Showing 147001 words to 150000 words out of 429394 words

Chapter 50 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1039

mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 39

Ya samu Khausar a inda tace su hadu, ya rigata isa dan haka ya samu Table ya zauna sannan yayi order abin sha gaba daya hankalinsa a rabe yake yana ta raba ido da dube duben ko wani na daukarsa a hoto irin na wancan ranar. Seda yayi kusan minti Talatin kafin ta iso taci uwar kwalliya kamar me zuwa biki se yauqi da karairaya takeyi tana zuwa kusa dashi ta tafi kamar zata rungume shi ya kauce yana yaqen dole qasan ransa kuwa ji yakeyi kamar ya shaqeta a gurin kowa ya huta.

"Sannu kaga har fuskarka ta fada kuwa daman baka da lafiya ne?" Ta fada bayan data zauna. Murmushin dole yayi yace
"Nafi sati banajin dadi daman, jiya da yau nema na dan samu sauqi" ya yanko qaryar dan karta dauka barazanarta ce ta firgitashi harya rame dare daya seta katse shi da cewa

"Ayya sannu Allah ya qara afuwa, kace kana so muyi magana gani nazo amma karka batamun lokaci dan daga gurin aiki nake na dauki excuse".

"Bari a kawo miki abinci" ya fada yana yafito masu karban Order Abinci dayazo wucewa ta kusa dasu, Yar takadda ya bata, ta zabi abinda take so ya tafi kawo mata se Ya kalleta yanaMarairaicewa kamar wani qaramin yaro yana kallonta cikin ido yace
"Na kasa gane kan saqunan da kika aiko mun dasu jiya ne, yanzu tsakanina dake idan kina da buqatar wani abu har se kinyi mun barazana bazaki iya zuwa kaitsaye ki gaya mun buqatarki ba?" Ya fada yana qara tsareta da idonsa, dadi yaji ganin tayi qasa da nata idon alamar kallon nasa yana tasiri a kanta, daman ya sani ko Umaimah data fita jidali bata iya hada ido dashi idan tsiyatakunta suka motsa sedai ta kalli wani gurin tayi masa badai ido cikin ido ba.

Shirun da Khausar tayi ya bashi damar ci gaba da magana yace
"Kuma abin naki harda Sharri Khausar kinje kin hada wasu hotuna kamar wasan yara, waya gaya miki Hadiza har takai ajin da zan iya hada jiki da ita? Ni daman qaddara ce ma tasaka na fara kulata, kuma daga baya dana fuskanci ba Aji na bace na rabu da ita, ko ranar qarshe da kika saka aka dauke mu wannan Video ita ta damu se mun hadu saboda na dena daga wayarta ta dameni shine naje na sameta, ai kin sani tunda kuna tare a lokacin kuma na jaddada mata babu ni babu ita ta nemi wani shine har ta nemi ta tayar mun da Aljanu dalilin daya saka na kamata na sakata a mota kenan har aka dauki wannan video kuma tun ranar bamu sake magana da ita ba se jiya".

Dadi Khausar taji na maganganun daya fada, dukda tayi zargin basa tareda Hadizan a yanzu amma bata tabbatar ba saboda ta dena gaya mata tsakaninta da Khalil din bata san me ya saka ba shiyasa ta yanke shawarar rabasu ta wannan hanyar Ashema basa tare data sani ai kawai zura kanta zatayi base ta tsaya wani yi masa barazana ba ga asarar kudi da tayi dan hada mata wadannan hotunan da akayi kusan dubu dari biyar ta biya banda kashedin da suka mata akan idan ta kwabe karta kuskura ta sako su a ciki in ba haka ba se sun hada mata Wanda ya fishi muni sun baza a duniya. Duk fadar tana da wasu da suka fi wannan ko kuma ta ajiye wani copy barazana kawai tayiwa Khalil din da Hadiza ta kuma samu yanda take so dan Hadizan ta tsorata dagaske ko a jiya seda ta tura mata dubu dari biyu data sake tura mata saqo

"Ni fa daman tun Asali ke na fara so banma san ya akayi na koma kanta ba abin kamar tayi mun Asiri kuma daya karye na rabu da ita kawai naji tsoron idan na dawo miki bazaki karbeni ba saboda Aminiyarki ce shi yasa na haqura daku gaba daya" Khalil ya sake sakin wani dialogue din ganin ta sakawa guri daya ido tana faman doka murmushi ai kuwa tayi saurin kallonsa ya kashe mata ido daya ya sake cewa

"Eh mana kema ai kina sona ko tunda gashi kin kasa haqura kina so ki kwatoni daga gurin Hadiza ta qarfin tuwo" yayi maganar cikin sigar tsokana yana kallonta ya rausayar dakai irin taji kunyar nan har sannan batayi magana ba sedai murmushi dan haka ya sake cewa

"Kinyi shiru baki ce komai ba ko baki son nawa ne? Kinyi shiru kiyi magana" ya sake fada yana leqa fuskarta data sunkuyar qasa, seta dago tana hade fuskarta daga murmushin da takeyi tace

"Ina sonka mana kaima ka sani kuma ni daman saboda na sameka ya saka nayi abinda nayi. Amma dukda haka bazan yarda da dadin bakin ka ba dan jiyan nan na gama jin kana gaya mata zaka kaini gurin DSS waya sani ko yanzun ma kayi report?
To dai koma yayane na gaya maka kuma zan maimaita idan ka saka an kamani kamar ka qarawa wuta fetur ne dan na raba copys na hotunan nan dama wasu da baku san dasu ga ga Qawayena da abokanaina. Ko yanzu da zan taho seda na gaya musu inda zanje kuma dakai zan hadu idan wani abu ya sameni karsu jira komai su sake su a Internet".

'Dum' qirjinsa ya buga a zuciyarsa yace
"An yanka ta tashi" amma afili qoqari yayi ya daidaita nutsuwarsa yace

"Haba dai kina wata magana kuma ko jiyan da kikaji na fada mata haka nayi ne dan na kwantar mata da hankali bawai dagaske nakeyi ba dan haka ki kwantar da hankalinki infact ni koda ace kin fitar da hotunan da kike fada babu abinda ze shafeni saboda ni namiji ne kin sani me hausawa suke cewa ai duk abinda mukayi Ado ne kawai dai ita nake jin tausayi a matsayinta na Mace"

"Oh haka ma kace baka tsoron Abokanan huldarka su gani ko yan uwanka? Bama wannan ba matarka da take da bala'in kishi idan ta gani me kake tunanin ze faru?" Khausar ta fada fuskarta ta kasa boye mamakin jin yace wai babu abinda ze dame shi ita duk kanta ya kulle ma. Jiya fa ya rikice a waya amma yanzu ya ringa nuna abin be dame shi ba kuma har kan fuskarsa bata ga alamar qarya a abinda yake fada ba, maganar sace ta katse mata tunani yace

"A ina kika san Matata da har kika san tana da Kishi?"
Seta harareshi qasa qasa kafin ta danna wayarta ta nemo number Umaimah data kwafa ranar daya nuna musu hotunanta a waya ta juya masa wayar tana cewa
"Ko ba wannan ce Number taba? Na tabbata idan taga hotunan nan seka gwammace kida da karatu dan kaida kwanciyar hankali har abada".

Dariyar da shikansa ya rasa ta mecece yayi kafin cikin tsananin dauriya daga rudun ganin number Umaimah a wayarta yace
"Toh ko zaki gwada aika mata yanzu ko gani? Kinga naga alamar bazamu daidaita ni abinda nake miki magana akai daban ke kuma kina wani shirme daban, kina zaton zakiyi blackmailing dina ne kiringa mun barazana da wata Matata ko wani abu to bari kiji ki koma ki sake shiri dan wannan bazeyi aiki ba, maganar soyayyar ma kuma na fasa tunda naga ba ita bace a gabanki na barki kije kici gaba da shirmen da kike ganin dabara ce a gurinki" ya fada yana miqewa tsaye zuciyarsa na wani tsalle akan fargabar abinda ze biyo bayan hargagin nasa amma ga mamakinsa se yaga itama ta miqe tsaye tana kallonsa tace

"Ta yaya zan yarda gaskiya kake fada mun ba yaudarata kakeyi ba?"
Ajiyar zuciya ya sauke a boye kafin shima ya kalleta yace
"Kibi abinda zuciyarki tafi yarda akai".

Seta koma ta zauna ganin haka shima yaja kujerarsa ya zauna yana Addu'a a zuciyarsa, shiru sukayi na wani lokaci kafin ta bude baki tace
"Ni ba soyayya ko bata lokaci nake so muyi ba Sonka nakeyi da aure dan haka idan ka shirya belin kanka a shirye nake ko a gobe ka tura a nema maka aurena ni kuma nayi maka Alqawarin zan goge duk wani hoto da video na gurina da gurin wadanda na bawa Ajiya"

"Well, ni idan zan aureki zan aureki ne a ra'ayin qashin kaina badan wata barazanarki ba, sannan idan dan wannan nema ai kin rigada kin lalata abin tunda har kin turawa wasu a matsayin Ajiya ko? Ta yaya zan yarda suma basu nunawa wasu ba kinga kenan idan ina gudun fitarsu ne magana ta qare kin rigada kin fitar dasu tunda bake kadai kika mallake su ba" Khalil ya fada yana tsareta da ido, shikansa yayi mamakin yanda ya iya dakewa yake magana ba tareda ta gano shi ba.

Duburburcewa tayi cikin in ina tace
"Toh ai toh nasan wadanda na bawan zasu boye ba zasu nunawa kowa ba, kuma ma ni da kaina na boye su kansu basu san menene a ciki ba"

"Amma dazu fa kikace kin gaya musu zaki hadu dani idan wani abu ya sameki nine kinga kenan sun san abinda yake faruwa ko?" Ya sake jefa mata wata tambayar yana kallonta kamar wani Jami'in tsaro seta hade rai ta miqe tana cewa

"Saboda kaga na tsaya muna magana shine har kake nema ka titsiyeni ka raina mun hankali ko? Toh shikenan kaje zakaga abinda ze biyo baya, zakazo kana dana sani da bashida amfani tunda har ka kasa amfani da damar dana baka. Kuma wallahi kaci sa'a ina sonka ne amma a yanda na quduri daidaita rayuwar Hadiza dan saboda kaine na rangwanta mata abin ya tsaya iya haka amma tunda bakaga abinda nayi maka ba, zaka gwammaci kida da karatu" ta dauki jakarta da wayarta dake ajiye zata juya shima ya miqe yana cewa

"Na gaya miki ni bana tsoron ki yada koma menene amma ki sani kin dabawa kanki wuqa kuma ita ramuwar gayya akace tafi ta gayya zafi. Idan kin sabayiwa mutane haka kina cin banza ki tabbatar wannan karon kin tabo tsuliyar Dodo dan Khausar idan bakiyi wasa ba seba batar dake" yana gama gaya mata haka ya juya ya wuceta fuuu kamar iska ya barta tsaye tana binsa da kallo daidai sannan.

Khausar
Sosai tsoron yanayin da Khalil din yayi magana ya kamata daman kuma ta fuskanci kamar ya gano duk wani shirinta amma yanzu yaya zatayi? Batar da ita fa yace zeyi ta tabbatar da kuma ze iya tunda komai kudi ne yake aiki a yanzu.
Komawa tayi ta zauna ta dauki wayarta dake ajiye ta shiga kiran qawarta Shema wadda da ita suka qulla duk wani shiri ita ce ma ta hada ta da wanda yayi mata hotunan da Video

"Ke kamarfa gayen nan ya gama gane shiri na gaba daya fa ya nuna baya jin tsoron ma na saki hotunan ba kamar jiya da nake gaya miki ba" Khausar ta fada bayan da Shema ta daga wayar, tsaki Sheman tayi tace
"Kefa banzace daman ai dole ze nuna miki be damu ba saboda ki karaya ki fasa abinda zakiyi Allah sa dai bake ce ma kikaje kikayi abinda ya gano ki ba"

"Ko daya wallahi nuna mun yayi shi be damu ba ko jiyan ma saboda Hadiza ne kuma ma ashe basa tare yanzu harfa yana maganar daman yana sona kuma ze aureni to fa daga na tambayeshi ya zaayi na gane ba yaudarata yake so yayi ba shine kuma yayi fushi har yana cewa Ze iya batar dani" Khausar ta sake fada se Shema ta buga tsaki me qarfi tace

"Ai daman ke banza ce wai wa ma yace ki hadu dashi daga fara abu jiya har zaki bari ku hadu yau dole ma ya gane bada gaske kike ba, yanzu ya turo miki da kudin da kika nema jiya ne? Seda nace miki idan be turo ba kaitsaye ki aikawa da Matarsa shine ze tabbatar bada wasa kike na amma jiki na rawa daga yace kizo kuyi magana kinje seki shirya tarar abinda ze biyo baya tunda daman idan baka iya kama barawo ba ai shi se ya kamaka"

"Toh yanzu ya zanyi Shema, ni fa batarwar nan daya ce ta daga mun hankali ke kika bani labarin qawarki da haka ta fau da ita fa" Khausar ta sake fada kamar zatayi kuka daga can bangaren Shema tace

"Minal ba shekara biyu????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
kenan babu labarinta se tashin zancen, iyayenta ma da suka gaji da nema Addu'a kawai aka mata sun saddaqar ta mutu amma ita ai babban mutum tayiwa, daman a lokacin seda muka hanata wata qawarta tace mata babu komai itama ta tabayi ta samu kudi sasai dan daman su badan a aure su bane kawai Kudi suke karba a gurin mutanen, aiko randa ta tura masa da Video washe gari ta fita aka dauketa a hanya shikenan qila se a lahira".

Cikin Khausar ne ya bada qarara quuu jin wai a hanya aka dauketa tace
"Karfa nima yanzu kiji babu ni ko kuma yasa a tareni a kwace mun waya kin san komai yana ciki kawai bari in jira kizo mu tafi tare ne kinji dan Allah"

"Ai seda nace ki tura a wayata saboda tsaro ke ga me wayo kika ce Aa, Ai se ki zauna barazana yayi miki kuma kin rufta Allah yasa ma ba labewa yayi yaga yanda zakiyi ba kinga kuwa idan haka ne kina ruwa wallahi ya gano lagonki, ina yaga kudinda ze biya a batar dake banda ma ke sauna ce da har zaki wani tashi hankalinki? Dallah ki kamo hanya ki taho musan yanda zamu gyara shirmen da kikayi" tana gama fada ta kashe wayar.

Waigawa Khausar tayi iya hangenta bata ga Khalil ba babu kuma ma wanda hankalinsa yake kanta, Muryar wanda ya kawo musu abinci taji daga sama yana cewa
"Hajiya kin gama ne zamu gyara gurin wasu zasu zauna" bata iya magana ba ta daga masa kai kawai, ka garindaukar kwanukan ya ture mata wayarta data ajiye kan Table din cikin sauri ya dauko ya miqa mata yana bata haquri ta harareshi kafin ta karba ta jefa a jaka, jiki babu kwari ta fice daga gurin, Adaidaita ta tare ta hau, bata samu nutsuwar baza'a tareta a sace ta ko a kwace mata waya ba seda ta ganta a Office dinsu. Tana zuwa ta tararda Mata biyu da suka zo shigar da qara, Ogarsu tace taji dasu dan haka suka shiga ciki ta ajiye jakarta ta dauko wayar da suke recording ta kuna ta fara tambayar matar.

Mijinta ne yake dukanta shine data gaji yau da yazo dukan nata ta kwada masa Tabarya ta gudo, dayar da sukazo tare qawarta ce kuma daman ita ta bata shawarar ta nemi madoki a kusa dik randa ya sake yunqurin dukanta ta rama toh kuma an samu kuskure tana rafka masa tada ya fadi a gun bata da tabbacin yana da rai ko ya mutu shine ta gudu qawar tace suje Human right ta shigar da qarar yanda koma menene ya faru abin ze zo da sauqi.

Seda ta gama nadar komai taje ta kaiwa Ogar tayi mata bayani se tace ta tura mata Matan. Kujerar Hadiza da? babu kowa a kai ta kalla tayi murmushi a fili tace
"Tukunnama, se kin rasa komai da kike taqama dashi a duniya ai duk wanda yaci tuwo dani miya yasha".
Tunawa da barnar da tayi kuma ya sakata miqewa da sauri ta suri jakarta da sauran tarkacenta ta fice ba tareda tayiwa kowa sallama ba kaitsaye gidan su Shema ta wuce dan tana so su tattauna.

Khalil
Seda ya tabbatar da Khausar tabar gurin dan akan idonsa ta hau Napep kafin ya fito daga gurin daya boye ya koma ciki, kiran Hafiz ne ya shigo masa ya daga daga can bangaren Hafiz yace
"Yaya, an dace kuwa?"
"Yanzu nake komawa bata dade da barin gurin ba" Khalil ya bashi Amsa.

Gurin yaron daya kai musu Abinci ya qarasa yana zuwa ya dauko masa waya ya miqa masa ya karba yana murmushi tareda yi masa godiya. Kudin da shi kansa be san nawa bane ya zaro daga Aljihunsa ya bashi kafin ya juya ya hau motarsa ya bar gurin a zuciyarsa yana fatan Allah yasa qarshen matsalar kenan. Jin kansa yakeyi kamar an dora masa dutse saboda Nauyi da ciwon da yakeyi masa, haka kawai yarinya na neman ta dora Masa Hawan jini babu gaira babu dalili.

Daga gurin kai tsaye office dinsu Hafiz ya koma,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login