Showing 117001 words to 120000 words out of 429394 words

Chapter 40 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

989

za'a kirashi a sanar dashi dan haka ya yanke shawarar kiran Mama tunda dai bata gida ya tabbatar da idan ba gidansu ba babu inda zataje dukda be bata izinin hakan ba.

Cikin mutuntaka suka gaisa da Mama bayan daya kirata ya sake yi mata gaisuwar Mijin Anty Hafsa ta amsa tana tambayarsa aiki tareda godiyar Kayan Sadakar da aka ringa kaiwa daga gidan Hajiyarsa. Shiru sukayi gaba daya a ransa yana tunanin idan Umaimah bata gidan fa tsahon wannan lokacin ya za'ayi, Kukan Mu'ayyad da yajiyo ta cikin wayar da Ashar din da Umaimah take korawa wata da be san ko wacece ba ya warware masa damuwarsa dan haka kawai ya cewa Maman daman ya kira su gaisa ne yayi mata sallama ya kashe ransa na masa suya, kenan tana sane ta kashe wayar tunda tasan batayi daidai ba tunda Koda ace wayarta ce ta lalace ai yaci ta ari ta wani ta kirashi sannan da izinin wa ta bar gidan kuma meye dalilin qin binsa da tayi.

A bangaren Mama kuwa yana kashe wayar ta dakawa Umaimah dake zagin Munawwara yarinyar maqotansu dake shiga tana daukar mata Mu'ayyad din, ta tasata a gaba tana zagi saboda ta riqeshi ya zille ya kifa da baki,
"Wai ke baki san tsautsayi ba tana sane zata bar shi ya fadi ne ko yaya da zaki tasa yar mutane a gaba kina zagi, ki kiyaye ni kuma wannan zaman naki ma ya ishe ni haka yanzu Mijinki ya kirani daga yanayinsa na karanci akwai magana a bakinsa amma ya kasa fada, daman ina an kare dake tunda kika zo gidan nan banji ko sau daya kunyi waya dashi ba idan ma wata tsiyar kika tafka ya koroki gida tun wuri ki sanar damu a san yanda za'a magance ta"

Zumbura baki gaba tayi ta kalli Maman tace
"Ni me zanyi masa ya koroni tafiya yayi baya gaya miki bama shine yace mu dawo gida, wayata kuma ta lalace na fi so se ya dawo ya kaita gyara da kansa dan kar a batamun" ta fadi haka ne kawai amma gaskiyar magana kashe wayar tayi kamar yanda Rufaida ta bata shawara bayan ta qufuri aniyar bazata bishi ba.

Mama ta wuceta ba tareda ta kulata ba amma jikinta yana bata qarya Umaiman takeyi dan a saninta tafiya kota kwana biyu ce tare sukeyi dukda wani lokacin se an yi sulhu kafin tafiyar ta yuwu shine yanzu kusan sati biyu ace baya gari ta taho gida gaskiya akwai lauje cikin nadi.

Khalil kuwa bayan ya ajiye wayar sa shiru yayi yana tunanin ta inda ze hukunta Umaiman, rainin dake tsakaninsu ya fara yawa har ya zamana kenan be isa ya bata umarni tabi ba se abinda ranta ya ayyana mata koh dole kuwa zeyi maganinta.
Tun da ya bar Kano haquri kawai yakeyi musamman da yanda Umaiman ta sake chanza masa tun bayan data haihu saboda ingantaccen jego da kuma gyaran data samu ko tunaninta yayi se hankalinsa ya tashi, a lokacin ma abinda ya faru dashi kenan lokaci daya jikinsa ya farayi masa babu dadi shikadai yasan yanda yake bacci yake tashi ya gama saka ran zuwan nata shine tayi masa wannan cin kan yanzu besan ya zeyi ba, yanzu dole yayi qoqari yaje Kano a weekend din nan dan bashi da inda ze kai lalurar sa idan ba canba.

Wunin ranar gaba daya haka yayi shi sukuku harya tashi daga aiki ya koma gida, flat ne me daki biyu da duk wani abun buqata a ciki aka bashi yake zaune sanda aka kaishi masaukin a ransa har yana cewa anyi maganin mitar Umaimah da take cewa ita ba tafiya dashi ne bata so ba Aa haushinta zaman Hotel kullum tana kulle a daki kamar kaza yanzu ga gida nan ta samu kuma taqi zuwa.

Ruwa ya fara watsawa kafin yayi sallar Magriba data riskeshi a hanya, fridge ya bude ya tarar da babu wani abin kirki naci da ze qosar dashi yaja tsaki ya rufe, a yanda yake jin yunwa baze iya tsayawa dafa komai ba dan ya siyo kayan abinci duk a shirin zuwan Madam din tasa se kawai ya zari key din motarsa ya fita, a bakin Get din compound din sukaci karo da Sa'id Abokin aikinsa ya fito shima a shirye da alamar fita zeyi, gaisawa sukayi ya shiga qoqarin tada motarsa Sa'id din ya tsayar dashi, be fiya son doguwar magana tana shiga tsakaninsu ba saboda sam halinsa dana Sa'id din basu zo daya ba. Sa'id nada rawar kai ga shegen kule kulen Yammata kullum da macen da zaka ga tazo gidan gurinsa shi yasa sam Khalil baya bashi fuskar da wata magana me tsayi zata hada su data wuce gaisuwa.

"Mr Bayero fita zakayi ne, ur face shows that you are tired and
Famished, nima fita zanyi naci abinci idan babu damuwa muje tare motana na barta gurin gyara"
Badan ran Khalil yaso ba suka fita tare, a hanya se surutu yakeyi masa shi dai amsar sa Eh ko Aa ce dan gaba daya ransa a dagule yake, a gurin cin abincinma seda yaji kamar ya tashi ya bar gurin saboda shegen surutun Sa'id da yanda yammata suke ta zuwa yana gaisawa dasu.

Magana yaji daga gefensu, haka nan yaji kamar ya taba Jin muryar kuma jin suna hausa kuma kamar gulmar wani sukeyi haka kawai ya samu kansa da juyawa ya kalle su karaf idanunsu suka hadu, ya kalleta na tsahon seconds uku kafin ya dauke kai kwakwalwarsa na qoqarin tuna inda ya san fuskarta.
"Na gaya miki wallahi shine, ai bazan taba manta fuskar Guy din nan ba dan yayi bala'in burgeni" ya sake jin muryar data sakashi waigawar tana fada nan take ya tuno da inda ya sansu, yammatan daya taba taimakawa ya kaisu gida ne wata rana da daddare amma me sukeyi a nan? Ko daman yan duniya ne kawai raina masa hankali sukayi ranar da sukace biki suka zo.

Sallamar daya ji a saman kansa ta dawo dashi tunanin, me shegen rawar kance tana tsaye tana masa murmushi tace
"Sannu Malam, ka gane ni kuwa"
Kallon banza ya mata ita kuwa ko a jikinta se uban murmushi takeyi masa Sa'id ne ya mayar mata da martani yana cewa
"Zauna mana yammata kin tsaya kuma" seta ja kujera ta zauna har sannan tana kallon Khalil kamar zata lashe shi.

"Tunda kuka shigo na gane fuskarka, na cewa Hadiza kai ne tayi mun musu gashi ashe daman zamu sake haduwa tun waccen ranar nake Addu'ar Allah ya sa na sake ganinka dan ko godiya bamu samu damar yi maka ba waccen ranar" yarinyar ta fada tana yauqi kafin ya samu damar yin magana ta ci gaba da cewa
"Ni sunana Khausar, kai dai na san sunanka Khalil dan na gani a motar ka tun waccen ranar"

Tissue yaja ya goge bakinsa dan gaba daya abincin ya fita a ransa saboda surutun da tazo tana yi masa akai, shi daya sani ma Cornflacks yasha ya kwanta kawai da wannan fitowar da yayi haka kawai zata qara masa ciwon kai, tsaki yayi ya dauki muqullin motarsa tareda ajiye ATM card dinsa yana kallon Sa'id yace
"Gashi nan idan ka gama ka biya ni na wuce seka taho" yana gama fadar haka ya juya abinsa yana jin dayar yarinyar tana cewa
"Seki tashi mu tafi ai tunda kin gama zubarwa da kanki mutunchi aikin banza kina ta rawar jiki kamar kinga wani autan Maza".

Waiwayowa yayi ya kalli me maganar, waccen dayar ce wadda ta saka Hijabi ranar ya gane fuskarta ne saboda duk ta fisu haske fara ce sosai se yayi murmushi kawai wai Autan Maza.
Washe gari yana zaune a office aka kirashi da baquwar number, be dauka ba dan ba kasafai ya fiya amsa number da be sani ba musamman idan ya duba true caller yaga be san sunan me kiran ba.
Yana kallon wayar seda tayi masa kira biyar kafin message ya biyo ba ya dauka ya duba
"Khausar ce, ina fatan ka tashi lafiya" iya abinda ta rubuta kenan yaja tsaki bayan ya gama karantawa ya goge ya tabbatar Sa'id ne ya bata number sa nan take ya dannan ta a blacklist, to shi ko bufurwar zeyi me zeyi da ita babu abinda ta ajiye se shegen rawar kai.

Umaimah ce ta fado masa a rai kawai ya hasaso ace sun hadu ita da Khausar din wayaga yaqin duniya na uku ya tabbatar da haukarsu zata zo daya.
Wasa wasa Khausar ta mayar da kiran sa a waya dayi masa text kamar ibadah, data fuskanci yayi blocking layinta seta canza lamba, zata kira sau daya sannan ta tura masa da saqo safe da yamma, a cewarta idan da rai da rabo wata rana ze kulata abinda ta gayawa Hadiza lokacin da takeyi mata gorin rashin zuciya.
Aiki ne ya kaisu Lagos din qarqashin qunyar su me rajin kare haqqin mata da qananan yara, a qa'ida sati daya zasuyi amma tunda Khausar ta hadu da Khalil seda ta san yanda tayi aka qara musu lokaci saboda tace bazata tafi ba har seta samu soyayyarsa.

Sa'id ne yake qara mata kwarin guiwa akan hakan yana kuma bata tabbacin zata samu Khalil din indai tayi haquru, kuma shi ya gaya mata yana da Mata daya da Yaro hatta da irin sin da yakeyiwa matarsa da baqin kishinta daya samu labari ya gaya mata tace taji ta yarda kuma a shirye take data tunkari kowacce ya mace akan Khalil.

A bangaren Khalil kuwa be san ma tanayi ba dan ko messages din nata datake faman aikawa ba dubasu yake ba, shi yanzu hankalinsa gaba daya yana kan aikinsa ne saboda ayyukan da yake kula dasu suna da yawa tuni kuma ya yakicewa kansa Umaimah da tunaninta dan ya fuskanci idan ya daka ta tata baze moruba,lalacewa zeyi da ciwon bacin ranta kawai dan har yanzu da ake kusan kwana goma da zuwansa bata kunna wayarta ba kuma nemi wata wayar ta kirashi ba.

Da yammaci yana kan hanyar dawowa daga duba ginin wani company da sukeyi, a hankali yake tuqi saboda yanda gaba daya jikinsa bayayi masa dadi. Damuwa da buwatuwar mace a kusa dashi sun hadu suna neman saka masa ciwo a yankwanakin qarfin hali kawai yakeyi ya kuma yi rantsuwar seya koyawa Umaimah hankali abinda ya dakatr dashi daga tafiya Kano kenan dan a jiya harya hada kayansa ze tafi ya fasa. Tuqi yakeyi sam hankalinsa yayi gaba Allah ya taqaita ya tsayar da motar yayi gefe cikin wani ruwa daya kwanta saura qiris ya bige budurwar dake qoqarin tsallaka titi.

Dafe kansa yayi yana mamakin zurfin da yayi a tunani da har beganta ba, seya kashe motar ya fita ganin ta tsaya tana duba jikinta da alama ya watsa mata ruwan daya fada.
A fusace ta kalle shi daidai sanda yake bata haquri tace
"Dama se anyiwa mutum ba daidai ba ake bashi haquri ai, tun daga nesa dana hango motar nasan koma waye a ciki ba a daidai yake ba, duk yanda nayi qoqarin kauce maka amma ji sda ka batani da ruwan kwata haka kawai".

Tunda ta fara maganar yake kallonta, qawar wannan mayyar yarinyar ce, to wai su a nan garin suke ko kuwa yawon rashin jin nasu ne ya kawo su?
Kallonta yayi sama da qasa yanzuma tana sanye da doguwar rigar Atamfa ta saka Hijabi Light blue daya zarce guiwarta, sosai Hijabin ya baci da ruwan kwatar daya watsa mata, cikin gajiya da masifar da takeyi masa yace
"Kiyi haquri, banganki bane"
"Dama ai bazaka ganni ba"
"Nace kiyi haquri" yayi saurin tareta ganin tana neman tara masa mutane, shiru tayi shima ya tsaya, kamar baya so yace mata

"Ina zakije ga magriba tayi?" Sedata harareshi sannan ta gaya masa, kallonta yayi fuskarsa na nuna mamakin jin sunan Hotel din data fada amma kuma meye nasa a ciki ma, juyawa yayi ya bude motar yana cewa
"Muje na saukeki" seta juya tabi bayansa. Tafiya sukeyi babu me magana da wani, wayar dake hannunta ta dauki qara ta daga da sallama yanda take maganar ya fuskanci da Mahaifiyarta suke wayar, sannan a maganganunta ya gane cewar aiki ne ya kawota Lagos din to amma aikin me takeyi? Bayan ta gama wayar ta kashe haka kawai ya tsinci kansa da tambayarta aikin me tazoyi nan, seda ta harareshi kafin ta gaya masa suna aiki da NGO ne kuma an turo su yin wani assignment ne.

Har qofar Hotel din ya sauketa, ta kalle shi fuska babu yabo babu fallasa tace ta gode, kallonta yayi yace
"Nawane kudin wankin Hijabin naki da kike tayi mun tsaki a mota saboda ya baci" seta harareshi bata ce komai ba, murmushi yayi dan se ya ganta kamar Umaimansa dukda a yanzu daya qare mata kallo ya fuskanci ba yarinya bace, a qalla zatayi shekara Talatin ko fin haka. Wayarsa dake ajiye ya miqa mata yace
"Ki saka mun number ki idan kin tsayar da farashin se ki gaya mun".
Kallonsa tayi kamar bazata karba ba kuma seta miqa hannu ta karbi wayar ta shigar masa da number ta bashi yayi Dialing wayarta tayi qara ya kalleta yace
"I'm Khalil, and you"
"Hadiza"
"Nice to meet you Khadija" ya fada yanayiwa motar key ta dan ya mutsa fuska tace
"Hadiza sunana"
"Khadija ne sunanki na Asali ni dashi zan kiraki, ki shiga ciki se wani lokacin" yana gama fadar haka ya taka motar ya bar gurin.

Yana tafe yana tuhumar kansa dalilin daukota har zuwa karbar number ta da yayi, zuciyarsa ta bashi amsa da yana da buqatar Abokin hira ne daze debe masa kewa shine dalili, sannu sannu Abota ta qullu tsakaninsu a hankali shaquwa me qarfi ta shiga ya zamana cewa a kullum se sunyi waya dukda Hadizan ta koma Kano amma a koda yaushe suna maqale da juna a waya musamman da dare bayan ya koma gida bashida abinyi sedai ya kiraya su sha hirarsu. Yasan kusan komai a kanta, Ita din Lauya ce me zamankanta kuma tana aiki da qungiyoyin kare haqqin mata da qananan yara.
Yanzu idan ya tuna da Umaimah to kewar Mu'ayyad ce ta dame shi akan dole kuma ya sakawa kansa haquri tunda bashida hanyar da zeji lafiyarsa ko ya ganshi, abinda ya sani dai ko bajima ko ba dade dole ta nemi shi, idan bata neme shi ta arziqi ba zata neme shi ta tsiya.

UMAIMAH
Tun tana daukar abun a wasa harta fara shiga taitayinta ganin ana neman wata daya da doriya babu Khalil babu dalilinsa, a tunaninta data kashe waya ze nemeta kota wayar Mama ne ko ya aiko Khalifa se gashi babu daya daga ciki hasalima ita kanta Maman bata ce mata komai ba akan zaman nata, kowa ya zuba mata ido ne kawai suga iya qarshen Al'amarin.

Kudaden hannunta da suke rudarta sun qare tas ko na siyan Data bata dashi dan daman wayarta a kunne take, layinta da aka santa dashi ta cire ta ajiye ta dora wani duk a shawarar Rufaida taci gaba da sabgoginta, sanda tayi mata maganar ita zata Kira Khalil dan da alama yayi fushi da yawa ce mata tayi idan tayi haka ai ta zubda kanta, ta daure kawai harya gama fushinsa ya sakko duk tsiya dai ai ze dawo baze koma can da zama gaba daya ba.

Yau ta tashi gaba daya babu yanda take, Allah ya sani tana son mijinta kuma tana kewarsa da????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
urewa kawai takeyi kamar yanda Rufaida take gaya mata wai ta kama Ajinta karta kuskura ta bari ya gane ta karaya dan daman yanayi ne dan ya qureta.
Salma ce ta shiga dakin da sallama ta ajiye mata Ruwan zafi a babban Mug se burodi a leda, kallon kayan tayi daman tun tuni ake wulaqantata a gidan nan abinci se a bata kamar wata mabaraciya wani lokacinma idan an dafa seta roqa za'a bata cewa suke sun manta da ita.

Kayan taja gabanta ta kalli baqin ruwan shayin ta ja tsaki, gwangwanan kayan Tea din da Khalifa ya kawo mata tun wancen watan da tulin siyayyar Mu'ayyad su Diaper, wipes, madararsa da cereals sabulun wanki da duk wani abun buqata seda ya hado musu da yawa kuma yanda zata dade kafin ta buqata.
Kallon Madarar tayi bata wuci kwata a ciki dukda qaton gwangwani ne amma ta kusa shanye shi cikinta ita kadai saboda yanda take barnarsu haka kawai ma kwabawa take tana sha gashi yanzu sun kusa qarewa bataji daga me siya mata dinba kai ita wannan zaman ma ya isheta haka ita ba sakakkiya ba ita bame aure ba bari kawai ta karya billenta ta kira shi ai durqusawa wada ba gajiyawa bane.

Layinta data ajiye ta dakko ta saka a wayar, Allah ya taimaketa tana duba balance taga akwai kudi a ciki, layin Khalil ta shiga kira tana kallon Agogo ta san dai yanzu duk inda yake yaja Gym kamar yanda yakeyi duk Asabar da Lahadi se yaje.
Seda tayi masa kira uku be amsa baana hudun yana shiga akayi rejecting se ta riqe wayar sororo a hannunta jikinta yana qarayin sanyi, tasan fushin Khalil yana daukar lokaci kafin yayi amma fa idan ta taboshi seta sha wahala kafin ya sauka amma dukda haka ita a yanzu buqatarta ya haqura da gayyatarta idan zeyi tafiye tafiyensa idan dai haka ta samu zata san yanda zata lallabashi su shirya.

Maida wayar tayi ta ajiye ta shiga karyawa a ranta tana ayyana qaryar da zatayi dan ta samu hankalinsa cikin ruwan sanyi batareda wata matsala ba. A dakin taci gaba da zaman tsammanin ko ze biyo bayan? kiran da tayi masa, Mu'ayyad na can gurin Anty dan kusan kwanciyar baccin dare kadai ke kaishi gurinta se shan Nono wanda bema damu dashi sosai ba tunda ya kama abinci.

Tana nan jiran gawon shanu har aka kira sallar Azahar, seda tayi sallah ta quduri sake kiransa. Tana zaune akan sallayar ta janyo wayarta ta shiga kiran layin Khalil din ringing uku taji an daga taja wani numfashi ta dire ta narke murya kamar Kitse yaji wuta tace
"Habibi"
"Umaimah, ina aiki ne. Idan babu damuwa ki bari zuwa dare idan na koma gida zan kiraki ok" Khalil ya fada cikin dakakkiyar murya daga daya bangaren, kafin ta samu cewa wani abu dif ya kashe wayar seta cireta da kunnenta ta zura mata ido kamar zata ganshi ta cikin wayar,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login