Showing 264001 words to 267000 words out of 429394 words

Chapter 89 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

950

kin Shiga ki gaya mata na wuce" ya fada yana kallonta kafin ya juya ya nufi qofa. A sanyaye ta miqr tabi bayansa, maganar bata son Ibrahim bata ma taso ba amma fa Yaya Khalil a matsayin Ibrahim shine abinda ta kasa yarda dashi. Ta yaya ma zata iya zama dashi a matsayin Miji abin da wuya wai gurguwa da auran Nesa.

Binsa ta ringayi a baya har zuwa gurin motarsa. Khalil da besan tana biye dashi ba saboda yanda take tafiyar kamar mara Laka ya juyo ze bude motar ya ganta se ya tsaya yana kallonta.
"Kayi haquri" ta iya fada dakyar idonta yana kawo ruwa
"Haquri kuma name? Ai ni ya kamata na baki haquri bake ba, sannan ki goge wannan hawayen kar mutane su dauka wani abun nayi miki" ya fada ganin Samarin dake zaune a Majalisar Habibu suna kallonsu. Hannu biyu ta saka tana goge hawayen kafin cike da quruciya tace
"Nidai dan Allah idan wasa kuke yimun ku dena, ka gayawa Ibrahim kawai inason sa daman ai cewa yayi sena fada masa sannan ze zo qila ma shiyasa ya turoka kayi mun wayo".

Murmushi yayi yace
"Me yasa ni bakya sona se Ibrahim?"
"Kai ai Yayanane" ta bashi amsa da sauri se ya sakeyin qaramar dariya yace
"Shikenan yanzu dai tunda bakya sona bari na tafi, zan roqi Allah ya bani wadda zata soni tunda nayi baqin jini a gurinki".

Shiru tayi ya bude motar ya zauna kafinya janyo wata Leda me kyau daya ajiye a dayan sit ya miqa mata yana cewa
"Ga Alqawarinki".
Kasa karba tayi ya janyo hannunta ya saka mata ledar kafin ya tada motar. Bata motsa daga gurin ba har yaja motarsa ya tafi bayan ya daga mata hannu, fizgar da akayi mata ce tare da radadin da taji a fuskarta daya tabbatar mata da marinta akayi suka dawo da ita daga tunanin data lula lokacin har Motar Khalil ta bace daga gurin.

"Wato wannan ne dalilin daya saka kikamun qarya akan aiki kikeyi har wannan Wawan yazo yana gayamun? Wani Dan iska ne yazo gurinki har kika rakoshi qofar gida dan ki nunawa yan unguwa ke kin riqa ko kin fara tara Samari?" Noor dake numfarfashi kamar wnada ya hadiyi kunama ya fada. Farar fuskarsa ta rikide tayi ja kanar wanda ya shafa Barkono. Kallonsa take har ya ida maganar cikin bacin rai ta fizge daga riqon da yayi mata, bata iya ce masa komai ba saboda yanda ranta ya shiga tafasa lokaci daya ta juya ta shige gida tana jinsa yana kwala mata kira amma bata ko juya ba. Haka ta wuce Mama dake zaman jira ta dawo ta gaya mata yanda sukayi da Khalil, tunda yazo suka gaisa be tsa qumbiya qumbiya ba ya fayyace mata cewar shine Ibrahim da yake waya da Humaira haka itama bataji kunya ba a gabansa ta ringa jera Hamdala ta kuma jaddada masa goyon bayanta akan hadin nasa da Humairah. Shigarta daki kuwa kaf seda ta kira yaranta ta shaida musu Mansur ne kadai bata samu ba kuma kowa yayi murna da hadin hatta da dangin Maman Humaira seda ta kira qanwar Mahaifiyarta ta gaya mata saboda tsabar zumudi.

Kasaqe tayi tana kallon yanda ta shigo ta cillar da ledar hannunta ta wuce daki, tana shiga ta fada kan gado ta rasa abinyi se kawai ta fashe da kuka. Abinda Noor din ya mata ya bala'in qona mata rai,a gaban yan unguwa ze mareta kamar wani ubanta? Tunda take dashi kullum yanamata abun da bata jin dadi amma bata taba jin haushin sa irin na yauba kuma ta tabbatar da baya darajata dan idan yana ganin darajarta ko kallon banza wani yayi mata se inda qarfinsa ya qare ballantana ace shi da kansa ze daga hannu ya mareta a bainar jama'a. Kuka me ciwo ta ringa rerawa, Mama data biyo bayanta a tsorace ta dagota tana tambayarta lafiya seta fada jikin Maman tana sake rushewa da kuka har seda tayi me isarta kafinta haqura bacci ya kwasheta.

Mama kuwa cike da damuwa ta koma falo ta zauna tana tunanin meya sakata kuka? Shigowar Habibu yana masifa nan ya gaya mata abinda ya faru a wajen baya nan abokansa suka kirashi yazo
"Wallahi Mama Yan sanda zanje na dakko masa, akan me ze Mareta ce masa akayi jaka ce ko bata da gata da ze mareta? Idan bashida hankali ya shawo kwayarsa ta gaya masa qarya to zan hada shi da wadanda zasu ladabtar dashi" Habibun ya fada. Mama dake jimami ta tareshi da cewa
"Aa Habibu abin be kai ga hukuma ba, ka bari ni dakaina zan rufa gyale na shiga gidansu na samu Asaben na gaya mata ta jawa danta kunne, ni tayi masa iyaka ma da Humaira tunda abun ya zama da haka toh kowa yayi takansa babu shi babu ita dan na gaji da wannan sa magana na Nura, kuma Alhamdulillahi ubangiji ya kawo mata Miji se yaje yaji da quruciyarsa daman abinda yasa tuntuni ban rabasu ba ganin bata da wani tsayaye ne".

Dakatawa tayi a bakin qofa saboda jin abinda Maman take fada, yanzu rabata da Noor zasuyi kenan? Hawaye taji suna zubo mata, dukda haushinsa da taji akan abinda yayi mata bataji cewar zata iya rabuwa dashi ba dan tana sonsa, shi ta fara so kuma bata zaton akwai abinda ze rabata dashi. Wayarta dake hannunta ce ta shiga qara, sunan Ibrahim ta gani akai, duk yanda taso taqi daga wayar amma ta kasa, haka ta amsa ta saka a kunne amma ta kasa cewa komai.

KHALIL
Yanayin Humairan ya nuna mass koda ace be gama samun karbuwa ba yo yanada yaqinin hakan dan haka zuciyarsa a washe ya koma gida. Be tarar da Umaimah ba, shi sam ma ya manta da batunta seda ya shiga Hajiya ke tambayasa abinda ya hadasu sannan ya tuna. A taqaice ya cewa Hajiyan
"Kishinta na rashin dalili ne ya tashi kawai dan taji ina waya kuma na shirya zan fita shikenan ta tayar da hankalinta"

"Khalil kenan, nasan Umaimah nada rikici amma batayi haka kawai, dole sedai idan kai ka tsokanota ko kayi wani abu da ze tonota tukunna, kuma ko ba Umaimah ba, ni kaina daka shigo a haka daga yanayin shigarka zuwa fuskarka na zargi cewar akwai wani abu a qasa, duk kuma inda ka fito daga gurin Mace kake" Hajiyan ta fada tana karantarsa.

Murmushi yayi yana cire hular kansa ya kalli Hajiyar yace
"Kin canka daidai daga gurin sabuwar autarki nake. Ita kuma waya taji munayi da yarinyar shikenan ta tada hankalinta". Baki Hajiya ta saka tana kallonsa jin yanda kai tsaye yake sanar mata gurin Macen yaje, lallai ta tabbata koma wacece wannan dagaske take dan Khalil nada kunya kai tsaye baya iya sanar da ita irin wadannan maganganun sedai taji a bakin Yayyensa amma yau kai tsaye ya kalli idonta yake gaya mata gurin autarta yaje, wato auta ma ya sake yo mata.
Gyara zama tayi tana kallonsa tace
"Nikam Khalil meye ribarka idan ka dagawa matarka hankali ne? Sanin kanka ne idan ta tashi ba kai kadai ba duk Wanda ya shafe ta seta raba bacin ranka dashi me yasa bazaka haqura da duk wannan kule kulen Matan ba ku zauna lafiya tunda nidai banga ta inda ta rageka ba iyakar kyautatawa da kulawa koni Mahaifiyarka babu ta inda ta rageni ballantana kai da kake zaune da ita to me kuma kake nema da bazaka iya haquri da ita kadai ba? To idan har da gaske kake maganar auran nidai bada yawuna ba, bana son abinda ze kawo mana wani tashin hankali cikin gida muna zaune lafiya "

A hankali ya zame daga kan kujerar da yake zaune ya durqusa kan guiwarsa a gaban Hajiyar yace
"Hajiya, kiyi haquri da abinda zan fada kinga a lokacin da na hadu da Umaimah har na fara sonta baki sani ba. Na sani Soyayyar da kike munce ta shafeta da kuma kyautatawar da take miki yasa kike zaton kowa ma haka takeyi masa har ya zamana tasa kika fi sonta da kiyaye bacin ranta ma a yanzu sama dani da kika haifa. To muje a hakan Hajiya a gurinki Umaimah mutuniyar kirkice saboda ban taba kawo miki aibunta ba to mu cigaba da tafiya akan haka, amma ina roqon kiyimun adalci a wannan gabar ki ajiye tasirin Umaimah a zuciyarki ki kalleni a matsayin dan da kika haifa nazo miki da buqata ina so zan qara aure, badan Umaimah ta gaza ba sedan ina son wadda nake so na auro kamar yanda itama nake sonta. Dan Allah karkice Aa Hajiya, kar kuma ki kafamun wani sharadi kiyimun izini ko a gobe naso na daura aure karki hanani a duk sanda buwatar hakan ta taso mu ".
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 61

Sosai jikin Hajiyar yayi sanyi dan ya gama daureta da jijiyoyin jikinta, ya roqeta da karta hanashi kar kuma ta gindaya masa sharadi, daga yanayin muryarsa da yanda yake magana ita ta haifi abinta ta karanci wani daci a ciki ta tabbatar akwai abinda yake damunsa Wanda yake hadiyewa shikadai baya amayar mata. Kuma tabbas yayi gaskiya, dukda cewar tun a sanda ta fara ganin Umaimah haka nan yarinyar ta shiga ranta kuna ta qudurce zata nema masa auranta a sannan ma bata san da wata alaqa a tsakaninsu ba amma Soyayar da takeyi mata ta qara tasirabtuwa ne akan Son da takeyiwa Khalil din. Shidin na daban ne a cikin Yaranta ta fi sonsa saboda yafi kyautata mata. Sannan kamar yanda ya fada a kullum yana sake nanata mata Alkhairan Umaiman a gareshi kuma itama tana gani. Daidai da rana daya be taba zuwa ya kawo mata qararta ba idanka dauke abubuwan da suka faru wanda suma da idonta ta gani ba wai shi ya sanar mata ba kuma har kawo yanzu duk abinda ya faru ya wuce shikenan be taba dawo da maganar akan su sake tattaunata ba shi yasa take jin cewar Dan nata bashida wata matsala ita ma kuma take qoqarin ganin ba'a tauye yarinyar ba ta kowanne bangare kamar yanda itama bata tauye kowa ba.

Ba yanda ta iya dan ya kashe mata bakin Magana ko qorafi a sanyaye tace
"Shikenan Babana, Ina roqon ubangiji idan ya tashi baka ikon qarin ya hadaka da mace ta gari wadda zaku hada kanku ba tazo ta wargaza maka gida ba. Sannan ka kula dan Allah, bana so ka zama cikin irin mazan da suke wukaqanta matansu idan suna shirin kawo wata. Ka kula da matarka ka rarrasheta ka kuma nuna mata badan baka sonta ko ka gaza zaka kawo wata ba, Allah yayi muku Albarka yayi muku zabi na gari"

"Amin Hajiya naji dadin maganar da kikayi kuma in sha Allah bazakiyi dana sani da zabin da nayi ba dan seda na duba yarinyar data dace dani tukunna saboda ba zanyi aurene haka kawai saboda ganin dama ba Aa ina da dalili kuma dole seda na nutsu na samo wadda zata cike mun gurbin da nake da gibi kafin na saka maganar a zuciyata"

"Ikon Allah Babana wannan wace me sa'ar ce take neman ture gwamnatin Umaimah har kaniya aje kunyar nan take a gefe kake nuna mun muhimmancinta a gurinka" Hajiya data riqe haba saboda Mamakin Khalil ta fada. Seya shafa kansa alamar yaji kunya yace
"Wallahi Hajiya wata yar yarinya ce, takwarar kice inaga ma Habiba ta girmeta"

"Tofa, a ina ka samota kuma" ta sake tambayarsa, se ya miqe yana komawa kan kujera yace
"A gidansu Mansur take yarinyar Qanin Mama ce"
"Toh naji kardai wannan yarinyar Fara doguwa ko? sunzo lokacin tarewae mu tare da Hauwan. Ai kuwa tana da nutsuwa ga Hankali. Ni a sannan ma Khalifa nayiwa sha'awarta Allah nema be nufa nayi maganar ba saboda naga yarinya ce qarama sosai zasuyi daidai dashi to ashe yaya babba yayi masa shigar sauri, Allah ya tabbatar da Alkhairi amma batayi maka qanqantaba kuwa Babana?"

Sauke kansa qasa yayi yana murmushi yace
"Shekararta Sha bakwai fa Hajiya, in zan tuna su Jalila sanda aka musu aure ai duk basu wuce haka ba muna gama secondary kika ce aure za'a musu kowa taci gaba a dakinta to itama hakan ne bana ta qare makaranta zata ci gaba a nan idan tazo".

"Toh Allah ya tabbatar mana da Alkairi yasa zamuga lokaci, amma ka zauna da Matarka ka sanarwa mata ta lumana dan Allah bana son wannan tashin hankalin kodan Halin da take ciki" Hajiya ta fada ganin Khalil na nemanya baro mata aiki. Miqewa yayi ya dauki hularsa yayi mata sallama ya fita ransa fes, ita ce zata iya kawo masa cikar a cikin tafiyar tunda kuma ya gyarota duk wani wanda ze zo da matsalarsa me sauqi ce.

Dakinsa ya koma seda ya cire shaddar jikinsa kafin ya shiga kiran Humairan dukda bashida tabbacin zata dauka. Yana jin alamar ta daga yayi murmushi, kusan minti biyu yaji batace komai ba amma yanajin fitar numfashinta kamar irin na wanda take a tsorace ko wani abu
"Yammatana babu ko kira kiji ya naje gida ko?" Ya fada yana zama a bakin gado. Shiru tayi bata ce komai ba, ya ringa janta ta da magana har seda ta fara amsa masa da Eh ko Aa, wato tunda ya kallafawa kansa soyayya da ita ya koyi yanda ake tafida masu qananun shekaru kamarta shiyasa be sha wahala ba gurin shawo kanta harta bude baki suka shiga hira kamar babu abinda ya faru, cikin dabara yake sake jaddada kansa a gurinta tareda yi mata alqawarurruka na yanda ze kula da ita ya riritata idan har ta bashi dama ta zama tasa.

"Amma Yah Khalil Anty Umaimah fa? Na tabaji Anty Nusaiba tana fadar kishine da ita sosai, ni daman tun Asali ina tsoron Kishiya...."
"Aisha" ya kira sunanta da dole tasa tayi shiru da maganar da takeyi, jin tayi shirun ya sakashi ci gaba da cewa
"Ki fadamun tsakani da Allah kina so na kuma zaki aureni?"

Shiru tayi saboda yanda tambayar tayi mata girma, dukda har zuciyarta amsar tambayarsa 'Eh' ce amma bata jin harshenta ze iya furtawa saboda kunya
"Kinyi shiru ki bani amsa" ya sake katse mata tunani, kamar tana gabansa ta shiga mutsu mutsu tana so tayi maganar amma ta kasa se ji tayi yace
"Idan ba zaki fadamun a waya ba zan dawo yanzu se ki fada mun face to face"

"Aa karka dawo, ni wlh kunyarka nakeji" ta fada kamar zatayi kuka. Se ya saki murmushi ya ce
"Toh ina jinki ki gaya mun, kina sona? Kuma zaki aureni?"
Seda taja numfashi ta ajiye, ta kasa hana kanta cikin sanyi kamar me rada tace
"Ina son Ibrahim, kuma zan aure shi".

Kamar wanda ta kwararawa ruwan qanqara haka yaji wani sanyi ya ratsashi, qasa yayi shima da muryarsa sosai yace
"Dagaske kike? Kin yarda na turo neman auranki ko wanne lokaci?"

"Eh, amma ba yanzu ba ai sena gama makaranta na qara girma nan da shekara hudu" ta bashi amsa cike da sakalci se ya saki dariyar da be shirya ba yace
"An gama yarinya tunda har kika fada da bakinki kin Yarda ai kin gama mun komai insha Allahu kuma ba zakiyi dana sanin zabata a matsayin abokin rayuwarki ba" daga haka sukayi sallama ya kashe wayar. Cike da doki da murna ya fita daga gidan, seda yayi sallar Magriba kafin ya sake kiran Mansur yana dagawa kuwa ya shiga yi masa masifa akan ya dameshi.
"Kai qyaleni Mama tana kira idan mun gama waya zan kira ka?" Mansur din ya fada jin Kiran Mama na shiga wayarsa.

MANSUR
A rude yake cewa
"Mama Khalil? Khalil dai Abokina kike nufi ko wani daban?"
"Khalil nawa kake dasu Mansur da zaka wani kidime se kace wanda aka gayawq Sharri. Zancen aure fa nayi maka abin Alkhairi Amininka nason yar uwarka ai abin ka runtuma da gudu ka shiga Harami kayi sujuddushshukur ne amma ka tsaya kana wata barbarar baki. To shidin dai Ibrahim na gidan Alhaji Bayero, daman na gaya maka zaryar daya tsira a gidan nan duk zatona ma Qaninsa yakewa kamu ashe shi ta kansa yakeyi to yau dai yazo har gidan nan ya gaya mun da bakinsa yana sonta kuma sun dade suna soyayyarsu itama na tambayeta tace mun tana sonsa to me yayi saura kuma in ba muji daga gareshi yaushe yake son Auran ba kawai ayi a gama kowa ya huta. Daman na gaji da wannan yaron dake mana zarya, yau fa har Marinta yayi a qofar gida saboda ya ganta da Khalil din idan aka daura mata auranta ta tafi ba shikenan kowa ya huta ba yaje canya qarata da Rashin hankalinsa da zafin rai" Maman ta tare Mansur,

"Gaskiya Mama in dai Amincewata ake da buqata toh ban yarda ba. Mama Khalil fa? I mean ba shine me matsalar ba Mama kinsan Mahaukaciyar da yake zaune da ita a matsayin Mata kuwa kinsan wacece Umaimah da ita kike so a hada Humairah kishi?
Toh wlh ko Unaizatu bata isa tayi zaman kishi da Umaimah ba balle Humairah da a haihuwar Qauye ta kusa haifarta sedai idan kun shirya saka yarinya a masifa da bala'i to wannan kuwa idan ba haka ba tun wuri ki gaya mata ta kama kanta babu ita babu shi yaje can ya nemi mata amma ba'a gidan mu ba".

"Toh naji abinda kace amma ni sam banga wata hujja da za'a ce za'a hana Khalil auran wannan yarinyar ba. Kai da kanka kace mutumin kirki ne tun yarinta har girma tare kuke halinsa babu Wanda baka sani ba sedai ka gayawa wani to me kuma ake da buqata bayan haka tunda an samu kyakykyawar shaida akan Ma'auri ina ruwanmu da wata matarsa ita zata aureta ko akanta zata zauna?" Mama ta fada cikin Halin ko in kula. Mansur ya dafe kansa, yasan Mama da bala'in kafiya akan abinda tayi niyya sannan ba tun yau ba tun kafin qannensa su gama aure take nuna sha'awar Khalil dinya nemi wata daga ciki tasha yi masa magana akan shi ya samu Khalil din da maganar ya bashi daya daga cikinsu amma yaqi, yakance mata
"Ai Mama duk ya sansu idanda akwai wadda takr burgeshi a ciki da kansa ze magantu base na kai masa tallansu ba"

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login