Showing 120001 words to 123000 words out of 429394 words

Chapter 41 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

941

ita ze cewa yana aiki ta bari ze kirata daga baya? Khalil din data sani Sallah ce kadai zata kirashi yana yi da baze katse ya amsa kiranta ba shine yanzu ze gaya mata yana aiki ne.

Tagumi ta rafka hannu biyu karfa kwabarta tayi ruwa daga neman gira a rasa ido, to waima tsahon wannan lokacin da suka dauka Khalil din be nemeta ba ya ya yake rayuwa, wacece take debe masa kewarta da duk sauran buqatunsa ina yake kaisu? Kai wai ita wace toshewar basira ce ma ta sameta haka data sake shi a bariki shi kadai, sam ta manta da yanda Lagos din nan take. Mata ne suke neman maza ba maza ke neman mata ba ballantana irin Khalil daya hada duk wasu qualities da zasu saka mata su soshi, to yanzu shirun nan da yayi mata idan ya zama na wata ya samu take debe masa kewarta fa?

Zabura tayi ta miqe tana salati saboda wannan tunani daya fado mata dagaske idan ya zamana Khalil wata ya samu fa shiyasa ya manta da ita dan Khalil din data sani baze yi fushin wata daya da ita ba ballanta har ya iya zama a wani gari daban ba tareda ita ba na tsahon wannan lokaci bama ze yuwuba sedai idan kuma wani abin ne ya faru dashi bata sani ba kuma ba'a gaya mata ba.

Hannu ta dora aka tana juyi a dakin, tunani biyu ne suke mata zarya kodai Khalil ya samu wata ko kuma wani mummunan abu ya faru dashi an boye ba'a gaya mata ba. Wayarta ta dauka ta shiga sake kiransa, missed calls ta ringa tara masa ita kanta bata san Adadin kiran datayi ba kafin ya daga cikin fada fada yace
"Wai Umaimah bana gaya miki ina aiki bane ki bari zan kiraki idan na gama"

"Khalil ka amsa mun kawai lafiyarka qalau ko Aa? Idan kuma qalau kake wace yar iskar Karuwar ce ta dauke maka hankali da har ka manta damu tsahon wata daya baka waiwaye mu ba" ta fada cikin tashin hankalin daya rufeta ga mamakinta se ji tayi yaja wani shegen tsaki kafin tace wani abu ya kashe waya seta fasa ihu iya qarfinta tareda yin wulli da wayar ta fadi a qasa, Mama dake tsaye bayanta ba tareda ta sani ba ta watsa mata Marin daya sakata dauke wuta na wani lokaci, nuna ta tayi da yatsa tace
"Ki shiga hankalinki Umaimah, ki shiga hankalinki" kafin ta juya cikin matuqar bacin rai tabar dakin. Ta rasa wacce irin yarinya ce Umaimah, ita dai bazata taba yarda da lafiyar kwakwalwarta qalau ba dan abubuwan da Umaimah takeyi sam basuyi kama dana me cikakken hankali ba.

Uwar dakinta ta wuce Anty na tambayarta meya faru dan gaba daya sunji Ihun Umaimahn bata amsa ba ta wuce ta. Wayarta ta dauka ta shiga kiran layin Khalik, ta gaji da wannan zaman na Umaimah, gara ta sani idan kaso auran tayi ko ma menene dukda Abba yace ta bari ta saka mata ido kawai, koma menene idan ta gaji da boyewa zata fada.

*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 33

KHALIL
Tun kiran farko da Umaimah tayi masa yana tsaye a Site yana duba aiki,ginin wani company sukeyi da sun kammala shi finishing ne ya rage kuma suna buqatar gamashi cikin kwanaki biyu abinda ya fitar dashi da safiyar kenan saboda akwai sauran ayyuka kuma dole seya zaman na yana gurin. Yana tafe a hanya suna waya da Hadiza da yanzu baya iya shanye wasu awanni ba tareda yayi magana da ita ba. A rayuwar sa be taba zaton ze sake son wata mace bayan Umaimah ba se gashi Hadizan tayi masa shigar farat daya, yana jinta a zuciyarsa dukda babu hadi tsakanin soyayyarta data Umaimansa amma ya yarda itama yana sonta, tana da sanyin hali da dabi'u masu kyau da suka taimaka gurin jan zuciyarsa zuwa gareta.

Har ga Allah yanzu mantawa yake yi da ita idan ba ya kunna screen din wayarsa yaga hotonsu da yake kai ba shiyasa koda ta kirashin beji komai a ransa ba, ya qudurce indai dan yana nuna damuwa da ita ne take wahalar dashi to ze yaqi zuciyarsa ko zatayi yaya ze jingineta a gefe na wani lokaci har zuwa tasan mutunchinsa shima koda ace abubuwa zasu daidaita tsakaninsu.

Data sake kiransa yana cikin yin sallar da be samu yayi akan lokaci ba, yana tayarwa ta fara kira bata haqura ba kuwa har seda ya idar sannan ya daga tarin missed calls din daya gani ya sakashi tunanin ko wani abun ne ya faru sedai maganganun data tareshi dasu suka tunzurashi, lokaci daya ransa ya baci musamman kalmar Karuwa data hadashi da ita.
Ya rasa abinda yake damun Umaimah da sam harshenta bashida linzami, bata tauna magana kafin ta fadeta musamman shi datafi rainawa sama da kowa duk abinda yazo mata a zuciya fada masa tayi amma zeyi maganinta.

Kiran Hadiza ne ya shiga wayarsa, cikin girmamawa da mutuntawa ta gaishe shi tareda tambayarsa aiki. Yanda take yi masa ba qaramin dadi yake masa ba dan shi a rayuwarsa mutum ne da yake son a girmama shi kuma babban abinda ya rasa daga Umaimah kenan shiyasa Hadiza ta samu wani matsayi babba a zuciyarsa. A taqaice sukayi magana da ita, daga muryarsa ta fahimci kamar yana cikin damuwa dan haka bata barshi ba seda ta fada masa kalaman da suka rage masa kaifin fushin da ya ke ciki sukayi sallama akan idan ya koma gida ze kirata.

Can bangaren Umaimah kuwa kuka ta dasa kamar wadda akacewa Mama ta mutu, Anty ta leqa tana tambayarta abinda ya faru tunda Mama taqi magana tayi mata banza se qara rusa kuka takeyi haka ta gaji tabarta sedatayi me isarta kafin ta tashi ta shiga hada kaya. Tas ta hada akwatunanta danma Allah yaso jiya anyi mata wankin da seda Mama taci ubanta kafin ta hada kayan su Nazifi suka wanke mata dan a gidan ma babu abinda ta ajiye idan ba chatting da waya da qawaye ba se bacci wanka kansa se da daddare in tazo kwanciya zatayi taimakon My'ayyad daya Anty gurinta yake wuni ita take gyarashi tsaf har kayansa duk suna gurinta da shi kansa Allah kadai yasan qazantar da ze ringa sha.

Sanda ta gama hada kayan tsaf ta zura Hijabinta ta fita,Mama na daki Anty kuma sun kwanta baccin qailula ita da Mu'ayyad Umaimah ta ringa jidar kayanta tana lodawa a Taxi din data kira seda ta gama tsaf ta shiga dakin Anty ta dauke yaron tayi tafiyarta ba tareda kowa ya sani ba.
Gidan Rufaidah ta shiga bayan da me mota ya gama sauke mata kayanta, gidan yayi budu budu bazata iya gyarab sa ita kadai ba dan haka ta shiga roqon Alfarmar qanwarta dake zaune da ita tun bayan data haihu akan tazo ta tayata nan Rufaidan tace mata ta kirawo Hauwan Maman Hauwa su hadu dan sufi sauri haka kuwa akayi yaran suka zage sosai suka gyara mata gidan tas har dakin Khalil suka wanke tsakar gidan ta tattara musu ragoye ragoyen Turaruka da sauran kayan kwalama irinsu chocolate da biscuit suka tafi.

Seda dare yayi ta fara jin tsoro kuma dan bata taba kwana a gidan ita kadai ba, goma harta gota ta goya Mu'ayyad ta shiga gidan Maman Hauwa ta roqeta ko Hauwa zata tayata kwana jiki na rawa Maman hauwan ta tasota dan harta fara bacci suka tafi, a dakinta tace ta kwanta ita kuma suka kwana dakin Khalil da Mu'ayyad. Da safe seda ta sake gyara mata gidan tsaf suka karya tayi wanke wanke kafin ta wuce gidan su ta gaya mata yau ma tazo, Khalil baya nan zata ringa tayata kwana har zuwa sanda ze dawo.

A can gidansu kuwa duk abinda tayi akan idon Mama dake tsaye jikin window tana kallonta ne, girgiza kai tayi a fili tace
"Allah ya shirya ki Umaimah" ta koma ta zauna ranta sam babu dadi. Anty kuwa data farka a bacci ta fito tana tambayar waya dauki yaron, lokacin Mama tana sallah gaba daya yaran dake tsakar gida suka ce basu ganshi ba, Mama data idar ta leqo tace mata uwarsace ta dauke shi sun koma gidan su seta kama baki cikeda mamaki tace
"Se a gaida Umaimah wace irin tafiya ce haka babu shiri ko Khalil din ne ya dawo ai da tayi magana se aje a gyara musu gidan tukunna, ga kayan megidan nawa ma ta barsu a bita dasu daga baya" ita dai Mama batayi magana ba dan ranta a matuqar bace yake da Umaiman kawai bata son furta wani abu ne balle ta fadi mara dadi.
Umaimah kuwa seda ta shafe kwana biyu tana dakon kiran Khalil amma taji shiru, abin ya dameta sosai, tana so ta kirashi amma ta kasa saboda gaba daya zuciyarta qarya take gaya mata akan Ita Khalil yayiwa laifi daya yi tafiyarsa uwa duniya yaqi ya waiwayesu sam ta tak nata laifin na qin bin umarninsa da tayi ga wani bangare dake mata hudubar tabbas Khalil wata ya samu a can shiyasa har ya iya daukar wannan lokacin be waiwayi gida ba, idan kuwa haka ne ta rantse da Allah daga shi har koma wacece sun tarowa kansu abinda bazasu iya dashi ba, tana nan ze dawo ya iske ta ze kuma gane kurensa.

Sabgoginta taci gaba dayi bata aikin fari balle na baqi se chatting da bacci su kadai ta saka a gaba dan yanzu Hauwa keyi mata komai a gidan, da sun tashi zata yi mata shara da duk wani aiki daya kamata tayiwa Mu'ayyad wanka ta bashi abinci ta goyashi su tafi gidansu, a can yake wuni zir idan ta maidashi to sedai idan ya saka rigima sunyi sunyi yaqi shiru shine zata kaishi yasha Nono daya gama ta kuma sabarsa ko su zauna anan gidan kota koma can gidansu dashi ita kuma hamshaqiyar ta samu guri tayi yanda take so ta qudurce bazata sake kiran Khalil ba, Maman Hibban ce ta tallata mata wasu kayan mata datace ta siya a gurin
*Sumayyas herbal aphrodisiacs*? tana jin sunan bata bata lokaci ba lale kudaden data gaya mata ta bata dan ta san mutunchinsu sune ingantattun kayan da Yayar Rumasa'u ta Dutse ta taba bata ta, taji dadinsu kwarai a lokacin ita kanta ta samu lafiya a jikinta ga Khalil seda ya zame mata tamkar raqumi da akala saboda yanda take gigita masa tunani da taimakon kayan *SUMAYYAS HERBAL APHRODISIACS (07031876677)*.

Murmushin mugunta tayi lokacin da Maman Hibban din ta kawo mata saqon, bata bata lokaci ba a ranar ta fara amfani dasu ga hadaddiyar dilkarta da take goge jikinta tas da ita saboda so takeyi duk randa Khalil din ya dawo mata idan suka gamu seya manta sunansa ta rigada tasan lagonsa ta wannan fannin zata kamshi ram babu boka babu malam shiyasa zatayi wasa da komai banda gyaran jikinta ta wannan fanni.

Ranar Juma'a misalin qarfe sha daya tana zaune a palour taci kwalliya da wani Lace fari ta kashe dauri yanda kasan me zuwa wani taron biki, wayarta na hannunta ta jona sabon ringlight din da ta siyo jiya saboda daukar videon Tiktok. Tsabar zaman banza da rashin abinyi da takeyi ya saka ta fara sha'awar Matan dake video suna dorawa a Tiktok din, daman Rufaida ta dade tanayi ta na kuma tayi mata maganar itama ta fara dan ita a yanzu ta kai yawan followers da har Tiktok sun fara biyanta saboda irin badalar da takeyi da sunan comedy marasa tunanin irinta suna kalla sunayi mata like wasu su zageta, bata mutunta kanta matsayinta na musulma mace ba kuma matar aure take banzatar da kanta a Social media.

Waqa ta kunna bayan data gama saita wayar ta ajiye nan ta shiga bin waqar daga zaunen da take tana dan juya jiki wayar na dauka. Waqoqi ta ringa sakawa abinta tana yin videos wasu a zaune wasu a tsaye wani ma jikin mudubi ta tafi ta dauka seda ta gaji ta koma ta zauna bayan ta kashe Ringling din ta shiga duba videos din tana editing. Hankalinta yayi nisa a abinda takeyi sam bataji sanda aka bude Get ba se sallamar sa da taji a tsakiyar kanta.

KHALIL
Ranar Alhamis aka fitar da sunan sabon manajan bangaren da aka dorashi ruqon kwarya dan haka a ranar ya tattara ya damqa masa duk wasu abu na office din da suke hannunsa musamman daya kasance ya kammala duk wata kwangila da aka fara se sababbi wanda suka fara proposing shiyasa be sha wahala ba gurin damqa masa komai a daren kuma ya hada kayansa yayi booking jirgi zuwa kano dan ya gaji da zaman garin matuqa sati kusan bakwai ba wasa ba yayi kewar Kano kullum Hajiya cikin mitar sun tafi sunyi zamansu takeyi dan duk a lissafinta da Umaimah suka tafi, kuma da yake itama yar gaske ce tunda ta fahimci tunanin Hajiyar ko kiran ta tayi a waya suka gaisa bata taba nuna mata basa taren ba.

Tara da yan mintuna ya sauka a Kano, ya taho da wasu takaddu dole ya wuce office kai tsaye danya bayar dasu kafin ya wuce gida tunda ranar aiki ce, be bata lokaci ba yana kai takaddun inda ya dace ya kama hanyar gidan. Sanda ya isa ya rigada yasan babu kowa a gidan shiyasa be kashe motar ba ya fita ya bude Get sedai mamaki ya kamashi jin daddadan qamshin turaren wuta yana tashi a tsakar gidan, ya kalli gurin dakyau yaga ko ina fes da alama ba'a jima da wankewa bama dan gurin be qarasa bushewa ba kuma ba lokacin damuna bane ballantana yace ruwa akayi seya tabe baki ya juya ya koma mota ya shigo da ita ciki.

Jakar computer sa kadai ya dauka dan ya gaji bacci kawai yake so yayi yanzu kafin lokacin sallar juma'a yayi yana so kuma yaje gidansu Hadiza, so yake ya shammaceta dan be sanar da ita dawowarsa ba.

Muqulli ya zura a qofar yaqi shiga seya zare dan alama sun nuna akwai wani ta ciki kenan ya murda handle din ya tura qofar hancinsa na sake shaqar qamshin turaren wutar da Hauwa ta cika gidan dashi. Da mamaki yake kallonta, tana zaune gaba daya hankalinta yana kan wayar da take dannawa fuskarta a washe tayi wani sanyayyan kyau seya ga ta qara masa haske da qiba irinta wanda yake cikin kwanciyar hankali.

Dauke idonsa yayi daga kanta ganin yana neman shagala da kallonta ya ci gaba da takawa cikin palour bakinsa dauke da sallama daidai nan ta dago a dan firgice ta kalle shi, wannan murmushin nata na yaudara ta sakar kafin ta ajiye wayar hannunta ta miqe tsaye ta nufeshi cikin takun jan hankali tana qarasawa kusa dashi kafin yayi wani abu se jinta yayi a jikinsa ta ta zagaye wuyansa da hannu biyu ta sajar masa peck akan lips dinsa kafin tayi far da idonta tace
"Sannu da zuwa honey".

Sakin baki yayi kawai yana kallonta tsabar mamakin abinda tayi, babu ko digon damuwa ko tashin hankalin daya zata zatayi masa idan sun hadu dukda be saka ran ganinta a gidan kuna a yanzu ba ko dab saboda haukan data so ta farayi masa waya ranar nan hakanan babu ko digon damuwa ko nadama akan laifin da tayi masa se zallar rainin hankali da iya bariki take nuna masa lallai Umaimah ta wuce duk inda yake tsammaninta.
Hannu ya saka ya janye ta daga jikinsa saboda yanda turarukan datayi amfani dasu da yanda take goga masa jikinta suke neman yin tasiri akansa ya shige daki ba tayi fushiba ta bishi tana masa sannu da zuwa.

Sake kama rigar da yake qoqarin cirewa tayi seya dago ya kalleta ido cikin ido yace
"No thank you i can help my self" fuska a daure haka muryarsa babu wasa a cikinta, a maimakon yaga tayi fushi sema wani munafukin murmushi ta saki tana cewa
"Toh bari na hada maka ruwan wanka sena sama maka abinda zakaji dukda dawowan naka babu sanarwa aida na hada maka special" ta wuce bandakin tana kada jiki.

Binta yayi da kallo kamar wani soko, yanda take abubuwanta yanda kasan sunyi rabuwar mutunci ya dawo daga office ko wata gajeriyar tafiya, kai shi baya jin ma ya taba samun tarba irin haka a gurinta fuska a sake, gida qalqal ita kanta tsaf se an samu wani abun be cika ba.
Yana tsaye ya gagara ci gaba da cire kayan ta fito daga Toilet din, ido daya ta kashe masa tare da hura masa kiss kafin ta saka kai ta fice daga dakin seda ya saki ajiyar zuciyar dabe san sanda tazo masa ba yaci gaba da cire kayansa a ransa yana jimamin hali irin na Umaimah. Ya fuskanci ta rigada ta san lagonsa akanta shi yasa take masa iskanci yanda ranta ya bata idab kuwa hakane wannan karon shima ze zama namiji baze

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login