Showing 261001 words to 264000 words out of 429394 words

Chapter 88 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1001

Lagos yau shiyasa yace ze zo dan idan ya tafi ze dade be dawo na shiyasa. Nima naso muzo tare amma ban samu dama ba ina wani abu duk yanda kukayi dashi zanji dukda ma dai nasan mun rigada mun cinye jarabawar ai" ya bata amsa se tayi shiru kafin a sanyaye tace
"Toh Allah ya kawo shi lafiya, amma dai ni da ya bari ma kawai seya dawo din"

"Aa yanzu kuma? Yaushe ne kike cewa kedai kin matsu ki ganshi seda zezo kuma kice wani ba haka ba saboda gulma" Khalil din ya sake fada seta rufe fuska kamar tana gabansa a ranta tace
"Shi komai mukayi magana s ya gayawa Yah Khalil" a fili kuwa tace masa
"Ni dai Aa, indai be fito ba kace ya bari ba yau ba wannan ma ai kwange ne dan kwanakin basu cika ba ai".

"Toh sedai idan kin fita ki gaya masa dan gashi nan yamun Text cewar ya iso yana qofar gidan, kiyi masa iso".

Ba shiri ta kashr wayar qirjinta ya shiga bugawa jin cewar ya iso, ta rasa me yasa take ta faduwar gaba akan haduwar tasu, ita dai ba zata ce bata damu dashi ba dan tasan ba wai Sonsa ta fara ba kawai tana jin dadin hira dashi kuma bata so su dena magana shiyasa ma tace ya bari se ya dawo daga tafiyar duk ma lokacin da ze dauka acan.

Qarar wayarta ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi, Noor ne, gabanta ya sake faduwa data tuna sunyi dashi zezo tasan kuma ya iso din ne shiyasa ya kirata dan Habibu yana gida yazo hutu shi kuma baya shigowa cikin gidan idan Habibu na nan dan basa ga maciji da dai baya nan daman a falon Mama ake hirar kosu saka kujera a tsakar gida.

A salube ta zura Hijabin da tayi sallar La'asar ta fita, babu batun tsayawa gyara fuska duk irin burin da ta ci na shan kwalliya randa zasu hadu da Ibrahim har kayan da zata saka ta ware su ta ajiye amma shirinya rushe. Mama na zaune tana Lazumi ta fito, da kallo ta bita ganin yanda take jan qafa fuska kamar me zazzabi tace
"Ke se ina haka kike jan qafa kamar me ciwo?"

Dakatawa tayi tana kallom Maman tace
"Abokin Yah Khalil ne yazo"
"Abokin Khalil? Ina gobe kika ce ze zo har na bawa Maryam tayi masa kayan kwalama kuma in shi din ne haka zaki fita da farar fuska qozai qozai kamar wadda ta tashi daga jinya?" Mama ta fada tana tashi tsaye daga inda take seta sake narke murya kamar zata fasa mata kuka tace
"Nima bansan ze zo yau ba kawai kirana yayi wai gashi nan zuwa goben zeyi tafiya, kuma ni munyi magana da Nuru zezo yana waje ma shima ya kirani".

Se Mama ta tafa hannu tace
"Ni Asiya naga ikon Allah. Yanzu saboda Allah kinsan mutum ze zo gurinki tun dazu ba zaki tashi ki gyara ba haduwar farko zaki fitar masa a haka kamar wata tsintacciya? Shi kuma Noor din da kika gayyato na magani da menene? Da yace miki ze zo ba zaki ce masa Aa ba?"

"Nifa Mama bansan yau zezo ba, seda muka gama magana da Nuru kafin shiya kirani nama kira Yah Khalil ko zece masa ya dakata yace wai ai ya kusa qarasowa ma da tare zasu zo" Humairan ta sake fada se Mama ta aika mata daquwa tana cewa
"Ba Nuru ba Fitila ma taci gidansu. Wuce ki cire wannan Hijabin kamar me takaba ki nemi kayan Arziqi ki saka kuma ki gyara fuskarki, shi Nuran zan saka Habibu yanzu ya korashi in Baqon ya tafi ya dawo kuci gaba da shashanci da batawa juna lokacin" tana gama fadar haka ta shiga kwalawa Habibu dake cikin daki kira.

Juyawa Humaira tayi dakinta dan tasan Mama ba zata bari ta fita a hakan ba tunda tace, ta bude Wardrobe din kayanta tana kallonsu, bata ma bi takan kayan da tayi niyyar sakawa ba ta zaro wata Abaya baqa Mansur ne ua aiko mata dasu kwanaki. Hijabin Jikinta ta zare ta mayar da Abayar. Ribbon din data daure gashinta me tsaho da santsi irin na Asalin fulani ta zare ta sake matse gashin ta mayar dan bata da lokacin tajewa, bama tason taba kan se dole zafi yake mata.

Farar hoda ta goga da Vaseline a bakinta kafin ta qara turare kadan dan bata jima da wanka ba ta shafa turare kuma, mayafin rigar ta rufe kanta dashi, qirjinta ya buga sanda taga kiran Noor, hannu na rawa ta daga wayar tasan za'ayi haka muryarsa a hade cikin fushi yace
"Da kinsan kina aiki me yasa zaki ce nazo kinsan daga inda na taho yanzu kuma ba zaki gaya mun da kanki ba se ki aikomun wancan Ajawo din yazo yanawa mutane hayaniya wallahi ki ja masa kunne ya kiyayi randa zamu hade dashi kuma karki kuskura ki kirani" be bata damar cewa komai ba ya gama bambaminsa ya kashe waya. Ta maida wayar kan mudubi jikinta na daukar rawa yanzu tasan yayi fushi kafin kuma ya sakko se Allah saurin da take tayi akan ta fita ita ta lallabashi ya tafi kafin Yah Habib yaje dan tasan daman seya ja mata gashi yanzu yace karma ta sake kiransa.

Goge kwallar data ziraro mata tayi jin Muryar Mama tana shirin shiga dakin, Maman ta shigo ta kalleta yanda taga fuskar Maman kamar wadda aka biyawa aikin Hajji ya bata mamaki amma tayi shiru
"Kina nan tsaye kina solobiyancin naki ga mutum zaune yana jiranki, yi maza da Allah ki fita in banda ma Allah me kyauta da qari har ina ke ina shi koda yake Addu'a tace ta karbu kai Allah na gode maka".

Ita dai bin Mama tayi da kallo danbata fahimci inda zancenta ya dosa ba, wannan murna da takeyi kuwa itama bata san ta mecece ba sedai jin da tayi tace baqon yana jiranta ta gane ciki suka shigo dashi kenan, to ko Mama tasan shi ne? Zama ta sanshi tunda shima Abokin Yaya Mansur ne. Tsaki taja a fili ta fito ranta babu dadi duk wani zumudin ganin Ibrahim ya disashe mata saboda batawa Nurun ta rai da akayi. Ji tayi bugun zuciyarta ya qara sauqi ta tsaya daidai corridor da ze fitar da ita daga inda dakunan su yake zuwa cikin falon tsabar yanda gabanta ke tsinkewa seda ta dafe qirjin da hannu biyu. Muryar Khalil take jiyowa qasa qasa yana magana da alama waya yakeyi, wannan ne ya bata kwarin guiwar daga qafarta taci gaba da tafiya kenan ba shi kadai yazo ba amma da Yah Khalil yace baze rakoshi ba.

Kanta a qasa kamar farin shigan munafunchi ta shiga falon da sallama. Daga bakin qofar ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, ganin Khalil din shi kadai a zaune yana waya yasa ta qarasa shiga ta samu kujerar gefensa ta zauna qirjinta naci gaba da bugawa a gefe kuma tana satar kallonsa yanda yayi kwalliya yasha shadda kamar wani sabon Ango se zuba qamshi yake ga Turanci yanayi yanda kasan Rainon Ingila. Seda ya qara kusan minti biyar bayan ta zauna kafin ya kashe wayar yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi.

Murmushin itama tayi ta shiga gaisashi ya amsa yana kallonta sukayi shiru na dan lokaci Humaira ta waiwaya ta kalli qofa, so take ta tambayeshi ina Ibrahim amma tanajin kunya dan haka ta mayar da kai qasa tana wasa da zoben hannunta. Khalil kuwa ido ya zuba mata yana sake qare mata kallo a yanzu ne yake sake ganin quruciyarta yarinya ce sosai kodan da da Jilbab yake ganinta shiyasa take dan cika masa ido? Lallai se abar zuciya idan ba haka ba shi da yake da cikakkiyar Mace ta ko ina me zeyi da wannan yar yarinyar.

"Yaya, naganka kai kadai" Humaira tayi maganar a hankali ganin kusan minti goma ya zura mata ido bece komai ba, komawa yayi ya jingina da kujerar da yake kai sosai ya sake zuba mata idanunsa da suka saka taji zuciyarta na tsinkewa ga wata sabuwar faduwar gaba da takeji seta miqe tsaye danbazata iya cigaba da jure kallon da yake mata ba Khalil na ganin ta miqe shima ya miqe da sauri ya tareta ganin tana neman barin falon yace.
"Ina kuma zakije?"

"Uhm ruwa zan sha" ta bashi amsa tana ja da baya tareda rarraba ido saboda yanda ya matsota. Da ido ya mata nuni da ruwa da Lemon da aka kawo masa seta hadiye yawu dakyar tace
"Daman na manta wayata ne a ciki zan koma na dakko"
"Koma ki zauna" ya fada yana sake tsareta da ido, kamar kuwa zata fasa masa kuka haka ta tabe fuska ta koma inda ta tashi ta zauna. Allah ya sani wannan kallon da yake mata ita tsoratata yakeyi kuma shi Ibrahim din ina ya tsaya da har yanzu be qaraso ba bayan yace ma ba tare zasu zo ba.

"Aisha" ya kira sunanta da wani sauti da seda tsigar jikinta suka zuba, sautin muryar da Ibrahim yake mata magana taji dan haka ta daga kai a hankali ta kalli bakin qofa dan taga shigiwarsa amma bata ga kowa ba.
"Aishatu" ya sake kiranta da ainihin yabda Ibrahim din yake kiranta gaba daya ta shiga rudani, me kenan hakan yake nufi? Wannan Yah Khalil ne amma ya akayi yayi muryar Ibrahim har ya kirata da sunan da shi yake kiranta.

"Aishatu, na kasa zurewa na jira har zuwa gobe, son ki yayi mun yawa idan na wuce yau banji matsayina a gurinki za'a iya wayar gari a ga na sheqa Soyayyarki tayi Ajalina" ya sake fada kansa tsaye yana kallonta, yanda take mutsu mutsu ya tabbatar masa da ta shiga rudani.
Humairah kuwa wannan karon a mugun firgice ta daga kai ta kalle shi jin abinda yake fada, kasa fassara maganar sa tayi dan haka tace kawai tace masa
"Ina Ibrahim?" Shi kadai ne amsar da take da buqatar ji a yanzu
"Gani" ya bata amsa kai tsaye seta ware ido akansa tana kallonsa jin abinda yace

"Nine Ibrahim Khalil, ko akwai wanda kike tsammanin gani daman bayan ni?" Ya sakw tambayarta yana dage mata gira. Yanda tayi da fuskarta seda ya bashi dariya harya kasa hadiyeta. Yanda kasan wanda ya gayawa wani mugun Abu haka ta miqr da sauri tayi cikin gida be tsayar da ita ba shima ya bita da dariya kawai, komai aka hada da yaro dai se an ga quruciya. Wayarsa ya dauka ya shiga kiran Layin Mansur.
"Yaya Mansur ina wuni ko nace barka da dare dan nasan ku daren ku ya shiga" Khalil ya fada bayan daya amsa sallamar da Mansur yayi m???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?asa. Daga daya bangaren Mansur yace

"Da alama shaye shaye ka fara ko idan ba haka ba ni zakace wa Yaya saboda Dan iska ne kai? Ni ba surukinka ba ba komai ba kace mun wani Yaya bayan ko a shekaru aka qirga ka girme balle kace hankali ka qaro yau zaka bani girma".

Dariya Khalil ya fashe da ita shima Mansur din na tayashi kafin yace
"Ka sani ko zaka zama surukin nawa ai abun na Allah ne"
"Wa Allah ya tsareni da zama surukinka dadai wannan matar a gidan ka ko yan uwan maqotan mu da na sani bazan bari su baka mata ba" Mansur ya sake fada se Khalil yayi murmushi yace
"Toh Yaya Mansur ya zanyi dakai tunda haka kace"
"Ka gama iskancinka ka fada mun abinda yasa ka kirani Malam" cewar Mansur, se Khalil yayi saurin cewa
"Zan sake kiranka zansu ina tsakiyar wani Important deal ne, kaidai da yayi clicking ka fara saka ranar zuwa Naija nan kusa" be jira amsar Mansur ba ya kashe wayar ganin ta qaraso cikin falon tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.

Humaira
Wani fitsari taji ya matsota saboda maganganun Khalil din ba shiri ta miqe dan karya zubo tayi abin kunya, dakin Mama daya fi kusa a cikin corridor ta fada, Mama na waya dukda bata san dawa suke magana ba amma tasan maganar ta akeyi dan taji Maman na cewa
"Wallahi in gaya miki, gashi can a falo" ita dai ta wuce ta tsula fitsarinta. Sink ta dafe bayan data wanke fuskarta ta tsaya tana kallon kanta a mudubi. Tunani takeyi ta yaya akayi Yah Khalil ya zama Ibrahim kodai wasa suke so suyi mata da hankali? Kiran da Mama take mata ya sakata fita ta tsaya a bakin qofar.

"Ke kuma lafiya kika shigo kamar an koroki?" Maman ta fada tana kallonta seta narke fuska tace
"Mama Yah Khalil ne, wai shine Ibrahim yace"
"Aa, ke da baki san Khalil Ibrahim bane ko Yaya?" Maman ta sake fada kamar bata fahimci abinda take nufi ba. Kan gadon Maman ta zauna tana cewa
"Mama bafa suna ba, wai shine Ibrahim din da muke waya dashi wai fa Mama Yah Khalil ne yake sona" ymta qarasa maganar kamar zata fashe da kuka dan tunanin wai Khalil ke sonta ma qara firgitata yakeyi, ita fa Humaira Khalil yake so ai abin ya mata nauyi.

"Ke fa shirmenki yawa ne dashi, to se akayi Yaya dan Khalil nasonki ina nan kike raba rana da dare kina zancen Ibrahim kuma yazo shine zaki bi duk ki kidima kanki kamar wadda tayiwa sarki qarya. Ni da Allah wuce kin baro mutum shi kadai a zaune"

"Mama wai baki gane abinda nake fada ba" ta sake fada ganin babu wata alamar damuwa a zantukan Maman, se kuwa Maman ta miqe tana cewa
"Wuce, idan ya tafi kya ganar dani koma menene". Babu yanda ta iya haka ta fito, tana qarasawa tajishi yana waya a hankali take tafiya harta zauna akan kujera kanta a qasa.

"Kin gama gudun da babu gurin zuwa" ya fada yana zura wayarsa a Aljihu, ita dai bata amsa masa ba kanta na qasa tana sake nanata wai Khalil ne Ibrahim dinta, dashi duk suka ringa wannan waya da hira. Tunanin yanda suka musayar maganganu ta ringayi taji kamar qasa ta bude ta shige, yanda ya ringa mata wayo yana tambayarta abubuwa ita ko ta ware tana bashi amsoshi daidai da saninta ashe duk Yah Khalil ne kai wannan abin kunya ina zata kaishi.

"Haba Mana Aisha, har cewa fa kikayi badan Haramun bane da idan muka hadu har Rungumeni zakiyi saboda yanda kike Jina a ranki ko kin manta" Khalil ya jefo mata maganar, ta daga kai ta kalleshi kafin taha pillow ta rufe fuska se jin shashsheqar kukan ta yayi ba shiri ya isa inda ta ke ya durqusa qasab kujerar yana cewa.
"Subhanallahi me kuma akayi na kuka daga wasa? Allah ya baki haquri baki ce haka ba. Ni ne nace da ze yuwu har rungumeki zanyi dan kiji yanda zuciyata taje bugawa akanki koba haka".

Rarrashinta ya ringayi har seda ta dena kukan ta dago fuskarta da tayi Ja.
"Me yasa ka boye mun baka gaya mun kaine Ibrahim ba?" Ta fada cikin muryar Kuka, Khalil dake tsiyaya ruwan sanyi a cuo ya miqa mata ta karba amma bata sha ba. Murmushi yayi mata yace
"Ki sha zan gaya miki komai".
Seda tasha ruwan ta aje cup din se ajiyar zuciya take shiko a zuciyarsa mamaki yake na abinda ya sakata Kuka, yanzu meye abin zafi a nan da har Mutu zeyi kuka banda dai Humaira da son maida qaramin Abu babba.

"Kinsan me yasa naqi na bayyana miki kaina? Saboda wannan abun da kikayi. Nasan idan na fito kaitsaye nace ina sonki zakiyita koke koke ne na rashin dalili kuma nasan be zama lallai ki yarda ba sannan daga qarshe nayi loosing respect din da kike bani na Yaya saboda ku Mata haka kuke, masu qananun shekaru precisely. Da babba wanda ya zarce shekarunku ya nuna yana sonku se ku maida abun wani daban ku dauka kamar wani babbanlaifi ya aikata dan ya ce yana sonku. Shiyasa na zabi na fara shigar miki da soyayya ta idan na samu karbuwa na yarda da kona bayyana miki kaina ba zakice Aa ba kamar dai yanzu na san na rigada na samu fili a zuciyar Aisha ko kawai nayita baza shanyata".

Kanta ma qaa harya qare magana bata iya dagowa ta kalleshi ba, da gaskeyarsa kamar yanda ya fada din gani takeyi kamar sabo ace kamar sa yana sonta shi kansa Ibrahim din kawai bata san yabda akayi ya shiga ranta ba. Amma ita ko a hanya taga Babba ya kula yar yarinya ma kallon Dan iska take yi masa a ganin ta kowa ya ji da daidai dashi babu dalilin da ze saka babban mutum irinsu Yah Khalil din yazo yana son yan yara irinsu sedai a barsu dasu Noor sune daidai shekarun su.

"Kinga bamuyi haka dake ba, kinyi mun Alqawari duk randa muka hadu zaki gayamun gaskiyar abinda kikeji game dani a zuciyarki babu kwange bare coge amma shine yanzu ina magana kinyi Shiru. Ki dago ki kalleni kiyimun magana. Ni na rigada na fada miki duk abinda ya kamata ki sani game dani, dagaske nake sonki da aure ba wasa ne ya kawoni gurinki ba, kuma saboda bana so na takuraki ko na zama silar da za'ayi miki dole ya saka na zabi neman soyayyarki da kaina kinsan idan naso kai tsaye zan tunkari magabatanki da magana sedai kawai ki ganki a gidana amma banyi haka ba saboda ina son aurenki aka yardarki shine ze bamu damar shimfida rayuwa irin wadda nake fata dake".

Ita dai kamar wadda aka daurewa baki haka tayi shiru tana jinsa harya gaji da magana shima yayi mata shirun kawai yana kallonta.
"Matsalar qananan yara kenan" ya ayyana a zuciyarsa, yanzu da babbar budurwa ce data san kanta ba ruwansa da wannan bata lokacin kai tsaye zeje ga buqatarsa amma yanzu kalleshi yanda ya lalace a gaban Kusan yar cikinsa yana lallabata ta masa shiru kamar gunki. Tsaki yaja saboda ransa daya sosu ya miqe yana daukar muqullin motarsa ya kalli Humaira da itama ta dago jin tsakin nasa suka hada ido.

"Bakya buqatar ki gaya mun baki karbeni ba dan naga hakan a aikace. Nagode da lokacin da kika bani inaso kuma ki dauka Ibrahim be taba wanzuwa a rayuwarki ba. Kici gaba da daukata a Khalil kamar yanda baki karbi alaqata ba bana so ki ringa tunota ballantana har ki kalleni da abinda ya wuce, ki gaida Mama idan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login