Showing 126001 words to 129000 words out of 429394 words

Chapter 43 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

960

ko?"

"Nifa karka daga mun hankali a daren nan bansan meya sameta ba idan na kunna da safe rana na dagawa zata ringa mutuwa tana kawowa sedai da sanyin safiya ko da daddare ne kadai take tsayawa" ta fada tana miqewa tsaye. Be sake kulata ba ya shige bandaki bayan ya sauke Mu'ayyad qasa. Itama fita tayi tana mita, badan wallahi da abinda take so ba da ko kallo be isheta ba shima ya sani.

Kallonta taci gaba dayi, Khalil kuwa seda yayi wanka ya shirya kafin ya fito da yaron a hannunsa. Ajiye mata shi yayi ya fita Chemist din bakin layinsu ya karbo Masa Bonababe syrup da akace yana taimakawa yara gurin sauqin laulayin haqori. Kuka ya tarar dashi yanayi ita kuma tana dannan waya abinta kamar batajinsa ma, cikin bacin rai ya fizge wayar yana cewa
"Meye haka yaro yana kuka kina ji kin zauna kina danne dannen banza a waya"
"To me zanyi masa? Na bashi abinci ya qoshi rigimar sa ce kawai kuma bacci zeyi ba wani abu ba" ta fada tana nuna masa kwanon abincin Mu'ayyad din dake gefe.

Base ki goyashi ba tunda bacci zeyi amma se ki barshi yaringa kuka bayan kince baya jin dadi" ya sake fada yana jijjiga yaron. Zama yayi ya bude maganin, da kansa ya bashi sannan ya bashi ruwa yasha ya ringa zagayawa dashi a palour yana jijjige har yayi bacci hamshaqiyar kuwa tana nan zaune qafa daya kan daya tana dannan waya, ai yasan bata goyo ita shima rigimar banza ce saboda ya saba da suna gida Anty zata goyashi idan zeyi bacci da suka dawo ma haka Hauwa take masa.

Dakinsa ya wuce dashi ya kwantar, seda ya duba Diaper jikinsa yaga bata dade da saka masa ba beyi komai a cikinta baka kafin yayi masa addu'a ya kashe fitilar dakin ya fito bayan ya tokare qofar ya barta a bude.
Kan dining ya wuce ya zuba abinci yana kai lomar farko bakinsa wayarsa ta dauki qara gabansa ya bada Ras ganin me kiran Hadiza ce, kamar me ciwon wuya ya juya ya kalli Umaimah karaf suka hada ido dan tunda ya fito dakin take binsa da kallo kamar yaci mata bashi.
Abincin ya hadiye dakyar kafin ya danne wayar gaba daya ya kasheta dan dai baze iya wannan gangancinba, amsa wayar Mace a gaban Umaimah.

Har ya gama cin abincin tana nan zaune tana kallo a Tv tareda danna waya. Daga kan Dining din ya tambayeta akwai Maltina a Fridge tace masa babu, yasan Babun dan daman shi? yake amfani da ita ita bata sha kuma tun kafin yayi tafiya ta qare be siyo ba seya miqe ya shiga dakinsa ya dakko kudi yana cewa
"Bari naje na siyo"
"A daren nan sekace shan ya zama dole ka bari da safe ka siyo mana" ta fada tana kallonsa, be kulata ba ya fice daga palour. Cana gaban gidan ya samu guri ya tsaya ya kunna wayarsa ya kira Hadiza, qarya yayi mata akan tana kira wayar ta mutu seda ya saka chaji yanzu ya kunnata tayi murmushi tace

"Nima seda na kira sannan na duba lokaci naga dare yayi karna shiga haqqin Yayata, ina taso tun dazu na kira naji yanda kaje gida ban samu kaina ba nima se yanzu".
Hira ce ta kunce tsakaninsu sam Khalil ya manta da me ya fito yi seda yaji alamar wani kiran yana shigowa kafin ya zare wayar a kunnensa ya duba, Umaimah ce take kira, ya kalli Agogo qarfe sha daya da kwata ba shiri yayiwa Hadiza sallama ya miqe yaci gaba da tafiya yana zuwa kantin ya tarar sun tashi dan daman basa wuce goma da rabi.

Auna abinda ze gaya mata ya samu bacci a daren nan kawai yakeyi haka ya qarasa gidan, a bakin Get ya tarar da ita da dogon Hijabi ga Mu'aayad ta sabo a kafada.
"Ina ka tafi daga siyo Maltina kafi awa daya na kira wayarka kuma baka daga ba" Umaimah da duk ta rikice ta fada seya kama hannunta suka shiga ciki dan da qarfi take maganar karta taso musu maqota a daren nan.

"Khalil tambayarka nakeyi fa ina ka tafi" ta sake fada yayi saurin tareta da cewa
"Ba gani na dawo ba, naje kantin Dan Baffa babu sena qarasa can titi ko zan samu, ina hanya kuma Muktar ya kirani kinsan bikinsa ya taho kuma be qarasa ginin sa ba shine muke lissafin abinda ze isa a qarasa gidan ban ankara dare yayi ba seda naga masu shagunan sun fara rufewa, kingama ko Malt din ban tsaya karba na taho" Khalil ya sheqo mata qaryar da shi kansa be san sanda ya qirqireta ba.

Kallonsa takeyi kamar meson gano gaskiyar abinda yake fada, amma idan bata yadda bama wace hujja take da ita ko kuma zargin me zata masa? Hijabin jikinta ta cire bayan ta kwantar da yaron tace
"Naji ka shiru na kira wayarka baka amsa ba shiyasa nace bari na leqa dan yanzu unguwar nan se a hankali mantawa nayi ma ban gaya maka ba an ce a rage kaiwa dare a waje bata gari suna shigowa"
"Toh kuma shine zaki dauki yaro ku fita bayan kinsan unguwar babu lafiya, duk inda na tafi ai zan dawo idan ma ba lafiya ba za'a sanar miki" Khalil ya fada yana miqewa tsaye se itama ta miqe tana cewa
"Tunda ka dawo ai shikenan Allah kiyaye na gaba" ya amsa mata da Amin ya shige daki yana sauke ajiyar zuciya. Message ne ya shigo wayarsa a garin ya danne wayar ta subuce ta fadi daidai nan Umaimah ta shigo da butar shayi, kallon tuhuma ta bishi dashi ganin yanda duk ya rikice amma se qoqarin hade fuska dan karta kawo masa wargi yakeyi.

Butar ta ajiye da dan cup a gefen gado ta wuce bandakinsa. Beko bi takan shayin nata ba ya haye gado bayan ya kashe wayarsa ya jonata a chaji. Yana jinta tana ta buruntu a dakin, harta gama shirinta ta fita babu dadewa ta dawo da Mu'ayyad ta kwantar dashi a cikin gadonsa kafin ta kashe musu fitila ta hau gadon itama. Duk yanda zuciyarsa da gangar jikinsa sukayi kewarta haka ya danne yayi mata shiru kamar me baccin gaske. Babu yanda bata shafashi ta shiga jikinsa ba amma yaqi motsawa haka ta gaji saboda haushi qarshe dakin ta bar masa gaba daya ta koma palour, kukan baqin ciki ya kufce mata ita Khalil yau ya wulaqanta abinda yake binta yana naci yau ta kai masa a arha amma ya wulaqantata yaqi tankawa ze kuwa san da ita yake zancan.

Duk su biyun kwanan wahala sukayi babu Wanda ya samu wadataccen bacci. Umaimah kwana tayi murqususun ciwon mara saboda ta rigada ta shirya masa, harda maganin qarin kuzari tasha gashi duk ya tashi a banza haka shima Khalil din kusan rabin daren a bandaki yayi shi yana faman kwararawa kansa ruwan sanyi ko zeji sauqin abinda ke damunsa amma a banza daya dawo ya kwanta ze sake komawa ji yakeyi kamar yaje ya dawo da ita ga mayataccen turaren data shafa ya kama Gadon da jikinsa duk ya rasa inda ze tsoma ransa yaji dadi amma yaci Alwashin baze saki da wuri ba, dole ya horata yanda gobe bazata sake masa irin abinda tayi ba.

Da safe haihai suka gaisa dukkansu babu me cikakkiyar walwala. Data so neman magana yawo ta ringayi rabi tsirara a cikin palour yana zaune yana kallon labarai ita kuma tana hada musu abin kari qarshe dayaga babu arziqi ya koma daki ko breakfast dinma a ciki ta kai masa yana gamawa kuwa yayi wanka ya bar gidan dan yaga abin nata qara lalacewa yakeyi.

Yana fita Umaimah ta kira Maman Hauwa a waya kan ta turo mata Hauwan, ita ta gyara mata gidan tsaf tayiwa Mu'ayyad wanka bayan ta gama mata komai ta goyashi suka fita ita kuma ta kulle gidan ta shiga ramuwar baccin jiya.
Khalil kuwa se bayan daya bar gidan sannan ya kunna wayarsa. Saqonni Hadiza guda biyu suka shigo, daya tun dare ne tana gaya masa yanda yayi kyau a jiyan da yaje gurinta se kuma na barka da safiya da fatan ze wuni lafiya.

Shikam ya shiga rudani da yawa, harga Allah yana son Hadiza kuma yana son auranta dan yana neman matar da zata tsamoshi daga wannan uqubar da Umaimah ke qoqarin jefa shi kuma daga haduwarsu da Hadiza zuwa yanzu yana ganin zata share masa hawayensa amma ta ina ze fara tunkarar Umaimah da zancen zeyi mata kishiya?
A ture maganar Umaimah ma shi a karan kansa yana ganin beyi mata adalci ba ace shekaru biyu da auransu kacal yayi mata kishiya koda yake halinta ne ya jawo ai.

Wani lokacin yakanyi mata uzurin cewar har yanzu bata gama sanin inda ta dosa a cikin zaman auran ba amma tsoronsa idan be dakatar da ita ya dorata a saitin da yake so ba haka zata miqe kuma a gaba se yafi shan wahalarta sama da yanzu. Sannan yana ganin kamar qarin aure ba shine mafita a matsalar sa da Umaimah ba, yana sonta baya qaunar abinda ze bata mata ko ya janyo matsala a tsakaninsu yanzu kuwa ya tabbatar tashin hankali ne babba yake shirin siya da kudinsa sedai kamar yanda wani abokinsa Sadiq ya taba gaya masa a lokacin yana neman aure yace saboda ya firgita matarsa tashiga hankalinta ta dena yi masa abinda baya so kuma yayi nasara dan tunda yace mata zeyi auran ta nutsu, har zuwa yanzu kusan shekaru biyar kenan be sake jin kansu ba amma da kullum cikin rigima suke kamar dai shida Umaiman sa toh amma shi yanzu idan yayiwa Hadiza haka ai beyi mata Adalci ba dan dagaske take sonsa idan yayi amfani da ita dan gyara zaman auransa ya kuma barta yasan haqqinta baze barshi ba dan haka dole ya zabi daya kodai yayi shahada ya aurota ko kuma ya rabu da ita yaci gaba da zama da qaddarar da Allah ya zaba masa.

Ranar ma wuni yayi a waje, yaje gidan Hajiyarsa ya dade sosai yana taso yayi mata zancen Hadiza amma taraddadin yanda zata karbi maganar ya saka harya tafi be gaya mata ba se maganar siyan gidansun da take ciki yayi mata. Daman ya dade da gaya mata yana so ya siyi gidan gaba daya ya fitarwa da sauran yan uwansa haqqin su ya zama nashi sunyi magana kuma gaba daya sun yarda dan haka yanzu ya taso da maganar saboda kudaden da yake hadawa sun kusa kammala, sunyi maganar da Hajiyan tace yaje ya samu Kawunsu Murtala duk yanda suka yanke shikenan.

Seda ya tashi tafiya harya kai qofa zuciyarsa tace ya gwada Sa'a mana, seya koma ciki Hajiya dake duba wayarta ta kalle shi tace
"Aa Babana ya ka dawo ko da sauran magana ne?".
Shafa kansa yayi ya zauna yana cewa." Wallahi Hajiya wanj abu ne yake damuna nace dai bari na gaya miki"
"Toh Allah yasa lafiya, ni daman tunda jiya da na ganka nasan akwai wani abu dukka fige kamar wanda yayi jinya amma na zata ko aikin ne tunda kace hidimar da kayi a can da yawa" Hajiya ta fada tana gyara zamanta se yayi shiru yana jinjina ta yanda ze fada mata maganar kafin yayi qundumbala yace

"Daman Hajiya wata yarinya na hadu da ita, toh kuma na yaba da hankalinta sosai mun fahimci juna shine da nake tunanin idan na samu yanda nake so kuma in Allah ya nufa zan qara da ita".

Kallonsa Hajiya tayi harya kai qarshe yayi shiru cikin muryar dake nuna babu wasa tace
"Akul dinka Khalil, wato saboda kaga ka fara samun dama shine zaka tattagowa kanka aure ko? Gaba daya shekarar ka nawa da auran fari ma da har ka fara hangen wata nawa ma kake da kake neman dorawa kanka Jidalin mata?
Toh karna sakeji na kashe maganar daga nan babu ita ko zaka qara aure ba yanzu ba kai sedai idan ma yana cikin qaddarar ka ne amma ban lamunce ba, Allah ya baka mata ta kwarai me hankali da nutsuwa tana sonka tana riritaka banga ta inda ta rageka ba ko kuwa jin dadi ne yasa kake neman qari? Toh babu wannan zance haka kawai yarinya na zaman zamanta ba zaka debo mata damuwa ka hanata walwala ba toh ban yarda ba koma wacece ka bata haquri ka gaya mata kana Son Matarka ita kadai ta isheka dan nasan qarshe tallan kanta ta kawo maka dan me mata irin taka dai a shekara biyu baza'a ace ka fara hange hange ba musamman kai da na farin ma da yaya kayi shi".

Kansa na qasa harta diga aya kafin cikin sanyin jiki yace mata 'Toh' kawai ya miqe tareda qarayi mata sallama ya fita. Daman yasan ko auran zeyi a yanzu kam se sun fafata da Hajiya dan ya rasa kalar Rufa idon da Umaimah tayi mata da sama bata ganin laifinta koda yake bata tabayin halin nata a gabanta bane shiyasa har take mata kallonta kirki tana haqilon ba za'ayi mata kishiya ba? amma duk wannan me sauqi ne, idan har maganar auran dagaske tazo yasan yanda zeyi ya lallabata ta yarda kai duk ma wani da ze kawo tasa maganar duk ze iya dasu ita babbar Madam dince abin tsoronsa dan baze taba manta kalmar kisa data ambata zatayi ba akan duk wadda ta shiga rayuwarsa.

Yauma seda yayi Isha ya koma gidan dan daga gidan Hajiya gurin Mansur ya tafi can yakai dare dan har abinci acan yaci kafin ya kamo hanyar gida. Ya zaci ze tarar da ita tana fushin kamar yanda ya barta da safe amma seyaga akasin haka. Yauma tasha kwalliya kamar me tafiya club harda lalle tayi baqi hannu da qafa ga Qananun kalba da akayi mata akanta dan in ya tuna jiya kamar kanta babu kitso. Ta gyara gidan ko ina se qamshi yakeyi tana bawa Mu'ayyad Abincinsa ya shiga.

Fuska a sake ta amsa masa sallama tareda sannu da zuwa, Ya dauki yaron yana mata sannu da gida itama a ransa yana jin dadin chanjin daya gani daga jiya zuwa yau musamman jiyan dukda bata san da dawowarsa ba amma yazo ya tarar da gida ko ina fes haka ita kanta a kintse, toshi indai zata gyara ta ringa abinda yake so ai babu maganar wata tunda daman rashin kulawarta ta sakashi bawa wata dama.

Qarar wayarsa ta maidoshi daga tunanin daya tafi, seda ya saci kallonta yaga tana tattare kayan abincin Mu'ayyad din kafin ya daga da sallama yana cewa
"Ina abu ne idan na gama zan kira" ya shige daki Umaimah da tun daga wayar tasa tayi sak dan sarai ta ga yanda fuskarsa ta canza ta bishi da kallo.
Bata so ta bar zuciyarta ta ayyana mata abinda ba shikenan ba amma yanda Khalil din yake abubuwa sun fara bata tsoro. Jiya kiran da aka masa yana cin abinci yanda ya rikice ya bata mamaki, sannan fitar da yayi ta kirashi taji call waiting tasan Khalil ko wayar aiki ce qarqarinsa qafe goma baya attending mutane bayan nan amma jiya sha daya ta gota sanda ymta kirashi call waiting dukda yace da Mukhtar yayi waya sannan A iya saninta dashi komai dare baya kashe waya se gashi jiya ta danna wayar da niyyar ganin lokaci ta ganta a kashe, tayi masa uzurin ko chaji ne ya qare gaba daya ta mutu kuma daya saka be kunna ba amma taga da safe harya futa tana lura bataji an kirashi ba kuma shima bata ga yayi amfani da wayar ba ga kuma na yanzu, dukma abinda yake boyewa ko yakeyi zata bincika idan kuwa taga abinda ba haka ba tashin hankali ne ze siyowa kansa dan ya santa bawai chanzawa tayi ba.

Khalil kuwa daya shiga daki Text yayiwa Hadiza akan tayi haquri ze kirata da safe yanzu ya rigada ya shiga gida tayi masa reply kan babu komai yana karantawa ya goge duka messages dinta, call log din ya shiga nan ma ya goge kiran da tayi masa har ya aje wayar wata zuciyar raya masa ya goge lambarta gaba daya bayan ya kalleta da kyau ya haddace haka yabi ya goge chat dinsu na WhatsApp ma sannan yaji hankalinsa ya kwanta.

A qasa ya ajiye Mu'ayyad ya kunna masa carton a Tv dakin ya shiga wanka, yana shiga ta tura qofar dakin ta shiga kai tsaye idonta ya sauka akan wayarsa dake ajiye akan gado, seda taje jikin qofar ta kasa kunne taji alamar saukar ruwa kafin ta dawo da sauri ta dauki wayar, call log ta shiga, lambar farko dataga an kirashi ta kwafe a wayarta cikin sauri ta shiga gurin messages tana yi tana kallon qofar bandakin ganin idan ta bata lokaci ze iya fitowa ya tarar da ita yasa ta ajiye masa wayar bayan ta goge shaidar da ze gani na ta bude wayar. Dakinta ta wuce tana shiga ta dannan kiran number data kwafo wayar ta shiga ringing seda ta kusa katsewa aka daga

Muryar Namiji ce daga ji ma ba bahaushe bane. Tambayarsa tayi ina me wayar yace mata shine, bata yarda ba ta sake ce masa Amina take nema yace shi besan wata Amina ba wannan layinsa ne sedai idan tayi missing number. Har zata kashe ta sake tambayarsa dan Allah waye shi toh dan dukda tabbacin daya bata na layinsa ne bata gama yarda ba, a fusace yace mata sunansa Bala kuma shi Electrician ne ya kashe wayarsa seta sauke ajiyar zuciya tanajin hankalinta ya qara kwanciya. Qila cikin jama'ar da suke kwangila ne masu aikin wuta kenan wani ya kirashi.

Palout ta fito jin yana kwala mata kira ya bata Mu'ayyad da yayi pupu ashe babu Diaper a jikinsa ya wanke masa ya sake masa wanka yace tayi masa shirin bacci. Ranar ma dai haka suka sake kwanciya kowa na juyi da murqususu a gado. Khalil ya qudure in har Umaimah bata bashi haquri akan abinda tayi masa ba ze zuba mata ido daga gaisuwa babu abinda ze sake shiga tsakaninsu haka itama ta ja nata layin dan ta san duk abinsa dole ya haqura ya sakko baze iya dogon fushi da ita ba, tana lura da yanda yake kwana wanka da shan Lipton da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login