata lokaci daya, na farko tsoron sabon Al'amarin daya risketa san a rayuwarta babu wani Da Namiji daya taba rungumarta kamar haka balle har ya kai ga kissinga nata. Duk rashin kunyarta da fitsara ta wannan bangaren babu ita a lissafi, bata yarda da Namiji ya tabata ba koda cikin kuskure ne se tayi maka tas balle ka aikata mata hakan a cikin sani ranar me rabasu se Allah.

A cikin samarin da tayi daman Alqasim ne me halin son taba jikin mace shima tunda tayi masa kadan daga haukanta ya kiyayeta se gashi yau Khalil ya fara dora mata karatun da ba'a kowacce makaranta ake koyashi ba.

Bata ankare daya warware mata laffayar dake jikinta ba seda taji su warwas a qasa, zip din rigarta da taji yana lalube ya sakata dawowa hayyacinta ta tureshi zuciyarta na tsalle kamar zata fito tsabar yanda ta tsorata ga Labbanta da lokaci daya suka dauki zugi na rashin sabo da abinda suka gamu dashi yau ji take kamar harshenta ma ciwon yake, dakyar ta ja jikinta ta takure a jikin kujera inda Gogan ya kwanta shiru kamar wanda ruwa ya cinye kusan minti biyar kafin ya yunqura ya tashi zaune, yanda Umaimah taga fuskarsa ta qara tsorata, wani irin jaa da idonsa sukayi suka qanqance gaba daya ta tafi tunanin maganar da Halima ta gaya mata da tace masu shiru shirun nanirin Khalil idansuka kama mace seta gane kurenta.

"Kuka kuma me akayi miki?" Ya fada cikin dasashshiyar murya kamar wanda yasha kayan maye se Umaimah ta kai hannu idonta ta shafa taji danshi kuwa ashe kuka take ita bata ma sani ba, hannu yakai ze taba ta ta zabura yanda tayin dole ta saka Khalil dariyar da be shirya ba yace

"Rekax, ba abinda zanyi miki yunwa nakeji sosai ki bani abinci naci".

A dari ta miqe ta tafi luu zata fadi saboda skirt dinta daya harde ta, "yah subhanallahi" ta fada a fili ta shiga tattaro skirt samata zuge kafainta mayar da zip dinrigar daya fara zugewa shima, toh wai duk a yaushe hakan ta faru ne?

Laffayarta ta sake tattarowa tana so ta daura amma rawar da jikinta yakeyi yasa ta kasa Khalildaya jingina da kujera kawai yana kallonta kamar ya samu TV ya miqe dakyar ya qarasa bayanta, Laffayar ya karbe ya dora kansa a wuyanta, cikin kunnenta ya rada mata

"It is just me and you, lullubin me kike nema? Ki barni na kalli baiwar da Allah yayi mun Babe"
Ai gaba daya ya idasa wargaza mata yar nutsuwar da tayi mata saura a jiki, yanda take wani abu kamar wadda Shocking ya kama ya sakashi dariya sosai, jan ta yayi ya zaunar da ita akan kujera kafin ya shiga kwashe ledojin da suka shigo dasu ya fita dasu kitchen.

Seda ya fitar da komai ya sakashi a inda ya kamata kafin ya daurayo plates da cups da duk abinda zasu buqata ya sake komawa palour har sannan Amarya Umaimah na nan zaune ta dai nemo dankwalinta ta lullube kanta zuwa qirji dashi.

"Oya come lets eat" ya fada bayan daya gama juye gasashshiyar kaza a plate dayan kuma ya zuba tsire, ga qatuwar robar yoghurt ya ajiye musu a gefe da lemon exotic be tsaya bata lokaci ba ya fara aikawa cikinsa dan rabonsa da abinci tun safe.

Ganin yayi loma biyu bata sakko ba ya waiwaya ya kalleta yace

"Umaimah sakko mana"
"Ni na qoshi bana jin yunwa" ta fada a hankali, se ya saki murmushi yace

"Gara ki sakko kici ko bakya jin yunwa saboda ki qara samun qarfin daukata" ya qarasa yana kashe mata ido seta saki baki galala kamar lefen sakara kawai tana kallonsa, kai itafa Khalil ya f???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ara bata mamaki yanzu duk kunyar nan tasa da shiru shiru ina suka tafi da ze ringa mata abubuwa haka yana zaro zance?

Naman daya kawo bakinta ya dawo da ita tunanin data tafi, ba yanda ta iya dole ya sakata ta sakko suka ci naman, dadin daya mata se gashi bata san lokacin da suka cinye kazar tas ba dan itaka kura ce ta gaske.

"Da kina noqewa gashi nan kin tashi da kazar ni ko ci ma banyi ba" ya fada cikin sigar tsokana seta sunkuyar da kai dan taji kunyar yanda ta zage taci naman.

Plate din tsiren ya tura mata tace ta qoshi, ya cika cup taf da madara ya bata ba yanda ta iya swda ta shanye ta ajiye masa kafin yana murmushi yace

"Good girl, yanzu se muje muyi wanka muyi sallah ko? Kinsan Ibadah bata yuwuwa se ciki ya dauka" ya fada yana shafa cikinsa.
Kwanukan ta fara hadawa ya dakatar da ita, dakansa ya sake kwashe komai ya fita dasu abinda basu cinye ba ya saka a fridge ya dauko qaramin akwati daga motarsa kafin ya sake tofe ko ina da addu'a kafin ya shiga ya kulle qofar palour gaba daya.

Be tarar da Umaimah a palour ba ta tattara yanata ya nata ta shige daki. Dakin da yake tunanin nata ya tura ya shiga tana tsaye tana cire kaya jin shigowarsa ta durqushe qasa da sauri tareda sakin ihul tana janyo Towel din data ajiye akan gado dan ta rigada ta cire skirt da rigar, Bra jikinta take ballewa.

"Duk ki gama boye boyen yarinya zakizo hannuna" ya fada yana ajiye mata ledar daya dakko kafin ya fita yaja mata qofar dakin.
Ajiyar zuciya ta sauke ta tashi da sauri ta murzawa qofar key.

Wanka tayo hade da Alwala ta shirya a nutse kamar yanda Anty Hafsa ta karanta musu. Ledar daya ajiye ta jawo ta bude, wata hadaddiyar rigar bacci ce kalar ja me jikin silk, yanda ta dagata tasan da kadan zata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login