Showing 285001 words to 288000 words out of 429394 words

Chapter 96 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1019

karba tunda Habiba basa nan sun fita da yaran wai zata kaisu Shoprite"

"Ba komai ai na motsa qafata nima" Umaimah ta fada tana dan murmushi. Hira suka shigayi jefi jefi, Hajiya naso ta kawo mata zancen auran Khalil tana tsoron abinda hakan ze iya janyowa dan haka ta kama tsufanta tayi shiru ita kuwa Umaimah jira kawai takeyi Hajiya taci naman ta kama gabanta dan ba dadin hirar takeji ba, a zuciyarta ko banda antaya mata zagi babu abinda takeyi. Me aikin Hajiya ce ta fito da Fulasan abinci data gama Hajiya tace
"Kinga zubomun farar shinkafar naci da Romon nan, kaima Khalifa idan zakaci gashi nan"
"Aa nikam Alhamdulillah" Khalifan da be saka musu baki ba tun dazu ya fada, Umaimah ta galla masa harara a fakaice ita dai Hajiya aka kawo mata shinkafarta ta zuba abunta ta fara ci tana cewa
"Ka huta ai, na ajiyewa su Auta sauran idan sun dawo suci".

Baya bar gurin Hajiya ha seda Jalilah ta shiga da sallama Sammani na biye da ita da uwayen ledoji niqi niqi kamar wadda ta siyo kasuwa gaba daya. Tana shigowa Umaimah ta miqe, kallon banza suka jefi junansu dashi ta wuce fuuu Jalilah taja tsaki tana qarasawa cikin falon Hajiya ta kalleta tace
"Meye haka Jalilah ya zaki shigo ki harari yarinya har ki bita da tsaki? Wani ni se yaushe zaki dena wannan halin da kika samu duk kinbi kin kwarzabeta na tabbata yanzu ma shigowarki ta sakata fita ba wani abu ba".

Ita dai bata ce komai ba ta samu guri ta zauna tana zare dankwalin kanta ta gaida Hajiyar ta amsa mata a cukule. Me aiki tacewa ta kawo mata abinci taja Flask din gaban Hajiya tana cewa
"Naman kai kuka samu haka duk ya cika falon da qamshi" ta fada tana kaiwa bakinta, Khalifa ya dago yace
"Mutuniyarki ce ta kawowa Hajiya"
"Wa?" Ta tambaya tana tauna na bakinta se ya ce
"Anty Umaimah mana" ai be qarasa fadar sunan ba Jalilah ta tofo naman daga bakinta kafin ta miqe da gudu ta shige kitchen. Gaban sink ta tsaya ta ringa kakarin amai seda ta janyoshi ta amayar da duk abinda yake cikinta kafin hankalinta ya kwanta ta dawo falon tana mayar da numfashi.

Cikin fada Hajiya ta kalleta tace
"Wane irin iskanci ne haka Jalilah zaki dawowa da mutane abincin baki kina kakari se kace wadda taci mushe a rashin sani?"
"Toh ai wallahi Hajiya gara ace Mushen naci ban sani ba Allah baze kamani da laifi ba akan naci abinda ya fito daga hannunta. Yanzu Hajiya ana wannan gabar zata dafo nama ta kawo miki kici hankali kwance babu abinda ya dameki?"

Harararta Hajiya tayi tace
"To se akayi yaya idanta bani nama naci zata bani abin cutarwa ne ko yaya?"
"Toh Allah ya rufa Asiri, koda yakr daman ai ta dade da gamawa daku ta daga ta baku kun cinye dake da Khalil din shiyasa bazaku taba ganin laifinta ba, to mudai munfi qarfinta in sha Allahu duk wani tsubbunta bazeyi tasiri akanmu ba kuma muna muku addu'a Allahya kwato ku"
"Toh Amin dai amma Anty Hajiya da Yah Khalil ai sunyi nisa. Jiya fa ta rotsa masa mota a gidan nan ace yau ta zo salin alin ta kawowa Hajiya abu taci shiyasa da aka mun tayi nace na qoshi to waya aikeni? Daman an ce Asirin da aka ci a abinci yafi tasiri kuma yafi wahalar magani" Khalifa ya fada yana tattara kayansa se Hajiya tayi shiru ta kuma kasa ci gaba da cin naman data qara. Me aiki Jalilah ta kwalawa kira tace tazo ta dauke sauran ta zubar.
"Saura kici nasan ku da shegen son zuciya zubarwa akace kiyi ki kai canbolar qofar gida ki zubar karnuka su samu" ta fada mata ta tattara harda na farantin Hajiya ta fita dashi Umaimah dake labe najin tahowarta tayi saurin barin gurin a ranta tana cewa
"Daga baya kenan wadda nayi dan ita taci kuma baki isa kisa ta amayo shi ba kema ina tafe kanki senayi maganinki wlh.

Basira me aiki kuwa tana fita Sammani ya tareta ganinta da kwano yana tambayarta ina zata, tana fada masa abinda zatayi ya karbe yana cewa
"Amma baki da hankali naman zaki zubar a bola maganin bera aka saka a ciki kome?"
"Nima ban sani ba, Anty ce tace a zubar" ta bashi amsa seya bude kwanon da aka kawo masa nasa da har yaci rabi ya juye a ciki yana cewa
"Ke dallah rabu da wannan matar tafi kowa fitina a yaran gidan nan na rasa meyw hadata da Hajiya Umaimah da bata sonta shine zata saka a zubar da abincin data dafa saboda mugun to mu zamu ci abin mu mayar da kwanon kice kin zubar kawai"
"Toh dan sammun wlh tunda aka kai yawuna ya tsinke" Basira ta fada seya dan yafita mata kadan a kwanon yana cewa
"Kinga wannan sake rabashi biyu zanyi naci rabi da dare rabi seda safe zan dumama abuna, Allah yasa ma Alhaji yayi wo mana tsabar balangu na hafa yau na kashe dadi abuna. Daga yanzu duk randa aka ce ki zubar da abinci ki ringa kawo mun nan kinji ko" ya dauke kwanonsa ya shige dakinsa.

A cikin gida kuwa Jalilah bayan ta zubo abinci ta zauna tana ci ta cewa Khalifa ya fito da kayayyakin da suke ledojin data zo dasu nan ya shiga zazzagewa a qasa kayane iya ganinka Atamfofi, Laces, Material sunfi Kala Hamsin ga Mayafai nan da gani sunfi Dozen biyu suma da sauran tarkacen mata na kwalliya. Da mamaki Hajiya ta kalleta tace
"Ke kuma Kanti zaki bude ko yaya wannan uban kaya haka da kika rakito?"
"Wane kanti Hajiya? Siyayyar Hussaini ce, wata qawata ce tayi sales shine naga an samu ragi sosai na kwaso su, dudduba ki gani manyan Atamfa Super kadai ya rage za'a qara ko guda biyar haka dan nan akwai su Holand da sauransu Chiganvy ce qarama a ciki Laces din kuwa sun isa guda Goma sha biyar ne ga Material biyar Voile biyar, nasa a kawo Lafaya Lace biyar ai sun isa ko?" Ta fada tana kallon Hajiya data saki baki kawai tana jin lissafi.

"To duk na menene haka kafinna gama jin abinda ya rage a ciki din" Hajiya ta fada seta miqe ta tafi gurin Fridge tana cewa
"Bakiji ba nace na Usainina ne kayan lefe na fara hadowa Khalil, ai yau bazan bar gidan nan ba se yazo munyi lissafi tas mun ga abinda ya rage a siya, se kuma inji batun inda ze ajiye Amaryar, daman ni Saman nan da babu kowa nayi mata tanadi ita wannan ta tattaro gaba daya ta dawo qasa daman nan aka san uwar gida ta bar Amarya a sama kusa dashi yanda zasu wataya da kyau babu me saka musu ido"
"Sannu Jalilah da iya tarar Aradu da Ka" Hajiua ta fada tana kallonta.

KHALIL
Qarfe biyar ya tashi aiki, seda ya tsaya yayi mata tsarabar chocolate da Ice cream kafin ya kama hanyar gidan. Maman kadai ya tarar a gida wai Humairan ta tafi Islamiyya.
"In banda shaqiyanci irin nata da tasan zakazo ai zeta haqura yau daya dai da Makarantar" Mama data kawo masa ruwa ta fada se yayi murmushi yace
"Ba laifinta bane Mama, jiya nace mata zanzo banzo ba inaga shiyasa ta dauka yau dinma bada gaske nake ba, daman daga office nake na biyo na kawo mata wannan" ya ajiye mata ledar siyayyar da yiwo seta dauka tana cewa
"To an gode Allah saka da Alkhairi a kuma ci gaba da haquri da mutuniyar kasan akwai quruciya akanta.

Dazun Alhaji Abubakar yazo da safe ai to har ma na bashi number Babban Yayanmu zasuyi magana dashi can se abinda suka zartar Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi yasa yin na Allah ne".
Kasa tantance yanayin da zuciyarsa take ciki yayi, farin ciki zeyi na kasancewar Manya sun shiga maganat auran sa ko kuwa Akasin haka? Ya Umaimah zata karbi Al'amarin abinda yake ta tuani a zuciyarsa kenan. Haka ya kama hanyar gida dukda Maman tace ya zauna ta aika a kira Humairan yace Aa ta barta kawai in ya samu dama da daddare ze dawo.

Yana fitowa a qofar gidan suka ci karo ta taho da sauri kamar wadda aka biyo zata shiga gidan ganinsa yasa ta dakata se kuma tayi sauri ta rabe shi ta shige jin Noor daya biyota yana koran sunanta. Kallonsu Khalil yayi ganin Noor din shima yana neman shiga cikin gidan har yana riqo mata Hijabi Khalil din yayi saurin riqeshi yana cewa
"Kai lafiyar ka qalau kuwa? Baka da hankali zaka kama mata hijab?"

"Malam kai kuma wanene? Dallah sakeni kafin na nuna maka danyan kai a nan gurin" Noor din ya fada yana zare ido tareda qoqarin kwace hannunsa da Khalil ya riqe. Mamakin tsaurin idonsa yayi yaron da befi sa'an Khalifa ba shine yake gaya masa haka take ya sake riqe hannun dakyau ya murde har seda Noor din ya saki qara kafin ya sake shi ya nuna shi yana cewa
"Idan ka kuskura koda wasa hannunka ya sake taba suturarta sena karya ka, wuce ka fita ka bawa mutane guri".

"Wallahi se kayi dana sanin abinda kayi mun, kw kuma ko bajima ko ba dade sena dauki fansa akan abinda kikayi mun zaki san ni kika yaudara" Noor din ya fada cikin wani irin fushi kafin ya juya fuuu ya fita daga gidan Mama da Hayaniyarsu ta fito da ita ta bishi tana cewa
"Babu abinda zata gani se Alkhairi Insha Allah mutumin banza kawai, kema shegen taurin kanki da nace ki fita a sabgarsa bakiji ba kenan".

Kuka Humairan ta saka tana cewa
"Ni Mama babu abinda na masa, haka kawai mun taho a hanya ya tareni wai dole se na tsaya munyi magana ni kuma nace bazan tsaya ba sedai ya zo gida idan maganar yake so muyi shinrme fa yake ta zagina ya biyo ni wai Macuciya mayaudariya zan auri wani bashi ba" ta qarasa tana sake rushewa da Kuka. Kallonta Khalil yakeyi wani mugun kishi na cinsa se kawai ya juya ya fice yana cewa Mama seda safe. Jiki a sanyaye taja Humairan suka shiga ciki ta ringa lallabata seda tayi shiru kafin tace ta kira Khalil ta bashi haquri.

Ransa babu dadi ya shiga gida. Yanasaka qafarsa a falon kansa ya sara kamar jiya, Umaimah na zaune a falon suna kallo da su Mu'ayyad suka tafi da gudu suna masa Oyoyo ya daga su sama daddaya kafin ya kama hannunsu suka shiga ciki. Idonta akan Tv tayi masa sannu da zuwa ya amsa yana zama a kusa da ita Ruqayya ta kawo masa ruwa ya fara sha kenan Wayarsa dake hannun Mu'ayyad ta shiga qara, be kawo ita bace dan haka Mu'ayyad din na miqo masa ya rigada ya daga dan haka ya danna speaker kawai yaci gaba shan ruwan bayan yayi sallama.

"Dan Allah kayi haquri Habibi, wallahi bani nace ya biyoni ba kawai ganina yayi a hanyar Islamiyya ya tsayar dani kuma ni bansan zakazo ba ma da na shiga gidan Anty Habi kawai saboda karka ganshi ranka ya baci" Humairan ta fada cikin muryar shagwaba. Kallon wayar yayi ya kalli Umaimah data zura ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?masa ido kamar farin shigar maita ya rasa abinda zece se kawai ya dannan ya kashe wayar, Mu'ayyad da Bibi ya kalla yace
"Kuje gurin Hajiya nima gani nan shigowa" suka kwasa da gudu suka fita seya juya yana kallonta zuciyarsa na wani irin tsalle yanda kasan wanda ya tsaya gaban Alqali yace
"Umaimah wallahi..."
"Ka riqe rantsuwarka munafiki karka kuskura ka gaya mun wata magana anan, abu daya nake so yanzu ka kira koma wace yar iska ce a gabana ka gaya mata daga yanzu koda wasa karta sake kuskuren kira layinka, idan kuwa ta sake ka gaya mata da bakinka seka lalata rayuwarta".

Zare ido ya shiga yi yana kallonta amma ya kasa bude baki yayi magana, ta yaya ma ze iya haka ya kira Humaira ya gaya mata wadannan maganganu gaskiya abun da wahala. Yawu ya hadiye yana qoqarin kama hannunta ta fizge yace
"Dan Allah base na kirata ba, zanyi blocking number kawai yanda bazata qara samu na ba"
"Kayi abinda nace Khalil idan kana buqatar kwanciyar hankali idan ba haka wallahi" Umaiman ta fada cikin daga murya se ya janyo wayar ya shiga kiran layin Humairah saboda yanda tayi maganar ji yayi akmar saukar aradu akansa.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 65

A fusace ta fizge wayar daga hannunsa ganin ya tsaya yana mata magiyar banza da wofi, seda ta fara ringing taji an daga kafin ta saka wayar a speaker ta cilla masa tana cewa
"Maza gashi nana ka gaya mata da bakinka idan ba haka ba wallahi ba zaka so abinda zanyi ba, ai ka sanni tsaf bana shakkar kowa idan nayi niyyar rashin mutunchi babu wanda ya isa ya dakatar dani"

"Haba Umaimah haba Umaimah yanzu ina hadaki da Allah amma kamar ba musulma ba aba zaki haqura ba? Dan Allah ki bari nayi miki alqawari ni da kaina zance gurinta amma kar kisakani yin abinda be kamata ba, ko wani naji yayiwa Humaira haka se inda qarfina ya qare guri kwatar mata haqqinta balle ace ni da kaina zan wulaqantata karki manta jinin Mansur ce" Khalil ya fada cikin rawar murya, wata gundumemiyar Ashar ta mulmulo ta watsa masa tana jifansa da wani matsiyacin kallo tace
"Ni kake gayawa haka Khalil? To karkayi abinda nace kaji har ka iya kallona kana gayamun dole ka kare darajar wata banza shashasha a waje amma ni kana wulaqanta tawa darajar ko? To karkayi, wlh se kayi nadamar qin yin abinda nace. Sena balbaltata na lalata darajar tata da kake iqirarin karewa"

"Babu abinda ze sameta da yardar Allah sannan kibi duniya a sannu Umaimah in har kina so ki mutu ki taradda ubangiji cikin salama to kiyi gaggawar tuba ki koma ga Allah in ba haka ba wlh ina tausayawa qarshen ki, sannan aure dai babu fashi da yardar Allah gara ma ki saka a ranki dan dazun ma munyi magana da Hajiya Aisha kuma a cikin satin nan masu zuwa nema zasuje can Jalingo" sukaji Muryar Mama daga cikin wayar, a firgice ya kai hannu ze dauki wayar dan shaf ya manta da cewar tayi kira suke ta wannan taqaddamar amma ta rigashi dauka ta miqe da sauri tana ja da baya tace
"Idan kutumar ubanki ne yake rabon Aljannar karya bani ko kuma idan nazo shiga ku hanani tsohuwar banza kawai"

"Ke Umaimah baki da hankali" Khalil daya yunquro ya figze wayar ya fada haryana tureta ta fada kan kujera se ta taso yanda kasan babu wani nauyi a jikinta, Ashar ta shiga dura masa ta uwa ta uba tana jifansa da duk kalaman da sukazo bakinta. Waiwayawa yayi ya kalli falon seya sauke ajiyar zuciya ganin Ruqayya da da take jera abinci a Dining bata gurin, yaran daman ya kada su da yanzu a gabansu zatayi masa tijarar kenan.

"Wallahi Tallahi Khalil se nayi Ajalinka in har kace ba zaka janye qudurinka ba, sannan kuma na kashe duk yar abu ta kazan da tace zata shigo gidan nan, ni zaka munafunta ka mayar sakarya to wallahi dakai da duk wanda suke daure maka gindin yin abinda kake shiri daidai nake daku se kun gane kurenku".

Kururuwa take tana surutai shidai tuni ya haye sama ya kullo qofar nan bakin qofar ya durqusa ya dafe kansa dake neman rabewa biyu saboda tashin hankalin daya riske shi. Yana jiyo yanda yake ihu daga qasan tana zaginsa shi da iyayensa kafin daga bisani ta fashe da kuka se kuma qarar fashe fashen abubuwa daya fara jiyowa da alama kayan falon take farfasawa seya miqe dakyar ya shige daki, bandaki ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi yafi minto talatin a tsaye har aka kira sallar Magriba kafin ya dauraye jikinsa ya fito zuciyarsa tana bugawa da qarfi. Jallabiyya ya jura a jikinsa ya dauki wayarsa da muqullin mota, cikin takatsantsan ya bar gidan bayan daya tabbatar da bata falon.

A bakin qofar sata raba bangarensu dana Hajiya ya tsaya saboda jiyo hargaginta da yayi tana cewa
"Haka kikace? Toh na rantse da girman Allah sedai kowa ya rasa, se nayi sana din Khalil dani da ku sedai kowa ya rasa" kafin ya gama tantance abunda take nufi aka bude qofar Umaiman ta fito buzu buzu yanda kasan farin shigan hauka gashin kanta a tsaitsaye fuskar nan tamkar Hadari banda kumburi da idonta yayi kamar an doketa a gurin. Wani kallo ta watsa masa da se da yaji hantar cikinsa ta kada taja tsaki ta wuce cikin gida ta barshi a tsayr daidai nan Hajiya ta fito itama tana kiran sunan Umaiman Jalilah na biye da ita a baya tana cewa
Haba Hajiya yanzu har zaki bita saboda son ki qarasa zubar mana da mutunchi a idonta, saboda ita ba mutuniyar kirki bace vata dubi ko darajat shekarunki ba idan ma bata kalli matsayinki a gurinta ba ta iya takowa har gabanki ta zageki to idan duk kun makance ta gama da ke da Khalil din wallahi mu ba zamu zuba ido qata yar iska ta taka uwarmu ba, kuma idan ta cika mara kunya ta dawo ta sake miki ko kallon Banza na rantse sa Allah sena karyata idan yaso a kaini inda bazan fito ba".

'Ki rufe mun baki Jalilah kima wuce ki dau gyalen ki kibar gidan nan tunkafin na saba miki, haka kawai muna zaune lafiya zaki janyo mana jidali ina ruwanki keta zaga ko kuwa? In ma haka ne ai abin zagin aka mata gara ita an ga kalar nata kishinke wayasan abinda zakiyi idan naki Mijin yace ze qara aure?" Hajiyar fada a fusace tana kallon Jalilah se tayi saurin tare Hajiyar da cewa
"Allah ya tsareni ya tsari zuri'ata da hauka irin na Umaimah dan wannanba kishi bane zallar jahilci hauka da son rai take gwadawa. Ita har tana da bakin crwa ba zata zauna da kishiya ba bayan data tashi gidan ubanta ma ina mata biyu ta tarar? Da haka tata uwar take ai da bata zauna a gidan ba harta haifeta shine mu zata zo nan ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login