Showing 393001 words to 396000 words out of 429394 words

Chapter 132 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1002

sake fita daga gidan nan ba gara nayi zamana nayita istigfari ina hailala har ranar da ubangiji ze dauki raina kawai bazaniya fita ba ina tsoron tozarcin da zan fuskanta idanna fita waje" Umaimah ta fada tana shirin sake fashewa da kuka se Maman Asad taja tsaki tana cewa

"Ai sekiyi, duk me cikakken Imani ya yarda da qaddara me kyau ko mara kyau dan haka idan ya ganta akan dan uwansa ba dariya zeyi masa ba sedai ya nema masa sauqi gurin Allah ya kuma nemi kariya daga afkawa irinta ki nemi yardar Allah kawai shine mafita a gareki ni bari naje yara sun kusa tasowa" daga haka ta fice ta barta. Komawa tayi ta kwanta tana cigaba da tunanin da ya zame mata jiki yake kuma neman zauta mata tunani. Ranar Juma'a su kazo kamar yanda ta gaya mata, Naziyya tazo tun Alhamis amma kamar yanda suka saba tun bayan dawowarta gida ta shata mata layin babu ita babu ita wannan karon ma haka akayi. Ranar Juma'ar da suka takura mata akan tayi haquri ta janye gabar ko babu komai ita babbace tayiwa qanwarta uzuri Kuka ta fasa musu kai tsaye tace
"Babu uzurin da zan mata ai da hankalinta ba mahaukaci bace ita kuma tana sane ta aikata duk abinda tayi ba tareda tayiwa kowa uzuri ba. Ni nasan girma da darajar Iyayena dan haka bazan taba shiri da wanda ya wukaqanta su ba, Yanda ta saka su cikin tasku ta jefe su da maganganu har tayi sanadiyyar zubar hawayensu bazan taba yafe mata ba kuma zata gani, itama ta haifa da ranta dan cikinta seya gwada mata abinda tayi koma wanda ya fishi, haqqin Khalil dana sauran mutanen da kika dauka Umaimah baze taba bari ki zauna lafiya ba".

Gaba dayansu suka dauki salati Cikin tsananin tashin hankali Umaimah ta rushe musu da kuka, Mama ta sallame sallar La'asar da takeyi babu bata lokaci ta dauke Naziyyan da mari tana cewa
"Wace irin zuciya gareki Naziyya dagani har mahaifinku bamu kasance masu taurin kai da kafaffiyar zuciya ba a ina kuka samo taku? taskun da yar uwarki take ciki be isheki ba se kin bita da mugun baki akan me? muda tayiwa laifin munce mun yafe se kece zaki qullaceta ki ja mata mugun Alkaba'i to ahiri dinki kuma idan na isa dake ki janye kalamanki kuma ki shirya da yar uwarki. Iyakar bakin data dibarwa kanta ya isheta base kin bita da naki ba Allah ka shiga lamarin Zuri'ar mu karka saukar da rabuwar kai a tsakaninsu" Maman ta qarasa tana fashewa da kuka itama. Tashin hankalin Umaimah ya qaru, yanda falon ya rikice da kuka kuma ita ce sila. Ta ringa wani irin kuka danta gagara cewa komai, nadamar rayuwarta ta sake daureta, tun usuli itace matsalarsu, itace kukansu duk wani jaye jayen rigima itace bata taba barin zukatansu su huta gashi yanzu tana neman zama silar rugujewar zumunchinsu Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

Dakyar take tafiya saboda yanda idonta ya rufe bata gani ta samu ta fada kan gadon dakin da take, Nuratu data bi bayanta tana kuka itama ta dagota tana cewa
"Ki kwantar da hankalinki, karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki"
"Gaskiya ta fada Nuratu nima kuma na sani, duk abinda yake faruwa a yanzu na tabbata ba komai bane domin tsiyar dana shuka ta zarci na fuskanci iyakar wannan matsin a matsayin sakayya na sani dole haqqi seya bibiyeni amma dan Allah ku tayani roqon Allah kar Yarana su kangare, bana so laifina ya shafesu bana fatan su tashi da mummunar dabi'a irin tawa" ta qarasa tana fashewa da kukan dayafi na farko rauni ta fada jikin Nuratu suka rungume juna suna kukan tare, yanda jikin Umaiman yake rawa ya sakat tsayar da nata kukan dole ta ringa bata baki, dakyar ta dena kukan itama tace mata ta kwanta bata musa ba ta kwanta maganganun Naziyya na mata yawo akai yar uwarta ta jini kenan to inaga wani bare? Wane irin maganganu mutane suke fada akanta? Wace irin tarba zata samu idan ta sake fita duniyar mutane?

Nuratu data fita ce ta koma dakin da ruwa da kwayar magani guda biyu ahannu ta bata, bata musa ba tasha dukda bata san kona menene ba amma tana da buqatar abinda zegusar mata da hankali a yanzu koda bacci ne ta samu tayi kafin zuciyarta ta ida tarwatsewa, kanta sara mata yakeyi kamar ze rabe biyu ga bugun da zuciyarta takeyi ya wuce qa'ida jikinta kansa rawa yakeyi. Tana sha ta mayar da idonta ta kulle bata dauki minti biyar ba bacci me nauyin gaske yayi gaba da ita se sannan Nuratu ta sauke ajiyar zuciya ta fita.

A falon Mama ko kukan da takeyi ya daga musu hankali Matuqa har Anty da hayaniyarsu taja hankalinta ta shiga tayasu kukan, ta kalli Naziyya dake kuka itama tamkar tace
"Kinga ai kun zama daya keda ita har gara ita dan yanzu tana qoqarin goge duk laifukanta ta hanyar farantawa Mahaifiyarku amma ke yanzu me kikayi? Kinyi sanadiyyar zubar hawayenta kin baqanta mata zuciya a zatonki abinda kikeyiwa yar uwarki dadi zataji ko kuwa kin dauka ta dena sonta ne kamar ku? A yanzu babu abinda ze faranta mata illah taga hadin kanku amma a maimakon hakan kina nema ki haifar da sabon tashin hankali a cikin gidan nan iya wanda muka gani a baya ya isa ina roqonku dan girman Allah ku sararawa rayukanku ku rungumi yar uwarku da qaddarar data afka mata dan bata da kowa sama daku.

Idan Umaimah nada laifi kuma kuna dashi saboda baku da wata hujja da zaku kafa data saka kuka barwa Duniya ita kuka zame hannunku daga al'amuranta qarqari kuce bata jin shawararku shiyasa kuka wofantar da ita, da ace kun cigaba da naci da cusa kanku cikin lamuranta da ko baku san komai ba dole zaku san da yawa daga abubuwan da suke faruwa da ita amma kuka barta a hannun qawayen banza da suka kaita suka baro a yanzu babu wanda ze zage su kudin dai ku za'a zaga akan idonku qanwarku ta lalace take abubuwa tamkar bata da kowa a duniya da ze nuna mata daidai. Ke kanki Mama yau zan fada miki kina da naki laifi domin ke kika fara bada qofar da Umaimah ta samu damar yin duk abubuwan da takeyi. Tunda kika san Umaimah zuma ce seda wuta be kamata kiyi mata sako sakon da har zata ringa aiwatar da abubuwa yanda taga dama ba.

Dukkan mu nan shaida ne duk sanda kika murde kika nuna mata fin qarfi tana lankwasuwa tayi abinda kikeso koda ace ba'a dadin rai ba amma zatayi idan kuma kika bata umarni bata qetarewa koda kuwa ranta be so ba, da ace kinci gaba da bibiyar rayuwarta kamar yanda kikeyi da farko da abubuwa da yawa basu faru ba amma se kema kikayi fushin zuciya kika zuba mata ido Alhalin kin san Umaimah tana cikin zubin Halittar da ubangiji yayi basu da tunanin kansu suna amfani da duk abinda suka gani ko sukaji kuma yayi daidai da qawa zucinsu basu duba kyautuwa ko rashin dacewar abu muddin yayi daidai da ra'ayinsu shikenan kinga kenan kamata yayi ace kinci gaba da zama tunaninta kamar yanda kika fara tun farko kina tursasata tabi ra'ayinki koda bata so da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Nida nake janta a jiki tana wulaqantani ai ba zuciya ce bani da ita ba data sa na shanye naci gaba jibantar lamuranta nayi hakan ne saboda karta rasa kowa cikin rayuwarta.

Muna yiwa Ubangiji laifi ya yafe mana wani ma ba tareda mun roqi afuwarsa ba me yasa bazamuyi koyi da haka ba muma mu zama masuyin uzuri ga junanmu? Mu rungumeta mu tayata fuskantar duk wani qalubale daze taradda ita bawai muci gaba da tunzurata ba harta sare nutsuwar data saukar mata ta barta ta koma ruwa abinda zata aikata se sunfi na baya muni sannan duniya taci gaba dayi mana tofin ala tsine saboda baza'a zagi Umaimah ita kadai ba tilas duk wanda labarinta ya riske shi seya hada da ahalinta".

Kalaman Anty suka kashe musu jiki muqus suka kasa yin ko wani kwakwkwaran motsi a gurin se jan majina da ajiyar zuciya sukeyi. Tabbas Anty batayi qarya ba suna da hannu cikin tabarbarewar Umaimah kuskurensu kuwa shine fushin zuciya da sukeyi akan lamuranta da kuma qin tsanantawa da cusa kai yanda bata daukarsu da muhimmanci suma suka saketa ta hadu da masu tunani irin nata suka qara dulmiyata ruwa gashi yanzu suna raba bacin randa ita dan duk inda suka shiga a shekarun baya se anyi zundensu wasu ma suna fadin da saka hannunsu tayi abinda tayin, a lokacin Maman Asad Mijinta fasa auran dayayi niyya yayi saboda ya tsorata da abinda Umaimah ta aikata. dukda be taba ce mata komai akan maganar ba itace dataji zancen fasa auran tayi masa magana kai tsaye kuma yace mata

"Daman bawai na matsu danayi auran bane kuma na haqura tunda ina sonki kar nayi biyu babu" maganarsa ta daure mata kai sosai kuka bata fahimce shi ba seda yan uwansa suka tasata a gaba suka ringa yada mata da magana sannan ta fuskanci tsoratar da yayi, har kuka seda tayi tana ce masa ko a tunani bata taba kawo cewar ta cutar dashi saboda zeyi abinda Allah ne ya halasta masa ba shi kuwa yace mata babu wannan maganar, daman rashin nuna damuwar da tayi ya bashi mamaki to maganin kar ayi kar a fara aure dai ya haqura har gaban Abada na bar maganar qara aure Hajiyayye ta ishe shi shikenan maganar ta mutu.

Ranar dai haka sukayi wunin jigum jigum Abba ya dawo Anty ta kwashe yanda akayi ta mayar masa ya ringa fada kamar ze ari baki ga baccin da Umaimah take tayi ya sake rufe Nuratu da bala'in me ta bata har yana rantsuwar idan suka kashe masa Ya duk se yayi qararsu ai badan basa son ta bane laifi tayi suke nuna mata kuskurenta ba kuma hakan ne yake nuna basa qaunarta ba. Nuratu ta ringa rantse rantae akanita maganin bacvi kawaita bata saboda damuwar data shiga komai ze iya faruwa da jininta ko zuciyarta amma idan ta samu bacci zata huta kuma hankalinta ya kwanta, be barta ta fita daga gidan ba se qarfe goma bayan Umaimah ta farka kuma Mijinta Dr Sagir yazo ya qara tabbatar masa da maganindata bata bashi da illah, wai ranar har Abba ne yakecewa shi be gama yarda da sahihancin Likitancin ta ba, ya manta da cewar ita take kula dashi, kaf jinyar hawan jinin da Umaimah ta sababamas aita ce take lura dashi amma yau da yake antabo tsomar zuciyarsa ya fitittike, daman abinda take amfani dashi kenan ta karanci sunfi sonta shiyasa take wahal dasu, kuma daman a rubuce take, duk abinda mutum ya kwallafa rai a kansa se an jarabce su dashi, babu wata soyayya data cancanci dukkan zuciya data wuci ta Allah da Manzonsa.

Wannan dambaruwa ta ninka damuwar Umaimah, duk yanda suka yi qoqarin nuna mata komai ya wuce hatta da Naziyya da kanta ta bata haquri ta kuma nemi afuwarta ta akan abinda ta fada ta gagara samun nutsuwa. Kalaman Naziyyar sunyi matuqar yi mata tasiri kuma sun qara tsoratata tareda maido mata da abubuwan da suka wuce tana hasaso ta inda haqqindata fada ze fara bibiyarta, a kullum ta daga hannu sama takance
"Allah ka bani ikon neman yafiyar wadanda na zalunta tun ina da sauran numfashi, ubangiji na roqeka karka karbi raina na dawo gareka da nauyin wani akaina Allah ka dubeni ka karbi tubana ka kawo mun dauki a cikin al'amurana", a haka rayuwa taci gaba da tafiya, duk yanda take tunanin samun sauqi abun ya faskara, damuwa ta mata yawa, hatta da zobon data fara ta saki dan masu siyan zobon da yawa da biyu suke mata cinikin izgili da wulaqanci yake sakasu siyan zobon dan hatta gidansu an canza masa suna zuwa gidansu Umaimah me zobo irin abubuwan da ake mata idan an shigo siyan zobo na izgili da wulanci ya saka Abba ya hanatayi, ta roqeshi akan ya barta taci gaba amma zata samu Almajiri ya ringa fita dashi waje a dena shigowa cikin gida siya dan har sannan dubi dayan nan yake bata zobo kuwa ba qaramin rufin Asiri yake kawo mata ba sannan suma yan gidan susha, na musamman takeyiwa Abban saboda yana da Sugar kullum kuma yasha ze saka mata albarka ko babu komai zata tasiranci bacin ran data sakasu a baya shiyasa ta nace akan ya barta taci gaba, sedai sau biyu tayi ta bari gaba daya dan ranar farko na dubu biyu tayi bama kamar yanda ta sabayi a cikin gida ba zubin Hamsin da Dari takeyi seta yi na dubu biyar ya qare tas har ana nema se gashi a na dubu biyun dakyar akayi dari bakwai, dari biyar ma Almajirin ya kai mata wai sauran bashi aka karba Jikokin gidan suka shanye dan ranar suna nan washe gari yanda aka fita dashi haka aka dawo mata dashi dan taja masa kunne akan karya bada bashi yace kuma duk wanda yaje wai se yace bashi shiyasa ya dawo mata dashi shikenan sana'ar zobo ta gurgunce ta tasa dan abinda ta tara a gaba da buqatu suka qare ta sake komawa yar gidan jiya amma duk wannanbe wani dameta sosai ba domin tasan kowanne tsanani yana tareda sauqi kuma wata rana komai ze zama tarihi.

Babban tashin hankalinta a yanzu fitinar Bibi da a kullum qara bunqasa takeyi, a yanzu bata kwana uku bataje gidanba haka zata tasata a gaba da kuka akan ta dawo gidansu idan tayiwa Dady magana se yace ta tambayeta shi babu ruwansa itace taqi dawowa, idan ta saka mata wannan darun seta ce mata
"Idan kinyi sallah kullum ki ringa mana addu'a idan da Alkhairi tsakanina da Dadynku Allah ya daidaita mu".
Bibin bama gane hausar takeyi ba, data gaji da nacin tambayar Umaiman ta ranar ta tambayi Mama yaushe Momynsu zata koma, kai tsaye tace mata

"Momynki da Dadynki sun rabu ya saketa ba zata sake komawa gidanku ba ga sabuwar Momy nan ya samo muku kuma tana sonku tana kula daku keda kanki kina fadamun koba haka ba? Dan haka itace matar Dadynku yanzu Momynku kuma gata nan anan gidan kina zuaa kina ganinta karki sake damun wani da tambayar yaushe zata koma gidanku dan ba zata koma ba".
Umaimah tayi tsam dan kalaman Maman basu mata dadi ba sannan gani takeyi ai sunyiwa Bibi girma ba zata fahimci abinda take nufi ba, ga mamakinsu gaba daya se ji sukayi yarinyar tace
"Dama Halima ta gaya mun indai Mamah tana gidan mu Momy ba zata taba komawa ba dan haka zan gayawa Dady sedai ya zaba ko Momy ko Mamah"

Umaimah ta riqe baki, Mama ta fizgota tana cewa
"Dan ubanki wacece wannan Halimar da kika samu da duk wani abu na diban albarka idan kinayi zakice Halima ce takeyi ko ita ta fada? Tun yanzu kema kin fara tara qawayen banza masu gurbata tunani ko to kuwa baze sabu ba da kaina zan kira uban naki sedai ya canza miki makaranta ya rabaki da koma wacece da take nema dasa miki mummunar dabi'ar qin matar ubanki" ta sata a hammata ta kileta, tana kuka take cewa
"Wlh sena gaya masa kuma ai yana sona nasan zeyi abinda nace" ta ringa birgima tana tijara, Mama ta dakko wata dorinar Yasir da yake zane yara a Islamiyya wai shi prefect ta ringa caula mata ba shiri ta miqe ta bita seda tayi mata lilis kafin ta watso mata hijabinta da wata yar Berbi bag tace
"Wuce ki tafi, daman zanzo har gidan na????!!!!!!! !
! ! !
!!!!!!!!!!!!!!!!!!! !!!"!#!$!%!&!'!(!)!*!+!,!-!.!/!0!1!2!3!4!5!6!7!8!9!:!;!!?!@!A!B!C!D!E!F!G!H!I!J!K!L!M!N!O!P!Q!R!S!T!U!V!W!X!Y!Z![!\!]!^!_!`!a!b!c!d!e!f!g!h!i!j!k!l!m!n!o!p!q!r!s!t!u!v!w!x!y!z!{!|!}!~!!?!ku Allah yasa naji wani labari mara dadi zaki gane kurenki yar banza me kunne kamar Area", ita dai bata ko debi takalmanta ba tayi waje seta dawo da gudu tana kuka tace wa Maman
"Kuma Hajiya tace na gaya miki Mamah ta haihu amma bazan fada ba tunda kika dokeni kuma dan kiji Babyn qato fari irin Aryaan sunansa ma Mukhtar Dady yace" tana gama fada ta diba da gudu ta fice, daman ita kadai aka kawo Manniru ya dauketa suka wuce gida tun kuma daga wannan zuwan seda aka kwashi tsahon lokaci basu je ba.

Wani irin Duum, kunnen Umaimah yayi mata, ta kalli Mama data bi Bibin da dariyar yarintarta tana cewa
"Ja'ira to ai kin fadi saqon Masha Allahu Allah ya dayyaba wannan karon ko zamuje barka in Allah ya yarda bari Alhaji ya dawo na gaya masa gashi ma Takwara ya samu, Allah ya rayashi yayi masa Albarka" har Mama tagama addu'arta ta juya tana zaune inda take wani irin abu ya shiga bijiro mata seta dafe zuciyarta a fili ta shiga maimaita Innalillahi, Mama ta kalleta ta gyada kai tana cewa
"Iska na wahal dame kayan kara, to ke yanzu Kishi za'ace yana damunki ko kuwa baqin cikin kinji matarsa ta haihu lahanin da kika masa beyi tasiri ba se kije ki dauki ruwan sanyi kisha kiyi maimaita Hasbunallahu ko kya samu ciwon naki ya lafa" taja tsaki ta shige daki hali irin na Umaimah dai Allah ya canzawa masu shi. Ita kuwa daki ta cige ta kife akan Gado ta shiga kukan da bata san dalilinsa ba, Khalil dai rayuwarsa yake yi ya manta da ita da alama ita ce take ta dakon soyayyarsa da yaqinin wata rana ze iya sake dubanta amma daga alamun da take gani bata da wannan sauran damar.

GIDAN KHALIL


*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 84

GIDAN KHALIL
Rayuwa taci gaba da tafiyarwa da ma'auratan cikin aminci da yarda da Juna, cikin Humaira ya shiga watan haihuwa, da kyar da lallami Khalil ya janye qudurinsa na canza mata Asibiti tunda ya tabbatar da cewar a nan Asibitin da suke zuwa Noor tsohon saurayinta yake aiki. Tun ganinsu dashi na farko hankalinsa ya kasa kwanaciya, haka kawai gabansa ya ringa faduwa idan ya tuna irin farin cikin daya gani akan fuskarta a dalilin ganin Noor din daya tabbatar shita fara so kafin shi. Da sati ya zagayo zata koma Asibiti tare sukaje dukda tarin ayyukan da suke kansa haka ya share ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login